Skip to content
Part 26 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Tana sauraren likitocin da suka tabbatarwa Alhajin babu abin da ya sameta da ya wuce jiri, ba mamaki tana ɗauke da yunwa. Hajiya Mami dai tana zaune ta zubawa Husna idanu. Alhajin ya jawo kujera yana dubanta sosai,

“Ke daga ina kike? Kuma ina zaki je?”

Husna ta dinga zazzare idanu tana dubansu, sai can ta buɗa baki ta ce,

“Nima bansan inda zanje ba. Nasan dai a hannun kishiyar Innata nake. Na mance sunan garinmu.”

Jikin Hajiya Mimi ya yi sanyi, don ba zata taɓa mance izayar kishiyar uwa ba. Zuhura ma ta ji tausayinta matuƙa, banda Zakiyya da take ta yamutsa fuska.

Alhaji ya ce duk su koma gida kuma su tafi da Husna idan yaso sai su bar fitan sai yamma. Ransu bai so ba, suka kama hanyan barin asibitin. Zuhura tana riƙe da hannun Husna, duk tafiya ɗaya biyu tana yi mata sannu.

Yunusa ya saki ajiyar zuciya, ya ci gaba da magana a waya,

“Yanzu naga sun fito daga asibitin zan ci gaba da bin su.”

M.Y ya saki ajiyar zuciya yana jin tarin damuwa yana ƙara rufe shi. Yunusa bai daina bin su ba, har sai da ya tabbatar sun shiga gidan Alhaji Mu’azu sannan ya juya.

 Ranar ko da barci yake ɓarawo ya kasa ɗauke M.Y tunanin Gwaggo da Husna ya hana shi sakat. Yana da buƙatar kwanciya a kafaɗar Gwaggo ya sanar da ita irin kewarta da ya yi. Duk juyin da zai yi sai ya ji kamar zai ga Husna a gefensa tana yi masa Karatu don ya sami barci. Da gaske ya yi kewarta. Dole doguwar rigarta ya ɗauka ya rungume tsam a jikinsa.

Gaba ɗaya dajin ya yi masa girma na ban mamaki. Bai taɓa sanin haka dajin yake ba, sai yau da ya rasa mai ɗebe masa kewa.

Husna kuwa duk da ta sami kulawa yadda ya kamata, amma hankalinta da tunaninta yana gun M.Y ko ba komai yakan yi mata rumfa da kirjinsa har ta sami barci. Juye-juye kawai take yi. Ji take da zata sami dama da ta shiga ɗakin tun yanzu ta ɗauko zoben. Irin kallon da Alhaji Mu’azu yake yi mata yafi komai ɗaga mata hankali. Kallo ne mai nuni da abubuwa kala-kala.

*****

Kwananta biyu a gidan, babu wani sakewa a tsakaninta da mutan gidan. Shi kuma Alhaji Mu’azu tafiya ta kama shi na gaggawa. Sai a lokacin ta sami daman sanin tsarin gidan, da kuma yadda za ayi ta shiga ɗakinsa.

Ranar da zai dawo ya kama ranar asabar don haka yana isowa kai tsaye suka shirya har Husna domin zuwa wurin shaƙatawa wanda yake mallakinsa ne.

Wurin ya yi matuƙar ƙawatar da zuciyar Husna har ta tsinci kanta da zagayawa tana kallon wurare. Ji ta yi anfizgota zata yi ihu yasa hannu ya toshe mata baki. Gaba ɗaya ta zube a jikinsa. Rungume shi tayi tsam a jikinta idanunta a rintse domin ko ba a gaya mata ba ta fahimci mijinta ne.

Murmushi ya suɓuce masa ya ɗagota gaba ɗaya suka zurawa juna idanu. Yasa hannu ya ɗauke ƙwallan da ke idanunta ya sake jawota can lungu ya haɗe bakinsu wuri guda na tsawon wani lokaci, sannan ya janye kansa yana son su sake haɗa idanu amma ta gagara hakan.

“Nayi kewarki Husy.”

Cikin sanyinta ta ce,

“Nima haka.”

Tana son ta ce ya rame ta rasa ta yadda zata gaya masa. Farin ciki ya mamaye ko ina a cikin  zuciyarta. Ya fahimci hakanne ta yadda ta kasa daina dariya.

“Na rame ko? Ni kaɗai nake kwana a dajin nan, ji nake kamar ni kaɗai ne ba aso, kamar bani da gata.”

Da sauri ta fara girgiza kai kamar zata yi kuka,

“Kana da gata. Insha Allah Komai ya kusan zuwa ƙarshe mu ci-gaba da addu’a.”

A lokacin ya ji ana ƙwala mata kira. Sai da ya sake rungumeta ya bata fake kiss a goshi sannan ya ce ta tafi. Jiki babu ƙwari ta kama hanya tana jin wani irin ƙunci a ranta.

Zuhura ta ce,

“Ina kika je kinsa hankalinmu ya tashi.”

Da hannu ta nuna mata baya ta ce,

“Wurin ne ya burgeni shi ne na je ina kallo.”

Alhaji Mu’azu yana ganinta ya saki ajiyar zuciya. A tunaninsa ko ta ɓace ne.

A gajiye suka dawo gida, idanunsa akan ƙirjin Husna. Hakan yasa Hajiya Mimi ta kafe shi da ido cike da tuhuma. Dole ya wayance ya daina kallonta.

Zakiyya ta dubeta a wulakance ta ce mata,

“Yauwa ke zo nan. Duk ranar da na sake ganin ƙafafunki a ƙofar ɗakina wai da sunan kin zo gaisheni sai na yi mugun ɓata maki rai.”

Jiki babu ƙwari ta wuce. A zuciyarta ta ce,

‘Da kin kwantar da hankalinki nima ba son zuwan nake yi ba.’

*****

Sha biyun dare ya buga, a lokacin ne Alhaji Mu’azu ya saɗaɗo ya shigo ɗakin Husna. Idanunta biyu, tana kwance sai juye-juye take yi ta kasa barci. Ganinsa ya firgitata ta tashi zaune jikinta babu inda baya rawa.

“Ke ki kwantar da hankalinki arziƙi ke kiranki. Zaki bani haɗin kai inmayar da ke ‘yar Gwal?”

Ta ɗan yi shiru ba tare da ta iya cewa komai ba.

“Ki bani haɗin kai, kinga a ƙungiyarmu ance ke ba alkhairi ba ce a cikin gidana inkoreki, amma na nuna masu ba zai yiwu ba zaki bani haɗin kai?”

Bakinta yana rawa ta ce,

“Ka bani kwana biyu zan yi tunani.”

Yaji daɗin furucinta hakan yasa ya fahimci ba zai sha wahala ba, kamar yadda yake tunani a farko, musamman yadda take nacewa hijabi. Juyawa ya yi ya fice. A hanya suka haɗe da Hajiya Mimi ta kalle Shi cike da zargi ta ce,

“Alhaji daga ina kake a daren nan?”

Ya dubeta sosai ya ja tsaki,

“Walh Mimi baki da yarda. Gara tun wuri ki cire haukan abin da ke cikin zuciyarki domin shirme kawai take gaya maki.”

Ya wuce yana godewa Allah da bata ga shigarsa ɗakin Husna ba. Har ya ɓace mata bata daina nazarinsa ba, kai tsaye ta doshi ɗakin Husna. A zaune ta sameta tana karatun Alkur’ani hakan yasa ta ji wani irin tarin natsuwa ya ziyarceta. Ko ba komai ta yaba da natsuwar yarinyar.

Tunda Alhaji Mu’azu ya fahimci akwai sa’ido mai ƙarfi a tsakaninsa da Hajiya Mimi sai ya fita harkar Husna yana son sai ta gama zargin da take yi sannan ya aiwatar da nufinsa.

A yau ɗin ma asibiti suka raka Hajiya Mimi ita da Zuhura. Bayan sun shiga ganin likitan ne Husna ta zauna shiru.

A jikinta take jin akwai abin da take so a kusa da ita, don tana son ganinsa tana son sanar da shi yadda suka yi da Alhaji Mu’azu. Tana son sanar da shi shiga ɗakin Alhaji Mu’azu sai wanda ya zo da shiri.

Waiwayo wa ta yi gefenta ta hango wani zaune yana sanye da rigar sanyi mai gashin mage ya rufe fuskars da face mask sannan ya ɗora hulan rigar sanyin akansa. Ta kasa janye idanunta akansa har zuwa lokacin da ya ɗago suka haɗa idanu.

Jikinsa bai ɓoyu a fuskarta ba bare akai ga ƙwayar idanunsa. Duk suka yi murmushi sannan ya tashi ya kama wata hanya ta bi bayansa.

“Uncle…”

Ya juyo ya cire facemask ɗin yana murmushi.

“Duk wani motsinki ina bibiye da shi Husna. Gaya min ya ake ciki? Na gaji da zaman nan, ina son ganin mahaifina ina son ganin Gwaggo nasan duk halin da take ciki a yanzu tana da buƙatana.”

“Ya ce min wai… Wai…”

Sai kuma ta yi shiru. Maganar ta yi mata nauyi. Kafaɗunta ya kama ya girgiza,

“Tell me! Ya ce maki yana son yayi lalata da ke ko?”

Ta gyaɗa kanta alamun hakane.

Ya ce,

“Masha Allah.”

Ta ɗago da sauri tana dubansa. Ya ɗaga mata gira,

“Yes! Mun sami dama. Ki ce ba zaki yarda da shi ba, sai a cikin ɗakinsa. Daga nan zaki sami daman ɗauko zoben insha Allahu. Yau ɗinnan zuwa gobe zansa ido sosai akanki.”

Ya gaya mata duk shirin da za su yi, sannan suka rabu kamar zata yi kuka. Ta sani abin da take shirin yi riski ne ga rayuwarta ko ta rayu ko kuma shikenan.

Bayan sun koma gida ta yi ta jiran Alhaji Mu’azu shiru. Har sai da akayi kwanaki biyu sannan ya shigo,

“Yanzu kin amince? Nasawa duk mutanen gidan nan maganin barci ta yadda har muyi komai mu gama basu sani ba.”

Mamakin hatsabibancin Alhaji Mu’azu ya bata mamaki. Yanzu akan cikar burinsa zai sa wa iyalansa maganin barci? Ta gyaɗa kai,

“Na amince. Amma ɗakinka zamu je.”

Ya yi shiru kamar mai nazari. Sai kuma ya ce babu damuwa ta zo su je. Babu musu ta tashi ya bi bayansa suka tafi. Yana shiga ta zauna tana ƙarewa ko ina na ɗakin kallo, a lokaci guda kuma tana sakar masa murmushi.

Ya kamo hannunta, ta rintse idanu tana jin damuwa aranta tana jin da aurenta ta bar wani ƙato da ba muharraminta ba ya taɓa hannunta. Da ƙyar ta ƙaƙalo murmushi ta ce masa tana son shiga banɗaki.

Ita kanta dabara ta ɓace mata, bata san ta yadda zatayi har ta sami nasara ba. Tunani kala dubu babu irin wanda bata yi ba.

Cikin rawar jiki ya ce mata,

“Shiga ki fito ina son infara watsa ruwa tukun. Yadda komai zai yi mana daɗi.”

A lokacin sai ta ji kamar warwarewar matsalarta ce ta zo. Ta ce

“A’a ka shiga ka fito zan ɗan kwanta.”

Bai tsaya dogon gardama ba ya faɗa banɗakin. A lokacin ta yi tozali da key ɗin bayin ancusa shi ta waje. Ta yi mamaki domin a ganinta key a ciki ake sakawa. Abin da bata sani ba, idan dai fita saboda tsabar rashin yarda da kuma yadda yake ajiye kayayyakin tsubbunsa a ciki rufewa yake yi watarana ma baya rufe ƙofar ɗakin amma banɗaki kam dole sai ya rufe.

Sai da ta tabbatar ya fara watsa ruwa sannan ta murɗa key ɗin a hankali ta rufe shi, sannan ta dawo ta shiga hargitsa ɗakin. Sai da ta gama hargitsa ko ina sannan Allah ya bata sa’a taga zobuna guda biyu. A ciki ta rasa wannene don haka ta kwashi dukka biyun ta ɗaure su a ɗankwalinta ta fice da gudun gaske.

Sai da ta tako tsakar gidan sannan ta ji gabanta ya faɗi. Ta tuna ko ‘ya’yan gidan basu isa su fita a ƙasa ba bare kuma ita da take matsayin baƙuwa. Yanzu fita cikin gidan ne wani sabon aiki. Tana da buƙatar komawa ta kashe na’uran gidan tukun kafin tasan abin yi. Da gudu ta koma sama ta shiga office ɗinsa ta kashe komai kamar yadda M.Y ya gaya mata, sannan ta fito ta tsaya cak tana roƙon Allah ya aiko mata da mafita.

A lokacin ne kuma ta ji alamun fitowar mutum cikin hanzari wanda babu ko tantama Alhaji ne ya samu fitowa daga banɗaki wanda ita kanta ba zata ce ga yadda akayi har ya iya fitowa daga rufe shin da ta yi ba.

Tohhh masu karatu… Husna ta ɗebo ruwan dafa kanta, a cikin tsakiyan dare… Ku ci gaba da biyoni domin jin yadda zata kaya.

‘Yar mutan Borno.

Babi Na Ashirin Da Bakwai 

Takun tafiyarsa da ihun kiran maigadi ya jawo hankulan wasu ma’aikatan da ke gidan.

“Ka datse ƙofar gidan nan tun kafin yarinyar nan ta fita.”

Abin da kawai yake faɗa kenan. Hakan yasa Maigadi ƙarasowa yana cewa,

“Alhaji ai gidan nan babu ta hanyar da wata halitta zata iya ficewa ba tare da izininka ba. Gida a rufe yake.”

Alhajin ya yi shiru yana nazarin wauta irin nasa. Ta yaya yarinya ƙarama zata iya yi masa wayo? Wato dai turota akayi. A can wani ɓangare na zuciyarsa kuwa zallar kwaɗayinta ne ke yawo a zuciyarsa. Har yana jin muddin ya kamota babu ko shakka bayan hukunci da zai yi mata abu na gaba aurenta zai yi.

Jikinsa da zuciyarsa sun tabbatar masa da tana cikin gidan nan, don haka ya ce duk su sa idanu yana zuwa. Da sauri ya nufi Office ɗinsa domin ya duba kwamfuta ɗinsa ta nan ne kaɗai zai gane inda take. Abin takaici sai ya sami ankashe komai. Hankalinsa ya sake tashi, ya fito yana zazzare idanu,

“Ku duba ko ina a cikin gidan nan ku zaƙulo min yarinyar nan, anturota ne kuma ta ci nasarar ɗaukan abin da ta zo ɗauka.”

Kafin ka ce me? Kowa ya haukace da neman Husna. Duban duniyar nan sun yi basu ganta ba, hakan ya ƙara tashin hankalinsa. Muddin yarinyar nan ta fita da zoben nan ya gama yawo.

Da sauri ya koma ɗakinsa yana duddubawa, wata ajiyar zuciya ta kwace masa, ganin ba asalin zoben ta ɗauka ba. A lokaci guda ya sheƙe da mahaukaciyar dariya. Ya dinga yi wa kansa kirari.

Yanzu abu ɗaya ya rage masa ya kama yarinyar nan ya koya mata hankali, ya kamata kuma ta gane ba irinsa ake yi wa iskanci ba.

Ya zama dole ya je Gombe gobe domin ya kashe mahaifin M.Y don ya gane shi kaɗai zai iya shiga gonarsa. Sai a lokacin ya tuna lokacin da Alhaji Saleh suka zo gidansa, Husna taƙi amincewa su haɗa idanu. Dole akwai lauje cikin naɗi.

Fitowa ya sake yi waje ya kafa kujera yana ta surutansa shi kaɗai.

Sai wajajen asuba mutanen gidan suka farka daga irin dogon barcin da suka sha. Anan yake gaya masu Husna ta sace masa zabba ta gudu. Sai kowa ya shiga kallon kallo. Zuhura ta dubi mahaifinta cike da mamaki ta ce,

“Daddy zabba kuma? Ai gani nayi idan satan zata yi kuɗi zata ɗiba, ko kuma ni ta sace min gwala-gwalai na. Me za ta yi da zoben maza?”

Hajiya Mimi ta zuba masa idanu tana jin a zuciyarta bata yarda ba.

Anan kuma sai ya fara kame-kame ya ce,

“Kuɗi nake son ince. Kuɗaɗena ta sace ta gudu.”

“Kai kuma lokacin kana ina har ta shiga ɗakinka ta saci kuɗi? Bana jin Husna ta taɓa bin hanyar ɗakinka.”

Idanu a warwaje yake duban matarsa,

“Ban sani ba nima. Zaki barni inji da abin da ke damuna ko zaki tsaya tsareni da tambayoyi?”

“Uhum! Alhaji manya. Kai dai kace ka yi abin kunya Husna kuma ta gudu saboda ba zata iya ba. Allah ya kyauta. Yarinya ta yi kyan kai tunda ta zaɓi mutuncinta fiye da zama cikin daula.”

Baki buɗe yake kallon matarsa da ta gama watsa masa magana ta juya abinta.

Bai tsaya wata wata ba ya koma ɗaki ya shirya ya fito da sauri ya shiga mota. Direbansa yaja suka kama hanyar Gombe. Tafiya suke yi yana ganin kamar ba za akai ba.

M.Y yana biye da shi a wata mota ta abokinsa Mukhtar. Dukkansu gudu suke yi akan shinfiɗaɗɗan titin kamar za su tashi sama. Ya ƙudurta aransa yau ko za a kashe shi sai ya fitar da mahaifinsa, domin kuwa yana sane da komai ya lalace. Husna tana nan a cikin gidan babu halin fitowa saboda maigadin.

Da isowarsu yaja ya tsaya yana nazarin ta yadda shima zai iya shiga gidan. Sun shiga basu daɗe ba yaga sun ƙara fitowa, don haka ya rufa masu baya.

Wani katafaren wurin shaƙatawa suka shiga hakan yasa shima ya afka ba tare da dogon tunani ba.

Bayan direban ya yi parking ne Alhaji Mu’azu ya fito hakan yasa M.Y ya rufe fuskarsa ya fito ya tsaya ta bayan motar yana nazarin abin da ya kamata ya yi.

Jikinsa da zuciyarsa suka bashi akwai wani abu da ke shirin faruwa. Yana jin wani abu a zuciyarsa, hakan yasa ya dinga waige-waige har zuwa lokacin da idanunsa suka faɗa kan boot ɗin motar Alhaji Mu’azu. Gani ya yi ana so a buɗe amma hakan ya gagara. Da sauri ya ƙarasa ya buɗe. Ya zaro idanu cikin firgita,

“Husna!”

Ya kira sunanta. Ita kuwa ƙoƙari take ta fito, hakan yasa ya kamo hannunta. Tana fitowa ya ji muryar Alhaji Mu’azu hakan yasa duk suka laɓe,

“Kana ji ko? Zoben da yarinyar ta ɗauka ba asalin zoben bane, shiyasa ban damu ba. Zuwa anjima da daddare zamu tafi da mahaifin yaron a kashe shi kawai, tun kafin yaron nan ya jawo mana aiki.”

A hargitse ya kalleta, itama shi ta kalla jikinta asanyaye. Cikin dabara ya janyeta daga wurin suka shiga motarsa. Duban juna suka yi ta fashe da kuka ta faɗa jikinsa tana jin zuciyarta tana tafasa. Shikenan aikin banza kenan ta yi? Duk wahalar da tasha ya tashi a banza?

“Ki daina kukan hakannan.”

Abin da ya iya furta mata kenan zuciyarsa tana zafi.

“Uncle ya zamu yi da Abba? Kana ji fa wai kashe shi za su yi. Mu yi sauri mu nemo mafita don Allah.”

Bai ce mata komai ba, har sai da ya lallashi kansa. Sannan ya ɗago kanta daga jikinsa ya ce,

“Kin tabbatar bai yi maki Komai ba?”

Ɗaga kan kawai ta yi. Ta ciro ɗankwalinta ta warware ta bashi zoben guda biyu.

Kallon zobunan yake yi, duk iri ɗaya ne. Yana ta jujjuya zoben har Allah ya kai idanunsa kan wani ɗan jan ɗigo wanda mahaifinsa ya yi masa kwatance da shi.

“Husna wannan zoben shi ne zoben da Abba ya yi min bayani akai.”

Zabura ta yi, tana dubansa.

“Tabbas zoben nan shi ne. Yanzu zo mu je mu sami masauki ki ci abinci ki kintsa. Da daddare zamu ƙona wannan abun kafin su kai ga cimma burinsu.”

Husna dai ta amince masa ne ba don ta yarda ba. Babu yadda za ayi ace Alhaji Mu’azu bai san wani zoben bane na gaske.

*****

Bayan sun natsa sun ci abinci ta yi Sallah ta zauna shiru tare da tagumi. Idanu suka haɗa ya yi mata alamun ta zo kusa da shi. Jiki babu ƙwari ta ƙaraso ta kwantar da kanta a kafaɗarsa idanunta cike da ƙwalla.

“Ki daina damuwa kinji? Insha Allah yau komai zai zo ƙarshe ko da zoben nan ko babu zoben.”

Ita dai binsa kawai take yi da ido.

Kusa da gidan ya yi parking motar suka nufi wani wuri a bayan gidan da nufin ƙona zoben.

A lokacin kuma Alhaji Mu’azu yana nan a haukace jin abin da shugabansu ya ce.

Lallai zoben nan da Husna ta ɗauka shi ne asalin zoben kuma komai yana iya faruwa da zarar sun aiwatar da abin da suke son aiwatarwa, don haka dole ya koma Kaduna ya nemo yarinyar nan da ke cikin gidansa a ɓoye.

Bai gama haukacewa ba, sai da aka tabbatar da shi da kansa ya fito da ita daga gidansa.

A cikin binciken da suke yi ne, suka ga M.Y da Husna suna ƙoƙarin ƙona zoben. A gigice Alhaji Mu’azu ya bada umarnin aje a kamo su.

Su M.Y kuwa suna ta ƙoƙarin ƙonawa amma yaƙi kamawa. Dukkansu sai suka fara mamakin tayaya zobe zai ƙone? Husna ta fara hango mutanan da suka tunkaro su don haka ta gigice, ta fara karanto addu’o’i bakinta yana rawa. A lokacin kuma ya sami sa’a yana kunnawa ya kama kamar kyandir.

Wani irin guguwa ya rufe wurin zuwa wani lokaci komai ya lafa. Babu mutanan nan babu dalilinsu, da sauri ya kamo hannun Husna suka nufi gidan da gudun gaske. Duk inda suka wuce babu kowa kamar anshafe su.

Mahaifinsa ya hango ya zama tsoho yana tafiya da sanda a hannu. Da yake jini ne tuni ya gane shi ya ƙaraso gabansa suna duban juna cike da tausayawa. M.Y ya rungume shi ba tare da ya damu da tarin dauɗan da ke jikinsa ba, ko kuma warin da yake yi.

Wani hawayen farin ciki ya sakko masa yana jin duk duniya babu wanda ya kai shi samun natsuwa.

Abba ya yi magana kamar ɗan koyo,

“Mu yi sauri mu bar nan.”

Suka juya da nufin barin wurin, amma tafiyar Abba zai iya kawo masu cikas, domin tafiya yake yi kaman wanda akayi masa kaciya. M.Y ya durƙusa Abba ya hau bayansa Husna ta karɓi sandar suka fito da sauri. Ita kanta Husna tunda ta ga Abba take aikin kuka. Tana kallon yadda mutane suke ta guje-guje. Tausayinsu ya karyar mata da zuciya.

A bayan mota ya sa Abba Husna ta shiga gaba M.Y ya bar wurin aguje.

Kai tsaye babban asibiti ya nufa da Abba cikin gaggawa aka wuce da shi domin bashi taimakon gaggawa.

Bayan gwaje-gwaje angano ba shi da jini a jikinsa, don haka M.Y ya ce a ɗibi nasa kasancewar O-Nagetive gare shi. Husna tana zaune a ɗakin da aka ba M.Y domin ya huta ta zuba masa idanu. Shima ita yake kallo cike da tunani kala-kala.

“Husna na gode.”

Ya furta a hankali. Ta kasa ce masa komai sai hawaye da ke bin kuncinta. Baya son ganin hawayenta ko kaɗan, don haka ya rufe idanunsa kawai.

*****

Wasa-wasa sai da Abba ya share wata ɗaya cur ana bashi kulawa, sannan ya murmure har ma suna fita da shi suna koya masa magana. Abin da ke basu mamaki bai taɓa tambayar kowa ba, bai taɓa cewa ina Gwaggo ba. Hakan yasa zuciya mai saƙe-saƙe zuciyarsa take gaya masa yanzu haka har ya mance da Gwaggo ita kuwa tana can tana dakon soyayyarsa.

A ranar da za a sallame su ne hankalinsa ya tashi domin bai san inda ya kamata ya kai mahaifinsa ba. Hakan yasa ya kira Mukhtar ya ce ya bashi aron gidansa da babu Kowa zai ɗan zauna zuwa wani lokaci.

Abba ya dawo fes da shi, sai dai ramar da ya yi ne har yanzu bai dawo daidai ba.

Har suka iso Kaduna Abba bai ce uffan ba, sai bayan da suka sauka suka zauna a falo sannan ya dubi M.Y idanunsa cike da hawaye,

“Na gode Mu’azzam. Haƙiƙa haihuwa ta yi min rana. Wannan matarka ce a kusa da kai? Ina Hafsatu? Ina mahaifiyarka? Mace mai haƙuri da tawakkali. Ban taɓa kwana na tashi ban tunata ba. Don Allah ka sadani da Hafsatu.”

Ganin hawayen mahaifinsa yasa ya kamo hannayensa yana jin wani irin ƙaunar mahaifin yana ratsa shi. Ya kasa yi masa magana, ya kasa yi masa bayani kawai sai ya kwantar da kansa a jikin mahaifin yana jin wani irin rauni.

Abban ya fahimci ɗansa yana cikin damuwa, don haka ya ɗora hannayensa akansa yana shafa kan a hankali,

“Ka sanyani farin ciki mara yankewa tun kana ƙarami. Insha Allah baƙin ciki ba zai taɓa tabbata a zuciyarka ba. Gaya min yanzu ‘ya’yanka nawa?”

Nan ma shiru babu amsa. Husna ta dube shi asanyaye ta gaya masa mahaifinta da kuma riƙonta Gwaggo ke yi. Mamaki ya kasa barinsa, yasa hannu ya yafito ta, ta matso kusa da shi tasa kanta a kafaɗarsa. Hawaye kawai Abba ke yi yana cewa,

“Allah ya yi maki albarka Husna. Kinga yadda rayuwa ta yi da ni ko? Na gode maki na gode maki. Husna tun bayan fitowana kullum ke kike yi min addu’a. Wannan tarbiyyar Hafsatu ce. Sanar da ni inda zanga Hafsatu don Allah ki sadani da Hafsatu.”

Dukkansu jikinsu ya yi sanyi. Don haka ne duk suka yi alƙawarin gobe za su haɗa shi da Gwaggo.

Suna nan zaune har aka kira Sallar Magrib, M.Y ya kama hannun mahaifinsa da nufin ya raka shi banɗaki. Ya dubi  M.Y yana murmushi,

“Ka manta babu abin da ba zan iya ba? Mu’azzam duk iyayen da suka sami jajirtaccen ɗa kamarka dole su gode Allah. Allah ya yi maku albarka.”

Ya juya ya shige. Duk suka bi shi da kallo. M.Y ya wuce shima ya yi alwalar suka nufi masallacin jikin gidan suka yi Sallah.

Har dare sosai suna ɗakin Abba, Husna ta haɗa mashi fruits salad Shi kuma M.Y yana goga masa man zafi a ƙafafun.

Suna nan zaune har barci ya kwashe shi, gaba ɗaya suka yi ajiyar zuciya. Yana barci yana ɗan magana kaɗan kaɗan, a ciki suka fahimci sunan Gwaggo yake kira. Suka sake duban juna sannan suka fice zuwa nasu ɗakin.

Suna shiga ya jawota jikinsa ya rungume tsam yana shinshinarta,

“Kinji Abba yadda yake ƙaunar matarsa ko? Insha Allah haka zamu tsufa ba tare da mun ji mun gundura da junanmu ba.”

Duk suka yi shiru. Shi M.Y ya yi alƙawarin ba zai yi wa Husna komai ba har sai Gwaggo ta yafe masa. Da haka suka hau gadon ya rufe su da bargo ɗaya.

Babu abin da kake ji sai bugun zuciyoyinsu.

Juye-juye kawai suke yi babu wanda ya iya yin barci. A hankali ya yi magana,

“Husna gabana yana faɗiwa bansan me ke shirin faruwa ba.”

Husna ta jinjina kai,

“Insha Allah Gwaggo zata sauraremu.”

Ya jinjina kai, amma kowannensu ya rasa dalilin da yasa yake jin faɗiwar gaba da zarar ya tuna haɗuwarsa da Gwaggo.

Duk suka juyo suna fuskantar juna shiru. Ya jawota gaba ɗaya ta yi matashin kai da ƙirjinsa. Yasa hannu yana shafa kanta zuwa zara-zaran gashin girarta. A hankali take lumshe idanun tana jin wani abu yana yawo a dukkan sassan jikinta. Hannunsa ta riƙe cikin sanyin jiki. Kafin wani lokaci barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita. Ya zura mata idanu kawai yana ji a ransa ba zai ƙara samun mace kamar Husna ba. Yana fatan ko mutuwa ce idan ta tashi raba su ta fara ɗauke shi ne kafin ita. Kiss ya manna mata a goshi ya jawo masu bargo har saman kansu bayan ya tofe su da addu’a.

Washegari da wuri suka shirya suka ajiyewa Abba duk abin da zai buƙata idan ya tashi, sannan suka nufi gidan Dakta Salim gabansu yana tsananta faɗiwa.

A bakin gate suka yi wa Maigadi Sallama M.Y ya tambaye shi don Allah har yanzu wata tsohuwa tana nan gidan? Maigadin ya ce shi gaskiya a sanin da ya yi babu wata tsohuwa a cikin gidan.

A lokacin ne kuma Dakta Salim ya sawo kai, ganin su yasa ya tsaya yana dubansu cike da fara’a. Bayan sun gaisa ne suka shiga ciki. Gaban M.Y yana daɗa faɗiwa saboda irin kallon da yaga Salim da matarsa suna yi masa, kaman kallon tausayi.

“Dakta ina mahaifiyata?”

Dakta Salim ya dubi matarsa, itama shi take kallo. Idanunsa sun cicciko da hawaye, hakan yasa M.Y ya shiga cikin tashin hankali irin wanda  bai taɓa jinsa ba. Husna kuwa tuni cikinta ya fara ƙugi idanunta suka kawo ruwan hawaye, bata son ta ji me suke shirin furtawa…

Tohhh muje zuwa dai…

Taku ce mai ƙaunarku ‘yar mutan Borno.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mu’azzam 25Mu’azzam 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×