Skip to content
Part 5 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Husna tana kwance a cinyar Gwaggo tun bayan da ta farfaɗo bata sake cewa uffan ba. Gwaggo ta kai dubanta ga Mu’azzam cikin sanyi ta ce,

“Babban mutum ina ka sami bindiga?”

Mu’azzam ya yi ajiyar zuciya, tare da kauda idanunsa daga cikin na Gwaggo ya ce,

“A wajen aikinmu aka ba mu, saboda yanayin lalacewar ƙasar, ban kai ga amfani da ita ba ma, sai da zan taho ne na cusa a cikin kaya kasancewar tafiyar dare ce. Kinsan babban dalilin bamu domin mu kare kawunan mune da na iyalanmu.”

Gwaggo ta saki ajiyar zuciya, ko dama ba zarginsa ta yi ba, tasan dole yana da dalilinsa na ajiye bindiga. Yadda ta yarda da Mu’azzam bata jin ko mijinta ta yi masa irin wannan yardar.

Ganin ta gamsu yasa ya kai dubansa ga Husna, tana nan kwance idanunta a rufe, ya sake duban inda Salma take, gabaɗaya ta takure waje guda kamar mara gaskiya. Dukkansu haushinsu yake ji, irin haushin da ba zai iya cewa ga asalin dalili ba.

****

Yau ma kamar kullum, Husna tana ɓangaren M.Y tana gyarawa, ta ji muryar Amina tana waya. Har za ta wuce kunnuwanta suka zuƙo mata kalaman da dole ta ja ta tsaya.

“Yanzu kana ganin idan na dawo Kaduna zaka iya zuwa duk hotel ɗin da na gayyace ka?”

Bata ji irin amsar da wanda Amina take waya da shi ya bayar ba, sai ma sakin tsintsiyar da ta yi a ƙasa, ya faɗi cikin bokitin goge-goge, hakan yasa Amina ta firgita ta leƙo da sauri.

Ji ta yi kamar ta shaƙe Husna sai tsaki da ta ja ta juya abinta. Jiki babu kwari ta sunkuya ta ɗauki tsintsiyar ta kama hanyar waje.

Husna ta yi ringingine tana jin tarin damuwa yana addabar zuciyarta. A kwanakin da M.Y ya yi a cikin garin nan, shi da matansa ta gano munanan halayyar matan dukka su ukun, sai dai bata san dalilansu na aikatawa mijinsu haka ba.

Na farko ta gano Salima tana ɗaya daga cikin manyan matan da suke aikata maɗigo da ‘yan mata masu kwaɗayin abin duniya. Ta gano hakan ne a dalilin waya da ta ji tana yi sau babu adadi. Ita kuma Bilki Uwargida sata, da idanun Husna ta ganta ta sato kuɗi a ɗakin M.Y tana cusawa a cikin zani.

Sai kuma Amina da take zaton babu ruwanta ashe itama shaiɗaniyar kanta ce. Idan banda jaraba me za ta yi da namiji a waje? Dan zubar da mutunci ita ce ma take roƙonsa su haɗu a wurin sirri.

Wannan manyan sirrikan babu ko ɗaya da yake da daɗin ji. Fitar da sirrin nan daidai yake da mutuwan auren mata uku a rana ɗaya. Duk ace sanadinwa? Sanadin Husna?

Da sauri ta girgiza kanta tana cewa,

“Allah kada ka jarabceni da zama sanadin kashe auren wasu, kada ka bani ikon tona asirin da bani da hurumi a cikinsa.”

Mu’azzam da ke tsaye a bakin ƙofa ya ƙaraso cike da tsarguwa ya bugi ƙafafunta. A firgice ta tashi zaune tana zazzare idanu.

‘yar kujera ya jawo ya zauna yana fuskantarta cike da ɓacin rai,

“Kina ji ko? Ki koyi kauda kanki akan abinda bai shafeki ba. Kina ‘yar ƙaramarki da ke kin iya gulma da son haɗa fitina ko?”

Ya tsura mata idanu yana jin kamar ya shaƙeta. Ganin bata da niyyar bashi amsa yasa ya miƙe kawai ya kama hanyar fita. Har ya kai ƙofa ya waiwayo ya ce,

“Idan kika koyi rintse idanunki, akan abinda bai shafeki ba, zaki ci nasara a rayuwarki.”

Yasa kai ya fice, yana jin takaicin tsayawa yana yiwa yarinyar da idan haihuwa ce ma ya isa ya haifeta.

Har ya fice bata daina kallon ƙofar ba, tunani ne fal a cikin ranta na dalilin da zai sa ya dinga gaya mata maganar da ƙwaƙwalwarta ba zata iya ɗauka ba.

*****

“Gwaggo nan da kwanaki biyu zamu koma in sha Allahu.”

Gwaggo ta ci gaba da damun furarta ta ce,

“Sai kuma bayan shekara zamu sake haɗuwa, idan kuma ka samu na mutu shikenan.”

Ya yi murmushi ya ce,

“Ba zaki mutu ba insha Allahu sai na rigaki ma mutuwa.”

Gwaggo ta kauda maganar ta hanyar cewa,

“Zan sa a ɗaura maka aure da Salma nan da kwanaki biyun sai ka tafi da ita.”

Muryar Bilki suka ji tana magana cikin huci. Wanda a zahiri Salima ce Sarkin wayo ta zigota, dama haka take yi sai ta ziga su ta koma gefe ta yi kallo.

“Gwaggo me zai sa M.Y ya auri Salma? Gaskiya ba ayi mana adalci ba.”

M.Y ya zaro idanunsa yana kallon Bilki cike da mamaki. Ta yaya bai taɓa raina uwar wani ba, shi za a raina tasa uwar? A ɗan zafafe ya miƙe, yana dubanta,

“Ki bar nan wurin tun kafin in tattakaki.”

A yadda ta kalli ƙwayar idanunsa tasan zai iya aikata abinda ya faɗa don haka ta wuce da sauri. Gwaggo ta dube shi ta ce,

“Amma dai babban Mutum ba dukan matanka kake yi ba ko?”

Ya yi shiru yana jin zafi biyu, sai dai abinda Bilki ta yi, idan bai taka burki ba nan gaba za ta iya yin abinda yafi hakan ma. Ya miƙe a fusace zai koma ciki, Gwaggo ta kira shi. Babu yadda zai yi dole ya dawo ya zauna kawai,

“Ka ji abin da nace akan auren Salma?”

Ya gyaɗa kai,

“Na ji Gwaggo, amma abar maganar auren har sai na dawo nan da wata biyu. Ana iya saka rana goben.”

“Me yasa ba yanzun ba? Yaushe nake da tabbacin za ka dawo nan da wata biyun?”

Ya yi shiru, ta sauke ajiyar zuciya.

“Na matsa maka maka ko?”

Takowa ya yi har gabanta ya kama hannayenta ya zuba masu ido, daga bisani ya yi magana da ƙyar,

“Gwaggona, bani da farin ciki sama da ke… Bana jin ko dabba kika kawo min a matsayin mutum, zan yi tunanin dabba ne. Ban taɓa yi maki musu ba, bana fatan infara yi a lokacin da ya kamata infaranta maki. Fatana ki ci gaba da sa min albarka.”

Gwaggo ta kafe shi da idanu, tana jin ruwan hawaye suna tsiyaya daga idanunta. Idan haka kowacce uwa take ji a zuciyarta akan ɗanta, lallai ba ƙaramin so iyaye suke yi wa ‘ya’yansu ba. Idan har haka kowacce uwa take yin sa’ar haihuwa, lallai iyaye sun zama ‘yan gata.

Muje zuwa

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.1 / 5. Rating: 7

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mu’azzam 4Mu’azzam 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×