Skip to content

Ni Ustaz | Fasaha Haimaniyya 1

5
(1)

<< Previous

Ni Ustazu, Ni Ustazu, Ni Ustazu, Ni Ustaz

*****

Da sunan Rabbana Allah

Nake waƙe ni Ustaz

Da yai mini baiwa ba illa

Ga shi a yau na zama Ustaz

Kai min sutura da ba illa

Kowa na ce mini ya Ustaz

Amincinka da tsirarka

Sun tabbata gun manzonKa

Salatinka da yardarka

Su tabbata gu na manzonKa

Ahlul baiti da sahabbansa

Da duk masu son ɗan Ustaz.

*****

Na dage kan neman ilimi

Don shi ne aikin Ustaz

Tare da yaɗa shi ilimi

Don haka ne halin Ustaz

Ni burina a ilmantu

A bar gaba a gaban Ustaz

Fatana ni a zam gyara

A cikin al’ummar Ustaz

Sai dai an gaza fahimta ta

Ana zargina ni Ustaz

A da jama’ar Ka ya Allah

Sun san darajar waye Ustaz

*****

Amma jama’ar yau ya Allah

Sun manta darajar waye Ustaz

Izgilanci da ninanci

Ake mini yau ni Ustaz

Kallon raini da ɓatanci

Ina ko shan su ni Ustaz

Kana so ne ka ga ƙasƙanci?

Ka dubi abin da ake wa Ustaz

Wurin kwanan da bashi da kyau

Shi ne za a ba Ustaz

To ya jama’a ga tambaya

Zan yi ta akan ɗan Ustaz

Ustazu fa wai shi ƙarfe ne?

Ko ice ne shi Ustaz

Shin Ustazu bawa ne?

Ko ɗan aiki ne Ustaz?

Tabbas an shiga haƙƙina

Ina kuka ni Ustaz

A da in yanka za’a yi ma

Sai ka ji an ce ‘ina Ustaz?’

Raɗin suna idan za ai

A nan ma za’a kira Ustaz

Sauka za’a yi ma a gida

Can ma za’a kira Ustaz

*****

Kai ko da ‘yar walima ce

Dole can ma za’a kira Ustaz

Ɗaurin aure idan za ai

Tabbas za’a kira Ustaz

Idan fatawa kake nema

Da sauri za ka nufo Ustaz

Limanci ko na’ibanci

Haka nan ma za a taɓo Ustaz

Karantarwar Islamiyya

Wannan aiki ne na ɗan Ustaz

Wankan gawa da rabon gado

Wannan ita ce ranar Ustaz

*****

Du’a’i ko ruƙiyya ce

A nan kowa ya san Ustaz

Domin gyara na tarbiyya

Da an je za a kira Ustaz

Sasancin duk wata hamayya

A nan ma za a kira Ustaz

Ko me za ai na alheri

Za’a kirani ni Ustaz

Sai dai an gaza yin khairi

A gurina ni ɗan Ustaz

Sai ma bina da yin sharri

Na boni yau fa ni Ustaz

*****

Isgili haɗa ma har raini

Sun ƙare akan Ustaz

Idan fa na gyara gemuna

Ka ji an ce ‘hmm sai Ustaz’

Idan ko na goge haƙorana

Ace mini ‘uhm sai Ustaz’

Ko kuma na ɗagale wandona

Ace ‘an gaida kai Ustaz’

Da na saka kaya na mutunci

Ace mini ‘wai shi nan Ustaz’

Da na saka ƙananun kaya

Ace mini ‘kai ku kalli Ustaz!’

*****

Idan aiki na je nema

Ace ai ba a ba Ustaz

Ko da ma ɗan fa lesson ne

Nawa ne ake ba ɗan Ustaz?

Ka yo duba Islamiyya

Nawa ne albashin Ustaz

Ko aure ma fa ba a ban

Ina zan sa kaina Ustaz?

Budurwa ko da na nema

Sam ita bata son Ustaz

Babanta da zarar an magana

Ya ce shi ba ya son Ustaz

*****

Mamanta da zarar kai magana

Ita ma Sam bata son Ustaz

Ita kanta da zarar ki magana

Ta ce wai bata son Ustaz

Da zarar ka tambaye ta

Me yasa ne bata son Ustaz

Sai ta ce wai ya faye mita

Kuma ga tsanani a gun Ustaz

Da kai laifi ko kaɗan ne

Akwai aya a gun Ustaz

Kuskure ko ƙanƙani ne

Hadisi na wurin Ustaz

*****

Kuma babu fita kuma ba yawo

Akwai tsanani auren Ustaz

Kuma gashi fa shi bai da naira

Kuma ba mota a wurin Ustaz

Ta manta da alheri

Wanda yake a wurin Ustaz

Ilimi fa ai alheri ne

A wurin kowa har Ustaz

Babu talauci bayan ilimi

Ya kamata ku bar ƙyamar Ustaz

Ya ku jama’a ga tambaya

Akan sha’ani na ɗan Ustaz

*****

Wai me ya sa a yau ɗin nan

Jama’a sun raina Ustazu?

Shin yin hakan ko daidai ne?

Ya jama’a ku bar Ustaz

Ya ɗan huta ya sarara

A bar zagina ni Ustaz

Wannan ta’adi da ake yi

Akan rayuwata ni Ustaz

Hakan da ya sa na yo nuni

Akan lamari na ɗan Ustaz

Ustazu fa ba Kare ne ba

Ku bar zunɗe na ɗan Ustaz

*****

Ustazu fa ba Jaki ne ba

Ku tausayawa ɗan Ustaz

Ustazu fa ai ba dutse ba

A kai aure gidan Ustaz

Ustazu fa ba ɓarawo ba

A sam aiki a ba Ustaz

Ustazu fa ba ɗa na fashi ba

A bar zargin ɗan Ustaz

Ustazu fa ba hauka ya yi ba

Ya kamata a bar ƙyamar Ustaz

Ustazu fa shi ba ya zamba

A bar raini ga ɗan Ustaz

*****

Da rubutun waƙa na yi nuni

Akan lamari na ɗan Ustaz

Na aiko saƙo gun Haiman

Mawaƙin zamanin Ustaz

Da fatan za ka yayyaɗa

A san lamari na ɗan Ustaz

Ko jama’a za su hankalta

Su bar ƙyamar ɗan Ustaz

Domin abin da ya ci tura

An da matsa wa ɗan Ustaz

Fatana ni dai a gyara

Don Allah a daina bin Ustaz

*****

Da zance mara amfani

A so Ustazu kamar kowa

Ya Allah ni na yo roƙo

Ka shirye mu mu bar gaba

Ka yafe mana laifukka

Mu sam nasara da ci gaba

Ka yo ni’ima gurin kowa

Mu bar cutar da ɗan Ustaz

Ni Ustazu

Ni Ustazu

Ni Ustazu

Ni Ustaz!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×