How to post on Bakandamiya Hikaya

Marubuta na iya dora littattafansu a Bakandamiya Hikaya ta hanyoyi kamar haka:

A. Ta hanyar aiko da littafin nasu don a dora wa masu karatu kyauta. Ga masu sha’awar yin hakan sai su. latsa nan don aikon da littafin nasu da kuma karin bayani game da dora littafi ko wani rubutu da zai amfani marubuta.

B. Marubuci na iya sayar da littafinsa shafi-shafi. Bayan ya aiko da shafin littafin an dora, za a iya generating password a ba shi, sannan shi kuma sai ya sayar da password din ga makarantansa. Sai wanda ke da password din ne kawai zai iya karanta littafin. Ku yi amfani da 19856 a matsayin password don gwajin wannan tsari a littafin Cikin Baure: Babi Na Biyu na Hadiza Isyaku. Sannan marubuta na iya latsa nan don karin bayani game da wannan tsari.

C. Har ila yau, marubuci na iya sayar da littafinsa shafi-shafi ta hanyar subscription na Bakandamiya Hikaya. Bayan an dora littafin, makaranta za su sayi password guda daya don karanta littafin har lokacin da aka gama dorawa. Marubuci da Bakandamiya Hikaya za su dauki matsaya tare akan farashin kowane password. Sannan kowane password aka saya, marubuci na da 75%, sannan Bakandamiya Hikaya tana da 25%. Marubuci zai iya neman kudinsa a duk lokacin da suka haura N5000.

D. Ta hanyar sayar da kammalallen littafi ga Bakandamiya Hikaya don itama ta dora wa makaranta ta hanyar subscription. Duk marubucin da ke son shiga wannan tsari, to ya aiko mana da wadannan abubuwa a hade cikin document guda.

  • Tsakure (summary) da ba zai wuce kalmomi 1000 ba game da littafin baki dayansa, kuma ya kunshi bayanin babban hadafi da marubuci ke son isarwa.
  • Akalla babi guda shida daga littafin: babi na 1 da na 2, babi guda 2 daga can tsakiya da kuma babin karshe guda biyu.

A latsa nan don aiko da one document dake kunshe da abubuwan da aka lissafa a sama.

Kowane tsari marubuci ya zabi ya yi amfani da shi, babban muhimmin abu shi ne, labarin da za a aiko ya zama ya cika ka’idojin rubutun labari kamar yadda ya kamata. A latsa nan don karanta muhimman ka’idojin rubutu da masana rubutun labari suka rubuta.

Masu neman karin bayani game da wannan tsare-tsare da ma sauran abubuwa na Bakandamiya Hikaya, sai su tuntube mu ta ‘contact page.

You cannot copy content of this page.