Skip to content
Part 2 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Na shiga uku!!!”

Fareeda ta faɗi haka idanunta a warwaje, hannu bibiyu ta ɗora akai wasu sabbin hawaye suka sake ɓalle mata. Babu abinda take hangowa a idanuwanta da ji a kunnuwanta sai masifar da Mukhtar zai sauke mata, ba shi da haƙuri ko kaɗan.

Balaƴaƴƴe ne na bugawa a jarida idan aka yi kuskuren shiga gonarsa, ba shi da uzuri ko misƙala zarrah. Har wani kirari yake yi wa kansa cewar
“Ni fa kamar kunama nake, a taɓa ni aji ɗau.”

Da waɗannan tunanin da suka yiwa zuciyarta ƙawanya yasa ta fara jan wani irin numfarfashi sama-sama, kamar mai cutar athma.

Hankalinta yayi gaba saboda tsananin ɗimuwa da fargaba haɗe da tashin hankali, duk hayaniya da surutan da mazauna falon suke yi sam hankalinta ba shi a kansu.

Tana cikin wannan mawuyacin halin jiniyar ƴan sanda ya karaɗe unguwar, kasancewar unguwar ta masu kuɗi ce babu hayaniya sosai sai suke jin jiniyar ƴan sandan yana tashi tamkar a cikin gidan.

“Alhamdulillahi, ga ƴan sanda nan sun iso.”
Uwar biki Hajiya Mariya ta faɗi haka da fuska kadaran kadahan, duk hasashen mutum bazai taɓa gane farin ciki take ciki ko akasinsa ba.

Nan take waɗanda suke zaune suna ganin abin kamar wasa duk suka miƙe tsaye, hankula ya ƙara tashi, nan take ƙaton falon ya ruɗe da surutai haɗe da cece-kuce.

Ƙarara ake jingina rashin kyautawa ga Hajiya Mariya da daga taron arziki ya koma na tsiya da rashin mutunci.

Wata Aminiyar Hajiyar da ta sha kwalliya cikin wani danƙareren leshi da gwala-gwalai wuya da hannu ne ta taka ta matsa kusa da Hajiyar, ta fara magana fuskarta na bayyana matsanancin ɓacin rai.
“Yanzu ke Hajiya Mariya kina ganin wannan mutunci ne? Da girmanmu da arzikinmu daga zuwa miki taron Allah ya sanya alkhairi sai ki haɗa mu da ƴansanda? wannan ai tozarci ne da wulaƙanci. Tunda haka ne ni na ɗauki lamunin kuɗin, ki ƙiyasta nawa ne a cikin jakarki in Allah ya yarda biya bazai gagar…”

“Dakata Hajiya Balaraba, dakata dan Allah. Kar ki nemi ki faɗa min baƙar magana, kin sanni sarai bakina ba ya haila.”
Uwar biki ta katse ta tana harhaɗe girar sama da ƙasa.

Ta miƙe tsaye ta riƙe ƙuƙuminta kamar wata ƙaramar yarinya, ta ƙanƙance idanunta suna kallon juna ta fara magana cikin fushi da fusata.
“Tun farko na faɗa ba kuɗin cikin jakar ne damuwata ba. A can cikin jakar akwai muhimman takardun His excellency, ko yanzu da wacce ta ɗauki jakar za ta fito min da takardun na rantse da girman Allah zan iya bar mata kuɗaɗen ciki duk yawansu.”

Da faɗin wannan magana sai aka fara kallon kallo a tsakanin mata, ko wacce a zaƙe take ta ga ta inda takardun cikin jaka zai ɓullo, wace jajurtacciyar ɓarauniya ce za ta iya fitowa tsakiyar cincirindon matannan ta kawo takardu tunda anyi alƙawarin bar mata kuɗaɗen cikin jakar?

“Ƴan’uwana mata don Allah don darajar fiyayyen halitta muji tsoron Allah, duk wacce ta san ta ɗauki jakarnan ta fito da shi. Don Allah, ta rufa mana asiri mu koma gidan mazajenmu lafiya.”
Malama Aliyah mai ruƙya ta faɗi maganganun fuskarta na bayyana matsanancin tashin hankali da damuwa.

Bayan maganar da tayi har aka kwashi daƙiƙu sittin babu wacce ta motsa, izuwa wannan lokacin kuma ƴan sanda sun shigo cikin gidan har sun adana motocinsu, mata a cikin ƴan sandan ne suka matsa ƙofar babban falon suka fara bubbuga ƙofar da ƙarfi.

“Ai shi kenan! Tunda duk haka kuke so bari in basu dama suyi aikinsu, mu tafi caji ofis ɗin kawai. Acan ko ma wacece ɓarauniyar za tayi bayani idan ta ji matsa.”

Tana gama faɗin haka bata saurari magiyar da aka fara yi mata ba ta nufi ƙofar fita daga cikin falon da niyyar buɗewa, a kulle ta ga ƙofar, kuma babu ɗan mabuɗi a jikin ƙofar.

Ɓangaren da ƴan’uwanta suke tsaye cirko-cirko hannuwa naɗe a ƙirji alamun tashin hankali ƙarara a fuskokinsu ta kalla. Da cusasshiyar murya ta ce
“Ina ɗan makullin ƙofar nan?”

Cikin sanyin jiki Aunty Kubura ta zura hannunta a rigar mama ta ciro makullin ta miƙa mata.

Yamutsa fuska tayi, a ƙyamace ta kalli makullin sannan ta kalli fuskar Kubura da take miƙa mata makullin.
“Wani irin iskanci da ƙazanta ne za ki wani cusa min key ɗin ƙofa a rigar nono? ki tabbatar bayan kwaranyewar wannan al’amarin kin wanke min makulli tsaf sannan ki mayar min da shi jikin ƙofa.”

“To Hajiya, kiyi haƙuri.”
Ta bada haƙurin cikin ƙanƙan da kai.

Ƙasa-ƙasa ta ja tsaki, ta harareta, sannan ta bata umarnin buɗe ƙofar.

Tana murza makulli ta buɗe tiƙa-tiƙan ƴan sanda mata su takwas suka shigo cikin falon fuskokinsu a ɗaure, sai zare-zaren idanu suke yi kamar za su ci babu. A hannayensu riƙe da ƙananun bindigu.

Cikin girmamawa suka kai gaisuwa ga Hajiya, ta amsa musu a gadarance.
“Ga su nan, dambu da taliya na juya sun ƙi fito min da jakata, idan aka kwashe su zuwa caji ofis ko ma wacece ɓarauniyar za tayi bayani.”

Duk da a cikin matan gurin akwai masu dakakkiyar zuciya ƴan rajin rigima ubanwa ta kashe irinsu Fatima, da yawansu jikinsu yayi sanyi. Zuwa wannan lokacin ba Fareeda ba ce kaɗai mai kuka da hannayenta ɗore akai, mata da yawa sun fara kokawa ne da ƙarfi suka zube a ƙasa suna roƙon Hajiya Mariya ta rufa musu asiri, daga masu cewa idan aka kaisu station aurensu zai samu matsala, sai masu cewa tunda suke a rayuwarsu basu taɓa zuwa ofishin ƴan sanda ba, tayi haƙuri kar su fara zuwa daga sha’aninta.

Hajiya Mariya kuwa ta shafawa idanunta toka tana tsaye tana karkaɗe jiki ta ce bata san kalmar haƙuri ba, za tayi haƙuri ne kawai idan ɓarauniya ta fito mata da jakarta.

Masu ɗan ƙarfin zuciya a cikinsu ne suka zaro wayoyinsu da nufin su kira makusantansu don sanar da abinda yake faruwa, amma ƴan sandan nan suka katse musu hanzari ta hanyar ƙwace wayoyin hannayensu. Cikin waɗanda aka karɓewa waya har da Hajiya Balaraba.

Haka nan suna ji suna gani aka tarkatasu a motocin ƴan sanda shiga ba biya fita da Allah ya isa a cuccushe wata kan wata a wulaƙance ba tare da banbance talaka da mai kuɗi ba zuwa Ofishin ƴan sandan gidan gayu.

A gurin kashi biyu da rabi cikin uku na matan wannan abin da Hajiya Mariya tayi musu shi ne ƙarshen tozarci da wulaƙanci da aka taɓa yi musu a rayuwarsu. Masu arziki a cikinsu sun ɗauki munanan alwashi da yawa a kan Hajiyar, talakawan cikinsu kuwa a zukatansu suke ja mata miyagun alkaba’irai iri-iri.

Wani ƙarin abin haushi da Hajiyar tayi shi ne na ƙin shiga ɗaya daga cikin motocin ƴan sandan a tafi da ita, da ƙyamar shiga motar ƙarara a fuskarta ta ce su tafi, za ta biyo su yanzunnan ita da direbanta, ta ja kunnen ƴansandan ko da sun isa bata ƙaraso ba kar a kuskura a fara wani bincike sai ta ƙaraso, da haka suka bar gidan.

*******

Sun shafe awa biyu cur a cikin cell kafin Hajiya ta ƙaraso, tafe take tana taku ɗaiɗaya irinna manyan mata masu duniya.

Ta canza wanka, ta cancaɗa gayu a fuskarta wanda ya taka muhimmiyar rawa gurin ɓoye shekarunta. Saɓanin ɗazu da take sanye da leshi, yanzu wata ɗanyar shadda ce a jikinta wacce aka yiwa ɗinkin doguwar riga, an ƙawata rigar da aiki irinna zamani.

Tana shiga cikin gurin da sauri aka bata kujerar zama, a ƙasaice ta zauna tana huhhura hanci.
“Ya ake ciki? sunyi bayani?”
Tayi tambayar idanunta ba kallon ƴansandan.

Ko da suka tuna mata ta ce kar ayi komai na bincike sai ta ƙaraso taɓe baki tayi, irin alamun rashin damuwar nan. Ta buɗe baki za ta sake yin magana aka kira ta a waya, ko da ta duba fuskar wayar mijinta ke kira, wanda take yiwa inkiyar His Excellency saboda takarar gwamna da yake yi.
“Excellency barka da yamma.”
Tayi maganar a tausashe fuskarta na bayyana murmushi.

“Yauwa Hajiya. Na dawo gidan sai ban tarar da ke ba, ko har kun wuce mothers day ɗinne?”
Ya tambayeta daga can ɓangaren.

Yanayin alhini ta sakawa fuskarta sannan ta bashi labarin abinda yake faruwa, ta kuma ƙara da faɗa mishi inda take a halin yanzu.

“Hajiya? kinyi hauka ne?”
Abinda ya fara cewa kenan cikin fushi daga can ɓangarensa.

Da mamaki ta buɗe baki tana kallon wayar kamar shi ne a gabanta, ta buɗe baki za tayi magana ya katseta cikin fushi.
“Wane irin haukar tunani ne ya shiga cikin ƙwaƙwalwarki da za ki wulaƙantar da mata masu yawa haka waɗanda muke saka ran ba ƙaramin muhimmiyar rawa za su taka mana a zaɓen da ke tafe ba? To in dai wannan jakar taki mai ruwan madara ce ga ta nan ajiye akan gado cikin ɗakina. Ki gaggauta sakawa a sallami matannan yanzunnan, ko da yake ga ni nan zuwa in basu haƙuri da kaina.”
Kafin ta ce komai ƙit ya katse wayar.

Ya barta riƙe da tata wayar a hannu, baki sake, zuciyarta cike da maɗaukakin mamaki jin cewar a ɗakinsa ta bar jakar.

Sai kuma ta tuna ƙasa da mintuna sha biyar kafin ta ankara da ɓacewar jakar tabbas ta shiga ɗakinsa, don ta ɗauka ma Amarya Jidda set ɗin sarƙar da uban ya siya mata, za ta ba direba ya kai mata can gidan ƙanwarta inda suke tare da ƙawayenta. Ashe can ta ajiye jakar?

Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un! wannan wane irin abin kunya ne ta aikata ga ƴan uwa da abokan arziki har ma da manyan aminanta? Da wane ido za ta sake kallonsu tayi musu magana, ya rabbi ya rabbi.

Ta ɗaga idanu ta hango su can cikin cell, wasu daga cikinsu na tsaye, wasu kuma a zazzaune sun haɗa kai da gwuiwa. Fuskokinsu damalmale da matsananciyar damuwa da tashin hankali.

“Hajiya? Mu fara basu jikinsu ne ta yadda ɓarauniyar za tayi gaggawar bayyana kanta?”
Ɗaya daga cikin ƴansanda mata ta faɗi haka da salon cusa kai gareta.

Wani mugun kallo da ta aikawa ƴarsandannan ba shiri ta ja da baya tana sosa gefen wuya.

Da wata irin muguwar kasala da sanyin jiki ta miƙe tsaye ta tambayesu ina ne ofishin DPO?

An nuna mata kenan za ta shiga sai ga isowar mijinta Alhaji Lukman Mai Dala, a bayanshi motoci ne masu yawa. Tun kafin direbanshi ya gama daidaita fakin a harabar gurin ya buɗe ƙofa ya fita zuwa cikin ofishin, sai saɓa babbar riga yake yi cikin tashin hankali.

Cikin masifa ya bada umarnin a fito da matannan yanzunnan, saboda yawansu sun cike gurin taf. Ganin yawan matan da Hajiya ta sa aka kulle a wulaƙance saboda rashin tunani da rashin hankali irin nata ba ƙaramin sake ɗaga mishi hankali yayi ba.

Irin mugun kallon da da yawa daga cikin matan suke aika musu shi da matarshi da take rakuɓe a gefenshi ya bala’in ɗaga mishi hankali.

A matsayinshi na babban ɗan siyasa mai neman takarar kujeran gwamna ko ƙanƙani ba ya fatan abinda zai janyo mishi matsala tsakaninshi da jama’a, ya san idan bai ɗauki mummunan mataki nan take ba lallai aikinshi ba ƙaramin jiƙewa zaiyi ba.

Ya juya inda Hajiya take ya aika mata da wani haukataccen kallo mai cike da tozartawa, cikin fushi da fusata ya balbaleta da bala’i kamar bai san daga inda ta fito ba, ba kuma tare da ya duba yawan mutanen da suke gurin ba.

A ƙarshe ya dire maganganunshi da cewar lallai tana buƙatar saiti tunda har ta iya wulaƙanta iyaye da yayye da ƙannenshi mata haka akan abinda bai taka kara ya karya ba, nan gaba bai san me za ta ƙara yi ba na tozarci da rashin hankali.

Idan ya haye gadon mulki haka za ta tafiyar da al’umma a wulakance. Ta tafi gidansu ya saketa saki ɗaya.

Duniyar ce ta fara hajijiya da Hajiya Mariya, tunaninta ya tsaya cak! saki shi ne kalma na ƙarshe da ko a mugun mafarki bata taɓa tsammanin zai shiga tsakaninta da maigidanta ba.

Wannan abu da Excellency yayi ga Hajiya shi ya wanke kaso tamanin cikin ɗari na baƙin cikin da matannan suka ƙunsa. Rai fes sunan wata zani. Hatta ƴan’uwanta na jini sun ji daɗin wannan saki da aka yi mata, daman tuntuni ta ishe su da kaɗifiri da girman kai na tsiya, ko cikin dangi sai abinda tace ake yi, ko babu komai yanzu an karya alkadarinta.

Da kallo ɗaya yaga sassaucin tsana da ɓacin ran da yake kwance a fuskokinsu.
Duk a ƙoƙarinsa na sake wanke zukatansu nan gabansu ya zube gwuiwarsa a ƙasa yana sake basu haƙuri.

Idanu suka bubbuɗe, alamun mamaki. Babban mutum irin wannan shi ne ya durƙusa musu a ƙasa? bakinsu har rawa yake gurin cewa
“Honorable don Allah ka miƙe tsaye. Wallahi har ga Allah mun yi haƙuri, mun yafe abinda tayi mana. Yanzu kawai babban burinmu a sallamemu mu koma gidajenmu.”

Talatin da biyunsa a waje ya dinga yi musu godiya da fatan alkairi. Ya umarci direbansa ya ɗauko masa jakarsa a mota, ko da ya buɗe envelope ne ɗauke da kuɗi naira dubu ashirin-ashirin. Haka ya bisu ɗaya bayan ɗaya ya damƙa ɗai ɗai a hannayensu, sannan ya umarci direbobinsa su kwashe su ko wacce a aje ta a gidan mijinta.

Mata masu sukunin cikinsu kuwa waɗanda Allah ya huwacewa arzikin mallakar mota gidansa ya ce a mayar dasu, idan suka ɗauki motocinsu sai su wuce gida.

Sai a wannan lokacin aka damƙama su Hajiya Balaraba wayoyinsu da aka ƙwace. Suka fita daga gurin fuskokinsu babu yabo ba fallasa.

Farida da Fatima hanyarsu ɗaya ne, ita Fatima tana da mota, direbanta ne ma ya ɗaukota suka je gidan Fareeda aka ɗauketa daga can ya ajiye su gidan bikin.

Kasancewar yaranta suna daf da tashi a islamiya sai ta sallami direban da cewa yaje ya kwashi yara ya mayar gida, ƙarfe shida na yamma ya koma gidan bikin ya ɗaukosu.

To yanzu ƙarfe biyar da rabi, wannan abu da ya faru yasa jikinsu a sanyaye yake kamar an lakaɗa musu duka. Har gara ma Fatima akan Fareeda, ita kam har wata ƙwarya-ƙwaryar rama tayi kamar wacce ta yini tana amai da gudawa.

Idanunta sunyi ƙozai-ƙozai saboda kukan da ta kusan yini tana yi, wannan uban kwalliyar da tayi kafin su taho yanzu ko ɓurɓushinsa babu. Duk da an sallamesu har da ladan kuɗaɗe hankalinta ya ƙi kwanciya, tana ji a ɗazu yadda Mukhtar yaita kiranta akai-akai, ta kuma ji shigowar saƙonni a jejjere, saboda fargaba da tsoron abinda za ta tarar ta ma kasa ciro wayar ta duba abinda saƙonnin suka ƙunsa, babban burinta da fatanta bai wuce ta buɗe idanu ta ganta a tsakiyar falon gidanta ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rabon A Yi 1Rabon A Yi 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×