Skip to content
Part 7 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Sake gyara zaman shi yayi a cikin mota a karo na ba adadi, bacci yake ji ba dan kadan ba, saboda bai samu wadatacce ba da dare. Da ace babu hayaniya lafiya kalau zaiyi baccin shi. Tunda motar a kashe take dole ya sauke gilashin kadan dan shige da ficen iska. Amman hakan sai kwaso mishi surutan da baya bukata zuwa kunnuwan shi yakeyi. Harda yara da a lokacin ya kamata ace suna islamiyya amman sun cika unguwa da hayaniya sun hana kowa sakat. Inda unguwar su Daada yake yana da tabbacin da anyi gangami an tashe su ko da gidan nasu ne sai an sa sun siyar sun tashi.

Yaran da zai jera ya zane ma jiki ya kirga sun fi goma sha daya cikin kan shi daga parking din motar shi zuwa yanzun. Baya son hayaniya, baya son surutu gabaki daya, iya zaman da yayi ya gama tsara kalar unguwar da yake son siyan gida in har ya samu wadatar hakan. Kwankwasa gilashin motar yaji anyi ta gefen da yake, bude idanuwan shi yayi yana yatsina fuska saboda kamar cikin kwakwalwar shi aka kwankwasa haka yaji. Juyawa yayi yana sauke idanuwan shi kan fuskar Madina da take mai dariya da duka hakoran ta a bude.

“Hamma…”

Ta fadi cike da fara’a tana saka shi kai hannu ya kara sauke gilashin motar kasa

“Yaushe ka zo?”

Ta tambaya tana dorawa da.

“Me yasa baka shiga cikin gida ba?”

Ya san kafin ya amsa tambayoyin biyu in dai Madina ce ta kara jero mishi wasu, shisa yayi shiru yana jiran ta gama. A cikin watanni biyu baya jin akwai wata halayya ta Madina da bai sani ba, don tana cikin mutanen nan da ake ma rayuwar su lakabi da budadden littafi, ba su da wahalar fahimta. Haka kawai idan gari ya waye a tsayin rana bai ganta ba bayajin dadi, tunda ya san makarantar da take wasu lokuttan yakan dai-daici lokacin tashin su sai yaje. Ba zai manta ranar farko daya fara zuwa ba, yana tsaye ya jingina da motar shi ya hango ta.

Duk yaran da suka fito zaka gansu su biyu har fiye da hakan ma, Madina ita kadai ya hango, ba gilashin fuskarta yasa ya fara gane ta ba, uniform din jikinta da yake tunanin zai wahala bai iya shigar da jikin shi cikin kafar wandonta daya ba, bai taba ganin wando irin na jikin Madina ba, har rigarta tasha bamban da ta sauran, hijabinta ce kawai bata ma kai ta wasu tsayi ba, idan iska me karfi akeyi zata iya yawo a samanta saboda girman kayan da suke jikinta, tana hango shi ta washe mishi baki tana kara saurin tafiyar ta, sanda ta karaso kasa rike dariyar shi yayi

“Madina…”

Ya iya kira, bata san dalilin dariyar shi ba ta fara taya shi.

“Wanne irin kaya ne wannan?”

Dan juyawa tayi har lokacin dariya take yi.

“Bana so inji kaya sun matseni”

Kallon ta Salim yakeyi, komai nata daban yake, ba zai kirga yawan matan da ya sani ba, amman ko mai shigen muryar Madina bai taba cin karo da ita ba. Bambanci da take da shi da sauran mutane ne abinda yaja shi. Ko yanzun da take mishi murmushi da dukkan hakoranta a waje bambanci yake sake gani.

“Yau baki dawo da wuri ba…”

Ya soma a gajiye, kafin ya karasa ta katse shi.

“A’a mun tashi fa, ai kullum-kullum karfe biyar da rabi ake tashin mu, akwai wa’anda suke zuwa daga unguwa mai nisa, ni ce na tsaya na siya awara, akwai layi kuma. Ban san ka zo ba da na taho.”

Numfashi Salim ya sauke yana nuna mata alama da hannun shi da ta zagaya ta shigo motar. Sai da ya dakuna fuska dan karta fadi a gudun da tayi tana bude murfin motar, ledar awarar da sai lokacin ya ganta ta ajiye akan kujerar motar tana fadin,

“Bari in kai jakata ciki in fada ma Daada na dawo kar ta dauka na tsaya wani waje.”

Bata ma jira amsar shi ba, ko murfin motar bata rufe mishi ba ta juya. Numfashin dai ya sake saukewa da murmushi a fuskar shi. Hannun ta da ta dauke ledar awarar ya fara gani dan yanda ta shigo motar kamar an jehota sai da ya sake yin dariya, duk idan yana tare da Madina sai ya dinga jin tamkar yana biyan bashin duka lokuttan daya kamata ace wani abu ya saka shi nishadi bai ji nishadin ba, da wahala kaga fuskar shi babu murmushi duk idan suna tare, ko ita din ya gani kafin ta bude bakinta ta ce wani abu shigar jikinta ta bashi dariya.

“Ga ruwa na dauko maka.”

Ta fadi tana sauke numfashi hadi da mika mishi ledar ruwan da ya karba ba dan yana jin kishi ba, ya siyi ruwa har roba biyu a hanya, tsintar kan shi yayi da fasa ledar ya dan sha ruwan yana rike ledar a hannun shi.

“Daada tace tana gaishe ka.”

Kai ya jinjina mata yana kallo tana bude ledar awarar da tayi mishi kyau a ido, harda albasa da kabeji yankakku a ciki sai yaji kulle a farar leda ta bude tana ajiyewa daga gefe a cikin ledar awarar.

“Ka iya cin awara? Ka san awara?”

Yar dariya yayi mai sauti.

“Lallai yarinyar nan…”

Cewar Salim yana sata yin dariya.

“Nasan unguwar ku ta yan gayu ce, ba masu sai da awara shisa.”

Tayi maganar da dukkan gaskiyar ta, tana daukar awara daya ta saka cikin bakinta.

“Adee tana mana a gida ai.”

Tauna awararta Madina takeyi tana mika mishi ledar da ya saka yatsu ya dauki guda daya ya dangwala yajin ya saka a bakin shi.

“Hamma Nawfal baya son yaji shi.”

Maganar ta kwace mata batare da tasan dalilin da yasa tayi ba, numfashi Salim ya sauke, Nawfal din da ta kira na saka shi jin wani yanayi da bai da fassarar shi. Wani irin shiru ne ya ratsa cikin motar saboda. Ita kanta Madina ji takeyi kamar anyi wasu shekaru ne masu yawan gaske da tafiyar Nawfal din, ba zata ce tunanin shi baya fado mata ba, ko agogon shi da yake ajiye akan gadon ta yana tuna mata shi, da tana sakawa, sai ta cire ta ajiye, ko karatu takeyi wani lokacin zaka ganshi a hannunta tana ta jujjuya shi. Idan zatayi bacci ma lokutta da yawa agogon na hannunta ko da ba tunanin Nawfal takeyi ba ta riga da ta saba dauka.

Daina saka agogon ya zama hanyar ta guda daya ta nuna fushin ta da karya alkawarin shi da Nawfal yayi na cewar shekara daya kawai zaiyi ya dawo. Amman yanzun kam anya akwai wannan fushin?

“Kullum kike siyan awarar?”

Salim ya tambaya saboda yau ne karo na farko da shiru yayi mishi yawa, baisan ko dan in dai tana waje ya saba da hayaniyar ta bane ba.

“Um um fa, ni kadai nake ci. Daada wai mai yayi yawa yana saka mata heart burn.”

Shima kwara hudu yaci ya kara shan ruwan da yake hannun shi. Yana kallo ta kulle sauran da alama itama ta isheta.

“Zan tafi, yanzun za’a kira sallah.”

Salim yayi maganar yana mika hannun shi bayan motar ya dauko wata bakar leda yana dorawa akan jikinta.

“Komai kika ce kina karantawa, bana karanta duk wani abu da bai shafi karatuna ba, sune suka mun kyau a ido.”

Bude ledar Madina tayi tana lekawa, sai da ta gyara zaman gilashinta sannan ta kalle shi da wani yanayi a fuskarta da ya saka zuciyar shi daukar dumi, idan litatttafai zasu bayyana wannan yanayin a fuskarta duk zuwan da zaiyi zai kawo mata ko dan ya gani.

“Nagode Hamma, kasan duk na karanta na dakina, maimaita wasu nakeyi. Daddy yace zai kawo mun amman bai zo ba jiya… Nagode sosai sosai.”

Murmushi kawai ya iya mata yana kallo ta sa hannu ta zaro littafi daya tana shafa shi a gefen fuskarta kamar akwai wani abu a tare da littafin da ita kadai ce take gani, dayan hannunta ta sa tana bude murfin motar ta fita, harta kai kofar gida ta dawo tana daukar ledar awarar ta hadi da fadin.

“Sai anjima…Allah ya tsare maka hanya.”

Bata jira amsar shi ba ta sake juyawa, murfin motar ma sai shi ya rufe abin shi, hankalinta gabaki daya yayi kan litattafan. Da murmushi a fuskar shi ya kunna motar da yayi dai-dai da kiran sallar Magriba da akayi. Yana hanya ana tayi a masallatan da yake wucewa, banda sallar asuba da itama dan Khalid na tashin shi baya kowacce sallah a cikin jam’i. Baisan lokacin da hakan ya fara ba, rana daya ya wayi gari za’a kira sallah yana kwance bai mike ba duk da wani duhu da yake ji yana karuwa a zuciyar shi. Wata rana yana aji haka zaiga mutane na fita dan gabatar da sallar su, ko ya fita yana komawa mota ya zauna har sai an idar.

Sai ya hada azahar da la’asar yayi su a lokaci daya. Ko yanzun daya karasa gida ya ajiye motar shi ya nufi bangaren su ya bude ya shiga a falo ya zauna yana sauke numfashin gajiya, saida ya huta ya mike ya shiga kitchen tunda Adee tana nan yasan abincin shi an kawo ba sai yaje ya zubo ba. Ai kam an kawo din, shinkafa da wake da miyar kifi. Daga Magriba har isha’i sai karfe tara na dare ya hada yayi su, ya sake yin wanka yana shirya jikin shi cikin kananun kayan da sukai matukar karbar shi sannan ya sake ficewa daga gidan.

*****

Adee da take tsaye a gaban shi ta daga kai cikin alamun son ganin fuskar shi sosai yake kallo.

“Dan Allah Hamma, kaji, dan Allah ka danyi fara’a idan zaku gaisa, a tsorace yake wallahi.”

Murmushin da zuwa yanzun zaice Madina tafi kowa gani yayi mata.

“Good…gara da yake a tsorace.”

Kallon shi Adee tayi kamar zatayi kuka. Sau wajen hudu Salim din yana wuce ta tare da Ahmad, cikon na biyar ne tana komawa ta ganshi zaune a falon Nanna, sai da zuciyarta ta buga.

“Waye shi? Ban taba haduwa da yan ajin ku fiye da sau biyu a cikin wata daya ba.”

Bawai bata so ta fada musu bane ba, ta rasa ta inda zata fara tun satin daya fita da Ahmad din ya matsa mata da yana son ya gaisa da Julde, ko kuma tayi magana da shi a saka musu rana yana son ko gaisuwa ce azo ayi, shine namiji babba a gidan su, kuma kamar yanda Hajiyar shi take cewa babu wani abu da yake jira yayi aure sai lokaci, yana da muhalli, dan kasuwa ne da yake harkokin shi a tsakanin Dubai da kuma nan Kano, suna da shaguna a cikin kantin kwari, inda yake mallakin shine, bai kuma boye mata matakin karatun shi daya tsaya a diploma ba tunda gabaki daya harkar karuwanci ce abinda suka saka a gaba. Diploma din ma yayine kawai dan ra’ayin dan samun karatun boko da abokin shi ya kwadaita mishi.

Da ta fadawa Nanna ta samu Julde da maganar saiya wakilta Salim da yayi bincike kafin a sati dayan da ya sakama su Ahmad na turo manyan shi. A tsorace Adee take dan har ranta tana son Ahmad, irin soyayyar da bata hango kanta a ciki ba, yana da duk wata nagarta da cikar halittar da kowacce mace zata yaba da ita. Sai dai a irin bincike na aure haka ake binciko halayen mutum da wasu kan toshe kunnuwan su tare da rufe idanuwa wajen kin yarda, sai binciken yayi hannun riga da halayen da kai aka nuna maka.

Ga Salim din yace mata.

“Ina son magana da Ahmad, ki kira mun shi.”

Batare da yayi mata wani karin bayani ba, tsoron ta shiya kara tsorata Ahmad din. Da yazo din ma ya kirata ya sanar da ita yazo tana jin yanda muryar shi take rawa.

“Tunda azahar nake addu’a Adee, idan Yayan ki yace ban mishi ba fa? Ya zan da tarin soyayyar da nake miki?”

Kasa bashi wani kwarin gwiwa tayi saboda itama a tsoracen take. Dariya Salim yake sonyi amman ya danne yana kama hannunta ya janyeta gefe yana fita. Kaf unguwar su Ahmad harma kasuwar su daya shiga babu mutum daya bayar da shaidar banza akan Ahmad, asalima tarin nagarta da alkhairin shi suke fadi. Idan Salim ya kalli Fadila baya ganin shekarunta, yar kanwar shi yake gani, yar mitsitsiyar yarinyar da zaiyi komai dan kareta daga duk wata hatsaniya ta duniya. Dan baya hango aure a cikin jerin abubuwan da yake da niyyar yi a rayuwar shi baya nufin baya son yaga wani yayi.

Musamman kanwar shi da duk idan yaga wani da namiji a kusa da ita sai zuciyar shi tayi tsalle zuwa wuyan shi. Tsallen da bai taba hana shi bin kannen wasu ba, zuwa yanzun ya daina jin girman laifukan shi, baya hango kowa sai nishadin da zai samu na dan kankanin lokaci. Ya dai ji dadi har kasan ran shi da yaga zata nutsu waje daya, ya sake jin dadin samun Ahmad da nagartar da bashi da ita. Har hamdala ya tsinci kan shi dayi da jarabtar su ba zata taba Adee ba don ita dinma mutuniyar kirki ce. Ko yanda suka gaisa da Ahmad yasan a tsorace yake.

“Idan nace in ka ci amanarta Allah zai kamaka kamar ina fada maka abinda ka sani ne. Ga kanwata na Ahmad, dani zaka fara haduwa idan hawaye ya zuba daga idanuwanta saboda kai.”

Kai Ahmad ya jinjina mishi yana hadiye wani abu da yayi mishi tsaye a wuya. Murmushin da Salim din yayi mishi ma kara tsorata shi yayi, idan yana tsaye da Adee sai ya ganshi babba, amman yanzun a gaban Salim saiya raina girman shi.

“Allah ya tabbatar muku da alkhairi.”

Salim ya sake fadi yana mika ma Ahmad din hannu cikin alamar sallama sannan ya nufi bangaren su. Itama Adee data fito bata wani dade ba saboda tasan Julde na gab da dawowa. Ai kam ko mintina goma batayi ba tsakani ya dawo.

“Daddy…”

Ta furta cikin sigar sannu da zuwa tana mikewa dan ta karbi ledojin da suke hannun shi.

“Adee, sannu da kokari.”

Cewar Julde yana mika mata ledojin dai-dai shigowar Khalid.

“Daddy sannu da zuwa, yanzun naji motar ka.”

Hararar shi Adee tayi.

“Shisa ka shigo kenan…to sai ka juya ai tunda ka mishi sannu, bai kawo tsarabar komai ba.”

Dariya Khalid yayi yana shiga cikin dakin sosai hadi da kaima daya daga cikin ledojin da tayi saurin janyewa wawura.

“Daddy…”

Adee ta kira

“A’a kunga yanzun na dawo ko? Kaina ba zaiyi ciwo ba tunda kamar kaji haka kuke.”

Julde yayi maganar yana raba su ya wuce, a gajiye yake jin shi sosai. Dakin su ya wuce yana samun Saratu a kwance, tun daren jiya da tace tana son magana da shi yasa kai ya fice bai saurareta ba take shan kamshi har yau da safe ma da zai fita. Bata gaban shine, in dai zai dawo ya samu daya daga cikin yaran shi to hankalin shi ya gama kwanciya, wucewa yayi ya watsa ruwa ya fito yana neman wani yadi marar nauyi ya saka a jikin shi.

“Tun jiya nace maka ina so zamuyi magana kaqi saurarena.”

Alamar ciwon kai da yake ji ya sashi zama gefen gadon wajen kafafuwanta da ta tashi zaune ta mike akan gadon.

“Ina jinki”

Ya furta

“Akan maganar auren Adee ne, idan suka bukaci ganin dangin mahaifinta fa?”

Wani irin tsalle zuciyar shi tayi har saida kirjin shi ya amsa. Badan ya shafe wani abu dangi daga babin rayuwar shi ba, a’a, bukatar su a cikar neman aure ne ya manta, wani abu da yake neman taso mishi ya danne.

“Zan san yanda zan yi.”

Ya furta yana mikewa, bin shi da kallo saratu tayi.

“Julde kana ganin komai zai tafi dai-dai? Kana ganin laifukanka ba zasu taba yaran mu ba?”

Iskar da ya shaka dakyar ta wuce mishi yana fito da ita a wahalce, baisan me yasa take son hautsina mishi duniyar daya dauki lokaci yana dai-daitawa ba, amman daya kalleta babu komai akan fuskarta sai tarin damuwa, damuwar da tunda zancen auren Adee ya taso ta danne mata zuciya. Akwai sirrikan su da auren nan zai iya bankadowa, abinda tafi tsoron fitowar shi fiye da laifukan Julde da zai iya taba musu yara.

“Nace miki zan san yanda zanyi.”

Ya maimaita yanajin yanda muryar shi take rawa. Kafin tace wani abu ya fice daga dakin, duk surutan da su Adee sukeyi iya kunnuwan shi yake tsayawa, baya kaiwa kwakwalar shi balle ya fahimta, abincin ci kawai yake badan yana gane dandanon shi ba, har Adee saida ta taba shi.

“Lafiya dai ko Daddy? Fuskarka kamar babu jinni.”

Dan murmushin karfin hali yayi mata.

“Kaina ke ciwo ga shi akwai gajiya a tare da ni.”

Sannu sukayi mishi dukkan su, Adee ta tashi ta dauko paracetamol ta balli guda biyu ta bashi, karba yayi ya sha badan zai mishi maganin matsalar shi da ta girmi duk wata kwayar magani ta bature ba, sai dan damuwar da yake gani a fuskokin yaran, har yayi musu sai da safe suna bin shi da sannu. Daki ya koma, Saratu na inda ya barta, zagayawa yayi yahau gadon ya kwanta yana juya mata baya. Har alamun zazzabi saida yaji ya rufe shi. Yau fiye da kowanne lokaci yake jin kewar Mero, yana da yakinin ba zata rasa kalaman da zata fada mishi da zai kwantar mishi da hankali ba, ko jinta a kusa dashi da kamshin nan nata ya isa yasa hankalin shi ya kwanta.

Lumshe idanuwan shi yayi ko da hoton ta ne ya gani a zuciyar shi, amman sai hoton yazo mishi tare da kalamanta.

“Yanda kayi mun rami a zuciya, in Allah ya yarda duk lokacin da kake tunanin hankalin ka ya kwanta sai Allah ya aiko abinda zai birkita maka komai Julde…”

Babu shiri ya bude idanuwan shi. Zuciyar shi na ciwon daya dauka lokaci ya saba masa da radadin shi. Mero ce mutum ta biyu da take da muhimmanci a rayuwar shi da ta jefe shi da kalamai masu zafi irin haka, rashin sa’ar shi mai girma ne, batun yanzun ya san haka ba, shisa tunda ya samu su Salim kacokan duk wata addu’a da zaiyi, duk ma wani aikin kirki da zaiyi da niyyar Allah kar yasa rashin sa’ar da yazo duniya da shi karya taba su. Tambayar Saratu ta tokare mishi kahon zuciya.

Anya laifukan shi ba zasu taba yaran su ba?

Tambaya ce mai nauyin da shi kadai yasan shi, laifuka tace, laifukan shi idan zaiyi waiwaye masu yawan gaske ne, ko daya daga ciki za’a dauka ya isa ya tsaida duk wani jin dadi da yake gani a fuskokin yaran shi. Har Saratu ta mike ta kashe musu fitilar dakin bai ko motsa ba, wani irin tsoro ne yake ratsa dukkan sassan jikin shi, kome zai same shi in dai zai tsallake su Adee mai sauki ne. Bacci a daren ranar barawo ne ya sace shi cike da mafarkin rayuwar da zaiyi komai dan ganin ya shafe babinta. Sai dai wasu shafukan na kaddara suna da zumunci, ko baka waiwaye su ba sai sun sake kawo maka ziyara.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 6Rai Da Kaddara 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×