Skip to content

Rai Da Kaddara 1 | Babi Na Sha Bakwai

3
(2)

<< Previous

Da kyar yake iya daga idanuwan shi, ya san Allah ne kawai ya tsare mishi hanya daga asibiti zuwa gida.

“Idan ka gaji haka ka dinga kwanciya a asibiti ko baccin awa biyu ne kayi tukunna ka hau titi, ko ka kira Hamma Khalid ya zo ya dauke ka.”

Rokon da Madina tayi mishi kenan kwanaki tana dorawa da.

“Kaji Hamma, dan Allah, kaji.”

Bai amsa ta ba, saboda inya amsa zai zama kamar yayi mata alkawari ne. Bacci a asibiti ba zai iya shi ba kamar yanda yaga sauran abokan aikin shi sunayi, saboda akwai hayaniya, duk da ofishin shi ne can karshe, amman karar takun tafiya na zirga-zirgar mutane kamar cikin kunnen shi akeyi haka yake jin su, yana iya jiyo karar wayar wani daga ofishin shi. Duk kananun hayaniyar nan ba zai iya bacci a cikin ta ba. Tun kafin ya tura kofar ya jiyo sautin hayaniyar da yake da tabbacin tv ce a kunne.

Da tsaki a bakin shi ya tura kofar, sai da ya dan runtsa idanuwan shi saboda karar da yaji ta sa kan shi sarawa. Nawfal na zaune kan doguwar kujera ya jingina bayan shi sosai, yanda idanuwan shi suke a rufe ya tabbatar ma da Salim din bacci ne ya dauke shi, wani sautin mamaki Salim ya fitar yana karasawa cikin dakin sosai ya kai hannu ya dauki remote din da yake gefen Nawfal ya rage karar tv din gabaki daya sannan ya zauna gefe don ya zare takalmin da ke kafar shi.

Yana jin wata iska da ta ratsa kafafuwan tun kafin ya cire safar shi, numfashi ya sauke yana jin wani na mishi wahalar shaka saboda Nawfal da ya doro kan shi a kafadar shi batare daya yi tsammanin hakan ba, kafin yayi wani motsi Nawfal din ya zagaya hannuwan shi duka biyun a damtsen shi yana kara kwantawa a jikin shi.

“Ina ta missing din ki.”

Nawfal ya fadi cikin bacci, shima gajiyar ce a tattare da shi. Bai taba hasaso cewa haka kafa kasuwanci yake da matukar wahala ba sai yanzun da tun wajen karbar lasisin shi na tuki ya fara jin kan shi na nauyi, balle kuma daya fara zirga-zirga tsakanin Kano da Kaduna tun da nan din ya zaba a matsayin garin da zai zauna ya kuma kafa kasuwancin na shi.

“Me yasa sai Kaduna? Duk fadin Kano Bajjo? Baka ganin wasu daga Kadunan suna dawowa Kano don kafa kasuwancin su, ka zabi duk inda yayi maka a Kano zan sai maka fili idan akwai, in babu zan sai maka ko meye a wajen in dai zasu siyar mun saika rushe ka gina abinda kake bukata, ina da kudin, in banda su kai kana da kudin… Kaduna tayi nisa.”

Julde ya karasa maganar muryar shi dauke da nauyin da yake ji a zuciyar shi.

“Kadunan dai nake so Daddy, ai babu wani nisa fa, zan zo in ganku duk sanda nake so. Don Allah karkace a’a, kamun addu’a kawai.”

Yana kallon yanda Julden yake kokawa da zuciyar shi kafin ya jinjina kai a hankali.

“Allah ya zaba abinda yafi alkhairi, amman ka kara tunani dai.”

Shima ya amsa ne da to ba dan akwai wani tunani da zai kara ba. Ya dauke shi tsayin shekara daya kafin ya yanke hukunci zama a Kadunan. Tun kafin ya dawo kuma yake binciken hanyoyin da komai zai zo mishi da sauki. Sai dai ko da kudi ba zasu zamar mishi matsala ba, hanyar tana da tsayin da bai hango ba. Yau din ma yana dawowa ruwa ya watsa ya fito da nufin shiga kitchen ya hada shayi, sai ya zauna ya fara hutawa tukunna, bai san lokacin da bacci ya dauke shi ba. Kamar jiya ya zo, gashi harya shafe watanni biyu da dawowa amman bambanci lokaci ya kasa barin shi.

Da daddare idanuwan shi kamar an soya gyada a ciki, amman da rana kamar an bubbuge mishi gwiwoyin kafa haka yake ji saboda baccin da zaita dawainiya da shi. Sunyi waya da Murjanatu yana hanya, da tunanin yanda yake kewar ta ya shigo gidan, har bacci ya dauke shi ma yana tunanin yanda zata matsa mishi kafafuwan shi da suke a gajiye da tana kusa. Shisa kwakwalwar shi tayi mishi tunanin itace yaji ta zauna a gefen shi kamar yanda ta saba. Suna da bambanci lokuttan dawowa gida, tana rigan shi fita, yana kuma riganta dawowa.

Ranaku da yawa sai tsakiyar dare take komawa, saboda yanayin karatun su ma ba daya bane ba, kuma in ta tashi daga makaranta zata wuce aikin da takeyi na awa uku wani lokacin awa hudu, ya danganta da yanda take jin gajiya.

“Bajjo…”

Salim ya kira a tsakanin jan numfashi da saukewa saboda ya kawo iya wuya. Amman kamar ya tunzura Nawfal din daya kara riko shi.

“Jikina ciwo yake.”

Cewar Nawfal din, hannun shi Salim yake kokarin fisgewa amman rikon da Nawfal yayi mishi bana wasa bane ba, shisa yayi amfani da gwiwar hannun da yake rike da shi din ya zungure shi a hakarkari, babu shiri ya bude idanuwan shi yana kokarin gane inda yake da kuma abinda yake faruwa, a hankali ya juyo ya kalli Salim da yake watsa mishi wata irin harara da yasan yana gab da kwada mishi mari idan bai daina koma meye Salim din yake tunanin yanayi ba, hannuwan shi da suke sakale da na Salim ya kalla yana tunanin abinda sukeyi a wajen.

Bai san ihun da yayi cikin kan shi ya subuce mishi ba sai da yaji sautin shi a kunnen shi, hannuwan shi na nuna mishi bai isa da su ba saboda sun ki sakin Salim din.

“Ba zaka sakeni ba dan uban ka? Sai na karya ka tukunna ko?”

Sai lokacin ya saki Salim din yana mikewa cikin hanzari.

“Me kake anan?”

Nawfal ya tambaya cikin tashin hankali, wani irin kallo Salim din ya watsa mishi.

“Me yasa baka tasheni ba?”

Ya dora yana yarfe hannuwan shi hadi da goge su jikin rigar shi, kai Salim ya jinjina, an kwana biyu wani bai raina mishi hankali haka ba, ganin yanda ya mike yasa Nawfal din rugawa da gudu.

“Ka dawo kaji me yasa tashe ka ba.”

Cewar Salim din yana kallon Nawfal da har ya kai bakin kofar dakin su. Kwafa yayi yana komawa kan kujerar ya zauna.

“Karka dawo falon nan.”

Salim ya fadi yana kwanciya akan doguwar kujerar, yasan in yayi wanka da ruwa mai dumi sosai sai yafi jin dadin baccin, amman kan shi yayi mishi nauyi ba kadan ba.

“Hamma dan Allah… Shayi zan hada sai in koma daki.”

Nawfal yayi maganar daga in da yake tsaye.

“I will kill you if you make another sound.”

Dariya Nawfal yayi yana nufar kitchen, kafin ya gama hada shayin Salim ya kira.

“Bajjo!”

Cike da kashedi ya kuma watsa mishi zagi yafi sau biyar. Da gangan ya buga kofar dakin su wajen rufeta yana jin zagin da Salim din yayi mishi, dariya yayi ya saka mukulli a jikin kofar dakin. Yasan har yanzun baiyi girman da Salim din zai ki cin zalin shi in ya so ba, ko kafin ya tafi Kaduna da ya zo ya same shi kwance a falo yana kallo sai da ya kai masa wani duka da ya wuni yana murza wajen.

“Bana hana ku zama a falon nan ba.”

Da bai saurin tashi ba wani dukan Salim zai sake kai mishi. A ka’ida falo nasu ne su duka, amman tuni Salim ya hada ya mallake da nashi dakin. Ko wucewa zakayi in yana kwance saika dauke numfashi kar kayi ya karasa kunnen shi. Da suna zama suyi kallo in yana dakin shi, ya zo ya hana saboda basa rage karar tv din a cewar shi, yana jin surutan har cikin kwakwalwar shi kar wanda ya sake zama. Shayin shi Nawfal ya shanye ya kwanta ya dan runtsa ko na awa daya ne tunda yaga har biyar ta wuce, yasan dai zai tashi jikin shi yayi mishi nauyi.

*****

“Kin siyi JAMB?”

Fatima Atiku ta tambayeta lokacin suna rubutu NECO, kai kawai ta girgiza mata. Ita bata ga saurin da dalibai da yawa masu zana jarabawa sukeyi ba, tun kafin ma ta shiga aji shiddan tana ganin sauran dalibai na wannan zumudin. In tace bata hango rayuwar jami’a da yanda zata kasance mata zai zamana karya, amman banda haka bata wani zumudin shiga ko doki, a ganin ta makaranta dai duk makaranta ce, karatu kuma karatu ne, babu wani abu da zai canza mata, yanda bata da wasu da zata kira abokai haka ma acan din bata jin zata samu wanda zata kira da wannan sunan.

Ta fi so sakamakon jarabawar ta su ya fito tukunna, ta ga taci duk wani abu daya kamata kafin tayi wata JAMB, har Salim sai da yayi mata maganar.

“Ni nafi so jarabawa ta fito ne Hamma.”

Kallon ta yayi.

“Zaman me zakiyi a gida Madina? Da kinyi JAMB din, result na fitowa a shekarar nan ma zaki iya samun admission.”

Shi yayi mata bayanin muhimmanci yin JAMB din shekarar da ka zana jarabawa, amman yayi mata bayani a kurarren lokaci tunda har an gama saidawa, ko da ba’a gama saidawa ba sai dai tayi saboda shi bawai don ko daya a cikin bayanin ya gamsar da ita ba. Ta fi son bin komai a hankali, kuma daki-daki. Yanzun kuwa dadin hutun ma take ji, daga islamiyya sai in tana da wanda zatayi wa kunshi da kusan kullum ne, da dare tana da isasshen lokacin da zatayi karatu tunda tasan zata koma bacci da safe in ta gama aikin ta.

Bambanci da yake cikin kowacce rana a wajen ta shine yawan mutanen da ta yiwa kun shi sai kuma sabon abinda zata karanta. Banda wannan kullum iri daya ce, abu iri daya ne. Sai kuma Daada da take ganin kamar tana ramewa, kamar kuma akwai rashin kuzari a yanda take gudanar da al’amuranta ba kamar da ba, kusan kullum sai ta kai hannu ta taba fuska ko wuyan Daada dan taji idan akwai zazzabi sai taji lafiya kalau. Yau ma kuwa hakanne ya faru har ta sa Daada yin murmushi.

“Na ce miki lafiya ta kalau Madina.”

Numfashi Madina ta sauke.

“Kina ta ramewa Daada…ko dai in kira Daddy muje asibiti a kara duba ki.”

Dariya Daada tayi.

“Allah da gaske, ni gani nake kina ta ramewa.”

Kafin Daada ta amsa sallamar Nawfal ta katse ta.

“Hamma dan Allah ba Daada ta rame ba?”

Madina ta tambaya bayan ta amsa mishi gaisuwar shi, kallon Daada yayi sosai, yana kula da yanda shekaru suka nuna a fuskarta, bai gani ba da, amman akwai rama a fuskarta, duk da ita din ba mai jiki bace ba tunda can ma, amman fuskarta a cike take, yanzun kam har hancin ta da yake dogo ya kara fitowa, kana ganin kwanciyar karan hancin daya fara tun da tsakiyar girar ta.

“Baki da lafiya ne? Jikin ne?”

Kai ta girgiza musu.

“Ku me yake damun ku ne?”

Saboda bata son damuwar da take kan fuskokin su.

“Kuma bata yin komai da hanzari kamar da fa.”

Madina ta fadi.

“Yarinta nake karawa ne kullum? Jikin girma ne, kuyi addu’ar samun jiki me kyau irin nawa”.

Dariya sukayi gabaki daya, duk da a kasan ta Nawfal akwai damuwa, waje ya samu gefen Madina ya zauna har lokacin sai kallon Daada yakeyi, musamman yanda sai da ta dafa kujera sannan ta iya mikewa dakyar kamar tana jin nauyin jikinta.

“Bacci ma nake ji ni kam.”

Shagwabe fuska Nawfal yayi.

“Ko gaisawa ba muyi ba Daada shine zaki tashi? Ba zaki zauna muyi labari ba?”

Murmushi tayi.

“Ai nasan kana nan har in tashin… Wacce gaisuwar? Ba gani ba ka ganni ina lafiya, kaima kuma nagan ka kana lafiya.”

Kai kawai Nawfal ya jinjina yana sauke numfashi, har ta shiga daki bai daina kallon in da ta bari ba, haka kawai sai yake jin zuciyar shi tayi nauyi. Sai dai bai ce wani abu ba har akayi sallamar da ta sa Madina mikewa tana fita tsakar gidan dan ta ga ko waye ya shigo, sanda ta dawo yaja kafafuwan shi ya dora su kan kujerar.

“Kunshi zanyi Hamma, in zuba maka abinci?”

Kai ya girgiza mata, bayajin yunwa, wayar shi ya ciro yana kwanciya kan kujerar sosai ya shiga whatsapp yana sake kallon hotunan da Murjanatu ta turo mishi yana murmushi shi kadai, har Madina ta shiga daki ta dauko kayan kunshin ta, ta sake ficewa bai ma kula ba. Bai san lokaci na wucewa ba musamman da Murjanatu kamar ta duba zuciyar shi ta ga yanda yake kewar ta ta zo online. Earpiece din shi da bai cika mantawa ba ya ciro a aljihu ya saka saboda ta kira shi video call.

Sallar la’asar da aka kira ne ya sa shi yi ma Murjanatu sallama yana mikewa yaje ya dauro alwala, batare da ya kalli matar ko yarinyar da ta gaishe shi ba ya amsa yana wucewa, dan lokacin ma kokarin maida links din hannun rigar shi daya bude wajen alwala yake yi. Ita ma sallar ta mike taje tayi, don sallah na daya daga cikin abinda bata wasa da shi. Sanda ta karasa ma matar hudu kusan da rabi. Kudin da ta bata cikin wata jaka taje ta zuba, abinda take siye bashi da yawa, Julde na bata kudin kashewa sosai, Salim ya sa taje ta bude account a banki, shi ya dauketa sukaje tare. Yanzun ma idan kudin kushin sun kai dubu biyar ko fiye da haka sai ta fada mishi yazo ya kaita taje ta saka a ciki.

“In sun taru da yawa zakiyi wani abu mai muhimmanci da su.”

Salim din ya fadi, sai da ta fara tarawa tukunna zuciyarta ta raya mata tarin abubuwan da take son tayi da kudin in har sun kai mata yawan da take fata.

“Kunshi kamar kina ma mutum goma, tun dazun.”

Nawfal ya fadi bayan ta shiga falon ta samu waje ta zauna.

“Kasan wahalar kunshi ne Hamma?”

Kallon ta Nawfal yayi.

“Bawani wahala, ai na iya.”

Dariya Madina tayi, sosai dariya ya bata.

“Ka iya me? Bafa zanen kujeru ba Hamma, kunshi…kunshi irin wanda mata sukeyi.”

Kai Nawfal yake jinjina mata tunda ta fara magana fuskar shi babu alamar wasa.

“Ni nake yiwa Jaan, kuma kowa ya gani sai yace yayi kyau.”

Duk da taji wani iri a zuciyarta bai hanata cigaba da dariya ba.

“Baki yarda ba kenan? System dina dayan daya baci ne nake da hotunan da kin gani.”

Dariyar dai Madina ta cigaba da yi mishi.

“Ki dauko kayan kunshin ki kawo hannun ki kisha mamaki.”

Mikewa tayi ta nufi dakin ta tana dauko jakar kayan kunshin, akwai saura da yawa a kwarkwaron da tayi ma matar na bakin lalle ta kuwa mikawa Nawfal da ya sauko daga kan kujera shima yana zama kan kafet suka fuskanci juna da Madina da ke kokarin gintse dariyar ta tana son ganin iya ina Nawfal zai kai da maganar ya iya zanen lalle kafin ya fito ya fada mata wasa yake. Fuskar shi babu alamar wasa ya ware mata tafin hannun shi na hagu yana daga mata girar shi duka biyun. Wani irin tsalle zuciyar tayi kamar tana son bayyana kan fuskarta, hakan ya sata saurin sadda kanta kasa tana jan siririn numfashi, hannun nata da taji yana zufa ta goge jikin wandon ta sannan ta dora shi kan na Nawfal.

Salim ya sha rike hannunta, a rana sai ta rike hannun Daada babu adadi, tafin ta ne kawai kan na Nawfal, amman ji takeyi kamar ta dora shi kan murfin tukunyar da aka sauke daga wuta, dumin na gangarawa har cikin wani lungu a zuciyarta da sai yau ta san da zaman shi. Fuskar shi ta ke kallo da yanda ya nutsu akan hannun ta kamar a duniya kaf bashida wani abu mai muhimmanci da yafi zanen da yake mata, wannan karin duka jikinta taji ya dauki dumi sai kace zazzabi na shirin kamata.

Yawu ta hadiye tana dan daga wuya da nufin hango abinda Nawfal din yake zana mata ya kuwa sake yin sama da hannunta yana fadin.

“Kibari in gama Malama.”

Dariya tayi.

“Karka bata mun hannu Hamma, ka tsaya inga me kake.”

Kafada Nawfal ya makale mata yana saka idanuwan shi cikin nata.

“Allah ki tsaya in gama.”

Kai ta jinjina mishi haka kawai tana jin ba zata iya musu da shi ba. Duka bai kara minti goma ba yayo kasa da hannunta dai-dai lokacin da zata hadiye yawu, ta kuwa sarke wajen kokarin yin dariya, duk da haka ta kasa dainawa, taurari ne Nawfal ya zana mata, daya kwandalele a tsakiyar bayan hannunta, sai yayi yan kanana daga gefe, haka jikin kowanne yatsa yayi karami guda daya.

“Inalillahi…”

Ta fadi tana cigaba da dariya, turo baki Nawfal yayi dan baiga abin dariya ba

“Kowa a makaranta yana tambaya wanda yayi mun kunshin nan.”

Murjanatu tace mishi, tunda da a yatsunta kawai take saka ja idan ta siyo, shi yace ta kawo ya zana mata, batayi musu ba kuma ta bashi, da kanshi yake kirkirar zane kala-kala, mai taurarin shine yake ganin yafi kowanne kyau, ko kafin ya taho duka hannuwan Murjanatu biyu saida yayi mata, da yan yatsun kafa ma.

“Gidado ka kware da kunshin nan yanzun, kaga yanda na kafar yayi kyau.”

Har sumba ya samu ta godiya. Sai Madina ce zata saka shi gaba da dariya.

“Hamma… Hamma.. Meye wannan?”

Tayi tambayar a tsakanin dariyar da takeyi, kwarkwaron ta ya ajiye mata yana komawa kan kujera ya kwanta.

“Ai sai kiyi tayi tunda baki san abin arziki ba.”

Mikewa Madina tayi da sauri tana nufar dakin ta ta shiga bandakin da yake ciki ta bude famfo ta saka hannun, sai dai ya riga ya fito, zai kuma yi aqalla kwana uku ko hudu bai gama fita gabaki daya ba ko da tana yawan amfani da ruwa. Dariya kawai takeyi, tana fitowa daga bandakin taji wayarta da ta bari cikin dakin tana ruri, da sauri ta karasa ta dauki wayar, muryar ta dauke da dariya ta ce.

“Hamma…”

Bayan ta kai wayar kunnen ta.

“Ina kika je? Ina ta kiran ki. Ke da wa kike dariya?”

Dariyar ce ta sake kubce mata.

“Ina nan fa, na bar wayar a dakine, na ma wata kunshi sai nima akayi mun…”

Sai dai kafin ta gama dariyar da ta sake kubce mata ta bashi labari harya katse ta.

“Kunshi? Kikayi? Wayayi miki?”

Salim ya jera mata tambayoyin a numfashi daya.

“Hamma Nawfal fa… Wai ya iya, yana ma matar shi, kaga abinda ya zana mun a hannu?”

Ta karasa tana dariya, shirun da taji ya biyo bayan maganar ya sata fadin.

“Hello…”

Har sau biyu tana sauke wayar daga kunnen ta dan tunaninta kiran ya katse sai taga sakanni suna tafiya, sake mayarwa tayi.

“Hamma… Bana jin ka fa. Ka kashe ka sake kira.”

Numfashi taji ya sauke cikin kunnenta, muryar shi can kasan makoshi yace.

“Ina zuwa.”

Kafin ma ta amsa taji alamar ya katse kiran daga bangaren shi, cajarta ta karasa ta ciro tana daukar wayar ta nufi falo, har lokacin da murmushi a fuskarta.

*****

Baiyi tunanin kafafuwan shi zasu dauke shi daga dakin su zuwa na Salim ba saboda rawar da sukeyi, tashin hankalin da yake ciki bai barshi ya tuna cewa ana neman izini kafin a kwankwasa daki ba, turawa kawai yayi yana samun Salim a tsaye da alama wanka ya fito ya sake kaya.

“Bajjo…”

Salim ya kira ganin tashin hankalin da yake shimfide a fuskar Nawfal din.

“Hamma…”

Nawfal ya kira yanajin zuciyar shi akan harshe.

“Meye? Mene ne?”

Numfashi Nawfal ya sauke.

“Hamma Khalid…”

Kokawa yake da sauran kalaman

“Hatsari sukayi…ya kirani…banaji sosai… Hamma ina ta kira ba’a dagawa…ba’a daga wayar.”

Mukullin motar da yake kan gado Salim ya dauka, Nawfal baya bukatar Salim yace mishi ya wuce, gaba yayi yana bin shi a baya har suka fita daga gidan. A wajen ajiye motoci suka ci karo da Julde da zai fita, tashin hankali bai hana su duka biyun jin kamshin da yakeyi ba. Ganin Salim bashi da ko takalmi yasa shi tambayar.

“Lafiya? Ina zaku? Me ya faru?”

Salim ne ya iya amsa shi da.

“Khalid ne yayi hatsari.”

Wani irin rugugi Julde yaji cikin kirjin shi har hanjin cikin shi na taya zuciyar shi amsawa. Su duka ukun motar Salim suka shiga, dan Julde baya ya bude yana zama. Sai da suka hau titi sannan Salim yayi tunanin bai ma san inda zasu nufa ba.

“Yana ina? Ina akace maka yake?”

Kafada Nawfal ya dan daga.

“Nima ban sani ba, mu bi hanyar wajen aikin shi kawai.”

Kallon shi Salim ya yi.

“Baka da hankali ne? Kasan hanyoyi nawa ne zaka iya bi zuwa Asad?”

Kamar Nawfal zai yi kuka yace,

“Dan Allah ka zabi daya kawai kabi Hamma, kayi sauri.”

Dayar kuwa ya zaba yana karanta duk wata addu’a da zata zai iya tunawa, tashin hankali bakon abu ne a wajen shi. Ya sha ganin mutane a asibiti suna faduwa suna tashi akan tashin hankali idan sun kawo yan uwan su, ko kuma ya fada musu rasuwar wani makusancin su, sai dai ya kalle su kawai saboda ko da wasa ma baya son ya hasaso me suke ji, don hakan na nufin ya saka kan shi a takalmin su, ya kwatanta da wani na shi, ba zai iya ba, baya so ya ma iya. Sai gashi yau yana zaune tashin hankalin ya same shi har cikin gida. Daman zuciyar shi a jagule take tun wayar da yayi da Madina. Kai ya girgiza dan ba wannan bane abu mai muhimmanci yanzun.

Suna hawa titin Kawaji kuwa suna ganin cunkoson da aka hada a wajen, gurin ya cika, ko gefen hanya Salim bai samu ya sauke motar ba, a tsakiyar titi ya tsaya suna fita daga ciki gabaki dayan su. Sai da yaji shigar kwalta a tafin kafafuwan shi tukunna yagane cewar bai saka takalmi ba. Runtsa idanuwan shi kawai yayi yana fitar da numfashi, ta tsakanin mutane suke kutsawa. Nawfal najin kafafuwan shi na kara yin sanyi da duk takun da zatayi.

“Trailer ce akace ta kwace duk ta bi takan motocin nan.”

Ya tsinto muryar wani yana fada a cikin mutanen yana sa makoshin shi bushewa kamar an zuba yashi. Julde ya fara hango Khalid a tsugunne ya hade kan shi da gwiwar shi, har tuntube yakeyi wajen kokarin ya karasa wajen shi, Nawfal kam jinin da yake gani ya kara daga mishi hankali.

“Khalid…”

Julde da Salim suka kira lokaci daya suna sa Nawfal kallon inda suke, dagowa Khalid din yayi, har idanuwan shi sun zurma ciki saboda tashin hankali. Shi da yamma ma ya kamata yabar wajen aikin, sai abokin aikin shi ya kira cewar yar shi bata da lafiya suna asibiti, shine ya karbe shi har daren, cunkoso ya samu akan hanya, tsaye motar shi take kamar ta sauran mutane da dama, da kuma babura, ba zaice ga abinda ya faru ba, ihu da kara kawai yaji sai motar shi da yaga tana gaba da kanta, ashe trailer din data kwace sai ta danne motocin da suke can bayan su, da tafiya ake kilan sai hatsarin yafi haka muni.

Sanda wani ya bude motar shi ya fisgo shi ya juya bayan shi ya dora idanuwan shi kan wani mutum da kafar shi ta fita kasa motsawa yayi, tsaye yayi yana kallon yanda ake zaro mutane musamman masu mashina daga karkashin motoci, tunda yake bai taba ganin tashin hankali irin wannan ba. Nan take zazzabi mai zafi ya rufe shi, tunanin ya kira Nawfal ne ya zo mishi, sai da ya ma rasa abinda zaice mishi, bai san ya kiran ya kare ba ko ya akayi ya samu waje ya tsugunna, kawai yasan ko kifta idanuwan shi yayi sai ya dinga ganin mutane da jini na gifta mishi

“Khalid…”

Salim ya sake kira yana kama hannun shi ya mikar da shi tsaye.

“Kaji ciwo? Ina kaji ciwo?”

Yake tambaya yana bin jikin Khalid din da kallo.

“Daddy…”

Khalid ya kira da dukkan zuciyar shi yana jin yanda babu wani girma da zaiyi a duniya da za’ace baya bukatar lallashin iyayen shi. Karasawa Julde yayi da sauri.

“Kaganni nan Khalid, baka ji ciwo ba dai ko?”

Kai Khalid din ya daga mishi yana jin wasu hawaye masu zafi da suka cika mishi ido, da shikenan fa, karshen ganin da zai musu yau da safe kenan, dan Adam da gaske ba abakin komai yake ba, kana tafiya ajali yana bibiyar ka, ko tsautsayi, duka tarin mutanen da tsautsayin ya fadama sun bar gidane batare da sanin ba zasu koma ba, iyalai da yan uwa suna can suna dubar hanyar komawar su, wasu sai dai suji ana sallamar su matsa za’a shiga da gawa, ko suzo asibiti kaza su dauka. Ko ina jikin shi bari yakeyi, wani irin tsoro na shigar shi.

Bashi da rabon wahala, amman bayan motar shi gabaki daya ya molaqe, ba dabarar shi ba, ba komai ba, ko addu’ar fita daga gida bai tuna yayi ba yau din. Allah ne kawai ya kubutar da shi.

“Baka ji ciwo ba?”

Julde ya sake tambaya, kai Khalid ya daga mishi, kamar haka Nawfal yake jira ya tsugunna saboda kafafuwan shi da yaji shima sunyi sanyi. Fuskar shi ya saka cikin hannuwan shi yana jero duk wata kalar godiya da zai iya wa Ubangiji da ya tseratar da Khalid din.

“Meye kai kuma? Ka tashi Bajjo, baka gan shi ba? Lafiyar shi kalau babu abinda ya same shi.”

Kai kawai Nawfal yake dagawa Salim din amman shi kadai yasan yanda zuciyar shi ta girgiza, baka isa ka hana kaddara yin aikinta akan makusancin ka ba, amman in zaka iya bayajin shi kam zai bar ko tsinke ya soki Khalid. Sai da Salim ya kamashi shima ya mikar.

“Ku taho ku koma mota…”

Cewar Salim yana jan rigar Nawfal din, Julde ya kama hannun Khalid, bayan suka shiga su biyun. Julde ya rufe bangaren Khalid yana daga kan shi yayi nasarar saukewa akan Mero da hasken fitilar wata mota ya haska mishi fuskarta dai-dai lokacin da ta shiga gaban wata mota tana rufe murfin tare da bude wani abu a cikin kirjin Julde da kafafuwan shi suka fara daukar shi.

“Mero… Mero Na.”

Ya furta a kasan numfashi.

“Daddy… Ina zaka je kuma?”

Salim ya tambaya, amman ko jinshi Julde baiyi ba, mutane yake turewa yana ratsa tsakanin motocin da suke wajen, kafin ma ya tsallaka har anja motar anyi gaba, wani mashin ya dafa yana mayar da numfashi, shekaru goma sha sai yau ya dora idanuwan shi akanta, kafin ya maida numfashin da yake fatan zai dan nutsar da bugun zuciyar shi yaji an dafa shi.

“Daddy… Lafiya kuwa?”

Salim ya tambaya yana ganin fuskar Julden ta kara mishi haske kamar babu jini a jikinta.

“Lafiya?”

Ya sake tambaya, kai Julde kawai ya daga mishi.

“Mu tafi gida kawai, gobe na dawo in duba motar Khalid da safe…”

Kan dai Julde ya sake daga mishi, bai yarda da muryar shi ba shisa bai amsa ba, haka suka karasa, Salim ya bude mishi gaban motar ya shiga. Zuciyar shi kamar kara bugawa take a cikin kirjin shi.

Ashe zai sake ganin Mero?

Ko dai alama ce kaddara take nuna mishi?

“Inajin kamar don kai kawai aka halitta mun zuciya a kirjina, ko dan kai ta fara numfasawa? Wanne irin so nake maka dana watsar da maganar kowa Julde?”

Kalaman ta kenan.

Kalaman da suka zauna mishi.

Kowanne RAI da tashi KADDARAR.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×