Skip to content
Part 3 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

2003

“Adee…”

Ya kira ta da sunan da Khalid ya saka mata tun lokacin baya iya kiran sunan ta, maimakon Fadila din sai ya gajarce shi zuwa Adee da kowa yake kiranta da shi yanzun.

“Ke bakya jin rana?”

Kai ta girgiza mishi, duk rashin magana irin ta Nawfal bai kai Adee ba. Dan ta ita duniya bata tashi ba, komai da sanyi-sanyi takeyin shi. Kusan ita ta kwaso jikin fulanin. Yanzun haka idan kaganta ita da Nawfal din babu wanda zaice itace babba, kanta da wahala idan ya kai kafadar shi, bata da tsayi kuma bata da jiki. Sai hasken fatar da kusan gadon shi sukayi. A gajiye take jinta, ta rasa inda Daddy ya tsaya da yau baizo daukar su ba. Ta riga da ta saba da anyi hutu ta fito a bakin gate take samun motar shi yana jiran ta.

“Yau Daddy ya dade…”

Tayi maganar cike da kosawa. Nawfal bai amsa ta ba, baisan me zaice mata ba. Inda yana da zabi zai zauna a makaranta abin shi. Duk satin duniya sai Daddy yazo ya gansu. Wasu satikan da Khalid yake zuwa. Sai dai a wani bangaren idan ya tuna zai ga Daada sai yaji komawa gida ba abu bane mai muni kamar yanda zuciyar shi take fadi. Sati ukune kawai hutun nasu, idan ya rike numfashin shi kafin ya sauke zaiga kwanakin sun wuce kamar ba’ayi su ba. Zai kokarin gujema Nanna a satikan.

“Daddy muna ta jiran ka”

Muryar Adee ta katse mishi tunanin da yake, yana daga kai ya kalli Daddy da yake mishi murmushin da yake mayar mishi. Sai yaji kamar anfi sati rabon da yaga Daddyn saboda yanda yayi kewar shi.

“Ba kun gujeni kun zabi boarding ba yaran nan?”

Dariya sukayi gabaki dayan su. In da zasu biye Julde sam ba zasu hada hanya da makarantar kwana ba. Ya fiso ya dawo gida ya gansu kafin ya kwanta, idan ya tashi da safe ma ya gansu kafin ya fita. Saboda su baya tafiya ta wuce kwana biyu, kewar yaran shi zata fara tambayar shi. Sai dai a lokaci daya kuma bashida zuciyar hana su abinda yaga muraran suna so. Da zai iya da ba zasu zo makarantar kwana ba, musamman Nawfal da baya kaunar yaga yayi mishi nisa. Su Adee yaran shine, jinin shine, daga jikin shi suka fita. Ba zai karya ba suna da matsayin da za’a kai ruwa rana kafin wani ya taka shi a zuciyar shi.

Amman Nawfal, matsayin Nawfal abune da ba zai iya furtawa ba, babu kalaman da zai iya amfani da su ya misalta yanda yake jin Nawfal gab da zuciyar shi.

“Amana ta ne Julde, yaron nan amanata ne.”

Abinda Daada ta dinga jaddada mishi, abinda yake so ya kalli ba ita ba har kowa yanzun yace,

“Nawfal amanata ne, ni ya kamata Bukar ya ba amana…”

Saboda Nawfal ya fito daga jikin bukar ne kawai, amman dukkan wata kauna da uba zai yiwa dan shi itace yake yiwa Nawfal. Kuma yana godewa Allah idan yaga irin murmushin nan a fuskar Nawfal. Idan yaga yanda Nawfal yake nuna mishi ko duniya zata hade waje daya tare da mutanen cikinta in dai zata sake budewa to zai riko hannun shi a matsayin Uba.

Soyayyar da take tsakanin su mai girma ce.

Sai dai rubutacciyar kaddarar da take tsakanin su tana son danne girman soyayyar.

“Bajjo jiba idanuwan ka, kana ma cin abinci?”

Dariya Nawfal yayi me sauti.

“Baka ga yanda Adee ta koma ba.”

Kallon su Adee tayi.

“Rabon da in koma wani abu anfi shekara uku, ina nan yanda nake… Da gaske idanuwan ka sun rame.”

Akwatin shi daya tashi daga kai yake kokarin dauka kafin Julde ya karasa ya karba, baiyi musu ba ya sakar mishi. Ko siyayya ya fita dasu shi yake rike ledojin, duk yanda zasuyi su karba zai ce,

“Yaushe hannuwan ku zasu iya daukar wannan kayan. Da nauyi sosai.”

Da akwatin Adee ya hada ya saka su bayan motar.

“Yanayin abincin ka ya sa bana son ka da makarantar kwana Nawfal, nasan wahala zaka sha.”

Gaban mota Nawfal ya bude ya shiga. Adee ta hau baya. Daddy ya zagaya ya zauna mazaunin direba ya rufe murfin. Har ya tayar da motar ya juya yana mitar yanda Nawfal din baya cin abinci duk ya rame. Murmushi kawai Nawfal yayi.

“Ina ci fa Daddy, dan baka gani na kullum ne shisa…”

Kai Julde yake girgizawa, ko satin daya fita da yazo ganin su bai ga yayi zuru-zuru haka ba. Shiru kawai Nawfal yayi, dan baisan me zaice ba. Julde baisan cewa yafi koshi a makaranta fiye da gida ba. Tunda yana da zabin na yaci abinda aka dafa ko akasin haka. Idan shinkafa da miya ne, ya amshi fara yana da kifin gwangwani zai juye a ciki yaci abin shi, wata rana zaici snacks. A gida bashi da wannan zabin, akwai kifin gwangwani da Daddy kan ce saboda shi yake siyowa. Kamar kuraye haka su Khalid suke akan nama, shine kawai bayacin nama Kwata-kwata.

Ba allergy bane ba, kawai bayajin zai iya cin nama tun yana da karancin shekarun shi. Da yagan shi a cikin miya ma hankalin shi tashi yake, daga kaza har sauran nau’in nama. Baisan a shekarun yarintar da ba zai iya tunawa ba ko yaci, iya wanda zai tuna kawo yanzun baya hada hanya da duk wani abu nama. Amman kifin nan bai isa ya taba ba. Idan danyene aka kawo dan ayi miya. Nanna zata sarrafa shi yanda zai zama haramiyar shi. Shisa bai taba saka rai a duk wani abu da saiya fito ta hannunta sannan ya iso wajen shi ba.

Idan Adee tazo hutu yana jin dadi, yana cin abinci da miya, da kanta take shiga kitchen tayi mishi miya ta kuma juye a rubber ta kai mishi dakin shi.

“Me yasa kike haka Nanna?”

Shine tambayar Adee duk idan Nanna tayi kokarin hanata. Wasu ranakun harda duka amman ko bandaki Nanna ta shiga sai tasan yanda tayi ta kaima Nawfal din wani abu da zaiji dadin shi. Kifin gwangwani kuwa ita da Khalid suna diba su kai mishi ya ajiye a dakin shi, Khalid da dai-dai zai dauka. Adee zata iya daukar kwalin gabaki daya, wata rana nata na makaranta randa ta dawo hutu take zuwa ta kai mishi. Kamar bata ci kwata-kwata tana tarawa ne don shi. Kananun abubuwa irin wannan yasa yake jinta har ran shi.

“Ka daina jira sai Nanna ta baka abu, idan kagani kana so ka dauka ka tafi abinka.”

Ta kan fada mishi wasu lokuttan idan ta kai mishi wani abin. Sai dai yayi dariya, baya son tashin hankali sam, duk wani abu da zaiyi ya gujema fadan Nanna zaiyi, wani lokacin zai rantse ganin shi kawai harzuka matar yakeyi. In ba Daddy yana nan ba baya shiga bangaren ta. Ko yunwa zata kusan halaka shi daya leko ta window yaga tana falo saiya koma, in Khalid yana nan zai mishi magana ya zubo mishi abinci. Idan baya nan kuma zaici duk abinda yake da shi a bangaren shi.

Yanzun ma da suka karasa akwatin shi yaja zuwa zai nufi na shi bangaren.

“Kamar jira kake Nawfal? Ba zaka shiga kaga Nannar taka ba?”

Murmushi yayi.

“Daddy nagaji, zan watsa ruwa tukunna…”

Kai kawai Julde ya daga ya rufe bayan motar yana daukar akawatin Adee da tayi saurin kamawa tana fadin,

“Bajjo zaka ba, akwai wasu kayan shi a ciki, idan ya kwashe naje in dauka.”

Ta karasa maganar tana kallon Nawfal da fuskar shi take dauke da alamar tambaya. Kai ta dan daga mishi, cikin sanyin jiki ya karaso yana jan akwatin nata ya hada da nashi ya nufi bangaren shi. Ita da Daddy suka wuce cikin gidan tana bashi labarin da bashi da kan gado dan kar ya tambayeta wanne kayan Nawfal ne a akwatin ta.

***** *****

“Takardun meye wannan?”

Saratu ta tambaya tana rarraba takardun a tsakanin hannuwanta, a karo na babu adadi tana jin takaicin rashin ilimi, daya daga cikin rashin gatan da maraici yayi mata. Duk da boko ce karshen abinda aka damu dashi a inda ta tashi, amman ko bakomai an sa taje makarantar allo, babu wanda ya damu da yanda rayuwarta zata kasance.

“Takardun filayen Bajjo ne za’a siyar da wasu a sai mishi gida.”

Wani abu taji ya taso da ba zata ce ga daga inda yake ba, amman dacin shi har akan harshen ta. Filaye Julde yace, hakan na nufin ba daya ba ba biyu ba tunda yana kiran wasu daga ciki za’a siyar a sai mishi gida.

“Yana da dukiyar shi Saratu, Nawfal na da dukiyar da tunanin ki ba zai taba hangowa ba. Ba taimaka mishi nake ba dan ina biya mishi kudinn makaranta, ganin dama ta ne kawai…”

Kalaman Julde suka dawo mata wani lokaci can baya da tayi tsegumi akan yanda zaman Nawfal din yake karin nauyi akan shi. Ba zata daina wahalar da kwakwalwar ta wajen tunanin inda Bukar ya samu arziki har haka ba. Bukar fa, Bukar dai daya bar kauyen su da sunan zuwa neman ilimi. Tsoron kar tunanin ta yayi karadin da wani zaiji shisa take tausar shi, amman akwai ayar tambaya mai girma akan wannan kudin da Bukar yabar wa Nawfal kamar yanda akwai babbar tambayar da kowa yaki yarda ya furta akan asalin haihuwar Nawfal.

“Dukiyar Nawfal bata karewa ne? Har nawa yake da…”

Sauran maganganun suka koma mata saboda yanayin juyawar da Julde yayi yana kallon ta.

“Meye matsalar ki da dukiyar shi? Sanin yawan ta amfanin me zaiyi miki?”

Kauda kai tayi gefe, abinda take ji yana kara ninkuwa, wannan dukiyar da yake kira Nawfal na da ita da su Salim take hangota, duk wani jin dadi da yake gidan duniya rayuwar yaranta take hangowa a ciki.

“Su Khalid ma ya kamata ace suna da gidajen su yanzun tunda kana da halin.”

Karamin tsaki Julde ya ja kafin ya taka ya fisge takardun da suke hannunta yana mayarwa cikin jakar shi. Bai san me yasa daya dawo hannunta kan jakar shi yake fara sauka ba, sai kuma ta dame shi da tambaye-tambayen da bayaso kan duk wata takarda da zata gani kamar ya aiketa.

“Duk takardar da zaki gani in ba zaki iya karantawa kiji ko ta mecece ba karki sake damuna da tambaya.”

Maganganun shi sunyi mata zafi ba dan kadan ba, duk da ba yau bane rana ta farko da yake amfani da duk damar da zai samu na goranta mata rashin ilimi kamar laifin nata ne. Karatun hausar da ya koya daga bayane da dan kalaman turanci daya tsinta akan titi suke kara bashi damar zaginta haka.

“Ka sama mun makaranta ko ta yaki da jahilci ce…”

Ta furta cikin wata irin sanyin murya. Sosai Julde ya kalleta wannan karin kafin ya kwashe da dariya yana girgiza kai kawai. Har ranshi dariya ta bashi. Duk tsayin shekarun nan batayi tunanin shiga makaranta ba sai yanzun? Saboda tana son saka ma shige da ficen shi idanuwa fiye da yanda takeyi yanzun. Takardun shi ya mayar tsaf ya gyara ya karasa yana samarwa jakar waje ya ajiye. Fita yayi daga dakin baccin nasu zuwa falo yana jin motsin Adee a kitchen, hakan yasa shi tunkarar kitchen din ya kuwa ganta tana wanke-wanke.

“Sannu da aiki…”

Da murmushi a fuskarta ta juyo.

“Daddy Am… Ba wani aiki bane ba fa.”

Kai ya jinjina, komai ma in dai ya danganci hidimar cikin gida amsa daya Adee zata baka, dan wajenta ba aiki bane ba, har mamakin kokarinta yakeyi a kankantar da take da shi, gashi sanyin halinta baisa tana da sanyin jiki ba.

“Ni ma zan leka Daada ne.”

Wannan karin fuskarta cike da roko tace,

“Dan Allah zanje… Saura kadan in karasa…”

Dan jim Julde yayi sannan ya amsa,

“Bari to in duba su Khalid, nasan zasuje suma sai su shirya duk mu fita gabaki daya.”

Murmushi tayi har hakoranta suka bayyana kafin ta juya kamar tana son kara sauri wajen ganin ta gama da wuri. Ficewa yayi daga bangaren nasu gabaki daya yana nufar nasu Khalid. Hannun kofar ya kama ya murza yana shiga da sallamar da Nawfal ne ya koya mishi yinta a ko ina zai shiga.

“Daddy baka yi mun sallama ba ka shigo.”

Ya kan fadi har saida ya saba da yin sallamar da a baya bata dame shi ba, kai tsaye yakan tura kofa ya shiga waje. Yanzun kam a kasuwa ko shagon wasu zai shiga da yake a bude sai yayi sallama, yana ganin yanda hakan ke siya mishi kima a idanuwan mutane da yawa. Ba kowa a falon sai Salim da ya kara shigewa cikin kujera kamar yana son hadewa da ita, tv nata aiki amman babu sauti hakanne ma yasa Julde jin sallamar shi da Salim ya amsa can kasan makoshi. Idan wani da baisan yaron ba yagani zai dauki hakan a matsayin rashin girmamawa. Kuma a wajen Salim ba haka bane ba, yawancin maganar shi duk daga kasan makoshi take fita da yanayin kamar an mishi dole dauke a fuskar shi.

“Daddy…”

Nawfal daya fito daga dakin baccin shi jin sallamar Daddy ya kira yana dorawa da,

“Ina kwana”

Murmushi Julde yayi.

“Lafiya kalau, kun tashi lafiya ko?”

Kai Nawfal ya jinjina .

“Ina Khalid? Ku shirya muje gidan Daada, amman ba kwana zakuyi ba.”

Dakuna fuska Nawfal yayi.

“Da ma ina so inje fa Daddy, munyi maganar zuwan da Adee.”

Kai Julde yake girgizawa.

“Kwana daya to, dan Allah, gobe idan ka dawo kasuwa saika biyo ka dauke mu.”

Numfashi Julde ya sauke yana dai-dai da lokacin da Salim ya fitar da wani sauti dake nuna alamar hirar su ta takura shi yana kara shigewa cikin kujera. Murmushi kawai Julde yayi.

“Ku shirya to.”

Sai da Nawfal ya jinjina mishi kai tukunna ya juya yana fita hadi da ja musu kofar. Nawfal kallon Salim yayi, baisan lokacin daya yanke hukunci dawowa bangaren da kwana da yini ba. Shima tunda yazo hutun nan yagan shi, kafin kaji hirar Salim zaka dade, zai iya tashi da safe baice wa kowa komai ba, ko hanya ta hadaku wucewa zakaga yayi kokarin ganin ya kauce karma iskar da kuka kwaso ta hadu da ta juna, magana ma idan yanayi kamar bakin shi cike yake da harshe saboda yanda take fitowa.

Nawfal zai iya cewa duk da Salim na cikin mutane shi kadai yake rayuwar shi, ko kasa shi cikin harkar ka da wahalar gaske ya shiga. Duk wani abu da zaisa ayi rikici Nawfal na guje mishi, shisa tunda ya dawo yaga Salim a bangaren da yake kira nashi ya daina zaman falo sam, akwai tv a dakin shi idan kallo yake son yi, shima zai saka sautin dai-dai kunnen shine kafin Salim yazo ya kwankwasa mishi yana fadin,

“Ka rage volume din TV dinka Bajjo yana shigar mun kwakwalwa.”

Duk wani surutu ma shigar ma Salim kwakwalwa yake kamar kunnen shi yafi na kowa ji.

“Anya Hamma Salim ba vampire bane ba?”

Khalid ya taba tambaya bayan ya baro dakin shi a bangaren Nanna ya same su a falon da tazarar shi take wajen taku goma harma da wani dan sirqakon lungu a tsakani yana watsa musu wani irin kallo.

“Me yasa ba zakuyi magana irin ta mutane ba? Ta ya mutum zaiyi bacci kun cika gida da ihu?”

Hada idanuwa kawai sukayi shi da Khalid suka mike suna barin bangaren gabaki daya. A cikin su babu wanda zaice ga rana daya da Salim ya taba lafiyar jikin su, amman akwai marin da yayi wa Adee kan tana wanke-wanke tana kida da cokula a cewar shi. Amman dukkan su suna shakkar Salim din. Nawfal ya juya zai koma inda ya shigo Khalid ya bankado kofar yana fadin ,

“Wai kasan wa nagani ku…”

Maganar ta koma mishi saboda idanuwan shi da suka sauka cikin na Salim da ya dage girar shi duka biyun, ko dan girar Salim kusan kullum a sama take, kamar baya sauke ta, hannuwa Khalid ya daga cikin ban hakuri yana motsa labban shi batare da yayi maganar da sauti ba yace,

“Yi hakuri”

Yana takawa a hankali ya karasa inda Nawfal yake ya tura kafadar shi suna nufar dakin baccin Nawfal din da kamar jira yake Khalid ya tura kofar dariya ta kubuce mishi.

“Ban san vampire na zaune a dakin ba ai.”

Khalid ya fadi da alamar dariya a muryar shi, har mamakin ji irin na Salim suke yi.

“Daddy yace mu shirya zamu je gidan Daada.”

Nawfal ya fadi har lokacin da alamar dariya a muryar shi.

“Ni ai nayi wanka…”

Kai Nawfal ya jinjina.

“Nima nayi wanka, ban dai ci komai bane ba… Zan karya a gidan Daada kawai.”

Da gabaki dayan su suke karyawa a bangaren Nanna din, yanzun tunda kowa ya fara girma sai suke zaben lokacin yin karin idan ba ranakun makaranta da Julde ba zai bar su fita basu saka wani abu a cikin su ba ko yaya ne kuwa. Nawfal yana da kayan Tea din shi, akwatin da Adee ta bashi nata harda katon gwangwanin madara da bata fasa ba sai na Milo karami, da kifin wajen gwangwani ashirin. To kuma ma ya ga Salim ya sake kwaso wasu kayan tea din ya ajiye a kitchen din bangaren nasu, da kofuna da yawa ma da kananun kayan amfani, ya ga har gas din kitchen din an hada.

“To mu jira Daddy ya fito sai mu wuce…”

Cewar Khalid yana dorawa da.

“Nasan da Adee zamu je, Lukman dai ba zai bar Nannar shi yaje wani waje ba.”

Murmushi Nawfal yayi.

“Auta kam babu inda za shi.”

Suna nan zaune suna hira, ta window din dakin Nawfal da yake ta waje yake suka hango Daddy, kusan a tare suka mike suna fita.

“‘Hamma sai mun dawo.”

Khalid ya fadi, hannu Salim din ya daga yana musu alamar su fita. Dariya sukayi a tare suna ficewa, daman dan neman tsokana yasa Khalid yima Salim din magana. Har wajen motar Daddy suka karasa kusan a tare da Adee da take sanye da riga da wandon da zaka iya gani saboda hijabinta iya gwiwa ya tsaya, ta rataya jaka a gefe sai robar take away a hannunta.

“Dare yayi sanda na gama jiya…”

Ta furta tana mikama Nawfal robar da ya karba yana jinta da sanyi alamar a fridge ta kwana, dubawa yayi ta kasan robar yana ganin farfesun kifi ne ko miyar kifi, ba zai iya ganewa ba, ya dai san taliya aka dafa jiya da dare da miyar kifin da yasan ba zai iya ci ba dan yaga Khalid da ita, sanda ya shiga bangaren ma dan su gaisa da Daddy ne.

“Meye kika bashi ni baki bani ba.”

Cewar Khalid da ko inda yake Adee bata kalla ba. Yanzun da suka kara hankali Nawfal yasan Adee dare take bi idan Nanna tayi bacci ta dafa mishi abu irin haka. Hannun shi na dama da baya rike da robar da ta bashi ya dora akan kirjin shi inda yafi tunani zuciyar shi take dan nan yaji ya dauki dumi sannan ya daga hannun yana nuna Adee da tayi murmushi, yasan ta fahimta, bashi da kalamai in dai akan kulawarta ne, amman tana da waje mai girma a zuciyar shi, Allah yake roko daya bashi aron rayuwa mai tsayi a tare da Adee dan ya kwatanta biyan ta duka kirkin da takeyi mishi.

Su baya suka shiga shi da Khalid ita tana shiga  gidan gaba. Har lokacin da murmushi a fuskar ta

Bata san duka labarin Nawfal ba

Amman tana hasaso rayuwar ta babu Daddy da Nanna

Tana hango dararen kadaicin da take tunanin yana fama da shi

Ita din ko kusa da matsayi na uwa ba zata hango ba balle ta taka

Amman in dai tana numfashi zata sama ma Nawfal duk wani sauki da yake a karkashin ikon ta In dai har yaya mace na zama mahaifiyar da mutane ke fada zata zamewa Nawfal.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 2Rai Da Kaddara 4 >>

1 thought on “Rai Da Kaddara 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×