Skip to content
Part 47 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Kallon shi takeyi, sai take ganin kamar ta kalli mudubi, saboda tana da tabbacin tashin hankali da ciwon zuciyar da yake tattare da ita ne a tare dashi, irin abinda take ji ne shimfide a cikin idanuwan shi, kuma tana da yakinin idan akwai wanda yasan ciwon Madina bayan ita, to Nawfal ne, idan akwai wanda yake son Madina kamar yanda take son ta, Nawfal ne. Wannan tunanin ne ya bata kwarin gwiwar numfasawa ta ce masa.

“A karo na farko zan roke ka alfarma Bajjo, shekaru biyu na rayuwar ka zaka aramun duk da nasan ba’a hannun ka suke ba, ba gabaki dayansu ba, dan lokaci kadan a cikin kowacce rana ta shekara biyun, ba asirin Julde zaka taimaka mun mu rufe ba, ahalina, sauran ahalina zaka tayani karewa, kar abinda ya rabo mu da tushen mu ya sake nasara akan mu a karo na biyu…”

Wani abu ya gilma ta cikin idanuwan Nawfal din kamar walkiya, yana tabbatar mata da karo na farko da rokon alfarma ya gifta a tsakaninta dashi zai kafa tarihi, saboda zai juyo mata da bukatarta ne ba zai karba ba, ta runtsa idanuwanta ganin ya bude baki yana shirin amsawa, kamar tana so tace masa yayi shiru, tana so ta roke shi ya bata wasu yan mintina ta shiryama amsar shi, ta shiryawa kin amincewar shi, ta kuma tabbatar duk fatanta kaddara ta rigata, yanda duk ta hango shi karkashin inuwa daya da Madina, hakan ba abu bane da zai taba yiwuwa ko a halin nan da suka tsinci kansu

“Idan wannan ya zama dalilin da zan auri Madina, kamar ba ayi mata adalci ba…”

Maganar ta fito daga bakin shi tana dukanta, numfashi taja ta baki tana kokarin fitar dashi ta hancinta taji an kira sunanta can nesa

“Daada…”

Yanayin yanda aka kirata din kamar da rashin tabbaci

“Daada”

Wannan karin Madina ta kira tana kai hannu ta kama hannun Daadar don ta tabbatar ba mafarki takeyi ba, zuciyarta nayo tsalle ta dawo makoshinta saboda murna, a hankali Daada ta bude nata idanuwan, tana fara karewa dakin kallo, saita mayar da hankalinta kan Madina da take kokarin tashi zaune. Tsakanin gidan Julde, daga inda take tsaye tana kallon komai kamar bata da wata alaka da abinda yake faruwa saboda jikinta da yaki bata hadin kai wajen yin wani yunkuri, ko da na motsawa ne taga abinda yake faruwa, ta kafe a wajen kamar anan tushenta yake. Kafafuwanta da takejin kamar sunyi sanyi na sanar da ita dadewar da tayi a tsaye.

Sai dai tashin hankalin da take ciki ya girmi gajiya, ya girmi duk wani abu da kalmomi zasu iya misaltawa, shisa ta cigaba da binsu da idanuwa, tana nan likitan da Khalid ya fita ya kira ya dawo, ta gabanta suka kamo Julde suna wucewa dashi bangaren shi, bata motsa ba, duk kuwa da alamun da suke nuna kamar Julden baya numfashi. Sai dai akan yara wanne abune ya rage da bata gani ba? Kaddarar ma da bata taba hasashen faruwarta ba yau alamu suna nuna ta faru, idan mutuwa Julde yayi ba zatayi mamaki ba.

Bayan yaran da ta haifa suna komawa, har bayan ta samu Bukar, baisa ta daina kallon Julde kamar zata iya rasa shi ba shima, Bukar da Yelwar ma da ta kwallafa rai akansu suna ina yanzun? Ji take ya kamata ace ma indai akan ‘ya’ya ne ta jima da sallamawa, ta jima da mika wuya saboda ita sune kaddararta. Sai dai ya kaddarar zata juya mata haka? Ya zata zagayo ta soma yiwa jikokinta dauki dai-dai? Anya tana da zuciyar daukar wannan kuwa? Tana jin abinda yayi mata saura a cikin kirjinta yayi rauni, bashi da karfin daukar koma menene yake faruwa.

“Daada”

Khalid ya fadi yana tabata, yanayin fuskar shi kuma data kalla na tabbatar mata ya dade yana kokarin rabota da inda tunani ya dauketa ya watsa.

“Daddy nata kiranki”

Kallon shi tayi tana nuna masa alamar labbanshi kadai taga sun motsa, amman abinda ya fada bai karasa kunnuwanta ba.

“Daddy ya farka yana kiranki.”

Ya fada da fulatanci wannan karin, ganin dai kallon shi takeyi yasa shi kama hannunta yana juyawa, batayi musu ba, tayi mamakin yanda ta iya motsawa tana bin bayan Khalid din har dakin da Julde yake ta kokarin tashi zaune likitan da kuma Saratu nata hanashi.

“Naji muryar Daada, naji sallamarta, ku barni inje in sameta.”

Yanayin yanda yake maganar zai tabbatar maka da ba’a cikin hayyacin shi yake ba. Yana kuwa ganin Daada ta shigo dakin ya sake zabura yana kiran sunanta, waje ta samu tayi tsaye tana kallon shi.

“Daada banyi mata komai ba, bansan meya sameni ba, wallahi bansani ba, bansan meya sameni ba.”

Ya karasa maganar muryarshi na sauka kasa tare da kanshi daya saddar kamar wanda ya fada cikin zurfin tunani, dagowa yayi lokaci daya kuma yana kallon Daadar.

“Me yake damuna?”

Yayi tambayar da nauyi cikin muryarshi, wani irin nauyi da Daada taji ya taba zuciyarta. Kallonshi takeyi ko zataji tsanarshi a ranta, amman babu komai banda tsanar halayen shi, shidin yana nan daram a zuciyarta, asalima duka laifukan shi take so ta dauka ta dora akan Datti, tayi amfani da kaunar da ya nuna musu, ta kuma fake a bayan bakin daya dinga bin Julde dashi, tayiwa danta uzuri, ta rage laifinshi a idanuwan duniya, ta roka masa gafara a wajen Allah kamar yanda takeyi a duk rana, dan nata bangaren babu wani abu da zaiyi ta kasa yafe masa, koya ranta ya baci dashi kuwa, ko da a cikin wannan laifukan akwai layin nan da yake tabbatar mata bai tsallaka ba yanzun.

Da gaske babban kuskuren da al’umma sukeyi shine dora laifukan yara akan mahaifiyarsu, saboda a duniya duka babu wata uwa data ke so ace yau danta ba nagartacce bane, ko da kuwa ita akwai ayar tambaya a tata nagartar. Kowacce uwa fatanta ace idan an jera yaranta cikin sauran yara ya kasance shine yafi kowa, kyau, kyan hali da komai da komai. Dan tayi kokarin boye laifinshi baya nufin tana goyon bayan wannan hanyar lalacewar daya dauka, tana kokarin boyewar ne don zuciyarta ta rage mata nauyin da takeyi, tana kuma yi masa uzuri kome ya akaita saboda shine zabin karshe da take dashi, tana ganin yanda kowa yake aibata shi, kowa yake kyararshi, ya ake tsammanin itama tabi sahu bayan batasan komai ba daya wuce kare shi daga duk wani abinki?

Ko bayan kwanaki a cikin satika, satika a cikin watanni, laulayi, kwanciya dakyar, tashi dakyar, rayuwa a cikin wata rayuwar da mai ciki ce kawai zata fahimta, awanni a dakin nakuda, duk wannan wahalar ana dora mata shi a hannunta abu na farko da yake zuwa ranta shine tabbatar da yana cikin kishin lafiya koda ita batajin wannan lafiyar a tare da ita, daga ranar komai na rayuwarta zai biyo bayan nashine, duk wata bukata da take da ita a kasan tashi take. Kuma sai ace tana so ta ga ya lalace? Ko da ta sake shi, ko da ta sangarta shi, ko da akwai nakasu a yanayin tarbiyar da ta bashi, a cikin zuciyarta tafi kowa son ganin ya kasance nagartacce. Wannan kaunar ta tsananin mahaifiya da yaranta babu wanda zai fahimta sai wata mahaifiyar.

Ko yanzun da take tsaye so take ta karasa ta rike shi, gani takeyi kamar yayi zuru-zuru, duk ya rame, amman wani abu ya rike mata kafafuwa, kallon shi takeyi kamar yanda shima yake kallonta, hakan ya ba likita damar yin allurar baccin da Julde yaki tsayawa ayi a cikin karin ruwan da akeyi masa, cikin wasu dakika ta fara aiki, jikinshi ya fara yi masa nauyi, dole ya kwanta, kafin wani lokaci bacci ya dauke shi.

“Yana bukatar bacci don jininshi da ya hau ya sauka.”

Likitan ya fadi yana yi musu bayanin dalilinshi nayin allurar baccin. Hannu Saratu da take zaune a gefen gadon ta kai tana dauke kwallar da take cikin idanuwanta. Juyawa Daada tayi, Khalid ya rufa mata baya, ganin tanayin hanyar waje ya sashi fadin.

“Bari in dauko Madina sai inzo in kaiku gida.”

Hakan kuwa akayi, idonta kur akan Khalid daya sabo Madina zuwa mota ya kwantar da ita a baya, itama bayan ta shiga tana daga kan Madina ta kwantar a jikinta, kamar bacci takeyi, tayi wani irin luf da ita, jikinta nade da zanin gado, kanta ne kawai a waje. Ko da tana yarinya bata da yawan rashin lafiya, hakora ma kanta ne kawai yake zafi, sai wasu ranakun idan ka taba jikinta zakaji akwai alamun zazzabi, amman wannan wahalar duka Madina batayi ba.

“Baki taso da uwa a kusa dake ba Madina, sai Allah ya dubaki komai yake zo miki cikin sauki.”

Daada ta tuna kalamanta bayan Madinar tayi wata kyanda da bata hada sati daya ba, ba kuma ta wani kwantar da ita yanda take yiwa sauran yara ba. Da ta fara girma, idan zatace kanta na ciwo ko cikinta, zai wahala ta tashi da safe ta sake maimaita wannan maganar, idan ta tambayeta ma zata ce.

“Tun jiya ne Daada, da na sha magani nayi bacci yau ban tashi dashi ba.”

Shisa ganin yanda Khalid din ya sabota yakeyi mata wani iri, haka da suka karasa gidama. Mukullan gidan kowa yana dashi ita da Madina, nata kuma yana tare da ita, don dakyar ta bawa Nawfal riko lokacin tafiyarsu, suna kuma sauka Abuja ta tambaye shi.

“Daada kamar wanda zai gudu da mukullin nan? A asibiti ma fa wajen sau hudu kika tambaya.”

Dariya ta yi.

“Mukulli na da tsautsayi, kai ka batar mana da guda daya, daga baka ko da zaka zo bama nan.”

Kai Nawfal ya dafe.

“Akan batan mukullin daya faru wajen shekara goma har yanzun banyi hankalin da za’a yarda zan iya ajiye wani ba, ai shikenan…”

Ya karasa yana zuwa ya dauko mukullin ya danka mata, ta saka a yar jakar da take makale da ita. Wani irin takeji ganin yanda duk inda akayi da Madina take bi saboda alamu sun nuna batasan inda kanta yake ba, kan kujera ya shimfidar mata da ita yana fadin.

“Likita ya dubata itama, yace babu abinda yake damunta, bacci takeyi zata tashi zuwa wani lokaci.”

Kallon Khalid din tayi, sai taga kamar yana kokawa da wani abune, yana kokarin danne abinda yakeji don yaga kamar su duka suna bukatar wanda zai tallafe su a wannan yanayin da suka tsinci kawunansu.

“Bakomai kaje kayi hidimarka Khalid…Allah yayi maka albarka.”

Kai ya jinjina.

“Idan kuna bukatar wani abu sai ki kirani Daada, zan dawo ma zuwa anjima In shaa Allah.”

Wannan karin ita ta jinjina masa kai, saida ya fita take karewa falon kallo, ya kamata ace akwai kura tunda an kwana biyu bakowa, abinda bata sani ba shine duk kwana biyu sai Madina tace Salim ya kawota, ranar farkon ta dade, data dawo yake ce mata.

“Tun dazun, kin barni ni kadai tun dazun.”

Da ta sake dawowa kuwa tare suka shiga, daya fara shara kaman abin kirki ya ajiye mata tsintsiyar.

“Ni bana son shara Allah.”

Ya fada, dan dakin shima yana kokarin ganin kome yaci bai zube yanda zaiyi shara ba, idan abune ya shiga dashi, yana gamawa yake tattara ledojin ya fito dasu. Daya yi barin shinkafa kwanaki zama yayi ya mike kafa ya fara tsincewa, haka Khalid ya shiga ya same shi.

“Bari kayi?”

Bai magana ba, irin wannan tambaye-tambayen ne na Khalid baya so, abu yana gabanshi, ya gani amman saiya sake maka tambaya akai.

“Shinkafar zaka bi ka tsince da dai-dai Hamma? Maimakon ka share?”

Numfashi yaja yana fitarwa.

“Bana son shara, ka kyaleni Khalid, me ma kake nema ka shigo mun daki kayi tsaye kana damuna da magana?”

Dariya Khalid din yayi, karshe shine ya share masa, sai yayi sati bai share daki ba, kome ya zuba zai tsince. Shisa Madina take bashi mamaki, ta tattara duka natsuwarta sai shara takeyi, waje ya samu ya dinga kallonta harta gama. Haka duk zuwan da zasuyi, tayi shararta, tayi goge-goge yana zaune, idan yaji kamar bashi da wani amfani ne ma zaice mata.

“Kawo in fasa miki omon.”

Ya kuwa bata dariya ranar, ko kuma ya ce,

“In kara dibo miki ruwa?”

Idan ta gaji ne za ta ce.

“Hamma kayi zamanka, ai kayi babban aiki tunda ka kawoni, kuma zaka mayar dani, gashi kanata tayani da idanuwanka ma.”

Daman dan kar taga kamar bai tayata bane shisa yake magana. Ai kuwa gidan ko ina tas, dan da ta shiga tayi sallar azahar kamar bataje ko ina ba, sai dai sau daya Madina ta motsa. Khalid ya dawo kamar yanda yace, da ledojin da inda ya ajiyesu nan suke har zuwa yanzun. Anan falon tayi la’asar da alwalarta ta azahar da take rike da ita. Da Madina bata motsa ba zata kira wani ne yazo ya taimaka mata su kaita asibiti, ko a kira likita ya sake dubata. Tunani babu irin wanda Daada batayi ba, tasha babu wadda bata kama ba, sai dai inta kama din subuce mata takeyi.

Wannan ciwon da tayi ta dauka karshen rayuwarta ne yazo, duk da Bukar da Yelwa suka cika tunaninta a lokacin, Madina saita danne su, saboda a wajen Madina itace komai, itace matsayin mahaifi da mahaifiya, bata taba tunanin zata roki Allah ya kara ara mata wasu shekaru a duniyar da ba dadin zamanta takeji ba sai saboda Madina, saboda tana son ganin wanda zai mayewa Madina gurbinta kafin tabarta. Tasha hango Nawfal ne zaiyi wannan aikin, sai yazo da maganar aure, sai kuma ta ganshi da Murjanatu a India, taga yanda yake kallonta kamar bashida sauran wajen da Madina zata zauna a rayuwar shi.

Sai kuma ta ga yanda Murjanatun take kallon shi itama, yanda ko abinci ne saita fara ci kamar tana son dandana zafin shi a harshenta kafin ta mika masa, duk da haka idan akwai wani abu a kusa da ita da zaiyi fifita zaka ga ta dauka tana sake fifita masa abincin sanin bayason shi da zafi, tunda tazo ita take fita tayi abubuwa da yawa shi yana tare da ita. Idan kifine zaici, zata wanko hannunta ta zauna ta zare duk wata kaya da idanuwanta zasu iya gani kafin ta mika masa. Soyayya ba bakuwar Daada bace ba, bayan Hammadi da Abu, itama ta taba kalar tata soyayyar, yaranta kuma sun sake nuna mata indai soyayya ce suna cikin wanda Allah ya zaba ya kadartawa ita a filin duniya.

Tun a asibitin saita cire rai, saboda Nawfal ya rigada ya gama samun abokiyar rayuwa, amman yau, tana so ta roke shi, tana so tayi masa magiya ya dan matsar da Murjanatu ya samarwa Madina wajen zama, saboda yanda bata taso kusa da iyaye ba, haka shima, sunfi kowa cancanta da su kula da junansu. Wannan zaren take ta sakawa tana warwarewa batasan bacci ya dauketa ba, a cikin baccin harda mafarkin ta roki Nawfal din kuma yaki amincewa, in ba mafarkin ba, ita da take hasaso su karashe rayuwarsu da juna, me yasa zata roke shi shekaru biyu?

“Daada”

Madina ta sake kira, tana murza idanuwanta wannan karin, gilashinta da yake gefe da Khalid ya bawa Daadar ta dauka tana mika mata, sakawa tayi ta kalli Daada, idanuwanta cike da tarin tambayoyi wannan karin, tana kuma saka bugun zuciyar Daada karuwa saboda bata san me zatace mata ba.

“Jikina yayi mun nauyi kamar nayi kwanaki ina bacci…”

Ta karasa maganar tana zaro jikinta daga bargon da take ciki, sai dai jikin nata ta kalla, ta rage kayanta kafin ta kwanta, tana da wannan yakinin, amman ba zata taba fitowa haka ba, kanta yayi nauyi na gaske, girgiza shi tayi a hankali tana dafa kujerar ta mike, duk wasu tambayoyi zasu iya jira ta watso ruwa ko zata dawo dai-dai. Harta taka saita dawo ta rankwafa tana riko Daada jikinta.

“Daada nayi kewarki sosai, kamar in biyoku wallahi.”

Yanda ta sauke wallahin muryarta na karyewa da alamun kuka zatayi yasa Daada saurin fadin.

“To ba gani na dawo ba, kije ki watso ruwan ki fito, kinga abinci Khalid ya kawo mana tun dazun nake jira ki tashi muci.”

Raba jikinta tayi dana Daada dakyar, tana kai hannu ta kasan gilashinta ta goge kwallar da taji ta tarar mata.

“Yanzun zan fito.”

Cewar Madina tana nufar dakinta cikin hanzari, Daada ta bita da kallo, wani abu na hadewa a cikin kirjinta.

Kamar lokaci ya yi.
Lokacin da zata amsa tambayoyin da Madina bata taba bude baki ta furta mata su ba…

*****

Comments da likes din karku gaji, idan kunyi like ku daure da comment din, sai mu koma whatsapp mu sha hirar acan, na fada zan kara tuni ne kawai, da su zan samu a biyani. Na gode da tarin goyon bayanku.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.2 / 5. Rating: 12

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 46Rai Da Kaddara 48 >>

1 thought on “Rai Da Kaddara 47”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×