Skip to content
Part 25 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

In da wani yace kafafuwan shi zasu sake daukar shi zuwa kofar gidan su Dije zai karyata. Ya hakura da ita, shine abinda ya gayama zuciyar shi daga lokacin da Allah ya nuna musu cewar basu isa su cire cikin da yake jikinta ba. Tun tana mishi aiken yara a boye har itama ta hakura. A wajen Hammadi yaji maganar haihuwar ta.

“Dije ta sauka lafiya, ta samu da namiji.”

Kalaman suka bi ta cikin kunnen shi suna sokar wani abu a kirjin shi da yaji zafin shi ya gauraye ko ina na jikin shi, yawun daya hadiya mai daci ne, dacin da bashi da kalaman da zaiyi amfani da su wajen misalta hakan. Bai furta komai ba, Hammadi ma bai sake ce mishi wani abu ba. Ranar daya koma gida, sanda ya shiga ya dauko Julde a wajen Abu yayi bacci, kwantar da shi yayi yana kwanciya a gefe, yanda yaga rana haka yaga dare, tunani babu wanda baiyi ba. Alkawurra kala-kala na rabuwa da Dije babu wanda baiyi ma kan shi ba.

Hanyar duk da yasan idan yabi zai ganta dainawa yayi, sau daya Abu ta ce masa.

“Da ka dawo da Dije dakin ta Datti.”

Numfasawa ya yi.

“Dan Allah Adda karki kara mun zancenta, na rigada na hakura, Allah ya hada kowa da rabon shi.”

Kuma Abu har kwanan yau da yake tsaye kofar gidan su Dije bata sake tayar masa da zancen ba. Kowa ya dauki idanuwa ya saka mishi, tunda shi yake azabtuwa da kadaici da kuma wata irin kewar Dije kamar zaiyi ihu, amman a gefe kishinta da yake ya danne komai, sanin ta hada shimfida da wani harda rabo ya shafe mishi komai, har safiyar yau daya dora idanuwan shi a kanta, ita bata ganshi ba, ta fito daga gidan Mamuda, amman shi ya ganta, ya kuma koma baya da sauri ya shiga kwanar daya fara cin karo da ita, zuciyar shi a cikin makoshin shi saboda tsallen da tayo.

Ta kara kyau, tayi kyau kamar bata jin rashin shi a kusa da ita, ko da yaje gona bai iya wani abin kirki ba yace ma Hammadi kan shi na ciwo ya koma gida ya kwanta. Ana idar da sallar isha’i yasan cewa koya ake ciki saiya ga Dije, in bai ganta ba sam ba zai iya runtsawa ba, shisa yayo kofar gidan su, ya kuma aika aka kirawo ta, ta dauki wasu mintuna da yake jin su kamar awanni kafin fa fito, da alama bata san kowaye ba, yanayin da yake fuskarta ya nuna hakan.

“Dije…”

Ya furta yana kuwa sa ta dube shi, duba na tsanaki, nan take hawaye suka cika mata ido. Yanda yayi ma kanshi alkawurra daban-daban a bangaren Dijen ma hakane, ko Autan maza ne shi ta hakura da shi, haka ta fadama kanta, haka kuma ta fadawa Abu randa tayi mata zancen shi, wacce wahala ce bata sha akan Dattin ba? Wanne aike ne batayi masa ba a tsayin watannin nan, kafin ta haihu duk kuwa da fadan da tasan zata iya sha idan Baba yaji ta tsaya da shi, bayan ta haihun ma haka, yayi biris da ita, amsar kirki ma bata samu ba daga wajen shi.

Watanni goma sha daya kenan da haihuwar ta, idan aka hada da watannin baya, kafin haihuwar shekara daya da wasu watanni da lissafin su yake hango shekaru biyu. Rabon da ta saka shi a idanuwanta, rabon da taji muryar shi cikin kunnuwanta. Da bata da Bukar a kusa da ita fa? Bukar da murmushi kawai zaiyi sai taji duk wata damuwa da take zuciyarta ta kau, Bukar da tun da cikin shi ya kamata ace ta gane cewa ko da tana da rabon wasu yaran a gaba zai kasance daban a cikin su, zai zama wata fitila da zata haska rayuwarta a duk wani duhu da zata shiga.

Hakorin nan da yara suke shan wahalar shi, hakorin da ta kusan fidda rai akan Julde lokacin da yayi shi, dariya Bukar yayi ta ganshi a bakin shi.

“Allah ya bashi sadaka.”

Cewar Innar A’i, sai dai mene ne ma Allah bai bawa Bukar dinta ba? A watanni goma sha daya, idan kofin ruwa ne Bukar ya kai hannun shi a kai kokarin shi yaga ya bata ta fara sha, ko cikin gidan wani ya bashi yar alawa sai dai taji yana kokarin saka mata a bakinta.

“Allah ya aramun rayuwa mai tsayi tare da kai Bukar.”

Ta kan furta idan yayi wani abin daya girmi watannin shi, saboda haka kawai take ji a jikinta kamar ba zata samu wani lokaci mai tsayi tare da shi ba.

“Dije…”

Datti ya sake kira yana katse mata tunanin da takeyi yana kuma ba hawayen ta damar zubowa, juyawa tayi duk da tasan yaudarar kanta takeyi, koya tsayar da ita, ko bai tsayar da ita ba ma ba zata iya kara wani taku akan wanda tayi ba.

“Dije dan Allah.”

Ya furta muryar shi cike da wani irin rauni da ya sake saka hawayenta zubowa.

“Na sake wani kuskuren ko?”

Juyowa tayi, ta kasa magana, ko zata iya maganar ma bata san me zata ce ba.

“Kishin ki ya yi mun yawa, akwai dararen da nake jin kamar numfashina zai tsaya idan na tuna kina da wani yaron da ba nawa ba…ya zanyi? Ya zanyi ne Dije? Ya zan kalle ki ba zanga yaron da kika samu batare da ni ba.”

Kuka takeyi sosai zuwa yanzun.

“Idan zaki iya sake zama dani ina so in sami Baba.”

Ya karasa maganar zuciyar shi cike da tabbacin har yanzun idan ya rufe idanuwan shi ya yawata cikin tunanin shi ba ya hango shi tare da kowacce mace da ba ita ba, ta ina zai fara? Ita din dai, Dijen shi da duk wasu halayen shi ta sani, ta saba da su kamar yanda ya saba da hakurin ta.

“Idan kika ce a’a ban san ya zanyi ba.”

Kai ta daga mishi, ta kasa magana saboda kukan da takeyi, duk abinda ta fada yaudarar kanta takeyi, bata kara tabbatar wa ba sai yanzun da yake gabanta, take jin kamshin turaren nan da yakan siyo duk ranar kasuwa, turaren da bata taba jin shi tare da kowa ba sai shi, kewar shi take ji har cikin kasusuwan jikin ta. Tasan kowa ma ba zai kiya ba, zazzabin kwana biyu Bukar yayi yana da watanni goma cif, saiya yaye kan shi, juyin duniya yaki kama Mama, kowa sai yace ta kyale shi kawai tunda babu abinda baya ci, kamar ya hango mata dawowar Datti shisa ya saukaka mata komai.

*****
Dangin Dije, wanda suka dinga kwashe ma Datti albarka ana zayyane duk wani mugun halin shi da suka sakani bayan ya sake ta, saboda hango yankewar alherin da yake giftawa a tsakanin su da sukayi, yanzun kowa sai karyata kan shi yake da labarin sake daura musu aure ya riskini kunnuwan su, harma da tsaida mako guda bayan auren akan lokacin tarewar ta. Ikon Allah take kallo.

“Kinsan dan Adam ajizi ni Dije, amman ai ke da Datti auren ku har a aljanna…”

Inji wata Gwaggonta, abokiyar wasan Baba, da ita tafi kowa zakewa wajen kwashe ma Datti albarka, dan kuwa in taje gidan su, Dije kan bata dan hasafi, kuma Datti ya aika mata nashi ta siyi goro idan yaji zuwan nata, ga soyen sallah da ake aika mata nata kullin daban, kusan da kadan Dijen ta fita jin zafin sakin da Dattin yayi mata. Surutu kala-kala babu wanda bata ji ba, musamman babin halayen kirkin Datti, wasu ma bakine a wajen ta, ita da ta kwana ta tashi dashi a karkashin inuwa daya na tsayin shekaru, sam bata san yana da wannan nagartattun halayen da danginta suke ta yabawa ba.
Harda yayyenta da ya ba kyautar zannuwa na binni da ya bayar aka taho mishi dasu daga birnin ikko, kudi yake kashewa kamar wanda zai dauki budurwa. Har Inna da bata da yawan magana sai da ta ce,

“Ki yawaita addu’a Dije, Allah ya sa zaman ku mai dorewa ne wannan karin, Allah kuma ya kauda mugun baki akanku.”

Duk kunya irin tata sai da ta amsa da,

“Amin”

Can kasan makoshi, sai take jin kamar kwanakin sunki sauri, kamar sunki matsowa. Kirgawa takeyi, amman tamkar sunfi karfin yatsun hannun ta. Sai dai me, ana ce mata tabar Bukar nan sai an kwana biyu an bita da shi taji zuciyarta ta fada, wani hadari mai rugugi na haduwa a cikin kanta, don wauta irin tata komawarta gidan Datti kadai ta hango, bata hango barin Bukar ba, bata kuma hasaso wani zaice ta ajiye shi ba. Tayi yaya to? Ta fara kwana bata gan shi ba ta saka zuciyar ta a ina taji sanyi? In an kwana biyu fa taji suna cewa, kwana biyun bahaushe da bata da tsayayyun ranaku.

Kamar suna cewa taje ne zata wayi gari ta wuni ta sake kwana bata rike Bukar a jikin ta ba, bai kira sunata da har yanzun shi kadai ya iya furtawa ba taji muryar shi mai sanyi, ina suke so ta saka ranta? Bayanannen tsoron da yake kan fuskarta yasa Innar A’i murmusawa

“Lallai Dije…”

Ta fadi saboda ta hango wauta shimfide cikin idanuwan Dijen

“Da shi kike tunanin tafiya? Kin dai san da ya kara wayau gidan uban shi zaki mayar da shi ko?”

Wannan karin zuciyar da tayi tunani saita nemo ta daga inda ta fada ce ta bazamo tana dawowa mazauninta kafin ta cigaba da dokawa da wani sabon tashin hankali, gidan uban shi? Gidan Baabuga? Mutumin da ko sau daya bai taba zuwa da nufin duba lafiyar yaron ko me yake ci ba? Baabugan da take mantawa daga jikin shi Bukar ya fito? Baabugan da yaran da suke da iyaye ma a cikin gidan shi bai iya basu kulawar da ta dace ba shine ake cewa ta dauki Bukar ta kai, tabbas wasa suke mata, ko kuma rayuwar ce basa kaunar ganin ta a ciki shisa suke son rabata da Bukar da zaiyi barazana da hakan.

“Gara ki sama ranki salama akan yaron nan… Ki kuma yi hakuri don bana tunanin Datti zai rike miki shi.”

Yayarta Kulu ta dora akan zancen Innar A’i, suna karasa hade mata dan wajen shan iskar da ya rage a cikin kirjinta, tana jin komai ya tsaya mata. Bayan nan yanda duk sukayi da ita haka take binsu dan bata da wani kuzarin kirki, doki da murnar da takeyi na komawa dakinta duk ya dishe, hasken fitulun daya gauraye gidan nata lokacin da aka kaita bai taimaka wajen haska duhun daya lullube mata zuciya ba. Wata nasiha da fatan alkhairi da ake ta mata take jiyowa can nesa, sai kace ba cikin daki daya suke da masu maganar ba, da wannan yanayin Datti ya same ta, fuskar shi dauke da haske kamar sabuwar auduga, bakin shi yaki rufuwa saboda farin cikin da yake ciki.

“Sai nake jin yau din kamar mafarki.”

Ya furta yana zama kusa da ita, shi yana jin shi kamar a mafarki ita tana jinta kamar ta farka daga mafarki, in tace ga inda ta tattaro karfin halin biye masa suka raya daren ba zata iya fada ba, surutan shi da alkawurran shi duka basuyi tasiri akan ta ba. Har washegari bata wani jin dadin jikin ta, shima ya kula da haka, dan kafin ya fita saida ya ce mata,

“Dan Allah ki saki jikin ki dani Dije, ba zan sake maimaita wannan kuskuren ba.”

Murmushin karfin hali tayi masa, duk da haka da kyar ta samu ya fita don ya dan bata sararin da zatayi tunani me kyau ko zata samu mafita. Ta rasa, mafita daya ce shine ta roki Datti daya barta ta rike Bukar a wajenta, tunda yana da halin da zai iya kula da su gabaki daya. Idan kuma yaki zata roki Inna da ta rike shi a wajen ta, amman ba zata taba mayar da shi gidan Baabuga ba, kome zai faru ba zata kai danta wannan gidan ba, sai dai in bata numfashi. Da wannan tunanin ta dan samu sassaucin kuncin da take ji, duk da kewar Bukar din da take nukurkusar ta.

Ta dan samu sauki da shigowar da Abu tayi, saboda sunyi hira suna ta raha, taso ta bita gidanta ta ce,

“Ki rufa mun asiri, ke fa yanzun sabuwar amarya ce, kafin wani ya ganni ace nayi girman banza nazo na fito da yar kanwar tawa.”

Dariya tayi tana sunne kanta.

“Kai Adda…”

Itama Abun dariya tayi tana mata sallama ta fita dan ta dora girkin rana. Bata kuma ba Julde ya shigo.

“Daada kin dade baki dawo ba.”

Hannun shi ta kama tana riko shi.

“Yanzun ai gashi na dawo.”

Ta karasa maganar tana saka dayan hannunta ta shafi sumar shi da take a nannade irin ta Baban shi. Tana godema Datti da ya sake bata damar kasancewa da gudan jininta a karkashin inuwa daya, jikinta Julde yahau ta kuwa rungume shi, tana jin shi yayi luf kamar yana son fada mata ya yi kewar ta amman bashi da wata hanya da ta wuce wannan, a jikinta yayi bacci tana kallon girman da yayi, tana kuma kallon yanda kyawun shi yake kara fitowa kamar ba danta ba, jikin shi a murje alamar hutu da cima mai kyau da kuma kulawar da yake samu, kulawar da take ma Bukar dinta mafarkin samun ta.

Ta katanga Abu tayi mata maganar abinci, nufinta ta tura Julde, sai kiran ya bata sanadin fitar da take son yi, ta kuwa saba Julde da ta kai daki ta kwantar saboda baccin da yake yi sanda zatayi sallar azahar, ta dauki mayafi ta ja kofar gidan ta shiga

“Oh ni Abu…fitowar dai kikayi.”

Dariya ta yi,

“Ai shima yasan zan shigo dole.”

Tsakar gida kan tabarma ta shimfidar da Julde, tare Abu ta zubo musu abincin da suna ci suna ta hira kamar sun shekara basu ga juna ba, hannu da Abu ta cire daga cikin abinci na saka Dije cewa,

“Ba dai har kin koshi ba.”

Kai Abu ta gyada mata.

“Ina jin cikina ne fa yayi datti, kinga dana fara cin abinci sai inji duk ya dagamun hankali, na jika magungunan da Hammadi ya kawo kamar ma ba sha nake ba, zan sake masa magana harna shawara a samo mun…”

Kallon ta Dije take tana ganin yanda tayi yar fuska duk da itama ba jikin ne da ita ba, abinka da farar fata duk sai Dije taga ta dashe mata sai kace mai karancin jini

“Kinsan yanzun idan na dora tukunya bana tashi daga wajen, dan koya na kishingida sai bacci ya kwashe ni, satin daya gabata sai da aka aiko karbar abinci na farka, ruwan zafi kawai na dora, wutar taci ta cinye…”

Dariya Dije tayi wannan karin tare da Abun, su duka basu kawo komai a ran su ba har suka rabu. Ko da wasa Abu bata saka ma ranta komai ba, bata taba batan wata ba, wannan karin da taga kwanaki nata wucewa batare da taga al’adarta ba, saita danganta hakan da canjin yanayin da wasu matan kanyi magana a kai, amman ita bai taba faruwa da ita ba, tana karawa da yawan rashin lafiyar da takeyi da ba Hammadu ba, har ita da kanta yanzun ta fara damuwa da shi.

“Anya ba zamu shirya muje binni a duba mun ke ba Abu? Duk kin fita hayyacin ka, bana son wannan zazzabin da kike kwana da shi.”

Murmushin karfin hali tayi mishi.

“Daga dan zazzabi?”

Kuma ita a cikin jikinta tana jin ya wuce dan zazzabi, yanayi ne da bata taba jin shi ba tunda take a rayuwar ta, kai kawai Hammad ya jinjina, raunin da ke zuciyar shi na nunawa har cikin idanuwan shi da basa iya boye sirrin da ke cikin zuciyar tashi.

Basu hango rabo ba
Basu hango samu da rashin da ya tunkaro su ba.

*****

Idan littafi na yayi muku dadi, ku taimakeni ta hanyar bude account da Bakandamiya don hakanne kadai zai baku damar yin like na shafin duk da zan saka da kuma yin comment ko da na fatan alkhairi ne. Hakan zaisa website din Bakandamiya su biyani.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 10

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 24Rai Da Kaddara 26 >>

1 thought on “Rai Da Kaddara 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×