Skip to content
Part 24 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Kallon ta Abu takeyi, in da wani ya ce zata taba kallon Dije da irin wannan idanuwan zata karyata, saboda Dije ce, Dije da ko lokacin da Datti ya auro ta da kuruciya bata ga alamar hauka a tattare da ita ba. Ashe dai hauka bashi da alaka da shekaru? Ashe hauka na iya samun ka ako wanne bigire na rayuwa.

“Haukan da ya same ki kenan Dije?”

Abu tayi maganar tashin hankalin da take ji na bayyana ta cikin muryar ta, hannu Dije ta kai tana dauke kwallar da ta taru a gefen idanuwan ta.

“Ba hauka nake ba Adda Abu, ke kadai ce zan iya tunkara da maganar nan…”

Numfashi Abu taja, wata dariya mai sauti da bata da alaka da nishadi tana subuce mata.

“Saboda ni kadai ce ban taba ko batan wata ba balle in san zafin haihuwa…shisa ko?”

Kai Dije take girgizawa tunda Abu ta fara magana, har ga Allah ba haka bane nufin ta, kamar yanda tace ne, babu wanda zata fara tunkara da maganar tana son zubar da cikin da yake jikinta.

“Me yasa to? Me yasa zaki tunkare ni da wannan maganar? Na dauka zaki fi kowa sanin nice karshen wadda ya kamata ki tunkara da cewa kin samu rabon da ya isheki a duniya har kike neman zubar da wani.”

Wannan karin barin hawayenta tayi suka zubo, saboda idanuwan Abun ma cike yake taf da hawaye da wani kwantaccen bakin ciki da Allah kadai yasan shekarun da tayi tana dauke da shi.

“Karki ce haka Adda…Julde kadai gare ni, kin san shi kadai ne…”

Numfashi Abu ta shaka ta bakinta saboda hancinta ya toshe da wani abu da ba zata iya fada ba.

“Da alama ya isheki, shi kadai din.”

Da zata iya da ta ciro abinda yake cikin Dije ta mayar a nata, a lokacin da wani yake nema ido rufe, yake nema da dukkan zuciyar shi a gefe daya, a dai-dai irin wannan lokacin wani yake samu yana kuma neman maraba da shi. Idan ba Allah ba waye zaiyi haka? Duka bangarorin biyu Yana sane da su, bai kuma manta da su ba, saboda dukkan su a cikin jarabawar Shi suke.

“Ba haka bane ba, ba haka bane ba.. Ba zan iya hada jini da Baabuga ba, ba zan iya ba… Ba zan iya ba Adda…”

Ta karasa maganar muryarta na sarkewa saboda dacin da take ji.

“Jini ne ba zaki iya hadawa da Baabuga ba ko kuma cikin da zai hanaki komawa gidan Datti ne bakya so? Ki fadama kanki gaskiya…ki bude zuciyarki ki duba gaskiya…”

Ba sai ta bude zuciyarta ba, amsarta a bayyane take, dula dalilan biyu ne, mikewa Abu tayi tana saka gefen mayafinta ta dauke kwallar da take shirin zubo mata.

“Dije kar wannan ya kara zama kuskuren ki…in dai cikine zaki zubar to ba da hannu na ba, ba kuma da goyon baya na ba.”

Bata ma bata wata dama ba ta fice daga dakin, da akace ga Abu nan, ta jiyo muryarta har wani sauki-sauki taji, ya Abu zata juya mata baya a wannan bigiren da tafi bukatar ta? Babu yanda za’ayi ta fita, ko meye ya faru tasan ba za’a taba bari ta fita batare da ta cika kwanakin iddarta ba, amman lokacin da zata cika kwanakin iddar lokaci ne da komai zai iya sake cakude mata. Ga idanuwa da Innar A’i ta saka ma duk wani motsi da zatayi, ko abinci sai ya zamana sai Innar ta duba ake bata shi, ko aike tayi sai tace a miko mata ledar ta duba taga meye a ciki.

Kuka ne abokin hirarta duk dare kafin baccin wahala yayi awon gaba da ita, tayi ciki ba daya ba, ba biyu ba, amman wannan bata laulayi, ciwo ko na girar ido, gyada ce da ta dauko tun washegarin ranar da ta gane akwai cikin ta rabarma yaran gidan ita tas, kilan wannan ta zama sanadin da zai fita, sai dai me, kamar mahaukaciya kwana biyu a tsakani dole ta sake fitar da wasu kudin ta bada aka nemo mata gyadar, shine ma tana gama ci tayi amai kamar zata amayar da kayan cikinta. Tun daga lokacin saiya zamana ko ambaton gyadar bata so ayi. Zuwa kuma yanzun kowa da yake gidan yasan tana dauke da juna biyu, babu dai wanda yayi mata maganar.

Kamar wasa haka kwanaki suka dinga wucewa da ita batare da ta samu tsayayyar mafita ba har ranakun daya kamata ace ta gama iddarta badon ciki ba suka cika. A ranar kuma Datti ya aiko kiranta, daman jiran shi takeyi, Allah kadai yasan jigatar da tayi da kewar shi a tsayin watannin nan, bata damu da fadan da Baba zai iya yi ba, batama jira wani yace komai ba, ko mayafin da ta dauka sa da takai soron gidan ta yafa shi, tana fita tagan shi tsaye, jikin shi sanye da rigar saki da farin wando na hadi, hasken farin wata na haske mata fuskar shi tar, murmushi ne ya kwace mata, kafin hawaye su cika mata idanuwa, shima murmushin yayi mata.

Jikin shi na bari da son riko ko da hannun tane, tun kafin Hammadi ya fada mishi ya rame yaji fuskar shi ta fada.

“Na yi kewar ki, sosai nayi kewar ki.”

Ya fadi muryar shi na fitowa a raunane, itama tayi kewar shi, siraran hawayen da suka zubo matane ta bari suka sanar da shi haka don ta kasa magana, wasu yanayoyi ne take ji da bai kamata ace sun hade mata a lokaci daya ba.

“Gobe zan samu Baba da maganar auren mu, ya mayar mun dake, ya dawo mun dake Dije ko zan samu nutsuwa.”

Wannan karin wani irin gunjin kuka ne ya kwace mata da ya fito daga lungun zuciyar ta, cikin tashin hankali Datti yake kallon ta, musamman da yaga ta durkushe tana zama kan dakalin da yake gefen gidan nasu saboda kafafuwan ta da suke barazar kin daukarta, shima zama yayi a gefe, sai dai maganar duniya da yayi mata baisa ta dago ba, saima sautin kukan ta da yake karuwa, wani irin kuka da bai taba ganin tana yin irin shi ba duk zaman su, ko da kuwa yayi mata fadan nan nashi da yake daga mata hankali, yau nashi hankalin ne a tashe.

Babu kalar tunanin da baiyi ba, har mamakin sauri irin na kwakwalwar shi yayi, saboda gudun aikin da takeyi mishi a cikin dan kankanin lokaci haka, kafin kalaman Dije su tsayar mishi da komai, idan yace komai yana nufin har da bugun zuciyar shi na dakika kafin tayi wani tsalle tana neman hanyar fita daga kirjin shi gabaki daya.

“Ina dauke da juna biyu…”

Kalaman suka sake dawo mishi kamar saukar aradun da bai taba yarda yana faruwa ba tunda bai taba cin karo da hakan ba, kafin wani duhun kishi ya lullube shi, duhu fiye da na dararen da kan samu saukin nasu da hasken farin wata ko na taurari, baisan ya tashi daga kusa da ita ba, sai da ta dago jajayen idanuwan ta tana saukewa cikin nashi yana ganin nisan da sukayi ma juna lokaci daya.

“Me yasa? Abu daya na roke ki Dije…me yasa zaki hadamun jikin ki da na shi?”

Mikewa tayi, saiya matsa taku biyu baya, yana sa bugun zuciyar ta yana karuwa.

“Dan Allah Datti”

Kai yake girgizawa, kwakwalwar shi na hasko mishi hotunan Dije da Baabuga batare da ta tausaya ma halin da zuciyar shi take ciki ba, idanuwan shi ya runtsa yana bude su. Ya sake runtsa su saboda wani hawayen bakin ciki da yake jin yajin su cikin idanuwan shi, ashe akwai sauran abinda zai iya bayyana hawayen shi haka? Wannan karin shine ya tsugunna, yana jin kamar ana zarar wani abu tare da shi, da farin ciki ya wuni, zuciyar shi cike taf da shi, ya daren shi zai juye haka? Ya zaiji zuciyar shi ta fada wani waje da yake jin ganota zaiyi masa wahala.

Hawaye ne wani nabin wani yake zubo ma Dije, ganin yanda Datti yake kokawa da numfashin shi, sai ace zuciya bata da kashi, sai ace tsoka ce zalla, abinda take ji yana karyewa cikin kirjinta yanzun fa? Meye shi? Abinda take gani yana karyewa yanzun a tare da Datti menene shi?

“Ina so in zubar… In zubar da cikin, tun da nasan da shi nake so in cire shi… Bansan ya zanyi ba…kuskure ne…wallahi ba yanda zanyi.”

Sai da Datti ya dafa kasa sannan ya iya mikewa, a sarari yake, fili ne gaban shi da bayan shi, sai dai yana kallon Dije yaji kamar tayi masa katanga da samun wadatacciyar iska. Juyawa kawai yayi yana jin yanda take kiran shi amman ko juyawa baiyi ba. Tafiya yake da Dije take jin takun ta kamar a cikin kirjinta da yake kara daukar dumi. Dakyar ta iya komawa cikin gida tana wucewa daki kai tsaye, maganar da Innarta take mata ma bata tsaya ta saurara ba, tana shiga ta samu wajen lungun gadon Innar ta zauna tana jan kafafuwanta ta hade su da jikinta hadi da sakin wani irin kuka mai cin rai.

Ba zata gaji da aika ma Baabuga Allah ya isa na yanda ya canza musu komai a dare daya ba. Ta tashe ni, ta tsani abinda yake cikinta. Haka Inna ta shigo ta sameta tana kuka kamar an labarta mata mutuwar Innar ko ta Baba.

“Kinga ki sahirta ma kanki wannan damuwar Dije, lamari na duniya a hankali ake bin shi, musamman abinda baka isa ka sauya ba…kiyi hakuri kibi komai a sannu.”

Maganar ta kunnen haggunta ta shiga tana bi ta dama ta fice batare da ta samu wajen zama ba, wacce duniya ce zata bi a hankali? Duniyar da batayi mata adalci ba? Me zata bi a hankali, daga sakin ta zuwa yau, babu wani abu guda daya da yazo mata da sauki, sai ita ce zata bi komai a hankali? Wannan magana ce da bata da hankalin daukarta a yanzun. Runtse dai bata runtsa ba, dan sai cikin dare ta samu tayi sallar isha’i, da alwalar ta mayar da asuba tana kwanciya dakyar. Koko da kosan da aka kawo mata haka akazo aka dauke da rana da aka kawo mata wake da shinkafa da ya sha man gyada, ko yunwar ma bata ji, dakyar ta iya mikewa ta dauro alwala tazo tayi azahar.

Tashin hankalin da take ciki bai bari ta tuna da wani wani wanka ba, da la’asar ta idar da Sallah kenan Innar A’i ta shigo tana jingina bayanta da bangon dakin.

“Kinki cin komai duk yau Dije, in baki duba kanki ba, ki tausaya ma abinda yake cikin ki kici wani abu dan Allah.”

Ta san Innar ta ce ta turo Innar A’in, wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, takai hannu tana dauke su.

“Kiyi hakuri, watannin zaki ga sun wuce kamar kiftawar ido in dai Allah ya bamu aron rayuwar, kiga kin koma dakin mijin ki kamar komai bai faru ba, amman in kika rasa lafiyar ki fa?”

Haka Innar A’i ta dinga bata baki, a cikin maganganun babu wanda suka fi mata tasiri irin jin zancen komawarta gidan Datti, shisa ma harta dauki kwanon abincin, aikuwa tas ta cinye shi, tana dorawa da furar da Innar A’in tasa aka kai mata, sai taji wani karfi na daban yana shigarta, da kuwa shafal take jinta. Bata sake samun wani karfin ba sai da aka aiko kiranta bayan isha’i, har tuntube tayi garin sauri, innar ta zatayi magana Innar A’i ta girgiza mata kai tana dorawa da,

“Ki rabu da ita, in ta ganshi ta samu nutsuwa, yaran yanzun na da bambanci da mu, in aka matsa mata mu duka lamarin ba zai mana dadi ba.”

Bayan Dijen ta fita ta samu Datti tsaye kamar jiya, sai dai fuskar shi ta kumbura kamar wanda yaci kuka. Wata yar leda ce ya zaro daga cikin aljihun shi yana bata.

“Kulli daya zaki juye duka a ruwa ki sha yau, ki kara juye dayan ki sha gobe.”

Karba tayi da sauri, sai dai bai jira amsarta ba ya juya. Tsaye tayi bata koma gida ba saida ya bace ma ganin ta. Jikinta bari yake sanda ta koma cikin gida, sai take ganin kamar wani zai ganta, kasa samun nutsuwa tayi har sai da dare ya raba, tukunna ta iya shan maganin, washegari ma bata samu wani sarari ba sai Magriba. Aikuwa wajen karfe daya wani irin ciwon mara da yasa ta kiran Innar ta cikin neman dauki ya dirar mata. Duka gidan babu wanda ya zaci zata kwana, Innar A’i kuka ta dinga yi don macece ita mai tsananin tausayi da raunin zuciya, harta Babba ya karaya da ciwon Dijen.

Bata samu kanta ba sai washegari da wajen azahar, cikin daren sumanta biyu. Duk wani jike-jike an bata, amman takai kwanaki hudu bata warware gabaki daya ba. In ta faki idanuwan mutane takan share kwallar da take silalo mata, saboda alama ta digon jini ma bata gani ba balle tasa ran cikin jikinta ya fita. A watanni biyu magunguna babu kalar wanda Datti bai kawo mata ta gwada ba, amman ciki saima fitowa da yake yi. Sun hadu su duka sunyi kukan yanda Allah ya nuna musu iyakar su akan cikin jikinta, tashin hankalin ta yafi na Datti, saboda na shi tashin hankalin yana kara mata nata ne.

“Ina jin karshen duniya ta ne yazo Dije, shisa zan ga cikin wani na girma a jikin ki, shisa zanga kin haihu da wani…”

Ya fada wani dare kamar wanda ya samu tabin hankali.

“Kuskure ne nayi, Hammadi yace in roki Allah ya yafe mun, watakila na makara wajen rokon, amman wannan hukuncin zan iya daukar shi kuwa? Cikin Baabuga ne a jikin ki, haihuwa zakiyi, ba dani ba da Baabuga.”

Idan yana irin wannan surutan sai dai taita kuka saboda bata da abinda zata fada mishi ta samu sauki. Ta tsani Baabuga da dukkan zuciyar ta, ta kuma tsani cikin da yake jikinta wanda ya zame mata karfen kafa, har tana jin tana haihuwar shi zata saka a zani ta aikama da Baabuga yasan yanda zaiyi da shi. Wannan ne kudirin da yake ranta duk sanda zata daga idanuwa ta dubi cikin jikinta.

Haka yaci gaba da faruwa har sanyin safiyar Alhamis din da ta tashi da nakuda, wata irin nakuda da tazo mata da saukin da bata taba sanin akwai shi a tare da ciwon nakuda ba, cikin kankanin lokaci, kukan jaririn da Innar A’i ta karbi haihuwar shi ya karade dakin tare da kabbar da tayi da kuma hamdala. Dije na runtse idanuwanta, wasu hawaye masu zafi na gangaro mata, duk bidirin da sukeyi tana jin su, ta daiki bude idanuwanta.

“Ungo, rike shi kiga dan ki, rike shi yaji dumin ki.”

Cewar Innar A’i tana saka mata yaron a jikinta, cikin yanayin da bata ko bata wani zabi da ya wuce na dagowa ba, tana gyara rikon yaron a hannunta, sannan ta sauke idanuwanta akan shi, zuciyarta na wata irin dokawa, ta rike yaranta da yawa, ta rike Julde fiye da sau daya, amman bata san irin wannan yanayin ba, bako ne a wajen ta, ta kuma ji labarai da yawa akan soyayya wadda take tsakanin mahaifiya da abinda duk zata haifa, shisa ta dauka ta gama sanin wannan soyayyar, sai yanzun, sai yau da take rike da wannan yaron da take jin zata iya gifta rayuwarta ya tsallaka in har bukatar hakan ta taso.

Hawayen ta na sauka kan fuskar shi, ya dan motsa, tana jin motsin ya faru tare da zuciyar ta. Kafin kwanaki bakwai su zagayo dakyar take iya kauda kai idan yana hannun wasu, da an dauke shi take jin kamar an dauke mata zuciyar ta har sai sun dawo mata da shi, ranar suna Baabuga ya kawo wani dan rago da yasa Baba sawa aka janyo daya daga inda yake kiwon dabbobi aka hada aka yanka. Yaro yaci sunan shi Abubakar, sunan wani dan Baabuga din da ya rasu. Ana kuma zuwa aka fadama Dije sunan da yaro yaci, wata mata na rangada guda tana dorawa da,

“Allah shi raya mana Bukar.”

Ta kalle shi ya sha askin suna yana bacci a hannun ta, wata irin kaunar shi ta soke ta, kauna mai tsanani, kauna kamar bata dauki watanni tana son zubar da cikin shi ba, kamar bata dauki karan tsana ta dora mishi a watannin da yake kwance a cikin ta ba, daga randa ta sauke idanuwan ta akan shi ya shafe komai, komai banda kaunar shi.

Bukar
Bukar dan ta
Abinda bata sani ba shine wata kaddarar bata ma soma ba.

*****

Idan littafi na yayi muku dadi, ku taimakeni ta hanyar bude account da Bakandamiya don hakanne kadai zai baku damar yin like na shafin duk da zan saka da kuma yin comment ko da na fatan alkhairi ne. Hakan zaisa website din Bakandamiya su biyani.

Next >>

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 7

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 23Rai Da Kaddara 25 >>

2 thoughts on “Rai Da Kaddara 24”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×