Skip to content

Rai Da Kaddara 2 | Babi Na Sha Bakwai

1
(1)

<< Previous

Ya dauka alfarma a tsakanin shi da Datti ta kare daga ranar da ya fara ja masa Allah ya isa, har kasan zuciyar shi ya dauka babu wata rana da zata sake zuwa da zaizo gaban Datti ya tsugunna da nufin neman alfarma. Sai dai wacce zuciyar? Zuciyar da take kirjinshi da ya dauka mallakin shi ce, mallakin shi da yake da iko da ita, ya santa, suka zauna na tsayin shekaru harma ya tabbatar tsayawarta dai-dai yake da tsayawar shi. Sai da zuciyar nan ta nuna masa iyakarsa lokaci daya, ta mayar da duk wata yardarshi ta koma yaudarar kai, zuciyar nan dai itace ta ruga tayi tsaye a gaban Mero ta cigaba da dokawar da a wata uku kacal har fitar numfashin shi yake jin idan batare da Mero ba zaiyi wahala, balle kuma ita zuciyar da ta zama tata.

Tsintar kafafuwan shi ya sakeyi a kofar gidan Baabuga washegari, bai ko yaudari kanshi ba ya aika aka kira masa Mero, Mero da tayi masa wani murmushi bayan ta fito kamar ta tsammaci zuwan shi, kamar hakan ba bakon abu bane a wajen su biyun, kafin su fara hirar da take fito musu cikin sauki, kamar sauran abubuwa a tare da ita. Bai sake sanin shakuwar da sukayi a dan tsakanin tayi karfin da tayi ba saida ta koma Kano, sai daren da ta koma daya kwanta yaji wasu wajaje suna masa ciwo da son ganinta. Kirjin shi ya bude yanajin wani fili daya lalubi Saratu ko zata rage masa wannan fadin, amman na yan mintina ne, daya mirgina gefe Mero ce a kowanne shige da ficen numfashin shi.

Bai san ya soyayya take ba sai da ya tsinci kanshi a ciki, shisa tana dawowa bai bata lokaci ba, bai tsaya dogon shiri ba ya bude mata zuciyar shi, kamar yanda soyayyarta bata bashi damar shiryawa ba, ya fada mata yana sonta ya kuma dora da.

“Ni ba mutumin kirki bane Mero, idan bakiji ana labari ba a gari, idan nazo da maganar aurenki zaki ji, ni ba mutumin kirki bane ba.”

Ya karasa yana saka idanuwanshi cikin nata, yana rokonta da duk wani abu da yake motsi a jikinshi karta guje shi, sai dai taji, daga bakin Bukar ta fara ji kafin ya koma

“Hamma na ne Mero, ina kaunar shi fiye da tunaninki, amman kiyi wani zabin, bashi ba. Ko menene tun kafin yafi karfin ku biyun ki dakatar da shi.”

Sannan daga bakunan da duk suke tunanin suna da mutuntakar fada mata ta saurare su, sai dai ta ina zata fara? Da wanne yaren zata fahimtar dasu cewa daga ranar da ta saka idanuwanta cikin na Julde ta jita a wani waje tare dashi, wajen da ko taso ba zata iya barowa ba? Zuciyarta na dokawa tana sanar da ita shekarun da tayi a baya cikin jiran lokacin da zata hadu dashi ne, shisa tasa auduga ta toshe kunnuwanta daga duk wani aibun shi da ake haska mata.

“Bakowanne abu da zuciyarka ta haska maka bane alkhairinka.”

Mutane kan fadi, a bigiren da Mero take tsaye wannan kalamaine da basu da wani tasiri, zuciyarta ta haska mata shi, alkhairi ko akasin haka wannan zabinta ne bana kowa ba.

“Zaka canza.”

Ta fadi kamar tana magana da kanta ne bashi ba, saboda yanayin yanda sautin ya fito, a hankali, a nisance. Kalmomi biyu, kalmomi masu nauyin gaske, kalmomi masu tarin ma’anoni.

“Banda abubuwa da yawa da zan baki Mero, bayan zuciyata, banda wani abu da zan iya baki sai gaskiyata.”

Wannan karin akwai wani abu a cikin kallon da tayi masa da yasa wani gashi mikewa a bayan wuyan shi.

“Bansan ko ina so in canza ba, bansani ba. Idan ina so dinma bansan ko ta ina zan fara ba…zan iya cewa zan canza saboda ke, zan canza saboda son da nake miki. Amman shi kanshin son bangama fahimtar shi ba balle in dora alkawurra akan shi.”

Batace komai ba, ta jinjina kai, alamar taji shi, sannan ta mike tana bar masa wajen. Da nauyin shirunta ya koma gida, washegari da yaje baiyi zaton zata fito ba, ya daiji a jikin shi ko da bata fito ba zai sake dawowa, zai dawo ko sau nawa ne har saita fito. Wannan karin idan tabar Marake zai bita. Sai ta fito, tana sake tabbatar masa da karfin kaddarar da take tsakaninsu.

Kaddarar da inda sun hango kurar da take cikinta da sun yanke alakar da take tsakanin su.

Da sun hango shafin da zai fara dasa musu aya a alakarsu da sun hakura da juna.

Akwai samu.

Akwai rashi.

Rashi na rai a tafiyar su.

Rashin da zai zama farko ya zama karshen komai.

Sai dai wauta irinta tunani, da taja Julde, ta kuma ja Mero da furta.

“Halayenka ne karshen abinda zan duba a yanzun Julde, ina sonka, ina son kasancewa da kai. Halayenka, abinda kowa yake fada bayan wannan suke.”

Kalamanta suka nutsar da duk wani abu da yake a tashe a tare dashi. Suka kuma zame masa akala lokacin da yazo ya tsugunna a gaban Datti yana rokonshi.

“Dan Allah Baba…karkace mun a’a, kace kabarni da duniyar dana zaba akanka. Wannan karin kawai, ka sake bani dama.”

Kallon shi Datti yayi, kallo ne mai cike da gajiya. Shi kanshi Julden rabon daya kalli Datti irin yau harya manta. Yanda shekaru suka nuna a fuskar shi, akwai kuma wani yanayi da gajiya da lamurran duniya ne kadai yake bayyana shi shimfide a fuskar Dattin.

“Baba dan Allah, ka nema mun aurenta.”

Numfashi Datti yaja ya sauke.

“Waye zai baka aure Julde? Waye zai dauki yarinya ya baka? Wa zan kalli idanuwan shi ince ya baka auren ‘ya?”

Kirjinshi Julde yakejin kamar wani ya zira hannu a ciki ya kama zuciyarshi yana matsawa yana hana musu numfashi su duka biyun.

“Baka gwada ba, ka gwada… Dan Allah ka gwada.”

Ya sake roka, shi ba ma’abocin kuka bane ba, amman yanda yake ji yanzun idan Datti yace masa a’a tabbas fashewa zaiyi da kuka. Sai ya dan daga masa kai, a zaune Julde yake, amman sai yaji kamar ya sake zama, yaji shi sakayau, kamar an dauke masa wani nauyi daya shigo dakin Dattin dashi.

“Meye a tare da Kabirun? Yana da kyau?”

Ya tambayi Yelwa data girgiza masa kai, tana amsa tambayar da ba zaice wacce ce a cikin biyun da yayi mata ba.

“Me kika gani bayan kinsan Baba ba zai taba yarda ba?”

Kafadu ta dan daga masa alamar itama bata sani ba, ya numfasa da nufin sake tambayarta ta rigashi da.

“Kana son Adda Saratu?”

Yadan dakuna fuska saboda yanda tambayar tayi masa bazata, yana zaune da Saratu, suna hada shimfida, akwai yaro a tsakaninsu, gana biyu na hanya. Amman idan ya kalleta har yanzun yanajin yanda dolen da akayi masace kawai abinda ya kulle su zama waje daya. Da kanshi, ba zai taba zabenta a matsayin macen da zai karasa sauran kwanakin shi da ita ba.

“Randa kaso wata, sai ka sake tambayata Hamma, bansan ya zan maka bayani akan abinda baka san ya yake ba.”

Fada sukayi a lokacin, duk da Yelwar shiru tayi ta kyaleshi, amman ya fahimta yanzun. Ko da ta fada masa a baya ba zai taba ganewa ba. Yana son mace da zai kalla yaga ta amsa sunanta mace, duk da kowa ta tari gabanshi yana so yaji yanda take, amman idanuwanshi basa iya sauka daga kan irin wannan matan da suka amsa sunansu na mata. Shisa ya dauka inda zabin mata yayi da kanshi cikin irin wannan zai zabo, macen da ba zai gaji da bin duk wani motsinta da idanuwa ba. Sai gashi idanuwan Mero ya fara gani a jikinta zuciyar shi ta rabu da kirjinshi tana samun wajen zama a tare da ita.

Bata da muni, ba kuma zaka kirata me kyau farat daya ba. Idanuwanta ne abinda yafi komai kyau a jikinta. Idan Saratu ta tsaya a gabanshi, idan ya rungumeta yanajin kanta a kafadarshi, saboda doguwace. Bai rungumi Mero ba, amman yana da yakinin da kadan zata wuce cikinshi. Karamace, Mero bata da girman jikin da cikar halittar da yake tunanin yana so a tare da mace. Da gaskene, ba kowanne so yake da dalili ba. Yau dai, baccin da zaiyi yau da sanin Datti ya amince da nemar masa auren Mero dabanne.

Sai dai a gefe daya, a dai-dai wannan lokacin ne Yelwa take bude ido duk safiya tana jin duniyar na kara hadewa da ita da yanda kwanaki sittin suka rage a daureta a karkashin inuwar aure da Modibbo. Modibbo da ko a tunaninta ya gifta sai taji numfashinta yana mata barazana. Ji take ya kamata ace littafin kaddararka yana hannunka a rike, yanda zakayi masa zama daya ka karanta, idan kaga yau kasan me gobe take rike dashi, yanda komai ba zai zo maka da bazata ba, ciwon zai dan rage idan kasan da zuwan shi. Ka shiryama zuwan shi. Amman rayuwar ba haka take tafiya ba.

Ji take kamar tana rike da wani sashi na numfashinta ne tunda aka rabata da Kabiru, shisa duk iskar da zata shaka bata kai mata inda ya kamata, komai baya mata dadi. Yanzun yanayin ne ya ninku, dutsen da yake danne da kirjinta Datti ya dauko wani ya kara a kai. Ba saiya hadata da Modibbo ba, tasan karfin ikon shi akanta, tun akan Kabiru ta fahimta, ba iya haihuwarta yayi ba, ya share wani titi da ya saka ma ranshi akai zata bi, kome ita ta hango a sama in dai shi bai ganshi ba bata da ikon sake hanya. Tayi kokarin magana, tama yi maganar, ita da Modibbo akan titin nan ba abu bane da take so, amman yaki bari duk maganarta ta wuce kunnuwan shi balle ya fahimceta harta canza kudirin da yake zuciyarshi.

Yaki fahimtarta kamar yanda yake tunanin taki fahimtar shi, taki gane duk wani zabinshi akanta gatane yake tunanin yayi mata. Mahaifin Modibbo da ma Modibbon a karkashin shi suke samun rufin asiri, shisa mahaifinshi baiki ba da yayi masa tayin fadada alakarsu. Ko bayan bashida rai Modibbo da ahalin shi basu isa su wulakantata ba, basu da wannan karsashin saboda zata gaji kaso mai girma a cikin abinda zai bari, kason da yasan Julde zai kular mata dashi har numfashin shi na karshe, tana da arzikin da tafi karfin wulakanci kowanne namiji a fadin marake. Gashi dadin dadawa shi Modibbon bafullatani ne gaba da baya. Me take so bayan wannan? Menene abinki a tare da Modibbo?

“Daada shirunki na cutar damu, shirunki a abubuwa da yawa ya taimaka wajen kawomu inda muke yau, kiyi masa magana, dan Allah ki bude baki kiyi masa magana. Ki fada masa wani abu zai mutu a tare dani daga ranar da ya auramun Modibbo.”

Yelwa ta karasa maganar wasu irin hawaye masu zafi na zubo mata, shirun dai Dije ta sakeyi, shirun da ta fara koyan shi akan lamurransu daya hada da Datti bayan taga yanda maganarta batada amfani indai akansu ne. Tun suna kananansu kuwa, su suka kara taimaka masa wajen dishe muryarta a duk wasu lokutta da zata shata musu layin da take tunanin zai amfani gobensu, Datti ya goge musu shi su tsallaka. Idan kudi ya dauka ya basu take tunanin sunyi yawa ta kwace, zasu fita ko me zatayi kuwa, zasu same shi, zai dauki wanda suka ninkasu yawa.

“Ubansu mai kudine, su yaran mai kudine Dije. Ki barmun yara suyi abinda suke so tunda ina da halin da zasuyi hakan…”

Idan fada tayi musu, a gabansu zaiyi mata wanda sai ta shiga daki tayi kuka. Shima irin yau din ta dinga hango masa, da duk wata tsinuwa da zaibi yaran wasu dashi, da duk lokuttan da yake ganin shine ya isa akan tarbiyar su, dama lokuttan da yake ganin duk idan yaro yayi wani abu da bai kamata ba to laifin na iyayenshi ne, sune suka gaza a wani bigire na tarbiya, ikon canza kaddarar yaransu a hannun su take, sai Dije tayi kokarin fahimtar dashi. Yaran duk da suka kasance nagartattu, bayan kokarin iyayensu akwai addu’a, akwai addu’a da itace mataki da kuma jigon komai.

Sosai taso ta fahimtar dashi tarbiya abune mai matukar wahala, bayan godiya lokacin da Allah yayi maka kyautar samun da, ya kamata tsoro ya cika zuciyarka, mutum ma ya baka amana kana taraddadin karka kasance cikin wanda zasu kasa sauke wannan amanar, ya kamata tsoro ya cika zuciyarka sanin Allah ne ya baka amana, amanar yaran da kai dasu zaku tsaya a gabanshi ya tambayeka akan wannan amanar. Idan kayi iya kokarinka wajen ganin ka sauke amanar nan, saika hada da addu’a, ka hada da sadaka don karesu daga abinda idanuwanka ba zasu taba hangowa ba. Idan kaga wani ya gaza a tashi tarbiyar ka bishi da addu’a, ka godewa Allah da baisa ka gaza ba, idan ba zaka iya ba kayi shiru, ka kiyaye harshenka.

Idan yarane ka gani suna abinda bai kamata ba, kayi musu nasiha idan zaka iya, ka bisu da addu’a bayan nasihar, ko ka tsaya da addu’ar kawai, kana da zabi kala-kala, a ciki harda mai sauki, kaja bakinka kayi shiru. Karka aibatasu, karka bisu da mugun baki, karkai tir da halayensu, karka dora laifin lalacewar su akan iyayensu, watakila sunyi iya kokarinsu, kaddara ce ta rinjayi wannan kokarin. Idan ma sun taimaka wajen wannan lalacewar baka da hurumin da zaka nuna musu yatsa. Allah daya zabeka, Allah daya baka ikon sauke amanar daya baka, shi ya basu amanar, a karkashin Ikon shi suka kasa saukewa. Babu wanda yafi karfin kaddara, kowacce iri ce.

Amman Datti yaki fahimtar yaren duk da fulatanci tayi masa ba hausa ba. Sai hakanma ya dinga ja mata fadanshi da idan ya fara baisan yayi shiru ba. Suma da ta nuna musu makahon sone Datti yake musu, soyayyar da ta samo asali da samu da rashin sauran yaran da suka dingayi a baya. Ta nuna musu lokaci zai iya zuwa da Datti zai kasa basu duk wani abu da zasu bukata, zai kasa karesu daga abubuwan da suka fi karfin ikon shi, sai suka koma bayan Datti suka labe, suna nuna mata akwai rauni a tata soyayyar.

“Kinfi son Bukar, Daada kinfi son Bukar damu.”

Julde ya taba fada mata kai tsaye, sai dai tana ganin a lokacin kamar shekarun shi basu kai ya fahimci tana sonsu duka ba, tana kaunarsu gabaki dayansu, wata irin kauna da bata da misali. Kawai akwai wani rauni a tare da Bukar da basu dashi, akwai wata kaunarta da Bukar din yake nunawa da a cikinsu babu mai nuna mata irinta, bawai tana kishi bane da yanda suka dinga zabar Datti akanta. Kawai shakuwar da take tsakaninta da Bukar, ko nisan da yayi mata ya kasa dishe haskenta. Kowacce uwa tana son yaranta, tana sonsu dai-dai da junansu, hanyoyin da take nuna wannan soyayyar ce take da bambanci.

“Ban fi son Bukar ba, ku duka ina son ku.”

Kallonta yayi, kallonta yayi kamar bai yarda da ita ba, kamar kalamanta basuyi masa tasiri ba. Amman ya dora kanshi a jikinta, saboda Julde ne, ko fada tayi masa, ko fada yaja Datti yayi mata zai zo ya dora kanshi jikinta, kamar yana bata hakuri, kamar idan yayi hakan zuciyarshi na masa sanyi.

“Kiyi masa magana Daada.”

Yelwa ta sake rokonta. Tace masa me? Tace karya aura mata Modibbo? Ta ina zata fara shiga wannan maganar? Shiru tayi, hakan yasa Yelwa ta sa bayan hannunta ta share fuskarta tana ficewa daga dakin. Idan Dije tace tayi niyyar magana to zatayi karya. Amman da Datti ya dawo, saita tsinci kanta da fadin.

“Ka kyaleta Datti, tunda tace bata son shi ka kyaleta. Ya kamata daga kai harsu ku fara saurarar juna ko zaku samu maslaha.”

Saiya kalleta, irin kallon da yasata ganin yanda a cikin yaran duka Bukar ne kadai yayi yanayi da ita, ko yanayin yanda Julde yake cin abinci irin na Datti ne, muryar shi ma haka. Akwai abubuwan da Yelwa zata furta duk da tana mace sai muryarta tayi mata iri daya da ta Dattin.

“Babu wanda ya isa yasa a fasa auren nan, ko ita da kanta Yelwar.”

Wani abu Dije taji ya tsirga mata, wani abu da bashi da kalma, saiya hado mata da tsoro, tsoro da firgici mai yawa. Yanda suka zo inda suke yanzun, yanda tarin kaunar da take tsakanin Datti da su Julde ta birkice tana juyewa zuwa haka cikin dan lokaci. Sai taji tana son magana da Abu, ta kudura a ranta washegari wajen Abu zataje, su tattauna akan yanda babu wani abu da yake da tabbas a cikin rayuwa. Yanda komai yake canzawa abin tsoro ne. Jikinta taji ya dauki dumi cikin wani yanayi da ta kasa fahimta, kamar zuciyarta na son sanar mata da komai na gab da birkice musu, kuma babu wanda ya isa ya hana hakan faruwa.

Next >>


How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×