Skip to content

Rai Da Kaddara 2 | Babi Na Sha Shida

5
(1)

<< Previous

Idan yace baya so ya daina abinda yakeyi zaiyi karya, ba don kowa ba sai don Dije, sai dan yanayin da yake gani shimfide a cikin idanuwanta duk lokacin da Datti ya bude baki ya bishi da kalaman da suka zame masa jiki yanzun.

“Allah ya isa”

Wannan sune masu sauki a cikin kalaman Datti da suke fitowa daya bayan daya kamar ya jingine alakar da take tsakanin shi da Julde, yayi katanga da duk wata soyayya da ta taba giftawa a tsakaninsu. Idan Julde ya rufe idanuwan shi yana tuna lokuttan da suke zaune karkashin inuwa daya da Datti, suke cikin farin ciki, suna wasa da dariya, sai yaga kamar wasu shekaru ne masu yawan gaske suka shude. Shi da kanshi idan ya duba zuciyarshi babu komai a ciki a yanzun sai wani nauyi da duhun da ba zai misaltu ba.

“Idan baka duba kowa ba, bakayi tunanin halin da kowa zai shiga ba, nima ban gifta a ranka ba kenan Julde? Ko abinda zanji bashida muhimmanci a wajenka kaima?”

Kowacce kalma ta Dije ta dira kunnuwan shi tana samun wajen zama, inda har yau yake jin nauyin su, musamman da ta dauki idanuwa ta saka masa bayan wannan kalaman. Tabarshi da abinda ya zaba. Saratu tun yana biyewa tashin hankalinta idan taji ko da canjin kamshine a jikin kayan shi, harya gaji, musamman yanzun da yake mata uzuri da cikin da yake jikinta, cikin da yazo mata da wani irin laulayi mai zafi, amman hakan bai hana mata neman rigima dashi ba ko da yaushe, inda take samun karfin hali yana bashi mamaki. Yelwa ce kawai batayi masa magana ba.

“Ba ki tambayeni komai ba Yelwa, ba ki cemun komai ba…”

Idanuwanta ta saka cikin nashi, kafin ta sauke numfashi.

“Me zan tambaya Hamma? Yaushe ka fara? Me yasa ka fara?”

Ta karashe tambayar tana dauke idanuwanta daga cikin nashi kafin da wani yanayi a muryarta ta sake cewa.

“Me zance? Abinda kakeyi bashi da kyau? Ba mutuncinka kawai ka zubarba har da namu? Me zan fada wanda tunaninka bai kawo maka ba ka ture kayi zabin zuciyarka, me zance Hamma?”

Harta tashi bai sake magana ba, yanayin dake tattare da muryarta ya kashe masa jiki. Bayan maganganun nan bata sake masa wasu dasu dangancin abinda yakeyi ba. Duk da itace ta farko a wajen rikicin shi da mutane duk idan nema ya hadasu, tsinuwar Datti da ya koyi hadawa yayi musu tare bata taba hanata ba. Sai yakejin kamar ita kadai ta rage masa a duniyar shi da bata bari laifukan shi sun shafi kaunar da take masa ba, sai Salim da zai fara mika hannuwan shi daya hango Julden, Salim da bai damu da tarin daudar da take lullube dashi ba zai rungume shi, zaiyi masa dariya, zai kuma yi kokarin yi masa yarensu na yara cike da son bashi labarin da shi kadai yasan ma’anarsa, sai kuma Saratu da baisan ya akeyi take gane me yake nufi ba.

Kamar akwai wata fahimta a tsakaninsu da ta tsaya iya su biyun. Ranakun da taga daman takan sake maimaita masa abinda Salim din yake kokarin fada. Idan kuma rikici take dashi, yaron na hannun shi zata zo ta fincike shi ta saba a baya, komin tirjiya da kukan da zaiyi kuwa. Da ido Julde yakan bita a irin wannan lokuttan, tunda kafin ma ya bar gidan ta fara dirka nishin da baya barinta da wani zabi daya wuce ta sauke Salim din. Takan bashi dariya, wani zubin mamaki, harda tausayi a wasu ranakun.

Abinda basu hango ba su duka shine zuwan Bukar a dai-dai lokacin daya zo. Bayan yazo din abinda Julde bai taba hangowa ba ko a mafarki shine ranar da wani abu zai faru da zaisa Bukar ya nuna fushin shi, har ya daga murya.

“Hamma…”

Ya kira bacin rai kwance kan fuskar shi, mamaki yasa sauran kalaman idan suka karasa kunnuwan Julde basa kaiwa cikin kanshi balle ya fahimce su, ga fulatancin da Bukar yake sirkawa da wani yare da alamu suka nuna na inda yake karatu ne, yaren Borno.

“Tafiya kayi Bukar… Ka zauna ne? Tafiya kayi kabarmu.”

Julde ya fadi bayan Bukar din ya rufe bakin shi, sai dai kamar ya sake harzuka shine.

“Tafiyata ce uzurinka? Hamma tafiyata ce uzurinka?”

Shirun da yayi yasa Bukar din jinjina kai yana sa kai ya fice daga gidan Julden ranshi a matukar bace. Sai dai Julde yayi nisan da bacin ran da kowa zai nuna akanshi ba zai juyo dashi ba, a wannan bigiren bashida dalili guda daya da yake jin zai saka shi barin abinda yake bari.

“Nabarwa duniya kai Julde, wallahi na sallamawa duniya kai tunda ita ka zaba akan mutuncina da naka dana ahalinmu duka.”

Datti ya fada masa kamar daga ranar ya daina bata rai da duk wani abu da zaiyi. Shida aka sallamawa duniya? Me kuma ya rage? Karshen abinda zai faru a gani da hangen Julde ya rigada ya faru, ya gama lalacewa, babu kuma wani abu da yake jin zai faru dashi bayan wannan. Shisa ya mike shima, da nufin barin gidan bayan wasu dakika da fitat Bukar. Kullum Saratu kallon shi takeyi, kallo irin na wanda ya yanke maka buri da samun dai-dai to, kallo daya rigada ya saba dashi zuwa yanzu tunda ba ita kadai takeyi masa wannan kallon ba. Shisa bai dauka fushin Bukar zai dame shi ba, sai da aka kwana, aka yini Bukar na cikin Marake amman bai neme shi ba. Sai gashi ya shiga gida yana tambayar Dije ko taga Bukar, ta kuma tabbatar masa ko da safiyar ranar yazo ya gaisheta.

A daddafe yaci abincin dare. Yana zame Salim da yayi bacci a jikin shi ya mike yana shirin ficewa.

“Ina zakaje?”

Saratu ta tambaya rikici fal a idanuwanta, rikicin da yakejin ya gaji dashi har cikin kasusuwan jikinshi, musamman yau.

“Ba dare bane kawai lokacin da namiji yake dashi na fita yabi mata Saratu…ki daina kallon duk fitar dare na haka, ki saka ma ranki duk sanda zan fita zai iya yiwuwa abinda na fita yi kenan, kuma bakya daya daga cikin dalilin da zan bari, kina jina? Karki sake tambayata inda zani tunda ba aikena kikayi ba.”

Ya karasa maganar yana ficewa yabar mata dakin, mamaki da zafin maganganun shi na rufe mata baki. Takawa yakeyi zuwa hanyoyin da zasu hadashi da gidan Baabuga, akwai wadataccen hasken farin wata, sai dai ko a cikin hayaniyar mutanen dayake wucewa da suka kafa majalissa akwai wani shiru, da kuma hayaniyar halittun da Ubangijin daya halicce sune kadai yasan da wanzuwar su, irin yanayin nan da dare kadai kan haifar. Tunda ya sha kwana ya hangota tsaye a kofar gidan, jikinta sanye da riga da zani na atamfa, sai dankwalin da ba daura shi tayi ba, ta dora a saman kanta ne, habar na sauka kowanne gefe na kafadarta.

Batare da tunanin komai ba ya karasa har gab da ita, ganin babu yaro ko daya da zai iya aikawa ya kira masa Bukar yasa shi ce mata.

“Dan Allah a gidan nan kike?”

Juyowa tayi da mamaki bayyane a fuskarta tana sauke idanuwanta cikin na Julde da yake tsaye, lokaci daya wani abu yayi sanyi a cikin kafafuwanshi. Baisan ko hasken farin wata bane yasa shi ganin kamar akwai maiko a cikin idanuwanta, wani irin maiko da bai taba gani a idanuwan kowa ba.

“Eh…”

Ta amsa cikin wata siririyar murya mai cike da rashin tabbas, tana sauke idanuwanta daga cikin nashi.

“Bukar fa?”

Ya tambaya yana rokon ta sake dagowa ta kalle shi, kamar taji rokon nashi ta sake dagowa tana sake saka idanuwanta cikin nashi a karo na biyu.

“Ya fita tun dazun, sai dai nasan yana gab da dawowa.”

Ta fadi muryarta na zarta kunnuwanshi wannan karin tana samun wajen zama a cikin kirjin shi, kafin ya yawata da idanuwanshi akan gabaki daya fuskarta, abinda bai taba faruwa dashi ba ya faru a karo na farko, ta wuce ta cikin idanuwan shi, ta yawata wajaje da dama cikin kanshi, yanajin saukowar hotonta daya dauka lokaci daya yana neman inda muryarta take ya zauna a gefenta cikin kirji na shi, zaman da nauyin shi yasa murmushi subuce masa. Murmushin da ta mayar masa, kyallin shi na haskawa har cikin idanuwanta.

“Zan jira shi…”

Maganar ta subuce masa, kai ta dan daga masa kafin ta sauke idanuwanta cike da wani yanayi daya saka jikinshi gabaki daya daukar dumi.

“Me kikeyi a waje?”

Wannan karin yayi mata maganar cikin harshen fulatanci, saboda sabo da yayi da magana dashi, yana kara kallon shigar jikinta da yanayinta gabaki daya da bai masa kama da matan cikin Marake ba, watalila shisa yayi mata hausa da farko, kuma ta amsa shi da hausarta da take fita tar a sabanin tashi da zakaji alamun cewa ba ita harshen shi ya fara lakanta ba.

“Nayi aike ne tun dazun…saina leko in gani.”

Ta amsa a takaice bayan ta dan juyo, ganin yana kallonta yasa ta dora da,

“Ya dade.”

Tana dan dakuna fuskarta, murmushi ya sake subuce ma Julde, tare da wani bangare daga zuciyarshi batare daya sani ba.

“Zaki gaji da tsayuwa ai.”

Yar siririyar dariya tayi da yaji sautinta yayi masa dadi.

“Ban dade da fitowa ba.”

Kai ya girgiza mata.

“Duk da haka..”

Dariyar ta sakeyi, haka kawai tana saka shi jin kamar ya santa tuntuni, kamar hira da ita na daya daga cikin abinda ya saba dashi na yau da kullum.

“Sai in jingina da bango.”

Ta amsa da alamar dariya a muryarta.

“Mu jingina dai, dan ni bana jure tsayuwa… In jira Bukar ki jira dan aiken ki.”

Bangon gidan kuwa suka samu suna jingina, hira sukeyi kadan-kadan.

“Baki tambayi sunana ba.”

Julde ya fadi.

“Na san sunan ka, ba Hamman Bukar bane ba? Julde?”

Ganin yana kallonta da mamaki yasa ta dorawa da

“Yana maganarka…”

Kai ya jinjina

“Ni ne ban sanki ba”

Yace, dan juyowa tayi idanuwansu ya sarke cikin na juna tare da kaddarar da ta hadesu tun kafin samuwar su.

“Mero…”

Sunanta ya fito daga bakinta yana shiga kunnen shi kafin ya maimaita a hankali kamar yana so ya dandana yanda kowanne harafi yake zama akan harshen shi. So yake ya tambayeta ko a gidan take ko zuwa tayi amma ya rasa ta inda zai fara, kamar yanda itama ta tsinci kanta da fada masa ba a gidan take ba. A kauyen Marake aka haifeta amman a garin Kano ta girma, mahaifinta kanin Baabuga ne uwa daya uba daya, kuma ita kadaice a wajen shi saboda mahaifiyarta ta rasu tana da shekaru biyu a duniya, babu wanda ya musa da kanin mahaifiyarta Musa da yake kasuwancin shi a Kano ya nuna son daukarta ya rike. Shekara daya tsakani Allah ya dauki ran mahaifinta da yayi jinyar kwanaki hudu rak.

Tashinta a Kano bai hana Musa kawota Marake ba, ko ba tushensu bane, ita nata ne, tsatson mahaifinta ne. Ba kuma zaiyi sanadin yankewar zumuncinta da dangin mahaifin nata ba. Har wata daya tanayi a Marake. Kauyen yayi mata. Karatun bokon da takeyi take kuma sone dalilin da yake hana mata dawowa marake gabaki daya, babu wanda yake takura mata anan, duk da abinci da wajen kwanciya ba daya bane ba. Amman tafi jin dadin zaman nan fiye da gidan Musa.

Shisa tasan Bukar, suka kuma shaku dashi a iya ganin da takeyi masa yanzun da zamanshi a Borno yafi zamanshi a Marake yawa. A dan sanin da tayi masane kuma tasan Julde. Ba kamaninsu ta gani da Bukar ba, duk da akwai wani kwarjini a tare da Bukar da Julde bashi da, yafi Bukar din kyau, nesa ba kusa ba yafi Bukar kyau. Akwai kuma kitso guda biyu a kanshi, daya a kowanne gefe na kanshi, inda babun kuma sumace cunkushe. Sumar da ta kara masa kyau tana kuma fito da karan hancin shi.

“Bukar bai dawo ba, dan aikena bai dawo ba, ga dare yanayi”

Ta fadi a maimakon tarin zantukan da suke cikin kanta, tana raba jikinta da bangon da take jingine dashi alamar zata shiga gida.

“Sai da safe.”

Ta furta cikin sanyin murya, yana amsata, lokaci daya yana ciza lebenshi kar son rokonta da ta tsaya ya kubce masa. Rabon daya samu nutsuwar daya samu a tsayuwar nan tasu an kwana biyu. Yana kallo ta shiga gida, nauyin zuciyar da ya daga masa ya dawo yana danne shi, ya taso masa da hoton Mero daya samu wajen zama yana soma jan zaren kaddarar daya hade su waje daya.

*****

Akwai wani fili da Kabiru yabar mata, filine da ko da wasa batayi kokarin cike shi ba. Bata yaudari kanta cewar zata iya ba. Ta ina ma zata fara? Kewarshi da takeyi? Kewar hirarrakinsu? Fara’arshi? Don shi mutum ne da baka raba fuskarshi da murmushi. Ko kuma sanyin halin nan nashi da bata taba gani a tare da kowa ba? Dame zata cike filin da rashin shi yabar mata? Daga ranar da Datti ya yanke musu hukunci batare daya duba halin da su duka zata shiga ba komai ya rage armashi a wajenta, komai ya rage kala, komai ya rage dandano.

Abubuwan da take jin dadinsu yanzun tanayi ne saboda Dije da Julde da suke duk wani kokarinsu na ganin ta koma dai-dai. Sai dai batajin wani dai-daito ko kadan, idan tayi dariya sai taji yanda tayi kewar fitowarta daga zuciyarta. Idan ta tashi da safe jira kawai takeyi dare yayi ta koma ta kwanta, idan daren yayi kuma sai baccin yazo mata cike da mafarkai marassa kan gado, duka akan Kabiru.

“Baba ba zai hanani aurenki ba Yelwa, zan fada masa ban fara rayuwa dake ba, amman inajin yanda kowacce rana da nayi babu ke tana shiryani ne zuwa lokacin da zan hadu dake, lokacin da kaddarar mu zata fara… Ba zai rabani dake ba. Ko kin taba ganin an raba mutum da kaddarar shi?”

Ya bata dariya, wasu kalaman na Kabiru takanji sune, sai sun rabu ta zauna taita tunanu tana neman hada ma’anarsu, sai ta rasa, ba kullum bane idan ya bude mata zuciyar shi take fahimtar shi. Sai dai abinda Datti ba zai iya ba bashi da yawa, ciki kuwa harda rabasu. Ba ita da Kabiru ba, har ita dashi Dattin da kanshi, kallon shi takeyi yanzun kamar bako, kullum idan ta gaishe shi da safe sai ta dinga kallon shi tana neman Babanta a tare dashi, Babanta da yake son duk wani abu da take so, Babanta da zasu zauna suyi hirar awanni cike da raha da son juna, amman yanzun kamar jira yake tayi wani abu dan karami, tsinuwa da bakin da yake bin yaran waje dasu ya sauke a kanta.

Tun randa ta saka kafa suka fita tare da Julde laifinshi yake shafarta. Ya rabata da Kabiru, Julden ma so yake tabarshi? Saboda yayi masa laifi sai itama tabarshi kamar yanda yabarshi? Shisa ta toshe kunnuwanta daga dukkan fadan Datti, tsinuwa da bakinshi, akan Julde zata dauki komai, ciki harda wadannan abubuwan. Idan ta gaishe shi wata rana ya amsa, wata rana ya shareta. Bata taba damuwa ba, itama yanzun maganarta idan ta yawaita to da Julde ne, ko kuma ta shiga gidan ta dauko Salim, shima itace zataita masa surutu, ko yana ganewa baya nuna mata alama sai dai yaita kallonta. Saratu ma akan Kabiru fada sukayi sosai, saboda irin kabilancin da yake zuciyar Datti shine a tata zuciyar. Saita rage shiga gidan kamar da.

Yanda take rayuwarta a yanzun ta dauka duka tashin hankali kuma babu wanda bata gani ba. Babu kuma wani abu da zai sake taba zuciyarta. Sai daren da Datti ya zabi ya kama kafafuwanta ya juyata ta tsaya da kanta, ya karasa birkita mata komai da kalaman shi.

“Na samo miki mijin aure Yelwa”

Yana dorawa da,

“Modibbo ne, zaizo gobe ku gaisa.”

Aure? A wawan tunani irin nata, haduwar kalmar da ita a waje daya ta kare daga ranar da Datti ya rabata da Kabiru. Ta hakura, da ta hakura da Kabiru ba wai tana nufin shi kadai ta hakura dashi ba, har da auren gabaki daya. Kasa magana tayi, kirjinta yayi mata wani nauyi na ban mamaki, washegarin ma kamar mai yawo akan gajimare haka ta yini har daren da ta dora idanuwanta akan Modibbo tanajin yanda baiyi mata ba, badon yana da wata makusa ba, kawai zuciyarta ce takeji an halitta mata ita saboda mutum dayane kawai kacal

“Baba bana son shi, wallahi bana son Modibbo.”

Ta fada masa numfashinta na mata barazana. Kallonta Datti yayi.

“Haka nace bana son Dije tun kafin in ganta… Shekarar mu nawa tare yanzun?”

Kai Yelwa take girgiza masa idanuwanta cike taf da hawaye.

“Bana son shi ko kadan, kayi hakuri kabarni.”

Ta karasa hawayen na zubar mata.

“Ni shine zabina Yelwa, gaya miki nayi ban tambayi ko kina son shi ko bakya son shi ba.”

Sune kalaman Datti.
Kalaman da suka canza mata komai.

Next >>


How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×