Skip to content
Part 33 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Tsaye yake ba don babu wajen zama ba, idan ya juya a cikin gidan da zai iya kira da nashi yanzun sai yaji shi a cikin wata duniya ta daban. Duniyar da kamar idanuwa ya rufe ya bude ga ganta a ciki. Nisan daya hangone ya hade da shi kamar almara.

“Ba zabinka na tambaya a maganar auren nan ba Julde, umarni ne. Idan na isa kenan, idan kuma ban isa ba saika nuna mun iyakata.”

Ko da ya daga ido ya kalli Datti amsar daya bashi daga farko ita ya sake maimaitawa.

“Bana sonta Baba, bana son Saratu.”

Maganar kuma ya sake maimaitawa Dije.

“Daada ki fada masa bana sonta ko zai jiki… Bana son yin aure yanzun.”

Kallon shi tayi da wani sanyi a cikin idanuwanta daya nuna mishi rashin ikonta a cikin maganar, sanyin daya nuna masa inda tana da zabi ba zai auri Saratu ba.

“Kayi hakuri Julde, watakila kaddararka kenan.”

Kai yake girgiza mata.

“Kaddara ta rasa ta inda zata dirar mun sai auren da bana so? Yaushe Baba ya fara mana dole a cikin al’amuran mu?”

Hakurin dai Dije ta sake bashi, hakurin da bai tausasa zuciyar shi da yake ji a hargitse ba.

“Ki fadawa Baba bana sonki, ki taimaka mana ki fada masa, zama dani ba zai taba miki dadi ba.”

Sai dai idanuwan Saratu sunfi nashi bushewa,  zuciyarta tafi tashi kafewa. Akwai wani kyalli na son nuna masa iyakarsa da yake gani cikin kwayar idanuwanta.

“Me yasa? Meye banda shi?”

Kai ya girgiza mata.

“Kawai saboda bana son ki, shi kadai ne dalili na.”

Akwai ciwo a murmushinta, wani irin ciwo da yasa shi jin kamar tausayinta na son kutsa mishi, sai dai wahala yake takaita mata, wahalar zama dashi da bai hango mata sauki a cikinta ba.

“In dai ba Baba yace mun ya fasa hada auren mu ba zan aureka Julde, kome zaka fada, kome zakayi zan jure.”

Yayi din, abubuwan duk da yasan zai gujema aurenta, ya fada, maganganun duk da yake tunanin zasu harzuka zuciyarta, zasu kure hakurinta. Ko biye masa batayi, yanajin nauyin Hammadi, yana ganin kimarshi fiye da yanda yake zato. Don jikin shi sanyi yayi da yaje gabanshi da nufin yace masa bayason Saratu.

“Julde… Lafiya dai ko?”

Ya tambaya cikin sanyin nan nashi da yasa yaji harshen shi ya nade da kalaman da yai nufin furtawa, baisan Hammadin ya kula kamar baya son auren ba, shisa ya cewa Datti.

“Datti kar a fara abinda ba zai yiwa kowa dadi ba, shi Julden ya amince har zuciyar shi? Yaran yanayin yanda suka taso dabanne da lokacin mu, a abubuwa da yawa ba’a bamu zabi ba, duk da an mana zabin da idan aka barmu da namu zai wahala muyi irin shi. Amman a lokacin rayuwar mu a bude take, su idan ka kula tunda suka fara girma suna da wata rayuwar tasu da bamu san komai game da ita ba, cikin wannan rayuwar harda ra’ayoyi da hasashe akan irin wannan abubuwan…watakila akwai kalar matar da ya hango ma kan shi.”

Kamar ko yaushe sai Datti yaki fahimtar shi.

“Ban haifi yaron da zai dora zabin shi akan nawa ba wallahi. Ita Saratun in mata magana ai amincewa tayi, sai shi dana haifa? Idan kaima iyakata zaka nuna mun akan Saratu dai kayi kawai, idan kuma bashi bane dan Allah ka bimu da fatan alkhairi.”

Saiya kyale Datti tunda in shekara zasuyi ba zai taba fahimtar inda ya dosa ba. Karshe ma zai fassara maganar ne ta yanda zai daure Hammadi ya kasa cewa komai.

“Saratu ke kadai zaki iya tsaida maganar auren nan, idan kika cewa Datti a hakura zai hakura.”

Saboda Hammadi ya kula kamar Datti na ma Saratun soyayyar da baya yiwa nashi yaran.

“Saboda me?”

Ta tambaya.

“Saboda kinsan Julde baya son auren, bai amince ba.”

Bakinta ta turo gaba.

“Baba ya amince, ko kowa bai amince ba ina so.”

Ko da Abu ta sake daga masa maganar haka yace mata.

“Addu’a da fatan alkhairi ne namu, daga ita har Dattin taurin kansu yafi karfina Abu, bana son fara janyo abinda banda riba a ciki… Saratu zata saurari Datti ne kin sani, kome zan fada mata sautin Datti zai danne nawa…”

Numfashi kawai ta sauke tana fadin.

“Allah ya kyauta.”

Saboda tasan gaskiya ta fada.

“Kayi hakuri Julde, duk wani abu da zakayi hakuri a cikin shi mai wucewa ne.”

Yace ganin Julden yayi shiru. Wata hirar yaja shi da ita har saida yaga ya sake kafin suyi sallama.

“Me yasa ka saba yi mana duk abinda muke so? Ka saba mana da bin ra’ayoyin mu idan kasan hakan ba zai dore ba?”

Julde ya jefi Datti da maganar yanajin yanda duniyar ta hade masa waje daya. Saboda akan auren Saratu ya fara sanin wata takura tun tasowar shi.

“Saboda ina tunanin randa na kawo nawa ra’ayin a cikinku babu wanda zaice mun a’a. Karka kure hakurina akan zancen nan Julde… Wallahi zan maka baki idan kace zaka bijire mun.”

Kalamai ne da Julde ba zai taba mantawa ba, saboda sun sake rura wutar tsanar Saratu a ranshi. A wajen Datti kuma sun zama makami, makamin da zai amfani dashi wajen tsorata Julde yabi ra’ayinshi. Amman bayan kwanaki biyu saiya sake daga masa maganar, ranshi kuma yakai matuka wajen baci. Me yasa Julde yake da taurin kai? Me yasa ba zai fahimci gata yayi musu daga shi har Saratu ba? Yasan asalinta, yasan daga inda jikokin shi zasu fito, bashi da wata fargabar cakuduwar ahali.

“Da nace zan maka baki baka yarda ba kenan? Gani kake ba zan iya tsine maka kabi duniya akan maganar nan ba ko Julde?”

Koshi Datti da yake furta kalaman bai hango zasu faru ba, shisa ya cigaba da hidimar auren kamar Julde bai fadi ya maimaita cewa baya so ba.

“Dan Allah Hamma kayi hakuri, ka hakura haka, kaga Baba ranshi ya baci.”

Yelwa ta roke shi.

“Ni kuma nawa bacin ran fa? Yelwa nawa bacin ran in kaishi ina? Don shi ya haifeni sai yaimun auren dole? Shi zai zauna mun da ita?”

Kai ta girgiza masa idanuwanta cike da hawaye.

“Nace yayi hakuri abar maganar, baka san me yace mun ba.”

Murmushin takaici me sauti Julde ya yi.

“Kema ca yayi zai tsine mikin?”

Yanda ta kalle shi ya tabbatar masa da hakan ya fada. Tsinuwa a bakin Datti ba wani abu mai wahala bane, tunda suka taso suke jin yana bin ‘ya’yan mutane da ita, harma da su kansu iyayen. Abu kadan da bai masa bane zaisa kajita a bakin shi yana aika musu kwando-kwando. Bata taba damun daga shi har Yelwar ba duk da suna ganin tana damun Daadar su. Tunda suna jin yanda take masa magana a kai har ta gaji ta daina. Saboda basu taba hango wannan tsinuwar zata waiwayo kansu ba.

“Meye a tsinuwar? Cikin wanda yake tsinewa duk rana wa kikaga ya fasa hidimar shi ta yau da kullum.”

Hawayenta ne suka zubo.

“Ance ta iyaye dabance, haka naji Gwaggo ta taba fada, ba’a so iyaye su tsinewa ‘ya’yan su lalacewa sukeyi.”

Wannan karin dariya Julde yayi. In dai a cikin lalacewa akwai bin mata, ya rigada ya faru dashi tun kafin Datti ya tsine masa. Shaye-shayen da ake magana akai, wanda ya gani wasu sunayi bai taba burge shi ba, saboda bayason ya taba kusantar abinda zai rabashi da hankalinshi. To bayan wannan biyun akwai wata lalacewa ne? Sai ma ta tirsasa shi yayi auren da baya so, idan ya auri Saratu ba zai daina bin matan daya fara ba. Ba zai daina ba, shisa baiga amfanin auren ba. Hankalin Yelwa da bayason gani a tashe yasa shi nuna mata zaiyi kokarin ganin komai ya wuce masa, yayi hakuri da maganar.

Amman kayanshi ya hada da nufin barin gidan da asuba kafin kowa ya fito. Saida yakai kofa ya fara tunanin inda zai nufa. Sai ya hango Daadar shi da halin da zata shiga, sai ya hasaso tashin hankalin da zai saka Yelwa. To ya gudu ma yaje ina? Saiya dawo, ya kuma ci karo da Datti a tsakar gidan, Datti daya kafe shi da ido ta cikin hasken alfijir daya fara ketowa.

“Gudu zakayi?”

Ya tambaya cikin wata irin murya.

“Allah ya kwashe maka albarka idan ka fasa tafiya!”

Ya fadi yana daukar buta ya nufi bayi kamar yanda yayi niyya. Kamar kuma bai fadi kalaman da suka saka jikin Julde mutuwa likis ba. Sai yaji kamar kalaman da suka dira a kunnuwan shi sun zagaya ko ina na jikin shi suna bin jijiyoyin shi sannan suka kwanta luf a wani wajen da suka fi karfin ganin idanuwa. Sai yake jin zaman nasu kamar wani iri ne na itaciyar da yake jira ya fara tsiro ya kafa rassa a tare da shi. Lokaci daya wani irin tsoro ya cika zuciyar shi, tsikar jikin shi ta mike kamar mai shirin zazzabi. Saiya koma daki, sallah ma sai da gari ya waye tangaran tukunna yayita.

Daga ranar ne kuma bai sake daga maganar cewa baya son Saratu ba. Hidimar bikin duk da ake tayi da idanuwa yake binsu. Haka Datti ya fita daga lamarin shi gabaki daya, wani abu daya zame masa sabo. Bayan gaisuwa saiya rasa abinda zaice mishi, sabanin da, abincin dare ma kusan ko yaushe tare suke ci sai dai idan a gidan Hammadi yaci. Sai har Dije tayi bacci tana juyo hirar su. Komai ya canza duk akan Saratu, duk akan aurenta. Da Dattin yace masa yaje yaga gidan da zasu zauna, magana mai tsayi data hadasu a cikin wata daya da ake ta hidimar bikin shi.

“In dai yayi maka shikenan ba sai na gani ba.”

Bai kuma je din ba sai yanzun da aka rakoshi a matsayin ango. Har suka gama duk wani abu da yake al’ada a wajen su jin shi yake wani iri. Asalima yana jin amsa kuwwar amin din data daure kaddarar shi da ta Saratu waje daya. Kallonta yake da fararen kayan saki a jikinta da suka sha ado irin na amaren fulani. Mayafin kayan da aka ja aka rufe mata fuska da shi. Ya rasa abinda yake ji. Dakyar ya iya jan kafafuwan shi ya karasa inda take ya zauna a bakin gadon bonon da aka shimfide da sabon zanin gado. Iya dakin idan ka kalla zaka san Saratu ‘yar gata ce, sannan gidan da ta fido kudi ba matsala bane ba.

Sai da ya jishi a zaune tukunna wata irin gajiya ta jiki da zuciya ta saukar mishi tana kashe masa jiki, kafafuwa yaja kan gadon ya matsa can karshe ya kwanta. Duk da bata ganin shi taji kwanciya yayi. Wasu hawaye sirara suka silalo mata, ta cikin mayafin ta kai hannu ta goge su. Kafin ta zame mayafin ta ajiye gefe, tana fara cire tarkacen sarkokinsu dake wuyanta, goshinta, kunne da hannuwa. Don ita ko dankunne bata iya kwana dashi komin kankantar shi sai ta cire, idan ta tashi da safe ta mayar.

“Idan nice kullum saina batar da dankunne.”

Yelwa takan fada idan ta ga tana mayarwa da safe. A saman soyayyar da take yiwa Julde akwai wani kunci daya dinga kunsa mata tunda aka fara maganar aurensu da ta dinga shanyewa, sai ya dunkule ya zauna wani waje cikin kirjinta da yake mata ciwo.

“Har an daura, yanzun na hango su Baba suna dawowa.”

Yelwa ta fada mata cikin farin ciki, tayi murmushi, amman ba zatace ga daga inda ya fito mata ba. Saboda jikinta yai wani irin sanyi da bata zata ba.

“Zama dani ba zai taba miki dadi ba Saratu.”

Kalaman da Julde ya dinga jaddada mata suka dirar mata. Har aka kawota gidan jinta take kamar mai yawo a saman gajimare. Gashi nan tun bata kwana ba ya fara nuna mata gaskiyar kalaman shi. Kasa ta sauka tana shimfida mayafin da ta cire, ta dawo ta dauki daya daga cikin filon dake kan gadon ta kwanta. Sai dai hasken fitilar da take kunne taji cikin idonta fiye da misali. Jiki taja ta dauki fitilar da mai batira ce, ta kashe. Duhun da ya mamaye dakin na ba hawayenta damar sauka, su suka tayata hira har barawon bacci ya sace ta.

****

Suna zaune cikin gida daya, amman tazarar dake tsakanin su zatayi daga Marake zuwa Dutsi. A tsayin satikan hudu ya koyi yin shiru ta fannin da bai taba hasasowa ba. Yaji dadin yanda Saratu ta bashi wannan tazarar da yaji yana bukata. Idan ta gaishe shi da safe bata sake ce mishi komai. Zatayi girki, zata ajiye masa. Idan ya dawo zai dauka ya ci saboda baida inda zaije yaci abincin. Kuma ba zai karya ba ta iya girki, a tsayin sati hudu yana tsintar kanshi da son komawa gida da cikin shi ya fara ruri saboda yasan zai sami abinci mai dadi yana jiran shi. Bayan wannan rayuwa suke a gida daya amman kowa harkar gabanshi yakeyi, idan dare yayi zatayi shimfida ta kwanta a kasa, ya kwanta akan gado.

Ya kanji tana yawan motsi alamar rashin sabo da kwanciya daga ita sai zannuwan da take shimfidawa kafin yaji canzawar numfashinta alamar tayi bacci. Sai yaji kamar bai kyauta mata ba, amman kwana a kasan zabinta ne tunda bashi yace ta kwanta ba, gadon yana da girman da zai ishesu batare da wani ya takura wani a kai ba.

“Na fita.”

Ya furta kamar kullum, addu’ar dawowa lafiya tayi masa cikin sanyin muryar da bayason ji a tare da ita. Saboda Saratu ce, sanyi-sanyi baya cikin halayyarta. Juma’a ce, yasan daga Hammadi har Datti basa fitowa da wuri, su kamar ranar juma’ar ce take zame musu ranar da sukeyin hutun karshen mako, dan wasu ranakun juma’ar ma cikinsu babu mai zuwa ko ina daya danganci kasuwancinsu, sai suyi amfani da ranar wajen ziyarar abokan arziki da kuma ‘yan uwa. Shisa shima ya fara zabar ya wuce gidansu ya fara gaisawa da Daada, su zauna suyi hira da Yelwa. Hirar tasu da Yelwa bata rasa abinda zata fada da zai rike shi na tsayin kowacce rana da yakejin shi kamar a cikin keji.

Yau ma da wannan yanayin ya tashi, ya fara tashi dashi ne tun safiyar shi ta farko da ya bude ido da auren Saratu akan shi. Ance idan wani babban abu zai sameka kana ji a jikinka, ko ka tashi da rashin kuzari, sanyin zuciya ko wani yanayi da bai zai misaltu ba. Julde ya yarda da wannan fadar a baya, ya yarda har lokacin daya karya kwanar gidansu ya hango cincirin mutane, saboda yanayin daya tashi da shi ba bako bane ba. Ya fara sabawa dashi, baisan kafafuwanshi sun kara sauri ba saida ya ganshi a kofar gidan.

“Rayuwa kenan…”

Muryar da baigane mammalakinta ba ta kutsa a kanshi, amman son shiga cikin gidan Hammadi da shine farko daga inda ya bullo kafin nasu, don yaga abinda yake faruwa yasa duk wasu surutai da akeyi bace masa, Dije ya gani a tsaye, kafafuwanta babu ko takalma, asalima kallo daya zakayi mata kaga tashin hankalin da yake tare da ita. Wajenta ya karasa yana fadin.

“Daada me ya faru? Lafiya? Me yasa naga mutane?”

Ya jera mata tambayoyin zuciyar shi a kan harshen shi. Yanda ta kalle shi yana sa tsikar jikinshi tashi saboda ya tabbatar wani abu mai girma ya fara dasu, girman da zai musu wahalar dauka. Julde ne a gabanta, kuma da alama magana yake mata, amman batajin komai sai muryar Abu.

“Lafiya kalau ya dawo sallah Dije, yace mun jikin shi a mace yake, ni nace masa ya kwanta watakila daren da muka raba ne muna hira, bacci ne bai wadace shi ba… Na tashe shi yaki tashi. Nayi nayi ya tashi yaki tashi… Ina Datti? Ku zo ko ku zaku tashe shi ya tashi.”

Har yanzun tanajin hannun Abu data saka cikin nata tana janta zuwa gidan da Datti da yake biye dasu cikin rudani. Sai dai yanda Datti ya dago shi taga ya koma ta kalli Abu, ta kalleta da zuciyarta a karye saboda tasan baccin da Hammadi yayi bana tashi bane ba. Ba Abu bace ta kasa yarda, Datti ne, Datti daya fita ya dinga zuwa da mutane kala-kala. Tun liman daya ce musu.

“Allah ya karbi abin shi.”

Abu ta zame tana zama, ta kuma ja kafafuwanta ta hade su da jikinta bata sake cewa wani abu ba. Datti ya kira mutane sunfi ashirin, kana cewa ya rasu zai sake fita ya kira wani. Yanzun haka da suke tsaye tashin hankalin da ake ciki kenan, ya kama Hammadi ya rike a jikinshi.

“Hamma ko zaka tafi zaka nuna mun alama, zakayi rashin lafiya, zaka kwanta jinya. Ba zaka tafi haka ba, ka tashi ka fada musu ba zaka barni ba saboda kai kadai ka rage mun.”

Ya karasa yana mayar da shi ya kwantar, ya sake dago shi a karo na biyu.

“Hamma wa zaimun fada? Wa zai gayamun banyi dai-dai ba? Dan Allah ka tashi…”

Ya karasa cikin wata irin murya da ta shiga kunnen Julde da wani irin yanayi, saboda hanyar dakin Hammadi kawai Dije ta iya nuna masa.

“Julde zo kaga Kawunka! Kayi masa magana ko zai tashi kai!”

Cikin dakin ya shiga ya kama gawar Hammadi yana kwantar dashi, ya kuma kamo hannun Datti da yake kokarin kwacewa.

“Karka cemun ka yarda da zancen su, karka cemun ya rasu.”

Yake fadi cikin fitar hayyaci, so yake ya kwace rikon da Julde yayi masa ya koma jikin Hammadi.

“Baba don Allah”

Julde ya fadi saboda duniyar duka yake jin ta tashi daga kasan shi ta koma sama kanshi tayi baya ta fado ta danne shi.

“Baba!”

Ya sake kira yana saka idanuwan shi cikin na Datti da sukayi wani irin fayau

“Ya rasu.”

Ya fadi, maganar na komawa cikin kunnen shi, girmanta na zauna masa. A karo na farko yana dandanar menene zafin mutuwa, yanayin da yake bako a wajen shi. Sanyin da hannun Datti yayi a cikin nashi ne yasa ya sake shi. Sake gyara zama yayi kafin yakai jikin shi kasa gabaki daya ya dago yana neman numfashin da yai masa tsaye, dakyar ya fito dashi tare da wani gunjin kuka daya da hawayen Julde saukowa. Zama yayi yana kamo Datti daya fada jikin shi yana kuka kamar karamin yaro, su duka dakyar aka fito dasu daga dakin. Dije na kamo Abu da babu digon hawaye ko daya fuskarta suka fito don bada damar a hada shi.

Zuwa lokacin gidan ya fara cika da mutane, saida aka fito da gawar, Abu ta hango su sannan ta zabura ta mike. Dije ta rikota, amman karfin da take ji ba zai kwatantu ba. Matan duk da suke gabanta ta dinga tsallakewa saida takai tsakar gida inda aka shimfide Hammadi cikin sutturar da itace zata zamo ta karshe a duniyar kowa. Ana kokarin shigowa da munkarar da za’a saka shi ciki.

“Hammadi Am”

Ta kira shi a karo na farko sunan na fitowa da zuciyarta da take da yakinin za’a binne tare da shi.

“Da kace mun hirar jiya bankwana ne, da ka fadamun sanyin jikinka tabin mutuwa ne. Dana zauna tare da kai, dana kwanta a gefenka ko bata dauke mu tare ba inji fitar numfashin ka…”

Ta karasa can kasan makoshi.

“Allah ya amsa addu’arka, ban tafi nabarka ba. Kai kabarni…kai ka fara barina Hammadi…”

Hawayenta suka rike sauran kalaman, a wajen ta durkusa tanajin karshen duniyarta yazo tare dana Hammadi. Bata san hannayen suwa ke kokarin dagata ba.

“Kubarni… Dan Allah kubarni.”

Ta roke su, sai suka saketa, amman tanajin su a gefenta. Har aka saka Hammadi a munkara aka fita dashi, ihun kukan mata na cika kunnenta.

“Allah ya yafe maka Hammadi Am… Allah ya hadamu a aljannar da kake hango mana tare da rabon da bamu samu ba anan.”

Idan tace bata ji barinta zaiyi a yan kwanakin nan ba zatayi karya, akwai bankwana a cikin duk wani abu da sukeyi, sai dai bata hango yau bane. Da suka sake kamata batayi musu ba, mikewa tayi suna janta zuwa dakin da ta fito. Yawan mutanen basu hanata jin wani irin fili da gidan yayi, har kirjinta take jin wannan filin, kamar Hammadi ya tafi da komai, a jikin Dije ta dora kanta tana jin yanda ta lalubi hannunta ta dumtse kamar tana son fada mata tana nan gefenta, babu inda zataje. Yanayi ne da bai hana mata jin kadaicin da zai kasance tare da ita har karshen rayuwarta ba.

Sai dai mutuwar Hammadi cikar lokaci ce.
Akan kowa mutuwa cikar lokaci take jira.
Kaddarar su yanzun ne zata fara.

****

Comments da likes din karku gaji, na fada zan kara tuni ne kawai, da su zan samu a biyani. Nagode da tarin goyon bayanku.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.2 / 5. Rating: 9

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 32Rai Da Kaddara 34 >>

1 thought on “Rai Da Kaddara 33”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×