Skip to content
Part 26 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

“Hammadi am”

Ta kira tana kara gyara kwanciyar ta a kusa da shi, muryarta na fitowa daga can kasan makoshi, kuma a raunane, da ba kusa da ita yake ba, da ba dukkan hankalin shi yana kanta ba, da baiji ta kira shi ba, da sunan shi da yake jin kamar an rada masa shine don harshenta, hannu ya kai yana sake taba jikinta a karo na babu adadi tun kwanciyar su, akwai zazzabin har lokacin.

“Hammadi”

Ta sake kira muryarta na sauka fiye da kiran farko, har tsikar jikin shi sai da ta mike. Duk wani labari na soyayya da ya taba ji bai kai matsayin a dora shi mizani daya da abinda zuciyar shi take ji akan Abu ba.

“Na’am!”

Ya amsa sanin halin ta, duk da tasan ba bacci yake ba, tana iya cigaba da kiran sunan shi batare da ta fadi abinda take so ba har saiya amsa ta, wasu lokuttan dan kawai ta ga ya daga ido ya kalle ta.

“Kinsan fa ina jinki Abu, ko ban amsa ba ina jin ki.”

Sai tayi dariya, dariyarta da yake so.

“Bafa wani abin zan fada ba, kawai dai ina son in kira sunan ka.”

Girma na shekaru dai ba zai taba canza wasu abubuwan a tare da ita ba, kuruciyar ta dashi kadai yake gani tana nan daram.

“Alfarma nake roko Hammadi, ba zan so takura ba, amman a lokaci daya kuma ba zan so kace a’a ba, dan Allah ba kunnuwan ka kadai nake so ka bude kaji ni ba, harda zuciyar ka.”

Numfashi ya sauke da taji hucin shi saman fuskarta saboda kusancin da suke dashi da juna. Tana son Hammadi, wani irin so da ba zai misaltu ba, amman a kwanakin nan sai take jin kamar zatayi mishi nisa, kamar jikinta na nuna mata alamar zata bar shi, zata barshi taje inda zata jira zuwan shi, bata son yayi kadaici kafin ya tarar da ita.

“Ka kara aure…”

Maganar ta dake shi fiye da zaton ta, kafin ya samu damar cewa wani abu ta dora da,

“Dan Allah ka kara aure, nasan duk alkawurran da muka daukar ma kan mu a baya… Ina so ka kara aure, inajin kamar rabon inga jinin ka a duniya na tare da hakan.”

Shiru ne ya biyo bayan maganar ta, shirun da kan zo da duhun dare, shiru irin wanda yakan biyo bayan magana mai nauyi da bukatar nazari.

“Abu…”

Hammadi ya kira sunanta, kirjin shi yayi masa nauyi, kalamanta sun danne shi, idan yace baya son ganin jinin shi a duniya yayi karya. Ko giccin Julde ya gani sai wani abu ya matse a cikin kirjin shi.

“Baffa…”

Haka Julde yake kiran shi, ko da na dakika daya idan ya rike shi ya so ya manta cewa ba daga jikin shi ya fito ba, ya so ya yaudari kan shi, na dakika daya kawai, sai kalmar ta fizgo shi ta dawo da shi, sai ta tuna mishi cewa Julde dan Datti ne. Tun kafin ma azo kan shi Dattin ma da baisan kara ba, Datti da baya gajiya da fada masa cewar Julden dan shine, ya sani, amman Datti baya gajiya da tunasar da shi. Bai fada ba, amman abin yana masa zafi har kasan zuciyar shi. Rashin da akwai ciwo, rashin haihuwa jarabtace da wanda yake cikinta kawai ya san zafin hakan.

Ba zaka taba sanin ka damu da haihuwa ba sai kaga alamun ba zaka same ta ba, sai kaga hakan yasa ka fita daban a cikin sauran ma’aurata, sai ka gansu rike da nasu yaran zakaji kamar suna nuna maka yanda ba zaka taba samun naka bane.

“Dana yayi kaza.”

Sai kaji kamar sun goga maka gishiri akan ciwon ka.

“Yar waje na ce.”

Kamar suna maka habaici ne a fakaice, suna nuna maka sun samu baka samu ba, suna da su kai baka da su, zasu iya, kai ka gaza. Sosai akwai ciwo, hakurin bana lokaci daya bane ba, musamman idan addu’ar kowa bayan ka kyautata mishi bata wuce.

“Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kawo rabo mai albarka kaima ka samu mai maka addu’a.”

Da zai iya, da yace musu subar sauran addu’ar, suyi masa ita iya zuciyar su ba sai sun furta yaji ba, ba sai yaga wannan tausayin a cikin idanuwan su ba, suna kallon shi kamar rashin haihuwa wata bayananniyar nakasa ce da yake tare da ita.

“Bana sha’awar kara aure.”

Hannun shi da yake jikinta ta kamo tana hade yatsun su waje daya, tana jin alamun aikin karfi na yau da kullum a duk lokacin da ta rike hannun shi, inda da haske ma tasan in zata duba ba zata rasa sabon ciwo a jiki ba.

“Na sani, shisa nace ka bude zuciyar ka.”

Numfashi yaja yana saukewa a hankali.

“Ko na bude babu wanda zai bani ‘yar shi bayan a bayyane yake bana haihuwa.”

Dumtsa hannun shi da yake cikin nata ta yi.

“Inji wa? Kaf garin marake ko ‘yar wa ka nema za’a baka… Dan Allah ka duba bukatata.”

Baice komai ba, matsawa ya sakeyi yana hade sauran wajen da yake tsakanin su, itama bata ce komai ba, barin kusancin su tayi ya karasa musu sauran zancen.

*****

“Bangane kince ya karo aure ba? Adda idan ta zo ta haihu fa?”

Murmushi tayi ganin tashin hankalin da yake shimfide a fuskar Dije.

“To ai abinda muke nema kenan daman.”

Kai Dije take girgizawa, maganar ta kasa zauna mata, bata kasance cikin mata masu zafin kishi ba, ta duba, ta hango Datti da wata, akwai ciwo a hasashen da tayi, amman ciwo ne da zata iya rayuwa da shi batare daya cutar da ita ba. Sai dai da ta saka kafafuwanta a takalman Abu, ta haska, ta hango rashin haihuwa, ta hango Datti da karo wata, ta hango rabo a tsakanin su sai taji numfashinta ya fara neman tsayawa, kirjinta yayi wani irin nauyi. Idan tayi mata gori fa? Idan ta hanata daukar dan ko yar? Miji ne ta rigada ta kwace shi daman, idan ta kore ta daga gidan gabaki daya fa? Shikenan? Babu haihuwa kuma mijin ma babu shi.

“Kayya… Adda maganar nan abar ta, karki fara abinda ba zai bulle damu ba gabaki daya.”

Dariya kawai tayi, ba zata ce bata jin kishi ba, soyayyar Hammadi duk kauyen sun shaida kalarta daban ce, balle kuma ita da akalar soyayyar ta karkata akan ta. Kishin raba shi da wata, ba kishin ta shigo ta samu rabo da shi ba. Tana ma Hammadu son da take addu’a da dukkan zuciyar ta rashin haihuwar su ya fito daga bangaren ta. Shi din ya zame mata komai a lokuttan mabanbanta, a wajen haihuwarta ta rasa mahaifiyar ta, kowa zai shaida wuya bata kisa, da Abu bata rayu ba saboda wahalar da ta sha a wajen kishiyar mahaifiyar ta.

Tana dakin Hammadi ta sake rasa mahaifinta, sai ya zame mata wani bango da take jingine da shi, bangon da har yan uwan da suka nuna mata tsangwama a baya sun rabota suna morar wannan bangon. Da zuciya daya take son Hammadi ya kara aure.

“Zata iya shigowa ta samu rabo ke kuma ta rabaki da gidan.”

Daya daga cikin maganganun da tayi ta ji kenan daga yan uwa da abokan arziki, kowa da kalar tashi, basu sa ta tsorata ba balle kudirinta ya girgiza. Idan ta shigo ta samu rabo ta kore ta, sanadi kawai zata zama, amman tasan akwai hakan a kundin kaddararta, akwai rabuwa da Hammadi, ko da matar da zai aura bata zama sanadi ba kuwa. Tun shi Hammadin da zai kara auren yana gujema maganar har nacin Abu yasa shi karbar hakan. Sai gashi ana masa tayin aure a cikin garin Marake kamar bashi da wani laluri na rashin haihuwa. Kwadayin su bayyane a kan fuskokin su tun kafin ma su furta masa bukatar su.Shisa duk yayi watsi da su, ya cigaba da dubawa.

“Bana so in auro wadda zata cutar damu Abu…ina addu’a kar muyi dana sanin auren nan.”

Amman yanayin ta na kara masa karfin gwiwa, sadaka tunda ya aminta da batun auren duk rana sai yayi tunda yaji wani Malami daya ziyarci kauyen nasu yana cewa tana kare masifu. Cikin ikon Allah ya sauke idanuwan shi akan Pendo, sai yaji zuciyar shi ta natsu, duk da yaje neman auren ta wajen Mahaifin ta da sanin cewa zai iya hana shi, bai hana ba. Daga baya yaji cewa mahaifiyar Pendo bata so auren ba saboda rashin haihuwar shi, amman Pendo ta kafe cewar ita Hammadi yayi mata. Ba’a wani bata lokaci ba tunda kudi ba matsala bane aka gama shirya komai.

A cikin gidan shi ya kara gyara dakuna biyu da zasu kasance na Pendo. Abu bata san haka kishi yake ba, bata kuma san wata yaudara da cewar ta shirya ganin Hammadi da wata ba, sai da taga ana shigowa da kayan Pendo da jerin mutanen da suke rangada guda da wake-waken murna irin nasu na Fulani, har wata nama Pendo lakabi da

“Amaryar Hammadi, uwar ‘ya’yan shi”

Zuciyarta ta tsinke kamar kunun kanwar daya sha sukari, ruwan ya zubo ta cikin idanuwan ta a matsayin hawaye. Hawayen da har bayan kawo Pendo bai tsaya ba, hawayen da ta kasa boyema Hammadi daya shigo dakin ya zauna gefen gadon ta kusa da ita

“Dan Allah ki daina kukan nan Abu, kinga baki da isasshiyar lafiya, kiyi hakuri ki daina kukan nan kar ya saka miki wani ciwon.”

Habar zaninta ta kama tana goge idanuwanta da suka rine saboda kuka, wanne ciwo kuma? Har akwai wani ciwo da zata ji fiye da wanda take ciki a lokacin? Sai ace zafin rashin iyayi yasha bamban da kowanne, bata karyata ba, amman ba layin su daya da zafin kishi ba, sam ba wajen su daya ba. A gurin ‘ya mace zafi na kishi kalar shi daban ne, har abada bashi da abokin kwatance. Duk tausasan kalaman Hammadi sun rushe lokacin da taga ya mike yayi mata bankwana, wani abu da bai taba faruwa ba tun farkon auren su, sai dai idan basa cikin gida daya.

Wannan daren, wannan daren da ba zata taba mantawa ba, yanda taga ranar shi haka ya wuce yana zo mata da wayewar gari mai cike sa sabon lamari. Da fari zama suke da Pendo na lumana da girmama juna, kafin ma ta yunkura da sunan wani aiki Pendon ta rigata, idan ba Dije ta shigo ba, kusan komai tare sukeyi ranar girkinta da ranar girkin Pendon. Shima Dijen ce yanda duk Abu ta so ta sakema Pendo ta kasa, bata taba ganin Dije taki jinin wani babu dalili mai karfi ba sai akan Pendo. Itama Pendon ta kula, duk in Dije ta shigo bayan gaisuwa bata sake bi takanta.

Sai Abu ta hakura ta kyale Dije, musamman yanzun da itama take cikin tata matsalar ga daban akan Bukar. Canji ne dai Abu bata daina jin shi a tare da ita ba, wannan zazzabin na duk dare kamar anyi ruwan shi an dauke, sai kace bata tabayin ciwo ba, har jikinta ta fara mayarwa, fatarta ta murje ta kara haske, har Hammadi saida ya zolaye ta.

“Amarya ce ta goga mun kyallin ta.”

Tace masa tana dariya, tana jin dadin yanda ko na dakika daya bata taba ganin wani sauyi a tare da shi don ya kara auren nan ba. Har lokacin da Pendo ta cika watanni biyu da wasu yan kwanaki, lokacin da ta fara wani ciwo da duk alamun shi suka nuna cewa ciki ne da ita. Abu tayi mata murna, tayi ma Hammadi murna. Ta kuma shiga daki tayi kuka, kukan daya fito daga wani lungu na zuciyar ta da ya tabbatar mata da matsalar rashin haihuwar su ba daga Hammadi bane itace, tagani, kuma haka kowa zai gani.

Cikin kasa da sati daya maganar ta gewaye garin tsaf, dangin Pendo kuma suka matsa ma Hammadi akan suna so ta koma gida ta reni cikinta har sai yayi kwari tukunna. Da yake ba mai son hayaniya bane saiya amince musu, ranar da suka zo daukarta haka sukaita yarda maganganu, Abu ko fitowa daga daki batayi ba gudun fitina, ta kuma hana Dije da jikinta ke ciri jin irin maganganun da sukeyi, har wata na cewa ai gara su dauketa kafin Abu ta kassara musu yarinya da abinda ke cikinta. Kamar duk garin basu san cewa inda Abu bata amince ba Hammadi ba zai taba kallon Pendo da zancen aure ba.

Yanzun ma auren nata zai iya girgiza idan yaji gorin da suke yima Abu. Ai kam bayan sun tafi Dije mikewa tayi tana share hawayen takaici tabar Abu da ta kwanta kan gado wani abu na konewa a cikin kirjinta. Abinda ta danne bata bari Hammadi da yake ta binta da kallo ya gani ba, baice mata komai ba, amman zuciyar shi a bayyane take cikin idanuwan shi, tausayinta ya hana shi murnar cikin Pendo, sai taji soyayyar shi ta karu a zuciyar ta. Har tana sakata kokarin maida komai ba komai bane ta kuma cigaba da hakuri da kaddarar ta kamar yanda ta saba a tsayin shekarun nan.

Sai dai me, Abu bata da tumbi, tana cikin siraran matan nan da cikin su yake hade da marar su, yanzun kuwa gani take yana kumburowa kamar ana hura mata shi, ba ita kadai ta kula ba. Har Hammadi saida yayi magana, sannan Dije, sannan duk wani da zata hadu da shi, kamar wasa har motsi-motsi taji wani dare, bata iya komawa bacci ba saboda firgici, gani take kamar wata cutar ce ta kamata. Ranar da taje gidan su ne, Inna ta kalle ta sosai tace.

“Abu cikine a jikin ki.”

Maganar da ta girgiza duniyar da take tsaye kai tana matukar kadata har tana rasa bakin musantawa, ciki, akwai ciki a jikinta tabbas, amman kamar cikin da Innar take nufi daban ne da wanda ta sani. A ranar zance yayi zance, lissafin da Abu ta dainayi na ganin al’adarta ya tashi yana bayyana watanni har biyar, yana kuma shafe mamakin rashin bayyanar cikin saboda na fari ne, idan da tana da jiki ma sai anyi da gaske za’a kula in dai ta batun girman cikine. Ko a mafarki bata hango ba balle kuma faruwar shi a gaske. Shikenan? Rana daya Allah ya wanke mata gorin juya. Da fari taki yarda, ta mike, ta koma ta zauna tana tuna yanda babu wani abu da yafi karfin Allah.

Kuka kuwa na murna babu wani makusanci na Abu da bai tayata da shi ba. Hammadi kuwa hannuwa ya dora kan cikin nata yana kasa cewa komai, a durkushe yake amman ya kasa dagowa, sai da ta dora nata hannayen kan nashi tukunna, hawaye yake, hawayen da bai san yanda akayi suka fara fitowa ba ballantana ya iya tsayar da su, hawayen shi da suka bude mata kofar nata.

“Abu kinga ikon Allah ko? Kinga munyi garaje? Munyi gaggawa, da mun hakura…”

Kai take girgiza masa, ba suyi garaje ba, har kasan ranta take jin auren Pendo da Hammadi babu garaje a cikin shi, ba kuma kuskure bane ba. Kallon shi tayi da wani yanayi cikin idanuwanta.

“Ka godema Allah kawai Hammadi Am, mu godewa Allah da tarin ni’imomin da yayi mana… Kar muce komai banda godiya.”

Kai kuwa ya daga mata, murnar da tayi ba zata misaltu ba, godiyar ta ga mahaliccinta zata cigaba dayi tana karawa har tsayawar numfashin ta, sai dai akwai wani sanyi da zuciyarta tayi, sanyin da take ji har cikin kasusuwan ta. Shisa murnar da kowa yake tayata da murmushi take amsawa. Da yake labari baya boyuwa, sati bata cika ba aka dawo da Pendo, dariya ma suka bata, maganganu dai basu gaji ba, ta kula a jinin dangin Pendon yake.

“Dan Allah kiyi hakuri da abubuwan da yan uwana suke ta fada…nayi miki murna har raina… Allah ya sauke ki lafiya.”

Pendo tace mata bayan kowa ya watse ta shiga tayi mata barka da dawowa. Murmushinta ta fadada.

“Babu komai Pendo, Allah ya sauke mu lafiya zakici.”

Murmushi Pendo tayi a kunyace tana kasa amsawa, babu komai a tsakanin ta da Abu sai alkhairi, karamcin matar daban ne. Zama suka cigaba dayi na aminci har cikin Abu ya cika wata bakwai, tana zaune tana tukin tuwon da Pendo take tsaye a kanta saboda taki tashi tabari ta tuka, taji bayanta ya amsa, amsawa da zata rantse kashin daya fara daga wuyanta zuwa kugunta ne ya karye, kafin ta kira sunan Allah ya sake karyewa a karo na biyu a waje daya, wannan karin yana hadawa da wasu kasusuwa cikin mararta da batasan akwai su ba, suma karyewar taji sunayi.

Pendo ta taimaka mata ta mike tana kiran duk wani sunan Allah da yazo bakinta ko zata samu sauki, har suka karasa daki Pendo na mata sannu, amman can nesa take jiyo muryar Pendo kamar basa daki daya saboda ciwo. A daddafe Pendo ta karasa tukin tana sake leka ta, amman ciwo kamar gaba yakeyi, ta katangar ta kwala ma Dije kira ta zagayo. Abu kamar wasa, nakuda ce ta taho ma Dije gabaki daya, Pendo ce ta saka mayafinta tana ficewa, dan aike ta samu aka aikama Hammadi da harda gudu ya hada yana ganin nisan da gidan shi yayi da gonar.

Zuciyar shi a cikin tafukan kafafun shi lokacin daya shiga gidan, ya samu cikin yan uwan Abu mutum biyu sun zo, kasa ce musu komai yayi, gaisuwar su ma bayajin ya amsa, wani gunjin ciwo ya juyo daga cikin dakin da yasan daga Abun shine, gunjin da yasa shi zabura kamar zaiyi cikin dakin ya rabata da abinda yake azabtar da ita haka. Dole ya fita daga gidan kar suga hawayen shi, tsaye yayi a kofar gida, anan Datti yazo ya same shi, suka tsaya suna jiran ikon Allah. Har akayo Magriba aka dawo babu wani canji, gabannin isha’i ta haifo danta da ya fado babu rai.

Tun kafin su fada mata taji a jikinta, sanyin da zuciyarta yayi randa tasan da cikin yasa ta fara shirya ma zuciyarta karbar kowacce kaddara tazo mata, saiya zamana dacin da taji takaitacce ne, tana maye gurbin shi da hamdala, ko yau mata suke zancen nakuda tana da labarin bayarwa, ko yau ake zancen haihuwa babu wanda zai kalleta ya wareta. Idan kyautar iya haka ta tsaya ta gode, ta kara godewa. Da ta rike yaron ma addu’a tayi masa, tana kara godema Allah kafin ta mika musu shi. Aka taimaka mata ta mike don ta gyara jikinta.

Hammadi ne ya kasa tsaida hawayen shi, a karo na farko ya dandani abinda Datti yaji, tausayin Abu na cika zuciyar shi fal, kima ta ‘ya mace da darajar ta na daguwa a idanuwan shi.  Haka aka suturta ta gawar akaje aka binne ta. Ko Pendo sai da tayi kuka har ya zamana Abu ce take lallashin ta. Gani take itama abinda yake cikinta kamar ba rayayye bane ba. Danginta nata hauka da yarda maganganu, idan kuma dakon gawa takeyi fa? Kowa mamakin karfin hali irin na Abu sukeyi, ita kuma mamakin yanda suka karkata hankulan su kaf akan rashin da tayi, suka kasa ganin girman kyautar da Allah yayi mata.

“Bansan me zance miki ba… Na rasa me zance Abu.”

Hammadi ya fadi bayan sun samu kebewa da juna, murmushi tayi.

“Ba sai kace komai ba, ka kara tayani godewa Allah, hakan kawai ya wadatar.”

Numfashi Hammadi ya sauke, kallon ta kawai yake yana jinjina ma karfin zuciya irin tata. Har zancen sai da Pendo tayi masa.

“Anya akwai irin Adda Abu kuwa? Gaskiya kaf Marake ban taba ko jin labarin irin ta ba.”

Dariyar alfahari yayi, Abu, Abun shi kenan.

*****

Duk wata kulawa Pendo na samu daga wajen Abu har cikinta ya shiga watan haihuwa, inda aka sake daukarta zuwa gidan da zata haihu kuma tayi wanka acan. Yanda Abu taji gidan yayi mata shiru duk sai kewar Pendon ta addabe ta, kaji motsin mutum ma wani abu ne, musamman yanda suke zaman lafiya. Da hakane har a wajen yan uwan Pendo da taje gida duba ta, to Dije ta fara mata maganar.

“Dan Allah Adda karki ce zakije gidan su Pendo, kin san ba mutunci gare su ba…suna iya yaba miki bakaken maganganu.”

Ko da Dijen batayi magana bama ba zataje ba, takan dai tambayi Hammadi, kuma tana cewa ta gaishe da ita, duk da shi da bakin shi bai taba ce mata yaje wajen Pendo ko kuma zaije ba. Ta san ba zai rasa zuwa ya duba su ta ba. Ranar talata labari yazo ma Abu cewar Pendo na nakuda, kamar tayi tsuntsuwa taje haka ta dinga ji, sai dai bata wani dauki lokaci ba, tunda duka gabannin azahar ne, kafin la’asar ta haifi yarta mace, Hammadi da kanshi yazo yana fada mata, saida ta rungume shi don murna. Su duka biyun sun kasa daina fara’a.

Tare suka koma gidan su Pendo, bata damu da kallon da aketa mata da maganganu kasa-kasa ba, kishine suke taya Pendo, bai kuma dameta ba. Musamman yanda Pendo ta wanke mata zuciya da murmushin daya nuna najin dadin ganinta ne

“Adda Abu nayi kewarki, baki zo kin ganni ba, yau dinma bani kika zo gani ba.”

Dariya Abu tayi, yarinya ce basu bata ba, tana goye bayan wata kakar Pendo akace wanka akayi mata tana bacci, ba’a so ana yawan sauke jinjira haka. Murmushi tayi tana amsawa da.

“Allah ya raya mana cikin aminci.”

Tayi musu sallama tare da yima Pendo alkawarin zata dawo ta sake duba su, har takai kofa ta juyo muryar Pendo.

“Adda Abu…”

Juyawa tayi, murmushi Pendo tayi mata

“Nagode da dukkan karamcin ki, na gode.”

Kai kawai ta daga mata, da ta san cewar wannan ce rana ta karshe da zata saka Pendo a idanuwanta da ta tsaya sun kara hira, da ta tsaya ko ba zasuyi hira ba tayi ta kallon ta, ta kara daukar wasu hotuna na Pendon da zata adana tana dawo dasu tamkar tarihin da Pendo ta zama a safiyar sunan ‘yarta da ta tashi da wani irin ciwon ciki. ‘Yar da dangin Pendo sun san cewa kulawar ta zata koma karkashin Abu ne gabaki daya da basu hanata daukarta a ranar da aka haifeta ba.

Sai dai wasu kaddarorin sun fi gaban hasashe.

Wannan shine tunanin Abu lokacin da take rike da yarinyar da taci suna Saratu, hawaye fal a idanuwanta.

Kaddara
Kowanne rai da irin tashi.

Dan Allah karku manta da danna mun like, idan kun dannan ku daure ku yi commenting ko da fatan alkhairi ne.

Nagode

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 11

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 25Rai Da Kaddara 27 >>

3 thoughts on “Rai Da Kaddara 26”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×