Skip to content
Part 56 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Hannunta ta saka cikin na Salim, bashi bane karo na farko da hannuwansu ya shiga cikin na juna, amman yanda ya dumtsa yatsunta yau sai taji kamar an halitta musu wajen zama a cikin nashi ne, daya dan juyo ya kalleta, sai ya dago dayan hannun shi yana goge mata jambakin daya haura gefen lebenta da yatsanshi yana yawatawa da idanuwan shi kan fuskarta kamar yana neman wani abin da baiyi mishi ba ya gyara, kafin ya dan daga kai alamun komai yayi. Yaja hannunta

“Hamma bana gani sosai”

Ta fadi saboda komai yayi mata dishi dishi, ya saka gilashinta cikin aljihun shi, so take ta ganshi sosai, yau da ya saka babbar riga, dinkin farar shadda, sai hular shi da aikin shaddar da suke ruwan kasa mai cizawa, itama farar rigace a jikinta da ba zatace ga tsafin da Adee tayi a cikin kwana daya aka dinka rigar ba, sai dankwalin da aka daura mata shine ruwan toka, aka yafa mata bridal net fari da yasha duwatsu ruwan toka masu kyalli, fuskarta takeji tayi mata nauyi da kwalliyar da akayi mata. Sai dai bai kai nauyin da takeji a zuciyarta ba

“Ni ina ganar mana komai…”

Dan rikoshi ta sakeyi har saida ya tsaya yana kallonta, ta turo bakinta da yasha jambaki tana saka jikinshi daukar dumi

“Ina so in ganka.”

Numfashi ya sauke yana janta har gaban motar shi, ya saki hannunta yana zagayawa cikin motar ya dauko sabon gilashin da tuntuni ya zabi frame daya tambayeta awon, ya manta ne saboda abubuwan da suka tarar masa, baije ya karba ba. Bude dan akwatin yayi ya ciro shi yana zagayawa ya sameta inda take tsaye, da kanshi ya saka mata madaidaicin gilashin daya zauna a fuskarta yanayi mata kyau, data kalle shi da mamaki a idanuwanta

“Bana son wannan frame din naki, yana karemun rabin fuskarki”

Dariya tayi mai sauti, tana kallon shi sosai, tasan yana da kyau, yana cikin irin mazan da ko a titi sai kayi sa’a zaka ga giccinsu, sai dai yanzun da waya ta wadata a hannuwan mutane to zakaga hotunan maza irin Salim na yawo a social media, musamman groups na mata ana musu lakabi da mazajen novel. Bambancin kawai, yawancin mazajen novel sun san suna da kyau, suna kuma da jin kai, sai kudi, zunzurutun kudin da Salim bashi dasu. Gasu miskilai na bugawa a jarida, Salim kuma hayaniya ce bayaso, amman yana magana, yana hira a zababbun wajaje da kuma zababbun mutane. Sannan sam yanayi kamar baisan yana da kyau haka ba.

“Kayi kyau…”

Ta tsinci kanta da furtawa a hankali, dariya yayi yana bude mata motar batare da yace komai ba, shiga tayi, ya rufe murfin, sannan ya zagaya yana shiga. Sun so kama waje ne don yin walimar da hotunan su, amman Yelwa tace in dai ba zata takura musu ba ayi a gidan Julde, suka amince, tunda kacokan walimar don ta gani aka shiryata, idan a cikin gida take son ta kasance zasuyi hakan. Daman da kyar likita ya basu aronta na awanni uku, a cewar shi jikinta yayi raunin da take bukatar taimakon likitoci kowanne yan mintina. Da suka karasa harabar gidan yayi parking, yana fitowa ya ga su Khalid a tsaitsaye, sai Adee da waya a hannunta, bakinta yaki rufuwa, kusan zaice shi kadai ya fita farin ciki da auren

“Hamma…”

Ta kira tana wani iri da fuska kamar mai son yin kuka, murmushi kawai yayi yana budewa Madina kofar ya mika mata hannu, ganin yanda take kallon shi yasa shi kamo hannun nata kawai yana dagota ya taimaka mata ta fito daga motar

“Woo”

Cewar Khalid yana sa Salim hararar shi

“Ina mai hoton ne wai? Yazo nan ya fara haskamun su ya baro tsofaffin can dan Allah”

Khalid ya fadi yana juyawa ya shiga cikin gidan ya kira mai hoton, tare da Nawfal da Murjanatu suka dawo, itama doguwar rigace a jikinta kalar ruwan toka mai cizawa, tayi kyau har mamakin kyan nata Madina ta kanyi, gata yar gayu, dinkin rigar iri daya dana Adee, itace ta karaso tana dan rungume Madinar da fadin

“Ina tayaki murna”

Cikin harshen fulatanci, murmushi Madina tayi a kunyace. Nawfal kuwa yana daga bayan Khalid, kamar yana son boyewa komai. Sai kallon yanda Salim yake kara riketa yakeyi, haka kawai yake jin zuciyarshi tayi masa nauyi. Ya san Madina zatayi aure wata rana, amman bai taba kawo mata auren nan kusa ba, lokaci daya haka, kuma da Salim. Ji yake bai shirya ba, anyi masa bazata, kamar ya kamata ace an bashi lokaci ya shiryawa ganinta tsaye a kusa da wani a matsayin tashi, mallakinsa. Yanzun ta ina ake so ya fara? Yana daga ido ya kuwa ga Salim ya tallabi habar Madinar yana kallon cikin idanuwanta, kafin ya girgiza mata kai a hankali kamar yana lallashinta, nata kan ta gyada masa, yanayi ne da shi da Murjanatu suka sha tsintar kansu a ciki, yanayi ne kuma da ganin Madina a cikin shi yanzun yasa shi jin kamar Salim dinne ya mika hannu cikin kirjinshi, inda zuciyar shi take ya rikota yana matsewa da dukkan karfin shi.

Da Khalid yaja shi don ayi musu hotuna ma binshi kawai yakeyi, duk abinda akeyi a wajen jinshi yake wani irin sama-sama, bai samu sauki ba sai da yaji hannun Murjanatu a cikin nashi, ta dumtsa kamar ta karanci wani abin yana damun shi, bata kuma sake shi ba har sai da suka koma falon, inda Julde, Saratu, Yelwa, Kabiru harma da Daada suke zaune. Yelwar tayi kyau cikin farin leshinta mai ratsin ruwan toka a jiki, fuskarta tayi wani irin fayau, idan baka sani ba, babu yanda za’ayi kasan tana dauke da ciwon dake neman rayuwarta. Idan kuma ka santa a baya, to tabbas zaka gane dalilin da yasa kaf Marake ake cewa ba’ayi matashiya mai kyawunta ba. Gefe da gefenta Salim da Madina suka zauna akayi musu hotuna wajen kala goma, kafin Salim ya mike yana bari a dauke su daga ita sai Madina da take ta kyafta idanuwa alamun tana kokarin maida hawayenta.

Yelwa ba ta da karfin tashi, shisa duk wasu hotuna da akayi a zaunen tayi su, suka sallami mai hoton kafin su baje a tsakiyar falon inda kayan ciye ciye da tarin lemuka suke shirye cikin farantai masu kyau, kowa ya dauki kananun filet yana zuba abinda yake marmari, Salim ne ya zubawa Madina ganin tayi wani irin sanyi, karba tayi tana daukar samosa daya ta gutsira tana taunawa a hankali badon tana gane dandanon ba

“Bani ruwa Madina…”

Yelwa ta fadi, da sauri Madina ta dauki robar ruwa ta bude tana mika mata, ta karba hannunta na rawa, dakyar ta kai bakinta ta kurba, ta dawowa da Madina da take nazarin yanayinta robar, ta karba ta rufe ta ajiye, jingina bayanta Yelwa tayi da kujerar da take zaune ta lumshe idanuwanta, taja wani numfashi

“Bansan me yasa ake saka cabbage a abin nan ba”

Khalid ya fadi yana bata fuska ya hadiye spring rolls din dakyar, yana kuma saka Madina dauke idonta daga kan Yelwa ta kalle shi

“Me kake so a saka a ciki to? Alayyahu?”

Cewar Nawfal da ya sake kurbar lemon da yake hannun shi, don duka abubuwan da suke a baje a wajen, ba cimar shi bane ba.

“Malam ina magana ne da mutane ‘yan uwana da zasu fahimci abinda nake cewa, ina nufin tunda ina magana ne kan abincin mu, mu mutane.”

Ruwa Nawfal ya zuba a hannu shi yana yarfawa Khalid daya kai masa duka yana kaucewa da sauri, ganin Khalid din na neman wani abu da zai buga masa yasa shi fadin,

“Hamma ka yi masa magana…”

Juya idanuwan shi kawai Salim ya yi

“Khalid karka dake shi, me yasa baka da hakuri ne wai?”

Cewar Adee tana kwalawa Khalid din robar lemon da ta gama shanyewa tana dorawa da

“Magana nake maka…”

Baki a bude Khalid yake kallonta

“Baki ga abinda yayi mun ba? Murjanatu”

Khalid ya karasa yana kallon Murjanatu da tayi dariya

“Kayi hakuri Hamma, bakina daure yake da igiyoyin aure”

Kai Khalid ya jinjina

“Bakin ki suka daure kawai, amman nasan basu hanaki ganin gaskiya ba, ki rabani da mijinki…”

Dariya takeyi, don ko kafin tazo ta gansu, ta waya ma da video call shi da Khalid din ba gajiya sukeyi ba. Idan kagansu daban daban zaka ga matasan samari masu hankali da cikakkiyar nutsuwa. Amman idan kagansu tare to zaka ga yara ne da suke makale a jikin samari, shekarun da hankalin suke ajiyewa a gefe suna zuba yarintar da Lukman ma da yake kanin su bayayi. Wani lokacin sai Salim ya raba musu waje.

“Kai Bajjo koma can kujerar.”

Amman ba za’ayi minti goma ba zakaji wani a ciki yana kai kara da cewar dayan yana kallon shi, karshe sai Salim din ya hada da zagi sannan zasu natsu. Wani irin shiru ne ya gifta cikin dakin na dakika, dan kowa a cikinsu zai iya rantsewa har iskar dake yawo a dakin sai dai ta tsaya tare da shirun, kafin zuciyar Madina tayi wata irin dokawa da ta sakata juyawa ta kalli Yelwa, tayi luf a cikin kujerar, idanuwanta a lumshe, kallonta Madina takeyi sosai tana so taga tayi motsi ko yaya ne. Ganin bata motsa ba ya sakata tabata tana rasa a cikin jerin sunayen da ake kiran uwa dasu wanne yafi dacewa ta kirata dashi kafin harshenta ya iya hada jimlolin

“Ummi…”

Yanayin da ta kira sunan yana saka hankalin kowa a dakin komawa kan Yelwa, Julde ne ya taso daga inda yake yana ture har Madina ya riko hannun Yelwa da kamar hakan take jira ta sulale akan kujerar, ya kuwa rikota gabaki daya yana dagota hadi da kallon su Salim cikin neman taimakon daya kasa furtawa. Salim ne ya tashi yana kokarin kama hannunta amman Julde ya hana shi, girgiza masa kai kawai yakeyi

“Daddy dubata zanyi, likita ne ni ka manta.”

Sannan Julden ya barshi ya rike hannun Yelwa da yaji yayi sanyi a cikin nashi. Baisan me yasa ya fara kallon Daada ba, ya kuma yi dana sanin hakan, murmushi tayi masa, wani irin murmushi mai ciwo kafin hawaye su silalo mata, ta kai hannu ta goge su

“Ta rasu ko? Allah ya karbi ajiyar shi.”

Ta karasa muryarta na karyewa, sai ta kalli Julde, tana jin yanda shi kadai ya rage mata

“Bukar”

Wani sashi na zuciyarta ya kira mata sunan shi, amman yana ina? Julde kadai take dashi, haka tata kaddarar take, haka Allah ya tsara mata, ta amsa sunan uwa, a tare da sunan ta fuskanci kalubale kala-kala, tun daga yaran da suka fito daga jikinta dan ta amsa sunan uwa kawai, har kan wanda suka fito suka rayu da ita ta amsa sunan a aikace, a lokaci daya suka nuna mata yanda ta gaza a matsayin uwa, shima Julden wanne tabbaci take dashi na cewar shi zai zuba mata kasa? Ba ita zata ga fita da gawar shi ba?

“Karka ce mun ta rasu Salim…karka fadamun ta rasu.”

Julde yake fadi yana jin duniyar na jujjuya mishi.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Madina ta furta, a zaune take, amman sai taji kamar ta sake komawa ta zauna, kamar kuma wani abu ya daki duka ilahirin jikinta

“Daddy…”

Salim ya kira a tausashe, duk wata alama ta mai rai tabar jikin Yelwa, sai dai in fuskarta ka kalla, da siririn murmushin da yake kai, zaka iya rantsewa bata rasu ba. Sai dakin da yayi shiru baka jin komai sai sautin kukan Saratu, Adee da Murjanatu da suke ganin abin kamar almara. Nawfal kuwa ji yayi kamar an zare masa lakkar jikin shi, zai iya tuna sau nawa yaje makabarta, kuma shima tun yana yaro ne, ya kasa dauke idanuwanshi daga kan Yelwa da yanzun suka gama hotuna da ita

“Bajjo…”

Ta kira shi kamar ta sanshi, tun ranar daya fara ganinta taji suna kiranshi haka, itama ta kira shi, tana kallon shi kamar akwai tarin abinda take son fada masa, da ta samu dama kalamanta basu tsawaita ba.

“Kayi kama da Hamma Bukar, sai dai baka da sanyin shi, wannan sanyin da shi kadai yake dashi…idan kayi dariya kamanninku sunfi fitowa.”

Murmushi kawai ya iya yi mata zai tuna, saboda baisan meya kamata yace ba, Bukar din ya bace a tunanin shi, baisan kamannin shi ba balle ya hadasu da kalamanta ya auna yaga gaskiyar su. Yau ma kuma tana ganin shi ta kirashi.

“Ina wuni, ya jikinki?”

Ya tambaya, tayi masa murmushi

“Alhamdulillah…gani a zaune.”

Sai ya tsinci kanshi da yin dariya.

“Allah ya baki lafiya”

Bai tuna ta amsa ko bata amsa ba, Allah dai ya amsa addu’ar tashi, ga lafiya nan ta samu, ciwon yazo karshe. Khalid ma ya kasa dauke idanuwan shi daga kanta. Ashe duk wani labari na mutuwa da yake ji, duk wani kai gawa da akeyi da shi, duk tunanin mutuwar shi da yakeyi a kullum, duk yanda yake fadawa kanshi ba wai sanin mutuwa kawai yayi ba, har zuciyar shi tasan da zamanta karyane, bata zo kansu bane shisa yake ganin haka. Wannan zantukane da yaudarar da kowanne dan adam yakeyiwa kan shi, daman haka mutuwar take? Lokaci daya? Ba zaice bata nuna alama ba tunda tana ciwo, amman haka kawai? Yau? Duka suna zagaye da ita suna labari, suna dariya har ta ratso ta cika umarni ta fita suna nan zaune basu ji alamunta ba.

Wanne irin zumunci ne wannan? Ba ma ance ko mutuwa na kunyar idon iyaye ba, ga Daada a zaune, amman mutuwar bata ki dauke mata yarinyar da bata jima da dawowa rayuwarta ba. Kallon komai Khalid yakeyi kamar shirin fim, musamman yanda Salim yake fama da Julde daya kamo gawar Yelwa ya kwantar da kanta a jikinshi yana dan bubbuga fuskarta cikin son ta bude idanuwan da ta riga da tayi musu rufewar karshe. A tsakanin kukan su Saratu, hawayen Mami, da wahalar Julde ta karbar mutuwar tilon yar uwar shi, haka suka tattara suka fita daga dakin dan a suturta, haka kuma kukan da sukeyi bai hana Adee da taimakon Saratu suka shirya Yelwa suna saka mata kayanta na karshe, ankon da yake jiran kowanne musulmi.

Haka su kuma da tarin mutanen unguwar su da suka zo sukayi mata sallah, suka dauki gawar suka nufi makabarta, a hanya Khalid yake jinjina Ikon Allah ganin tarin al’ummar da suke biye, ganin kuma Yelwar duka yaushe tazo Kano, waya santa da zaizo dominta? Wanda suka sansu suka zo donsu din mutanen unguwa ne, wannan al’ummar kuwa ta wuce mutanen unguwa, harda masu adaidaita sahu kasancewar makabartar tsallaken titi, haka suka dinga parking suna fitowa, can ya tsinkayi muryar wani yana tambayar

“Wai waya rasu?”

Wani kuma na amsa mishi da,

“Bansani ba wallahi, kamar wani yace wata babbar malama ce, shine nace bari ayi rakiyar dani, Allah ya yafe mana ya datar damu da kyakkyawan karshe”

Murmushi Khalid ya tsinci kanshi dayi, Allah kenan, mai son bayinshi da Rahma, a cikin alamomi na dacewa dai wannan dimbin jama’ar da suke raka Yelwa ya nuna cewa tana daga cikin mutanen da sukayi dacen karshe me kyau. Ya dauka abinda zaisa Salim hawaye ba karami bane ba, amman yanda aka gama binne Yelwa, Kabiru ya mike ya koma ya fadi a gefen kabarin suka kamo shi yana hawaye babu wanda bai karyawa zuciya ba.

“Ka sakeni Khalid, dan Allah ku bani yan mintina, zan tashi, nima ba dadewa zanyi ba, inaji a jikina ba wani tsayin lokaci zamu dauka a tsakanin mu ba, ku barni in kara bankwana da ita kafin in tarar da ita dan Allah…”

Sakin shi sukayi, suka tsaya, ya kusan mintina biyar kafin ya iya mikewa, su juya suna barin Yelwa da halayenta duk kuwa tarin soyayyar da sukeyi mata. Haka suka koma suka shimfida tabarmi aka kafa rumfa ana karbar gaisuwar mutuwar da ciwo baisa sun hangota kurkusa haka ba. Kamar yanda kwanakin suka shiga wucewa kamar kiftawar idanuwa, daga asabar din rasuwar har wata asabar din ta zagayo da ta cika kwanaki bakwai dai-dai, ranar da tayi dai-dai da ranar da za’a share zaman makokin, suna zaune da tsirarun mutanen unguwa da kan tayasu zaman, da kuma Julde da yake a tsakiyar Khalid da Nawfal, yayi duhu a cikin kwanakin yayi zuru-zuru dashi, alamar mutuwar ta dake shi ba kadan ba.

Kamar daga sama ya tsinkayo wata murya da lokaci ya fara dishe masa tasirinta na fadin.

“Hamma wa na rasa? Na zo a makare ko? Kace mun ba Daada bace ba, dan Allah kace mun ban rasa Daada ba?”

Ya kara maganar kafafuwan shi dake masa barazana na saka shi durkushewa akan tabarmar kan dole, wata irin iska na kadawa a lokacin da Julde ya dago idanuwanshi, ya sauke su akan Bukar, akan fuskar Bukar da take cike da kasumba, akan fuskar Bukar da yayi wata irin rama kamar wanda ya tashi daga jinya, akan fuskar Bukar da hawayen da suke saukar masa, sai yaji jikinshi ya mutu, yaji kamar bashi da sauran kalamai, kamar idan yayi kwakkwaran motsi zai farka yaga mafarki yakeyi, abinda bai tabayi ba a tsayin shekarun nan, har shakkun kaunar da yakewa Bukar saida ya darsar masa, ganin bai taba ko da mafarki dashi ba.

“Daada ce ko Hamma? Na rasata? Kaddarar haduwar mu ta kare tun a wancen lokacin…”

Kai Julde ya tsinci kanshi da girgizawa

“Yelwa ce…Daada na cikin gida”

Kai Bukar yake jinjinawa, wasu hawayen na sake sauko masa da jin mutuwar Yelwar, kafin ya maida dubanshi kan Nawfal da ya kura masa ido ko kyaftawa ba yayi. Ya bude baki da nufin magana Nawfal ya mike, ko takalma bai saka ba yabar wajen, baiga alamar lafiya a tare da Bukar ba, Yelwa ta fara dawowa, suka saka rai akanta gabaki dayansu, sai ta koma, ta tafi inda hakuri ya zame musu dole tunda ba dawowa zatayi ba, kwana nawa a tsakani, shikuma zaizo? Duk shekarun nan? Sai yanzun? Sai yau kamar sun hada baki da Yelwa.

Ba zai tsaya ba
Ba zai saka rai ba
Bukar ba zai dawo ya gina masa burin shi mutuwa ta gifta ta rusa komai ba…

*****

Comments da likes din karku gaji, idan kunyi like ku daure da comment din, sai mu koma whatsapp mu sha hirar can.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 55Rai Da Kaddara 57 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×