Skip to content
Part 29 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Lokutta mabanbanta tana jin ana bada labarai akan soyayya, idan kafin aurenta da Datti ta dauka so wani nisantaccen abune da yafi karfin mutanen karkara, kamar so din nau’i ne najin dadi da bakowa yake da rabon samun shi ba, da yawan mutane, cikin su harda wasu a cikin ‘yan uwanta mata, idan ana bada irin wannan labaran, ace an kalla a fina-finan hausa a binni, sai suyita dariya, suna daukar abin a matsayin shiririta.

“So ya wuce a baka ci, sha da suttura da wajen kwanciya?”

Daya a cikin yayyanta ta taba fada, zantukan da suka zauna mata, zantukan da ta hasaso ta kuma gina zamantakewa ta aure a kai, tunda yau da gobe tasa taga hakan a zaman Baba da kuma su Innarta, ciyarwa dai-dai karfin shi tsaye yake akan su, haka ta taso tagan su zaune a mazauni mai kyau, duk tsananin damuna ko naso rufin dakin su bayayi, a maimakon yanda takan ji makwabta na koken dakunan su sun kwana suna yoyo, har bacci yakan gagara samuwa a wasu dararen wajen iyaye da kuma yaran su. Haka tufafi, zaka kirga gidaje goma a bayan su, ka girka wasu goman a gabansu, haggu da kuma dama, ba’a samu kwara biyu da zasuyi gogayya da su wajen saka tufafi ingantattu ba.

Lokacin bikin sallah, sakin da zasu saka yafi na kowa kyawu da tsada, duk kuwa kasancewar Baba bahaushe, in har zasuyi shigar fulani, to sakine me kyau da saika duba zaka same shi a gidan wasu. Juma’ar duniya tun da Dije ta fara hankali, ta kuma fara bambance tsakanin ranaku Baba bai taba fita ya dawo hannu biyu ba, saiya riko ‘yar tsabarshi. Shisa ta kara aminta da zantukan duk da taji na cewar so dai baya wuce irin wanda Baba yake nuna ma su Inna, baya wuce irin wanda yake nuna musu sudin ma a matsayin ‘ya’yan shi, duk da a nasu kalar son, a wajen Baba ya bambanta da nasu Inna, yakan shigo da abu ya basu baiba su Inna ba, wannan so ne na tsakanin mahaifi da yaran shi.

Da zama na aure yazo kanta, a cikin yau da goben da ta tsinci kanta tare da Datti ta samu wannan soyayyar da aka ce itace karshe a zaman aure, da farko ta yarda, babu wani so a zama na auratayya daya wuce samar da ci, sha, suttura da makwanci me kyau. Sai Abu da Hammadi suka zirkita tunaninta, suka canza yardarta, suka nuna mata a zama na aure, idan har ana magana ta so, ya wuce duk wani lissafi da kwakwalwarta tayi. Sai ya zamana tana kallon duk wani abu daya danganci zamansu da Datti, tana dubawa, tana neman irin soyayyar Hammadi da Abu a ciki.

Ba don ta raina ta Dattin ba, da fari ma bata ganta ba, bata ga wata soyayya data wuce irin wadda kowa yake dauka ita kadaice a cikin zaman aure ba, sai da suka binne yaransu na biyu, sai da ya riketa a jikin shi a lokacin da suka rasa na ukku.

“Baki ga su Hamma suna nema basu samu ba Dije? A cikin matattun nan ba za’a rasa rayayye ba, Allah zai kara bamu wani, wanin da zai rayu.”

Sune kalaman daya fada mata bayan ya dagota daga jikin shi yaga hawayen da ta kasa tsayarwa. Sai kuma ta ga soyayyar shi da kaddara ta raba zaman su. Sai ta fahimta, auren ne abu daya, zaman ya bambanta. Mazan ne suke amsa suna daya, halayen su ya bambanta, soyayyar ce sunanta baya canzawa, amman hanyoyin nunata suna da yawa.

“Kina son Baabuga? Dije kin so Baabuga a zamanku?”

Tambayar ta Datti ta daketa, dukan da ko tunawa tayi sai ta sake jin zafin shi, da ta daga idanu ta sauke cikin nashi da nufin amsa mishi da abinda tasan zai kwana biyu yana jin zafin shi, sai maganganun suka makale mata. Kishin da ta gani cikin idanuwan shi nasa ta jin kamar an watsa mata ruwan kankara, ciwon da yake zuciyar shi ya bayyana a saman kishin yana sata bude tata zuciyar dan ta fahimci abinda yakeji, ta fahimci dalilin da yasa tun daga jin maganar cikin Bukar zuwa yanzun ya zabi yasa ta dora ayar tambaya akan duk wata kyautatawa daya taba mata, duk wata magana ta so daya taba fada mata.

“Me yasa kika yarda ‘dan shi ya zauna gidan Hamma? In shiga kullum in kalle shi? Me yasa ba zaki ga bana so ki hakura kibar masa ‘dan shi ba Dije? Me yasa kike nuna mun ni kadai ban isheki rayuwa ba sai da wani bangare na Baabuga a kusa dake?”

So take ta fahimce shi, amman da ta fara saiya fadi wani abu da zai dakushe mata hasken da ta fara gani.

“Dan Baabuga ne, na sani, dan Allah Datti ka bude udanuwanka, sau daya kawai, ka bude idanuwanka ka kalli Bukar, ka kalle shi kaga ba d’an Baabuga bane kawai, d’ana nima…”

Kai Datti ya ke girgiza mata tun kafin ta k’arasa zancenta, yana nuna mata ba zai taba kallon Bukar yaga wani b’angare nata a tare da shi ba, idan ya kalle shi Baabuga kad’ai zai gani, Baabuga da baya son tuna zama ya had’ata da shi, sai Bukar ya zame mishi wata tunasarwa da ya tsana fiye da komai. Hawayen da suka zubo mata ta share.

“Ya kake so inyi? Me kake so in fada maka? Yanda duk zance maka ban taba son Baabuga ba idan nace maka ina son Bukar zaka karyata hakan. Idan nace maka banyi dana sanin haihuwar Bukar ba zaka kara cewa dole na so Baabuga… Ka fadamun abinda kake so inyi ka yarda dani Datti, ka fadamun.”

Cikin idanuwa yake kallonta, yana jira ta sake goge hawayenta ta kuma kara saka idanuwanta cikin na shi.

“Ki mayar masa da d’an shi, ki mayar masa da shi Dije.”

Numfashi taja ta fitar tana kauda kai kawai, saboda ta sani, zuciyarta ce taso karyata ba hakan zai bukata ba. Hammadi ya roketa karta sake biye ma Datti akan maganar Bukar, amman taya zata iya kauda kai bayan duk rana idan bai mata maganar ba, idanuwan shi da suke cike da zancen suna bin duk wani motsinta? Bata da yanda zatayi ta kauce ma maganar Bukar da Datti, masalahar da Hammadi yake ganin ya samar musu bata zauna ma Datti ba, abinda bata ma sani ba shine Datti ya sami Baabuga.

“Ka zo ka dauki d’anka, ka yarda dani idan nace maka rigima dani ne karshen abinda zaka soyi a fadin Marake, kazo ka d’auki d’anka.”

Ya kuma baro Baabuga da baiba damar amsa shi ba a tsaye. Washegari a wajen da ake kular musu da dabbobi ya samu Hammadi, saboda ranar tayi dai-dai da ranar da za’a tafar musu da wasu shanu kudu don a siyar, har aka ga ware su aka saka a mota, Hammadi bai ko amsa gaisuwar Dattin ba, da ya gama ma, rabashi yayi ya wuce, shine yabi bayan shi yana sake masa magana, sai dai kallon da Hammadi yayi masa ya saka jikin shi yin sanyi, gwiwoyin shi kamar an buge masa su da sanda.

“Ban isa ba nasani, amman na dauka rashin isar zai tsayane a tsakanin mu, ba saika tsallaka waje ka nuna ma kowa ban isa ba Datti… Ka kyauta, na kuma gode.”

Hammadi ya karasa maganar cikin harshen Hausar da zakaji ta a bakin shi lokaci zuwa lokaci.

“Me nayi kuma Hamma?”

Datti ya tambaya duk da ya hasaso inda zantukan Hammadin suka dosa.

“Tambayata kakeyi? Baka sani ba?”

Sunkuyar da kai kasa yayi saboda bayason irin kallon da Hammadi yake masa.

“Dani ka samu kace in dauki Bukar in mayar bawai ka samu Baabuga ka fada masa yazo ya dauki d’an shi ba.”

Kamar Abu tana duba, sai da ta hango musu wannan matsalar.

“Ka samu Baabuga kayi masa maganar Bukar, kar yazo ya sake birkita mana komai, kaga inda wata matsala sai mu san yanda zamu shawo kanta.”

Ya kuma aminta, ba Baabuga da ya yarda masa da rike Bukar ba, har Baba saida yaje ya samu.

“Anya Hammadi, anya wannan hukuncin naku mai bullewa ne? Ita Dijen inace na gaya mata ta dauke kai akan maganar Bukar, mai rabon ganin badi fa saiya gani, wahala kuma ai bata kisa, baga sauran ‘yan uwa nashi nan ba suna rayuwa a gidan.”

Cewar Baba, sai dai ko babu kalamai masu taushi, akwai wani kwarjini a tare da Hammadi da yake cika idanuwan duk wanda zaije ma da wata bukata, bai dauki lokaci ba wajen gamsar da Baban kan zaman Bukar a hannun shi, lokacin da sukayi sallama, banda fatan alkhairi babu komai a bakin Baba. Ya dauka ya gama tufke wannan zaren harya zama igiyar da baiyi tunanin Datti zaibi ya nemi ya warware ba.

“Idan ban isa da kai ba, ina ce na isa da kai na ko? Ina kuma damar da zanyi duk abinda nake so ciki harda zabina na rike Bukar.”

Kallon shi Dattin ya yi.

“Ko da bana son zabin naka? Hamma ko da rike Bukar yana nufin kuncin tawa zuciyar? Me yasa kuke nuna mun yaron nan yafi ni? Yaron Baabuga, me yasa kuke ta zabar shi a kaina? Me yasa kuka fi son shi? Harda kai Hamma, me yasa kaima zaka zabe shi a kai na?”

Fushin da ya dauka baiyi tasiri akan Hammadin ba, yana gani shima saiya share shi, shariyar da ta kara kuntata zuciyar shi. Shisa ya dawo wajen Dije, idan ita tace ma Hammadi zata mayar da Bukar ba zaiki ba, dole zai hakura, amman itama yana ganin babu alamar nasara akan haka. Shisa yanzun da yake kallonta ya kasa furta mata kalmomin da suka kwana biyu suna masa yawo a kan shi, a karo na farko a tsayin wani lokaci da wani abu mai yanayi da tsoro ya cika kirjin shi.

“Ki zabi daya, koni ko Bukar, ki zaba Dije, ko ni ku Bukar.”

Haka yake so yace mata, sai kalaman suka makale masa, saboda idan ya taba ganin soyayyar shi a cikin idanuwanta, a yan kwanakin nan yaga yanda zata iya jingine komai akan Bukar, akan yaron nan da baya ko son gani, yaron da yake jin tsanar shi tun daga kasan zuciyar shi. Shisa ya mike yabar mata dakin, yabarta da soyayyar Bukar da ta zaba akan tashi.

**

Idan akace lokaci kan tafi da komai, sai Dije taji maganar tayi mata nauyi, idan akace komai, za’a iya nufin komai kenan? Anya? Anya lokaci kan tafi da komai? Da sunce lokaci kan tafi da wasu abubuwan zatafi yarda, saboda taga shaida, akan girman su Julde take ganin wannan shaidar, akan yanda rikon Saratu ya dawo hannun Abu, akan abubuwa da yawa, cikin abubuwan nan harda cire rai da tayi da samun wani rabon bayan shekaru goma cir da suka wuce mata batare da ko batan wata ta sakeyi ba, iya rabon kenan, ta binne wasu, ga uku nan sun rayu.

A cikin abubuwan da lokaci ya kasa tafiya da shi, shine tsanar da Datti yayi wa Bukar, Bukar din da wanda duk hanya zata hada da shi a Marake, babba ko karami sai hankali da karamcin shi sun tabashi, Bukar da duk wani abu da zai shiga hannun shi burin shi ya raba tare da wanda yake ganin sun fishi bukata. Bukar dinta, Bukar mai sanyin halin nan, Bukar mai taushin zuciyar da bai tsaya akan mutane ba kawai harda dabbobi. Bukar da zaka ga ana ruwa ya koro duk wata kaza da zai gani cikin gida ya saka su a dakin daya zama nashine a gidan Hammadi, har sai an gama ruwan sama zai bude ya fito da su, Bukar da zai hango tsuntsuwa ta makale a sama, duk fadan da Abu zatayi ba zai samu nutsuwa ba saiya taka ya warware mata abinda ya daureta.

Bukar da ke son tsuntsaye da dukkan zuciyar shi.

“In sa a kamo maka mana Bukar, duk kalar da kake so.”

Hammadi kance masa idan yana laburta masa wani kalar tsuntsun da ya gani, yana bashi labarin na’uin shi da yankin da yaji labari anfi samun irin na’in tsuntsun a wajajen, sai dai yayi dariyar nan, dariyar nan tashi da zakaga kyallinta har cikin idanuwan shi.

“Ai zuciyata ba zata nutsu ba idan na tsare shi a waje daya, baccin kirki ma ba zan iya ba…koni da kafafuwana ba kowanne gari zasu iya daukata su kaini ba zan takura idan aka tsareni waje daya, balle abinda aka halitta ma fuka-fukan da zai iya tsallakawa kasashe.”

Kafin Dije ta furta Bukar daban ne, halayen shi sun nuna haka, komai da zaiyi ya bambanta shi da yara sa’annin shi. Babu yanda za’ayi Bukar ba zai shiga zuciyar ka ba, sai dai shigar da yayi ma ta Datti daban ne. Baya iya boye tsanar shi, sau daya Bukar ya gwada kiran shi da.

“Baba”

Kamar yanda yaji su Julde suna kiran shi.

“Ni ba babanka bane, karka kara kirana da Baba, sunana Datti.”

Lokacin daya fadama Bukar, su duka sun dauka yayi yarintar da zai rike maganar, amman kuma sai ranar ta zama rana ta karshe da Bukar din ya sake kiran shi da wani suna ma gabaki daya. Yana shiga ya gaishe da Dije, baya zama, yanda duk zata so baya zama, ko abinci ta zuba masa zaice mata ya rigada yaci abinci ko kuma bayajin yunwa. Duk wani abu da zai hada hanyar shi da Datti tunda ya fara hankali guje masa yakeyi. Abin mamakin yana cikin shakuwar da take tsakanin shi da Julde da Yelwa, saboda shi saita wuni suma bata gansu ba, suna gidan Abu, sai dai ita ta kulle gidan idan ta gama abinda takeyi ta shiga can, saboda kadaici saiya addabeta.

Tana da yakinin duk soyayyar da take yiwa Bukar ba zatayi masa rikon da Hammadi da Abu sukeyi masa ba, balle kuma Baabuga. Da a hannunta yake ba zai taso da irin tarbiyar da yake da ita ba yanzun, ba ita zata gaza ba, irin sangartar da Julde ya taso ciki ce zata nakasa rayuwarshi, kamar yanda take ganin tayiwa ta Julde harda Yelwa ma. Yaranta, yaran da bata isa ta tsawatar musu ba saboda makauniyar soyayyar da Datti ya dauka ya dora akan su, laifi in har bashi yaga sunyi ba, fada idan har bashi zai musu ba, babu wanda ya isa. Idanuwan shi kullum cikin ganin laifukan yaran wasu yake, bakin shi kullum cikin aibata yaran wasu yake da dora ayar tambaya akan irin tarbiyar da suka samu, tun Dije na magana harta gaji ta saka masa ido.

Bakin Datti dai akan yaran da ba Julde da Yelwa ba, kaf Marake sai Saratu ce da ta ciri tuta ta tsira daga shi, saboda babu wanda ya dauka zai so wasu yaran da basu fito daga jikin shi ba, sai ita.

“Baba Am.”

Takan fadi, Saratu kan kira shi da Babanta, Saratu kan saka kujera ta zauna a bakin kofa idan lokacin dawowar su Datti yayi, Saratu zata ruga wajen Datti ko da shi da Hammadi ne a tsaye kuma su duka suka bude mata hannayen su, sai ya zamana kamar gasa ce takeyi da su Julde, gasar da suka rigada suka bar mata kambunta akan soyayyar Datti, shakuwar su Zata baka mamaki. Kara irin na Hammadi, ko na rana daya bai taba kiran Saratu da tashi ba, sai dai ya ce,

“Yar Datti”

Julde na da gaddama, idan ya kafe akan abu, babu wanda ya isa ya tankwara shi, kuma baisan ya nemi wani abu ya kasa samu ba, Yelwa na da yawan fara’a, tana kuma gudun bacin ran kowa, idan kaga kafiyarta to akan dan uwanta ne, akan Julde ne da take nuna batada wanda yafi shi a duka fadin duniya, ciki harda Datti da Dijen da ko da tana karama idan tana kuka Julde ne yake lallashinta tayi shiru, idan abu take so sai dai suji a bakin Julde. Idan har Yelwa ta kafe, to akan wani abune da Julde yake so Dije ta nemi hana masa, to su duka biyun zasu hadu su botsare mata.

Saratu a gefe daya, kowa idan ya kalleta zai dauka zaiga Hammadi a tare da ita, idanuwan nashine, har yankansu iri dayane, sai dai idan Hammadi ya kalleka zaka ga sanyin halayyarsa da yake cikin su, idan Saratu ta kalleka babu wannan sanyin a cikin idanuwanta, kamanninta irin na Pendo ne, in kasan Pendo, Saratu ta gifta saika san cewar jininta ce. Saboda ta taso a hannun Abu, saboda yanda Abu take tsaye akan tarbiyarta zaka dauka kaf Marake saika tona zaka samu mai nagartattun halaye irin na Saratu. Daga jikin Hammadi ta fito, kowa shaida ne, amman Datti ne mudubinta, idanuwanta akan Datti da duk wasu halaye nashi ya ke.

Tana da zafin rai, tana da riko, ko fadan yarinta idan ya hada su da Julde da yanda duk take nacin ganinta kusa da shi kuwa, ya kwadeta, saboda alamu da yawa na nuna yanda nata jinin ya hadu da nashi, shi din nashi jinin bai hadu da nata ba, yana zaune zaka ga ta shammace shi ta kwada masa wani abin. Ko kayanta ne ba’a isa a bayar dasu a gabanta ba, wuni zatayi tana kuka, da safe tana tashi zakaga ta sake saka wani sabon kukan, sai tayi kwanaki tana wannan tashin hankalin da idan Datti yaji zai goyi da bayanta.

“Ku daina bayar mata da kaya tunda bata so, koni bana so in saka kaya in cire su in bayar, garama in dinka maka sabo wanda bai kai nawa ba.”

Kai kawai Abu takan girgiza kaine, bata kara furta komai, saboda idan halayen Datti takalma ne, basu Saratu ta saka ba, inda ya dauke kafafuwan shine take saka nata, sawayen shine take takawa suna shigewa ta cikin kafafuwanta suna rabuwa tsakanin zuciyarta da kanta.

“Haka kawai sai zuciyata ta dinga tsinkewa idan ina duban yaran nan, halayen su na zauna mun a zuciya, wani lokacin kuma sai su bani tsoro, tunanin ya goben su zata kasance kan hanani bacci a wasu dararen.”

Dije ta fadama Abu lokacin da Julde ya shigo gidan batare da sallama ba balle ma su saka ran zai gaishe su, a zuciyar shi ya gaishe su da safe, baya bukatar ya sake musu wata gaisuwar, murmushi Abu tayi, idan tace tsoron nan babu shi a tare da ita zatayi karya.

“Allah dai ya raya ya shirya mana.”
Ta iya furtawa, Amin din Dije na tsayawa a iya zuciyarta saboda nisan da tunaninta yayi. Yelwa da Saratu take kallo, tana juyo dariyar Yelwa daga inda take, kafin ta Saratu ta ratsa cikin tunaninta.

A cikin dariyarsu zakaji yanda basu da wata matsala.
A cikin dariyarsu zakaji yanda basu san wata kaddara ba balle abinda ta tanadar musu.


Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.2 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 28Rai Da Kaddara 30 >>

1 thought on “Rai Da Kaddara 29”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×