Skip to content
Part 57 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Epilogue 1

Bayan Wani Lokaci

Duka hayaniyar falon yake jin ta zuqe mishi, babu wani abu da yake karasawa kunnuwan shi, kallon su yakeyi daya bayan daya da wani abu mai kama da alfahari, wani abu da ya girmi so, ya kuma wuce kauna, yanayi ne da akansu kawai yasan akwai shi, yake kuma jinshi. Anya akwai abinda yafi dangi dadi? Akwai abinda yafi ‘yan uwa? Sai ya kalli Bukar da ga Kaltume a zaune a falon amman yana kusa da Daada, yana zaune a kasa kan kafet din dakin a gefenta na dama, Madina tana gefenta na haggu, Salim kuma yana gefen Madinar, kallo daya zakayiwa fuskar shi kagane inda yana da wani zabi bayan zaman wajen zai dauka. Nawfal ya rufe idanuwan shi, ya sake budesu akan su Bukar, shekara daya, ya kamata ace ya saba, zuciyar shi ta aminta ta yarda da ba mafarki yake ba, su dinne suka dawo, iyayen shi, kuma duk wani alamu sun nuna zamansu ba mai karewa bane nan kusa.

Tunda Bukar din tare suke zuwa kasuwa da Julde, bayan ya bashi gida mai daki biyu (two bedroom) daya siya da sunan Lukman, yake kuma shirin zuba yan haya, sai dai kafin yayi hakan ne Bukar ya dawo. Zaice ya shafe kwanaki bakwai bayan dawowar shi yana kaucewa haduwa dashi, asalima kayanshi ya hada da kuma matar shi suna tafiya Kaduna saboda ya fuskanci abubuwan da suke gaban shi na kasuwancin da ya kafa a garin na Kaduna. Duk wani sauran kuzari da ya rage masa ya tattara yana mayarwa akan aikin da fatan ya dauke masa hankali daga dawowar Bukar, sai dai kamar duk wata sa’a da zata wuce da yanda amon muryar da yake fada masa idan kuma da gasken Bukar ta leko ta koma zaiyi masa kamar yanda Yelwa tayiwa Madina fa, yake karuwa. Ko da ta leko ta koma dinne kamar ya kamata ace ya tsaya ya samu wani lokacin da zai adana a zuciyarshi ko dan gaba.

Yaji dadin da Murjanatu bata tayar mishi da maganar ba, duk yanda yake ganin tana son yin hakan a lokutta mabanbanta, sai dai idan yaje jikinta zata kara rike shi, zata sumbace shi a kunshi ko duk inda labbanta zasu iya kaiwa tana son fada masa tana tare dashi duk runtsi, idan kuma yana da bukatar abokiyar tattauna damuwar shi tana nan, tana nan a kowanne irin yanayi da hargitsi da zai tsinci kanshi. Ya godewa Allah, ya godewa Murjanatu, ya godewa duk wani dalili, karami da babba daya hadu waje daya ya samar mishi da ita a matsayin matar aure, saboda yasan ba dabarar shi bace balle wayon shi. Sai dai kwanakin suka fara yi masa tsayi, aikin daya ke fatan binne komai a cikin shi ya daina bashi kariya daga tunanin da yake ta turewa.

A idanuwan shi zaka ga ramar daya fara a tsaye, idan kuma kasan shi yanda ya zama shiru-shiru zaka san wani abu yana damun shi, wani abu mai girma. A ranar wata laraba, ya yanke shawarar komawa gida wajen sha biyu na rana, gara yaje ya rabi jikin matar shi ko zai samu salama a ranshi, ya shigar da motar shi cikin gidan nasu da Murjanatu ke korafin har yanzun bai gama yi mata yanda take so ba, ya fito ya ga maigadin su yana bude gate din da alamun wata motarce zata shigo, zuciyar shi ta buga, ta kara bugawa ganin motar Khalid ce, wajen sati kenan yana gujema duk wani kira da Khalid din yayi masa a waya saboda yayi masa maganar Bukar.

Bai san dalilin da tunanin awannin dake tsakanin Kano da Kaduna ba wasu masu yawa bane balle suyiwa Khalid katanga a tsakanin su, zuciyar shi ta kara bugawa ganin Bukar ya fara fitowa daga motar, kafin Khalid ya fito, sai dai shi bai fara takowa ba, a jikin motar ya tsaya yana kallon Nawfal kamar yana son gaya mishi

“Ga abinda kake gudu nan na biyoka dashi”

Kamar kuma yana son ce mishi.

“Wannan baya cikin abinda zaka iya gujewa fuskanta Bajjo”

Ya hadiye wani abu da yaji ya tsaya masa a wuya, lokaci daya kuma jikin shi ya dauki dumin da bashi da alaka da zazzabi, kafin numfashin shi ya fara yi masa barazana ganin Bukar tsaye a gaban shi. Yadi ne a jikin Bukar din bula mai haske, sai hula data hau da yadin. Ramar da take fuskar shi a wancen lokacin babu ita yanzun, sannan yayi gyaran fuska, farin gashin da ya fara nuna shekarun shi ya kara masa wani irin kwarjini na ban mamaki, sanyin halin shi da kowa yake yawan magana akai shimfide a fuskar shi.

“Na so in baka duk lokacin da kake bukata, sai dai lokaci abune da yake karanci a ahalin mu Nawfal, ka yanke mun duk hukuncin da kake so, amman kayi hakan bayan ka saurare ni, dan Allah, ba uzuri zan baka ba, bayani zanyi maka, dalili na kawai zan fada maka…”

Ba zai iya tuna mintina nawa yayi a tsaye inda yake suna kallon-kallo shi da Bukar din, zai dai iya tuna Khalid ya karaso, yayi masa maganar da ba zai iya tunawa ba, a cikin wannan rudanin kuma suka shiga falon gidan shi, yanajin shi kamar bashi ba har lokacin da Murjanatu ta kawo musu ruwa, lemuka, kayan marmari sai snacks din da ba’a rabasu dashi saboda tana so, ta kuma yi wata magana da yasan ba zata wuce gaisuwa da kuma abincin da zata dora musu ba tunda basu sanar da zuwan nasu ba. Ruwa ma Khalid ne ya bude robar ya mika masa, baiyi musu ba ya karba ya sha yana ajiye robar hadi da kallon Bukar daya bude bakin shi ya fara bashi wani labari mai kama da shirin film din Hausa.

Yace masa sauran kwana daya ranar da suka shirya barin garin shi da Kaltume ta cika, hasashenta na faruwar wani babban abu da rayuwar su ya tabbata, ya dauki Nawfal din sun fita masallaci sallar Isha’i, aka kuma yi dace an gayyato wani bakon Malami da ya tsaya yin wa’azi akan matsalar da ake ta fuskanta ta yawan mace-macen aure da muhimmanci sauke hakkin iyali, hakikanin gaskiya zuciyar shi a wannan lokacin tana gida, tana ga Kaltume, amman babu wanda yayi kokarin barin masallacin, shisa shima baiyi wani yunkuri ba ya zauna kawai. Har aka gama wajen tara da rabi, dan Nawfal yayi bacci a jikin shi, sai sabar shi yayi suka nufi gida, zuciyar shi na tsananta duka, wani irin yanayi na ziyartar shi, musamman daya ga gate din gidan a bude, kuma yasan sun sallami maigadin su tun satin daya wuce.

Zuciyar shi ta mirgino ta fado kasa inda ta tarwatse bayan ya shiga gidan ya ganshi anyi masa dai-dai, kamar ana neman wani abu, kuma babu Kaltume babu dalilinta. Wani irin firgici da tsoro suka daki ruhinshi, duka tunanin shi ya tsaya akan dangin mahaifinta da basu daina bibiyarsu ba, basu dauke idanuwansu daga dukiyar da aka bar mata ba, kadarorin da ta dinga siyarwa tana siyen zinari tana ajiyewa, wasu kudin kuma ta barsu a cikin asusun bankin data bude dan hakan kawai.

“Idan zabi ya gifta tsakanin ni da Nawfal ka zabi yarona, dan Allah kayi nisa dashi yanda dangin Abba ba zasu cutar mun dashi ba saboda abin duniya…”

Duk wani abu mai muhimmanci yana cikin mota, sun gama tattara kayan da zasu dauka sun saka a ciki tunda safe, daya karasa motar cikin rashin hayyaci, jakar da tafi kowacce muhimmanci kawai ya iya dauka, daga shi sai kayan jikin shi da silipas, a kafa ya karasa tasha, acan suka kwana da safe ya kama hanya. Sai dai bayan yaje Marake ya ajiyewa Daada Nawfal batare da bayanin komai ba, juyawa yayi a ranar ya sake shiga mota dan ya bi bayan Kaltume, ya kuma sauka cikin rashin sa’ar samun dangin mahaifinta sun baza neman shi, Kawunta ya kai rahota ofishin ‘yan sanda cewar Bukar din ya batar da ita, ya gudu da tarin dukiya, yana komawa ana kama shi.

Bashida wata shaida, Kaltumen da zata zame mishi shaida baisan inda take ba, yaci wahala a hannun ‘yan sanda a nufinsu na tambayar shi inda dukiyar Kaltume take, case din daya dauki wata daya, da Kawunanta suka ga ba zaiyi magana ba suka maka shi kotu, inda yake da yakinin cin hanci akayi amfani dashi wajen garkama shi a gidan yari, laifin shi daya, da kaddara ta hada shi hanya da Baban Kaltume, ta kuma hadashi aure da ita. Bashi da wata hanya da ‘yan uwanshi zasu san halin da yake ciki. Sai dai a lokacin da suka garkama shi gidan yari, Kaltume gidan mahaukata suka kaita suka lakaba mata ciwon haukan da bata dashi, yanda take kiran mijinta da danta, suka kuma cewa likitocin tayi aure, amman mijin da dan duk sun mutu sakamakon hatsarin da suke tunani shine ya taba mata kwakwalwa take ta sambatu taki amsar mutuwar.

Ko da bata hauka, ciwon damuwa da kuma fargabar halin da mijinta da danta suke ciki ya taba kwakwalwarta, tun tana yunkurin yakice zuciyarta harta bar damuwar tayi nasara akanta, dalilin da yasa asibiti riketa kenan. Da shekaru suka fara tafiya sai ta amince, ta kuma fara yarda da cewar watakila da gaske haukan takeyi. A cikin yaran Kawunanta, yar shi ta hudu, Hamida ce tayi nasarar jin abinda ya faru lokacin da ta tsinkaye shi suna tattauna maganar da dan uwan shi, suna kuma tunanin inda Bukar da Kaltume suka kai dukiyar da har a lokacin suka kasa cire ransu daga kanta. Basu kuma bar zuciya da tunanin ba, saboda su kuma ta zabi fannin shari’a, har bayan tayi aure, shekaru sunja basu bar ranta ba, tana kuma kallon mahaifinta da zaluncin da bashi da nufin yin nadama akan shi balle kuma ya tuba.

Ita ta fara nemo Bukar bayan mahaifinta ya kwanta wata irin cuta da likitoci suka kasa gane kanta, Allah kuma ya matse shi da ta tayar masa da zancen su Bukar bai musa ba wajen warware mata komai, saboda a lokacin babu abinda yake bukata sai samun salama daga azabar ciwon da yake fama dashi, duk da mahaifin nata ya shirya tsaf dan bada shaidar da zata wanke Bukar a gaban alkalai, shari’ar bata zo da sauki ba, musamman data hada da ahalin da suka ki bawa Hamida goyon baya saboda tonon asirin su gabaki daya. Sai dai bai wani daga burin shi akan samun nasara ba, ya rigada ya sallamawa kaddarar da ta fado masa, a zuciyar shi kuma yayi sallama da kowa nashi, ya dai san duk inda suke fatan su da addu’o’in su na tare dashi, musamman Daadar shi.

Sai gashi sunyi nasara, sai gashi ya shaqi iskar ‘yanci da ya fitar da rai da ita, sai a lokacin kuma ya iya tambayar Kaltume, sai lokacin ya bari zuciyar shi ta tambayeta, ya kuma yi karo da labari mai dadi, an fito da ita, asalima ita suka fara fitowa da ita, tana dai karbar kulawa ne bisa turbar da ta dace a hannun likitoci saboda damuwar data taba kwakwalwarta, kuma ana samun cigaba. Kamar ganin shine babban maganin da tafi bukata, zaren da zata kama ya fisgota daga duniyar damuwar da take ciki. Sai ta samu wani sauki daya ba likitocin mamaki, ya kuma yiwa Bukar dadi saboda bayason su kara wasu kwanaki a garin na Borno batare da sun fice ba, duk wata neman yafiya daga Kawunanta, da nuna nadama bai taba zuciyar Kaltume ba, garama Bukar ya bude bakin shi ya furta ya yafe musu, ko dan darajar Hamida, amman Kaltume shiru tayi, tunda ko addini ya bata zabin yafewa ko akasin hakan. Sunyi mata babbar cutar da ba zata yafu ba a wajenta. Wata shari’ar sai a lahira.

Haka suka tarkata dan abinda ba’a rasa ba, bayan tarin godiya da fatan alkhairi suka nufi Marake. Komai ya kara zuwa masa da sauki bayan ya nufi gidansu yaga yanda yanda daga na Datti har na Hammadi suka zama kango saboda rashin mutane. Sai yaja Kaltume suka nufi gidan Baabuga, inda yayi murna da ganinsu, harda hawayen shi, anan kuma suka samu labari mai dadi, na zuwan su Nawfal, na ziyarar da suka sake kawowa a karo na biyu, suka kuma samu lambar wayar da Khalid ya rubuta yana bawa Baabuga da nufin ko da wani abin zai taso. Harda cikakken adireshin inda suke da zama a jiki, shisa Bukar din bai kira Khalid ba, suka kwana, washegari suka samu motar Kano, da kudin hannun shi yayi amfani ya kamawa Kaltume daki saboda yanda ta nuna alamar galabaita, ya barta acan da nufin komawa ya dauketa idan ya gano gidan.

Kallon shi Nawfal yakeyi, tunda ya fara magana, har wani jiri-jiri yake ji saboda yanda yake so ya nannade kanshi cikin duk bayanin Bukar da yake kama da almara ko zai fahimta. Daga yanda suke kallon shi yasan jira suke yace wani abu, amman ya kasa ko kwakkwaran motsi balle ya iya furta wani abu. Kiran sallar azahar shiya tashe su, tare sukaje masallaci, suka dawo, inda Murjanatu ta kawo musu shinkafa da sauce din kifi da tayi da tumatir da albasa, dan ba tattasai garesu a gidan ba balle attaruhu, ko nama basu dashi, idan tayi sha’awa zata fita ta siya ko tayi order, to a hankalima, saboda Nawfal din kaunar da takeyiwa nama ta kula kara nisa takeyi.

Sai salad da tayi musu, da kuma lemuka, ta bar musu wajen, Khalid ne ya zuba ma Nawfal din da ya dinga wasa da cokalin shi a cikin abincin har suka kammala. Suka yi masa sallama suka juya, ya dai rakasu bakin mota, ya koma ya samu Murjanatu harta kwashe komai. Kamar kuma ko da yaushe bata yi masa magana ba, bata tambaye shi wani abu ba. Shine ma a daren ranar ya dinga jaddada mata irin son da yakeyi mata da kuma godiyar da yake yiwa Allah da ta kasance cikin rayuwar shi. Haka kwanakin suka dinga zuwa suna wucewa har sati biyu bayan zuwan su Bukar, yana kwance Murjanatu tazo ta tsaya akan shi tana girgiza shi cikin wani yanayi daya saka shi tashi zaune babu shiri.

Kallonta yayi, hawaye ne cike taf da idanuwanta, ta kasa magana, sai wani abu da bai gama fahimtar menene ba ta mika masa, baiyi musu ba ya karba ya duba, sai dai so yake ya tuna inda ya taba ganin abinda yake rike dashi, kafin ya fahimci amfanin shi, zama tayi kusa dashi sosai tana zagaya hannuwanta ta riko shi jikinta

“Allah ya dubemu…”

Kamar wanda kalamanta suka wankewa kwakwalwa haka yaji, kafin ya fahimci menene dan karamin abinda ke hannun shi mai dauke da sakon da yake da nauyin gaske

“Zamu samu yaro ko yarinya?”

Ya tambaya muryar shi na fitowa a shake, kai take daga masa, ya kuwa sake riketa kamar zai mayar da ita cikin shi, tun shekarar farko ta aurensu da sukaje asibiti aka tabbatar musu da lafiyarsu kalau, babu mai wata matsala suka dawo suka barwa Allah komai. Yana danne tashi damuwar ne saboda ya karfafa mata gwiwa, amman yasan abin yana damunta duk da bata cika yi masa zancen ba, amman indai suka tare, a dararen alhamis da juma’a, koma basa tare takan tuna masa daya tashi yayi sallar dare don neman biyan bukata, gashi kuma yau Allah ya amsa musu.

Yaje Kano, a tsakanin samun cikin nata, laulayinta, kananun ciwuka da kuma taraddadin da ba’a raba mai ciki dashi, yaga Bukar, yaga Kaltume, ya gaisa dasu da wani yanayi a tare dashi da bai gama fahimta ba. Farin cikin da yake fuskar Daada na sanyaya wajaje da dama da baisan a zafafe suke ba tare dashi. Daga Bukar din kuma har Kaltume babu wanda yayi wani yunkurin karfafa alakar tasu, kamar sun matsa gefe suna jiranshi yaje musu da kanshi. Sai dai a daren da ciwon nakuda ya kama Murjanatu, ya dauketa a rude zuwa asibitin da take awo, ya kuma ki sakin hannunta duk yanda likitocin suka so, sai suka hakura suka barshi ya bisu dakin nakudar tunda ita kadaice a ciki, kuma kudine suke aiki balle a nuna musu fin karfi.

Ba zaice baisan wacece uwa dan bai taso tare da ita ba, a ranar da ya kara fahimtar wacece ita, ya kuma ga dalilan da yasa aka daga darajarta a addini, a gabanshi kan da ya fito, ya kuma tokare saida aka kara Murjanatu, wani abu da ba zai manta ba har karshen rayuwar shi, dan baisan yana hawaye ba sai da wata cikin Nurses din tace masa

“Haba dai oga, idan kana kuka ai zaka kashe mata jiki…”

Lokacin da kukan yaron ya karade dakin, aka goge shi aka mika masa, sai komai ya tsaya masa, idan yace komai a lokacin, yana nufin komai, harda zuciyar shi da bugunta yayi wani irin kasa. Lokaci daya yaji baisan komai ba, baisan kowa ba sai halittar da aka saka masa a cikin hannun shi, abu na farko kuma daya fara dawo masa shine iyayen shi, iyayen shi da a yau ya fahimci duk wani dalili da zai nisanta yara da mahaifansu fa ba karami bane ba, musamman uwa da tasha wannan gwagwarmayar. Daya dago yaron yana yi masa kiran sallah cikin kunnen shi hadi dayi masa hudu ba da Khalid, sai wasu siraran hawaye suka zubo masa.

Lokacin daya fito waje yayi waya ya fada ma Daada cewar Murjanatu ta haihu, da yammacin ranar baiyi tsammanin duka ahalin shi zasu taho ba, su dukansu suka yo mota uku suka taho. Wajen Kaltume ya fara nufa yana riko hannunta da fadin

“Ummi, Ummi Na”

Yana saka wasu hawaye kwace mata, saiya kwantar da kanshi a jikin kafadarta yana barinta ta rike shi, yaji duminta da zaluncin wasu mutane ya hana masa shi tsayin shekaru. Hannun shi na cikin nata suka shiga cikin gidan, suna bin bayan kowa saboda sun shige cikine suna basu wajen da suke tunanin suna bukata shi da Kaltume. Da Khalid yaji sunan yaron, saiya kalli Nawfal

“Nagode Hamma, da komai, nagode”

Nawfal ya furta a hankali yanda Khalid din ne kawai zaiji, bai iya cewa komai ba, shiru yayi yana kara rike yaron a jikin shi, saboda bai yarda da kanshi ba

“Wai Khalid kuka zakayi?”

Cewar Adee, ya harareta da idanuwanshi da sukayi maikon hawayen da yake cike dasu, yana sa kowa yin dariya

“To girma ya kamaka Khalid, sai kazo ka tsaida matar aure tunda ni dai nace banayi”

Daada ta fadi, murmushi yayi, daman yana da niyya, tunda sun gama dai-daita kansu shi da Maryam da watannin su shidda da haduwa a lokacin, ya dai san akalla za’a saka musu wasu wata shiddan, tunda yana bukatar ya shirya sosai, in dai ya samu yanda yake so gidan nashi yana fatan ya zuba duka kayan amfani ya daukewa iyayenta tunda ya kula ba karfi gare su ba, wadatar zuci ce da kuma kokari irin na talatan da zuciyar shi bata mutu ba.

“Yanzun fa mu da mu kara taruwa haka sai Bikin Khalid ko?”

Murjanatu tayi maganar tana fisgo Nawfal daga duniyar tunanin daya fada

“Ai Hamma na da matsala, biki wata takwas, mu an taba saka biki mai nisa haka a family dinmu?”

Fadar Nawfal yana hararar Khalid dake zaune da takwaranshi da suke kira Junior a hannu yana ta kara gyara masa kwanciya, yaron dake ta sharar bacci

“To abinka da bikin talaka, dole ina bukatar shiri, yanzun ba gashi saura wata shidda ba”

Salim ne yayi tsaki wannan karin

“Menene shirin a ciki?”

Kai Khalid ya girgiza

“Dan Allah idan ana maganar kudi, ka daina saka baki Hamma, albashinka da namu ba iri daya bane, ba zaka fahimta ba…kuma kai Hajiya Adee ta saka maka hannu”

Da mamaki Salim yake kallon shi

“Adee banda akwatuna, duk abinda aka saka a lefen nan ba kudina bane ba?”

Dariya Adee takeyi

“Na fa kara da takalmi da jaka Hamma”

Tsakin ya kara ja yana girgiza kanshi kawai, yaga alama so suke su bata masa rai

“Hamma kace duk abubuwan masu muhimmanci yi maka akayi, ai in ba wani auren zaka kara ba babu yanda za’ayi ka gane…”

Bai karasa ba saboda hararar da Madina ta dago kai tana watsa masa batare da tasan ma tayi ba

“Bajjo…”

Khalid ya kira yana dariya, shima dariyar yakeyi yana daga hannuwan shi cikin sigar dake nuna saduda

“Afuwan uwargida ran gida…subutar bakine”

Ya karasa maganar da dariyar data fito daga kasan zuciyar shi, duk da kara tsuke fuska Madina tayi, yana kuma jin kaunarsu da bata da misali na cika zuciyar shi, a gefe daya godiya yake yiwa Allah yana karawa, godiyar da yake da tabbacin ba zata taba yankewa daga bakin shi ba har karshen numfashin shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 56Rai Da Kaddara 58 >>

1 thought on “Rai Da Kaddara 57”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×