Skip to content
Part 58 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Epilogue 2

Mutuwa sunanta iri daya ne, sanadinta da sakonta ne yake bambanta, akwai mutuwar da zakaji labarinta kawai ta tabaka, akwai wadda zakaji labarinta ta baka mamaki badan wanda ta dauka yafi karfinta ba, akwai wadda zaka jita ta tuna maka taka mutuwar da kake zaman jira, akwai kuma wadda zata idan ka jita zata daga kafafuwanka ta sulmuyo da kai ta ka, ta hargitsa lissafi da duk wata natsuwa da kake tare da ita. Wannan mutuwar itace ta Yelwa a wajen Madina, mutuwar da ta basu notice tunda ta nuna alama ta hanyar rashin lafiyar Yelwar, sun kuma dauka a shirye suke da zuwanta sai da ta ratso din a lokacin da hankulansu sukayi nisa da tunaninta.

Tana da tambayoyin da ko a kasan ranta take tsoron furtasu saboda zasu iya saka ta fita daga addinin da shine rufin asirinta a duniya da lahira. Duk yanda ake mata gaisuwa, ake kallonta cike da tausayawa da ido kawai take binsu. Sai da Salim ya ratso taron matan dake cikin gidan bayan ya kirata tana kallon wayar ta kasa dagawa, ya kuma kama hannunta bayan ya gaishe da kowa, bai nuna ko a fuska ya damu da kallon da sukeyi masa ba, idanuwan shi na kan Madina da batayi masa gardamar mikewa ta bishi ba, akwai hijabin Daada a jikinta saboda sanyin da take ji. Bai tsaya da ita ko’ina ba sai bakin motar shi inda ya bude murfin yana sakata ciki.

Ya zagaya ya zauna, jingina jikinta tayi a jikin kujerar motar tana lumshe idanuwa, bata bude su ba sai da taji ya tsayar da motar, ta daiyi mamakin ganinta a gidansu, ya kuma zagayo ya bude murfin motar yana mika mata hannun shi, batajin karfi ko kadan a jikinta, batayi musu ba ta kama ya taimaka mata ta fita daga motar, ko takalma babu a kafarta sai socks, janta yake har bangarensu, zuwa dakin shi, inda kamar hakan yake jira ya kama hijabinta ya zare bayan ya rufe kofar, ya cire gilashinta ya ajiye a gefen gado, ya kuma zagaya hannuwan shi yana riketa hadi dayi mata rumfa da jikin shi. Ba tasan menene ba a lokacin, dumin shi? Kamshin shi? Ko kuma kulawar shi ce, ko duka ne suka hadu sukayi tasiri akanta.

Dan wani irin kuka da batayi ba a kwanakin nan ta tsinci kanta da rushewa dashi. Ya sake riketa, kuka takeyi tana karawa, kukan rashin mahaifiyar da bata jima da shigowa rayuwarta ba, kuka take a jikin Salim, Hammanta, kuma mijinta a yanzun. Kuka tayi har saida sauran karfinta ya kare, dan badan rikon da yayi mata bana wasa bane, kafafuwanta ba zasu iya daukarta ba. Da kyar da taimakon shi ya kaita bandakin shi ya rufo mata ya fita, fuskarta ta wanke ta kurkure baki ta fito, da bata ganshi ba sai ta kwanta akan gadon kawai, bata da karfin zama, bacci ne ya fara daukarta taji yana tashinta. Da kyar ta iya mikewa zaune.

“Kisa wani abu a cikinki.”

Ya furta yana mika mata robar yoghurt din da batayi masa musu ba ta karba, ta sha rabi, ya kuma sake bata dankalin turawa da wainar kwai, ta danci kadan, kafin ta girgiza masa kai.

“Ki kwanta ki huta, anjima sai in mayar dake.”

Komawa tayi ta kwanta, tana jinshi yana ta shige da fice kafin taji hawan shi gadon, haka kawai taji zuciyarta ta natsu, irin natsuwar da ta rasa a kwanakin bakwai, ya mika hannu ya jata zuwa jikin shi yanayi mata makwanci akan kirjin shi inda ta yi luf da ita, zata iya rantsewa kamar an halitta mata shi dai-dai ita, dai-dai kwanciyarta, dan inda kanta yake a kafadarshi yayi dai-dai, tamkar an auna kafin a halitta masa. Yaune karo na farko da ta kwanta a jikin namiji, ya kamata taji daban, yakamata taji wannan rashin sabon da fargabar, amman babu komai a zuciyarta banda natsuwa, irin natsuwar da taji bayan labarin daura musu aure ya risketa.

Shisa ta lumshe idanuwanta tana barin bacci ya dauketa. A bangaren Salim ne yanayin ya sha bambam, ba ita bace macen farko da ta hau jikin shi, ita daice ta farko da yake jin ba a jikin shi kawai take kwance ba har a zuciyar shi, yau kuma sai yake jin control din da yake yiwa kansa a lokuttan da yake tare da ita yana neman kwace masa. Wata wutar sonta nayin rassa a duk gabban jikin shi. Ya gyara mata kwanciya yafi a kirga ko zai samawa kanshi sauki, amman hakan ya gagara. Tayi bacci, amman shi ko idanuwan shi bai rufe ba, har azahar, shiya tasheta bayan ya zameta daga jikin shi ya shiga bandaki ya dan watsa ruwa yayo alwala.

Bai mayar da ita gida ba sai la’asar, sai kuma lokacin wata irin kunya ta yi mata rumfa, tasan kowa dake dakin zaisan cewa Salim mijinta ne, bama su ba, yanda zata shiga gidan ta hada ido da Daada shine babbar damuwarta. Taji dadi da bata ga Daada a falon ba, saita wuce dakinta kai tsaye. Ta kwanta akan gadon tana jin saukin nauyin da kirjinta yayi mata. Musamman data cigaba da jero,

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Tana kara maimaitawa. Kamar ko da yaushe, a dan tsakanin Salim saiya sake zame mata bangon da take jingina dashi ta samu saukin tsayuwar da take neman gagararta. A gefe daya kuma Kabir ne, mahaifinta da ta kira da 

“Abba…”

Karo na farko bayan rasuwar Yelwa da suka hadu, sai ya durkushe a wajen, kuka marar sauti na kwace masa, itama kukan takeyi, kuka sukayi a falon Daada batare da wani ya lallashi wani ba, kuka Madina takeyi na mahaifiyar data rasa, kuka take na mahaifin da yake gabanta, kuka takeyi na godiyar Allah daya sa tana da rabon ganinsu ta san su. Shi kuma kuka yakeyi na matar shi daya rasa, matar data tsallake kowa da komai nata ta zabe shi, matar da tayi gararamba a titi tsayin shekaru ta sanadin shi, matar da ciwon da basu taba tsammani ba ya dirar mata, kafin mutuwa ta risketa tana yi musu tsakani na har abada. Mutuwar da ta saka shi kokarin neman sauran yan uwan shi saboda yanda yake jin shima bashi da wani sauran lokaci mai tsayi.

Yan uwan da suka karbe shi kamar basu taba korar shi ba, suka yi nadama kamar sun jima da gane kuskuren su. Ya kuma yi kokarin daukar Madina ya hadata dasu da jagorar Salim daya rakasu. Taga ‘yan uwan mahaifinta, taga ahalin da idan ta juya a garin Kano zata kira da nata. Yanda duk in anyi wani motsi mai girma Kabiru zaice musu,

“Babu ni idan ba Yelwa, inaji a jikina tazarar mu ba mai nisa bace ba.”

Jinshi kawai sukeyi, suna kuma tausaya masa, ko Daada sai da tayi maganar shi, tasan Yelwa batayi zabi me kyau ba lokacin data tsallake su, amman alamu sun nuna ko su suka laluba zai wahala su zabo mata mijin da zai mata soyayyar da take gani a idanuwan Kabiru. Sai suka fara saka shi a addu’o’insu, da fatan Allah ya saukaka masa radadin rashinta ya takaita masa kewa. Sai dai jikin shi bai masa karya ba, kalaman shi duka akan gaskiya suke, a lokacin da ya bi Yelwa kwanaki arba’in da shidda cif a tsakanin su bayan zazzabin kwanaki biyu rak. Wata mutuwar da ta sake taba su dukansu.

Saboda Kabiru ba irin mutanen da zasu rabeka ka kasa kaunarsu bane ba, ko murmushin shi kawai da kyallin shi yake kaiwa har cikin idanuwanshi zai tsaya maka, balle kuma kirkin shi, komai a tare da Kabiru mai tsayawa a zuciya ne.

“Hamma daman sun dawo ne dan mutuwa ta lallabo ta dauke mun su daya bayan daya? Wacce irin kaddara ce wannan? Anya ina da zuciyar dauka?”

Madina ta tambaye shi hawaye na silalo mata, ya riko hannunta 

“Kowanne rai da tashi kaddarar Madina, amman Allah baya dorawa bawa wadda ba zai iya dauka ba, ki godewa Allah da kika samu lokaci tare dasu, duk da bai tsawaita ba kin samu, akwai yara da yawa da har abada ba zasu san iyayen su ba, tasu kaddarar kenan…wasu ma kafin haihuwar su suke rasa iyaye mazan, a wajen haihuwa kuma su rasa matan…kiyi hakuri, dan Allah kiyi hakuri, Allah zai sanyaya zuciyar ki”

Kauda kai kawai tayi wasu hawayen na zubo mata, saboda kowa sai dai yayi kokarin fahimtar halin da take ciki, amman ba zasu taba ganewa ba, wanda ya taba shiga cikin irin shine kawai zai fahimta. Kwanaki bakwai bayan rasuwar aka tsayar da ranar da zata tare gidanta, aka saka sati biyu. Da na farko ya cika aka kawo mata lefen da batayi tsammani ba, saitin akwati masu shidda guda biyu. Haka ta dinga kallon akwatinan tana hasaso kudin da Salim ya kashe wajen cika su. An sanarwa yan uwansu, na mahaifinta, dan tarewar har Marake sai da su Khalid sukaje da motoci uku ran daren suka kwaso dangin Daada, suka kuma bata mamaki da suka hado harda Abu. 

Abu data fito daga motar tana sharar kwalla, sababbi na zubowa bayan tayi tozali da Daada. 

“Dije wanne dalili na baki na watsar dani haka? Kika sa naji zumunci dake tsakanin mu bai kai inda nake tsammani ba.”

 Itama Daadar tana kuka take girgiza mata kai. 

“Na taho ne a halin kidima, ki yafe mun, kina daya daga cikin mutanen da tunaninsu bai taba barina ba…saboda kece kadai nasan kin soni, zaki kuma soni batare da kin juyamun baya ba a duk wani juyi da kaddara zatayi mun…”

Anyi koke-koke, anyi alhini, an kuma yi hirar yaushe rabo, kaunar da jini kadai kan samar ta nuna a fuskokin kowa. Kafin Madina tayi nata kukan lokacin da aka rakata dakin miji, tayi kuka kashi-kashi, amman fiye da rabin kukanta na farin cikin da taji ya dirar mata ne, ganin tarin mutanen da sukayi mata rakiya gidanta, kuma kusan kowa a ciki ta duba alaka ta jini ta hadasu, kowa kuma yana riketa kamar yana son tabbatar mata rashin Kabiru da Yelwa ba zaisa ta taba yin maraici ba. Kafin su tafi su barta da Salim da tun bayan sallar godiya da sukayi suka ci abinci dan yanata mata koken yunwar da yake ji, suka kwanta ya riketa a jikin shi yana fadin

“Nagode Madina, da kika zabeni, duk da ina da dalilai da yawa da nasan cewa ban cancanta ba. Daga ranar da aure ya hade mu waje daya, daga yau, zanyi kokarin ganin na kare miki mutuncinki, zanyi kokarin ganin nayi miki rikon da ba zakiyi dana sanin zaben da kikayi mun ba…”

Cikin sanyi yake maganar, a hankali, da wani taushi da ita kadai take gani a tare dashi. 

“Ni ce da godiya Hamma, kai da ka zabeni tun da ayar tambaya akan asalina, kai da ka zame mun bangon jingina a lokutta mabanbanta, Hamma ni ce zan gode maka daka zabeni, daka soni.” 

Wani abu yakeji yana tsirga masa, shekarunta da yaketa nanatawa kanshi da karantarta na bace masa, baisan komai ba a lokacin sai soyayyarta, kwakwalwar shi ta hade waje daya da zuciyar shi kamar yanda yake son hade duk wata tazara da take tsakaninsu shi da Madinar da batayi mamaki ba, a littafin hausa ne kawai zai tsaya rainonta, za’ace ya jirata saboda tayi kankanta, amman a irin litattafan da take karantawa shekarun nata ne kadai abinda zai jira, a wasu kasashen ta kai sha bakwai, a wasu ta kai sha takwas. Sai dai babu wani littafi, babu kuma wani hasashe da ya shirya mata wannan daren da ba zai gogu ba. Daren da tausaya, kauna da kuma lallamin Salim basu hana kwallarta zuba ba. Sai dai ta samu sauki da tabbaci a rikon da yayi mata kamar zai mayar da ita cikin shi. 

A hankali Salim ya bi duk wani lungu da sako da soyayyarsa ta samu zama a tare da ita batare data sani ba ya taso da son nan, tun tana mamakin yiwuwar kaso mutum da duk wani abu da zaka iya, amman duk rana sai yayi wani abu da zaisa kaji wannan son ya karu. Alkawarin da yayi mata kan karatu yayi kokarin cikawa duk kuwa da kishin da yanzun take sanin Salim din yana dashi. Ya kaita ta rubuta jamb da kanshi, ya jirata ta gama ta fito suka tafi gida. Karfi da yaji ya koya mata saka dogayen hijabi, ya kuma koya mata mota dan bayason ta shiga ta haya, kafin ya gama tara kudin motar da zai sai mata, tashi yake bar mata idan tace masa zata fita lokacin da yaci karo dana aikin shi. Shi ya hau ta haya.

A haka ta samu gurbin karatu a jami’ar Bayero. Bayan roko da tarin nasihar kula da kanta da Salim yake fada yana kara jaddada mata, duk idan zata fita haka zaiyi kici-kicin da fuska, kamar inda yana da zabi, inda baiyi mata alkawari ba, da ya hana karatun. In tana masa dariya wasu lokuttan kai kawai yake jinjinawa. Saboda ba zata gane ba, ba zata taba fahimtar baiwar halittar da Allah yayi mata a kasan kayan da take boye su ba, baiwar da yayi mata da sirrine a zuciyar Salim din. Taya zai san duk wannan ya kasa kishi da fargabar kar wani ya ko hango masa duk wannan?

Sai dai a cikin abubuwan da Madina ta kasa fahimta game da Salim, yanda baya bari taje gidan iyayen shi ita kadai, ko me akeyi kuwa zaice ta bari suje tare, idan sunje din kuma tare suke komawa gida. Ko kowa yana nan, ko ta roke shi ya barta zata ga ya hade fuska cikin yanayin da yake nuna mata ba zai tankwaru ba, dole ta tashi ta bishi su tafi. A ahalinsu kaf kuma babu wanda ya fahimci hakan sai Julde da Saratu, babu wanda abin yake damu a zuciya irin Julde, da zuwa yanzun yasan aura masa Saratu da Datti yayi gatane da son da baya mata ya hana shi gani. Har zuwa yanzun kuma mace daya ya so, Mero, kuma tazo a daya daga cikin kaddarorin da zasu horashi, ya sameta, halin shi ya nisanta shi da ita, nisa na har abada tunda tana gidan wani a matsayin matar shi.

Sai dai ko baiso Saratu ba, yanzun tilas ya girmamata, saboda ko Meron, duk son da yayi mata, duk ikirarin son da takeyi masa da tayi bai hanata tsallakewa ta barshi ba, bai kuka hanata fadawa kowa dalilinta ba. Wani tonon asiri da Saratu bata tabayi masa ba a tsayin zaman su, sirrin neman matan shi da duk wani wulakanci da ya taba yi mata a tsakanin su yake tsayawa. Abinda ya fahimta a kurarren lokaci, abinda kuma yake jin ciwon rashin fahimtar shi tare da ciwon yanda koya yaran nashi suke zaune a gidan, in dai Salim na nan da Madina ya shigo zaiga yanda nutsuwa ta kwacewa Salim, zai kuma ga yanda yake gyara zama yana duk wani kokarin kare Madina daga ganin shi, kamar yana tsoro, zai sake kallonta da idanuwan da suka wuce na mahaifi.

Abinda ya kasa sabawa da ciwon shi, abinda yake shiga daki ya zubar da hawaye duk idan ya kadaice. Tabbas ko dashi kadai aka barshi ya ishe shi horo, kuma ya ishe shi karin ganin girman Allah, da zaka yiwa laifi, ka maimaita, ka tuba ya yafe maka, ka sake maimaitawa, kaje da kokon tuba kuma ya sake duba ka da Rahmar Shi ya yafe maka. Shisa Julde a yanzun yake kokarin ganin ya gyara tsakanin shi da Allah, tunda ya gane, yana kuma da yakinin Allah ne kadai zai gyara tsakanin shi da sauran mutane, wata rana ya wanke shi a idanuwan Salim, ya yarda da kaddara ce da take tare da kowanne rai, ita ta fisge shi ya dubi Madina da wani ido na daban, kaddarar da ya san ba zata sake faruwa ba. 

Salim din bawai nadamar Julde bace bai yarda da ita ba, zuciyar shi ce baisan yanda zata wanke masa shi ba, baisan ya zai goge hoton data adana masa ba, watakila a gaba, watakila hoton na daya daga cikin abinda lokaci zai tafi dashi, ko kuma akasin hakan. A kowanne yanayi dai, shi din mai godiya ne, musamman a ranakun daya dawo daga aiki a gajiye, ko a ranakun daya ranshi yake a bace, saiya dawo gida, ya samu Madina da murmushinta, Madina da sanyinta, Madina da duk wani halaye daya hade ya samar da ita tana jiran shi, hannuwanta a bude a matsayin tashi, matar da Allah ya bashi duk da yanajin bai cancanci samunta ba. 

Sai ya godewa Allah, musamman da bincike ya nuna akwai karamar ajiyar shi a tare da ita. Saiya rikota a jikin shi. 

“Ina son ki”

 Ya furta yana dora goshin shi akan nata, ta lumshe idanuwanta kawai, bata gajiya da yanda yake yawan fada mata yana sonta, sai dai ita son da takeyi masa a yanzun tana jin kalmomin ukku sunyi kadan su misalta shi, tare da cikin da yake jikinta dai take fatan ya fahimci kadan daga ciki, tunda ta shirya tara iyali dashi, ta shiryama kaddarar data hada rayukan su karkashin inuwa daya, ta shirya ma zama dashi a kowanne yanayi zasu tsinci kansu. Tunda har abada din da kowa yake musu fata ana karawa da gaban abadan ma duka tafiya ce mai nisa. Sai dai zatayi ta, zasu cigaba da yinta cikin godewa Allah da kuma fatan kowacce kaddara, mai sauki da marar sauki idan ta riske su, ya basu mafita, ya basu karfin zuciyar daukarta.

Ta sauke numfashi tana zagaya hannuwanta ta rike Salim din, Hammanta, mijinta. Nima kuma na sauke alkalamina anan, cike da godiya ga Allah da naga farko da karshen tafiyar nan duk nisan da tazo da ita. 

Godiya ga daukacin mutanen da addu’o’in su suka sama mun kwarin gwiwa a duk lokacin da naso tsayar da tafiyar nan. 

Na gode da goyon bayan da kuke bani a ko da yaushe

Nagode da yanda kuke supporting dina da kalaman ku, wasu a ciki da katin waya, data harma da wanda sukayi mun kyautukan da suka bani mamaki

Nagode

Nagode

Nagode

Ku sani, batare da goyon bayanku ba, ni din a matsayin marubuciya ba kowa bace ba. Ko ban fada ba na sani, kun sani #AnaTare

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.4 / 5. Rating: 9

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 57

1 thought on “Rai Da Kaddara 58”

  1. Dukkan gdy da yabon sun tabbata ga Allah madaukakin sarki me kowa me komai tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayayye masoyin ubangiji shugaba kuma cika makin halitta ruhullahi Hakika Allah yayi bayanin baiwa da kuma basira acikin littatafansa masu tsarki ita wannan baiwa yana baiwa bayinsa nagartattu ne da kuma wanda yayi dace rubutu hikima ce naki hikimar ta zarce hikima anty lubna Allah yakara baseera yaja kwana lfy da zuriyya dayyiba.
    Amin ya rabbi
    Amin ya Rahman
    Amin ya Rahim.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×