Skip to content
Part 14 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Da yawa zasu ce tana jin ranar ne daban saboda ta kasance daya daga cikin ranakun da ya kamata ace suna da muhimmanci a tare da ita, tunda a yau din ta kammala jarabawar aji shidda da ake kira da WAEC. Sai dai ita din ba kamar kowa bace ba, yanda ta ga yan ajin su na murna da rawar kafa tunda ma suka shiga aji shiddan sai ya dinga bata mamaki, zaka rantse da sun gama sakandire shikenan sun rabu da karatu har abada, bayan tana jin tarin burikan da kowanne a cikin su yake lissafawa.

“Ke ba zakiyi su calender din da naga Adee tayi da suka gama makaranta ba?”

Salim ya tambayeta, dan shima yaga da yawa matan ajinsu sunyi a wancen lokacin, tunda duk sun bashi, wasu a ciki yana da tabbacin sun bashi fiye da abinda suka rarraba, da yake shima jeka ka dawo yayi, kuma Julde ya bashi mota tun yana aji biyar, da ba da ita yaje ba, bashida inda zai zuba kayayyakin da aka dinga bashi

“Um um fa, ni babu abinda zanyi…”

Dan ba burgeta sukeyi ba, bata da wata kawa da zata nuna ta kira da tata a cikin ajin gabaki daya. Sai dai tace abokan karatu, zasu gaisa dai, sunma fi kulata idan an bada wani aiki mai wahala da suka kasa fahimta suna son ta taimaka musu. Shisa yau ana gama jarabawa ta fito, taji dadin samun Salim yana jiran ta, sai hade fuska yake sanda ta shiga motar, ta kuma san baya rasa nasaba da hayaniyar da ta karade wajen da zaice mata yana jinta har cikin kwakwalwar shi.

“Mug…”

Ya kira, murmushi tayi mishi, bakar rigace a jikin shi, kamar yanda tunda ya fara aiki yake cikin su, sai ya dora farar rigar da zata nuna maka alamar likita ne a sama, yanzun take kara ganin dalilin da yasa wasu a ajin su suke tambayarta meye hadinta da Salim, yana da kyau, yana da kyawun da ba saika kalle shi sau biyu ba zaka gane hakan. Musamman yanzun da ya ajiye gashi kwance luf a fuskar shi, saiya kara wani irin kyau da Madina ta san ba ita kadai take ganin shi ba. Kaf gidan su babu mai kyawun shi, shine ya biyo Julde sak, sai dai takan ga idanuwan Saratu a cikin na shi.

“Hamma Am, yau fuskar ka ta mun wani iri.”

Numfashi ya sauke yana murza mukullin motar, kamar ba zai amsa ba dan har yaja motar ma sun fara tafiya.

“Nagaji ne, na kwana a wajen aiki, tunda safe ina can kuma…sai yanzun na taho.”

Har ta daina tambayar shi akan maganar shifting da tasan anayi a asibiti, wasu suyi aikin safe, wasu na rana, wasu na dare, tunda ya fara zuwa asibiti ta kula rabin rayuwar shi acan yake yinta, kamar bashi da wani abu a yanzun da yafi majinyatan asibitin da yake aiki muhimmanci. Kuma kusan hakanne, tunda yana jin kamar yana wani abu da rayuwar shi wanda ya kamata, kamar da duk wata dakika da zaiyi wajen taimakon tarin marassa lafiyan da ke asibitin da yanda daudar zunuban shi take dan ragewa, duk da a satikan yana jin da ya rage daudar daya sake maye gurbin ta da matan da yake bi.

“Ki dauki gifts dinki a baya.”

Salim ya fadi bayan ya tsayar da motar kofar gidan Daada, duk hirar da ta dinga mishi da um yake binta, yar maganar ma bata samu ba, kamar yanda yace mata a gajiye take duk wata alama ta nuna a gajiyen yake.

“Kasan ina son ka ko?”

Ta fadi tana murmushi, idanuwan shi kawai Salim ya saka cikin nata, shi ya fara cewa yana son ta, sau daya ne, bai kara ba har yau. Sai dai ya bude mata hanyar fada mishi tana son shi duk lokacin da zai mata wani abu da taji dadi. Bai sake fadi bane saboda ya ga soyayyar da yake nufi da wadda take nufi tayi hannun riga. Sai dai baya nufin soyayyar ta bata nukurkusar shi, bayajin ta har kasan ran shi, ya sha farkawa cikin dare ya duba zuciyar shi yaga itace dalilin tashin na shi. Bai kara sanin da gaske soyayyar da yake mata take ba sai lokuttan da ya samu kofar rungumar ta a jikin shi yaki yin hakan.

“Madina ce.”

Shine abinda zuciyar shi ta gaya mishi, a lokuttan ne kuma yaga yanda yake da zabi a rayuwar da ya daukar ma kan shi, idan yana son jinta a jikin shi da duka rayuwar shi amman ya iya rike kan shi, me yasa yake kasa rike kan shi akan sauran matan? Ya dauki tunanin ne yayi kasa dashi yasa wani abu mai nauyin gaske ya danne shi, Madina tana nan, babu inda taje, babu inda zataje, zai kara jira, zai tabbatar zuciyar ta na in da tashi take kafin bakin shi ya kara furta mata kalaman yana son ta.

“Ledoji biyu ne Hamma.”

Batare da ya juya ba ya amsa ta.

“Duka zaki dauka.”

Da ta dauka din ma, bayan addu’a sai da ta kara cewa tana son shi, baice komai ba yaja motar shi yana ficewa daga lungun. Ita kuma gida ta shiga da sallama tana kiran Daada tun kafin ta karasa cikin dakin.

“Daada…”

Ta kara fadi ganin ta a kwance kan doguwar kujera, takalmanta ta cire tana takawa har inda Daadar take, sai da ta ajiye ledojin hannunta a kasa tukunna ta kai hannu daya ta taba jikin Daada, har lokacin akwai zazzabi, mai zafi ma.

“Daada zazzabin nan har yanzun?”

Madina tace cike da damuwa, murnar da ta shigo da ita na dishewa.

“Da sauki, dazun ya sauka ma, dawowa dai ya kara yi kuma na sha magani.”

Bata yarda ba, tasan Daada da karfin hali

“Ko dai in kira Daddy?”

Da sauri Daada ta girgiza mata kai.

“Ki kyale shi, da sauki har abincin da kika dafa na dan ci fa.”

Numfashi Madina ta sauke, da yake sai karfe sha daya take da jarabawar ranar, tana tashi da asuba ta shiga kitchen, sai da ta dafa farar shinkafa, suna da miyar kifi a fridge, dumamata kawai tayi. Ta gyara ko ina tsaf tukunna ta fita, dan ko lafiyar Daada kalau ma, da daddare take wanke-wanke, sai ta share ko ina take tafiya makaranta, girki kawai Daadar takan yi musu kafin ta dawo daga makaranta, da ta gane yin miya da yawa ta saka a fridge ma sai dai ta dafa musu ko shinkafa ko taliya.

“Me kika samo haka?”

Daada ta tambaya tana son canza akalar zancen.

“Hamma ne ya bani… Bari in watsa ruwa in sake kaya.”

Kai kawai Daada ta jinjina mata, wankan kuwa tayi ta fito, wando ne daya dan wuce gwiwarta yana da madauri daga kasan, sai riga ta kusan kamo tsayin wandon, ta saka bakar safa doguwa. Hulace a hannun ta tana rike da ita, kan kujera ta zauna tana kwance abin da ta daure gashinta dashi dan ta gyara kan duk ya cakude mata, kallon ta Daada takeyi, da gaskiya gashi rabo ne, waye zaice Madina zatayi gashi? Babu kitso a kanta saboda ta tsani kitso, sai sun kai ruwa rana take zuwa ayi mata, shima guda biyu ne ko hudu. Duk idan tayi biyun nan tana kama jelunan dan ta nannade su sai wani abu ya soki zuciyar Daada.

Yanzun ma yanda take tattara gashin bayan ta warware shi tana kokarin gyarawa sai da taji zuciyarta ta matse, bata yi kama da Yelwa ba, sai dai ko jini, Yelwa na da kyau kamar mahaifinta da sauran yan uwanta da suke biyo shi, duk da itama Daadar fulani ce gaba da baya, ba zatace gashi ya saka Yelwa a tsakiya ba, tunda bata da wadatar shi, amman mahaifinta na da shi, a nannade ma. Na Yelwa ya sauka har kan gadon bayanta, gashi da santsi, kamar yanda na Madina yake yanzun, bambancin kawai shine Yelwa na son gayu, tana kuma ji da gashin ta, Madina bata damu da shi ba.

“Badon kar Allah ya kamani ba ko Daada? Da nayi aski, ko rabine dana yanke”

Ta kan fada kusan duk lokacin da zata taje kan ko inta dawo kitso, gashin bai dameta ba, yanda zata kama shi ta nannade ta daure ta saka hula, ba zaka tana sanin tana da gashi ba sam-sam.

“Kinki zuwa kiyi kitso ko?”

Lokaci daya yanayin fuskar Madinar ya canza, bakinta ta turo gaba, tana kai hannu ta gyara zaman gilashin ta, bata ko amsa Daada ba ta janyo ledojin da ta ajiye, da alamar dayan litattafai ne a ciki. Tana kuwa budewa taga sune har guda goma, murmushine ya kwace mata batare ma da ta sani ba tana fadin.

“Allah ne kawai zai biya ka Hamma.”

Har ranta taji dadin kyautar, batajin akwai wani abu da zakayi mata kyauta da shi da zai faranta ranta kamar littafi. Ko damuwar Yelwa da ta kasa cirewa a ranta, dan duk yanda ta so ta ture tunanin iyayen nata can kasan ranta sai ta kasa, tana zaune zata ji sun fado mata. Idan abin ya isheta zata dauki littafi, babu wani tunani da yake rage mata banda kalmomin da suke yawo a idanuwanta duk idan ta dauki littafi. Ko rike littafin tayi a hannunta sai taji farin ciki. Dayar ledar ta jawo tana budewa, wannan karin ihun da tayi sai da Daada ta dan runtsa idanuwan ta.

Waya, waya ce a kwalinta. Ta kasa daina ihun murna.

“Waya Daada… Waya…”

Take fadi kamar zata fasa dakin da karajin ta, tama kasa nutsuwa ta bude wayar da kyau, zuciyarta har makoshin ta saboda murnar da takeyi, dakyar ta iya samun nutsuwar dubawa taga Itel ce da sukayiwa laqabi da vision. Ta taba ganin wata itel a hannun Samira yar islamiyyar su, da yake yarinyar bata gajiya da nuna cewa babanta mai hali ne, duk tsanani irin na makarantar sai da ta zo da waya a boye, yana ta nunama kawayenta, wayar tayi ma Madina kyau, dan wata taji tana cewa.

“Itel ce, irin ta Yayana sak.”

Tunda daga nesa take hangen su, waya na burgeta, ko dan ma ta dinga daukar hotunan lallen ta, tana yawan jin ana zancen manhajar Instagram inda zaka iya dora hotuna irin wa’annan, ita duk a cikin kafofin sada zumunta nan ne take zumudin budewa. Saboda jin yanda Instagram yake ne yasa ta dan kulla abota da Nafi’un ajin su, shi yayi mata bayanin komai, har tana ganin ta gama fahimtar yanda manhajar take, waya ce kawai ta rage mata. Inda tace Julde ya sai mata, zai sai mata, amman tunda bai dauka ya bata da kanshi ba, tana da yakinin yana ganin lokacin da zata rike ne baiyi ba.

Gashi Salim ya bata, sai da tazo budewa ta kula da an ma bude wayar, dan babu ledar sabuntar nan, kwalin kawai ta cire, aikuwan an bude dan har pouch an saka mata baki, wayar tayi mata kyau matuka, fara ce.

“Daada kingani.”

Ta fadi cike da farin cikin da yasa Daada murmushi, karbar wayar tayi tana dubawa.

“Ma shaa Allah. Allah yasa alkhairi yabar zumunci…”

Farin ciki baibar Madina ta amsa Daada ba, wayar kawai ta karba tana kunnawa, cike take da caji, Salim kuma har sim ya saka mata, sa da ta gama kawowa ne taga kusan komai ma ya saita mata shi, dan har email ma taga ya bude mata, yar takarda ta kula da ita a cikin kwalin wayar ta dauko tana warwarewa, aikuwa email dinne da kuma password din shi ya rubuta mata, shafa rubutun tayi cike da farin ciki, tana tunanin yanda wannan cakudin rubutun da likitoci suke da shi na Salim ya bambanta, yana da rubutu mai matukar kyau.

Duba contact dinta tayi, ya saka mata lambar shi, ta Khalid, Adee, Julde, sai lambar Nawfal. Duka da sunayen su yayi saving, sakewa tayi tana gyarawa zuwa yanda take so, ta shi lambar ta saka “Hamma Am” a jiki. Murmushi yaki barin fuskar ta, earpiece din wayar da cajar ta dauko tana gyara kwalin ta rufe ta mayar cikin ledar ta kulle, murna fal cikinta ta dauka da ledar litattafan ta kai daki ta ajiye su kan gadon ta sannan ta dawo tana nufar kitchen, abinci ta zubo ta dawo ta zauna suka fara hira da Daada, duka yau hirar akan wayar tane da abinda zatayi da wayar.

*****

Ta dauka bambancin ranar zai kare ne da kyautar da ta samu daga wajen Salim, da kuma wayar da sukayi, duk da sukanyi a land-line din Daada, amman sai take jin wannan din ta sha bamban, sanda duk ta so magana da shi zata iya, flashing kawai zatayi mishi ta san zai kirata. Har ta fara bacci, wajen karfe goma da rabi ta farka, sai ta sauko daga kan gado ta nufi dakin Daada, ba bakonta bane ba, ba kuma ranar bace ta farko da ta saba barin dakinta taje bayan Daada ta kwanta, wasu lokuttan ma cikin bacci takeyin hakan, sai da asuba take sanin ta koma dakin.

Karfe daya da kusan rabi taji Daada tana zare jikinta daga rikon da tayi mata, saukarta daga kan gadon yayi dai-dai da bude idon da Madina tayi tana juyawa, wani yunkurin amai da Daada tayi yasa Madina dirowa daga gadon tana jin ta wartsake gabaki daya, bandakin ta shiga, da yake da wuta kwan a kunne yake, amai Daada takeyi kamar zata zazzage hanjin cikinta, banda sannu babu abinda Madina takeyi mata. Ita ta taimaka mata ta wanke fuskarta ta kuskure bakinta suka fito, zazzabi ne a jikin Daada kamar wuta, cikin kasa da minti talatin harta fara fita daga hayyacinta saboda zafin zazzabi.

Madina bata san hawayen ta zai iya yin nisa ba sai yau, banda bari babu abinda jikinta yakeyi, musamman da ta jijjiga Daada tana kiran sunanta taga ko jinta batayi, dakyar ta samu ta sauketa daga jikinta, dakinta ta nufa tana dauko wayarta ta kunna, sai take ganin ta dade bata gama lodin ba, tana karasawa lambar Salim ta lalubo tana kiran shi, tana jin bugun wayar na daidaituwa da na zuciyarta, sai dai harta yanke bai dauka ba, sai da tayi mishi kira hudu, ana biyar ya daga yana fadin

“Mug…lafiya?”

Numfashinta na wani irin sama, muryarta na sarkewa saboda nauyin da harshenta yayi tace.

“Da… Daada bata da lafiya… Hamma, Daada…”

Ta karasa a wahalce.

“Ki nutsu, ki tuna abinda na fada miki na taimakon gaggawa, kina jina? You can do this, kije wajen ta, yanzun zan taho.”

Kai Madina take dagawa tana fita daga dakin, wayar ta ajiye a gefe tana karasawa wajen Daada da sauri ganin tana yunkurin amai, juyata tayi kan hannunta kamar yanda ya sha fada mata, saboda a rigingine Daada take, zata iya shakewa idan tayi amai a haka, sai zazzabin jikinta yayi yawa, bandaki ta nufa tana zubo ruwa a bokiti ta dauko towel ta zo tana tsomawa, idan ta matse sai ta goge ma Daada duk inda ta samu a jikinta. Bata san iya tsayin lokacin da suka dauka, ko inda ta samo nutsuwar da ta samu ba.

Da Salim ya kira wayarta ma, da kanta ta dauki mukulli taje ta bude mishi gidan suka koma ciki tare, batayi mamakin yanda ya kama Daada yana dagata ya saba a kafadar shi ba, ko nishi bata ji yayi ba, hijabin Daada ta daukar mata, tana komawa dakinta ta saka karamin hijabi itama. A kofar gida ta samu Salim, shiya karbi mukullin yana rufe gidan, baya ta shiga kusa da Daada tana kama hannunta ta rike, Salim ya zagaya mazaunin direba yaja motar. Asibitin Aminu Kano inda can yake aiki suka nufa, babu wani bata lokaci aka samarwa Daada daki ita kadai aka kuma fara bata taimakon da take bukata, saboda Salim din, shi baibi sauran likitocin ba sai da ya tsaya aka binciko file din Daada tunda nan asibitin take zuwa duk idan bata da lafiya.

Da kanshi ya bude yana bincika record dinta kafin ya bisu dakin, har an saka mata ruwa an mata allurar jini, wata Nurse tace mishi an dauki jininta don a gudanar da gwaji, tambayoyi ya shiga yi ma likitan daya duba Daada din suna magana cikin harshen da in ba fannin aikin su ka karanta ba sai sun fassara maka zaka gane me suke cewa. Tare suka fito da likitan, shi yana wucewa, Salim kuma yana kallon inda Madina take tsaye ta jingina bayanta da bangon wajen, ko takalma bata da shi, safa ce a kafarta, dan dai tana da kauri, sai kayan baccin da ko shi ya saka tsayin wandon ne kawai zai mishi kadan. Dan murmushi yayi yana karasawa ya taba kafadarta.

Da sauri ta kalle shi.

“Hamma? Me yake damun ta?”

Kai Salim ya girgiza mata.

“Komai zaiyi dai-dai.”

Ganin yanda take kallon shi ya sa shi dorawa da.

“In shaa Allah”

Kai ta jinjina badan ta yarda ba.

“Ki shiga ki zauna da ita, zan kira Nanna in fada mata.”

Kan dai ta sake jinjina mishi, murmushin karin kwarin gwiwa yayi mata, baya son yanda tayi sanyi, sai da ta tura kofar dakin da Daadan take ta shiga tukunna ya sauke numfashi. Ya kanji Julde yace Daada bata da lafiya, ko kuma ya biya ya kai mata magungunan ta, wasu lokuttan ma tare suke zuwa su duba ta, amman yaune ranar farko da yasan tana dauke da ciwon zuciya, saboda bai taba tambayar Julde me yake damun Daada ba, yanzun ma a file din ta ya gani, jininta ma yakan hau ya sauka, amman baya irin hawan da za’ace yana barazana da rayuwar ta, ciwon zuciyar ne dai.

Da alama Madina ma bata sani ba, kuma ba zai zama na farko da zai fada mata ba. Lambar Julde ya fara kira sai yaji ta a kashe, hannu ya kai yana murza goshin shi, yana da round din da zaiyi, ba yanda za’ayi ya zauna da Madina, kuma ba zai yiwu abarta ita kadai ba. Baya son wayar ta tashi Saratu, Khalid ya kira, bugu biyu ya daga.

“Hamma, lafiya dai ko?”

Yanayin muryar Khalid din ya sa Salim fadin,

“Uban me kakeyi ba kai bacci ba har uku na dare?”

Yanajin yanda Khalid ya sauke mishi numfashi a kunnen shi, abinda ya tsana, shisa in zai waya yawanci yake sakata a speaker ya ajiye a kasa, ya rasa dalilin da zaisa anna waya ana numfarfashi da wasu kananun nishi da yake bakanta mishi rai.

“Kira na kayi kaji ido na biyu ko akwai abinda zaka fada mun?”

Cewar Khalid din.

“Daada bata da lafiya, gata a asibitinmu, ka fadawa Nanna, bana so in tasheta da waya.”

Yana jin motsi alamar Khalid din ya tashi.

“Subhanallah, tun yaushe?”

Kashe wayar Salim yayi, saboda zai iya watsama Khalid din zagi, yana da tambaye-tambaye marassa amfani, a aljihu ma ya saka wayar, yana barin bangaren gabaki daya zuwa inda ofishin shi yake.

****

“Daga jikin wa ka baro ka taho?”

Cewar Saratu bayan Julde ya shigo dakin tana binshi da wani mugun kallo, bacci takeyi taji ana kwankwasa dakinta, da kyar ta rabu da gado tana zuwa ta bude.

“Nanna…”

Khalid ya kira yana dorawa da,

“Daada ce bata da lafiya, tana asibiti, yanzun Hamma ya kira yake fadamun.”

Dan dakuna fuska tayi, kafin ta jinjina ma Khalid kai tana juyawa batare da tace komai ba.

“Bari in sakko dogon wando in dauko id card dina sai in zo mu tafi.”

Har ranta batayi niyyar zuwa ba, rashin lafiyar Daada ba matsalarta bace ba saboda dalilai masu yawa, amman akwai halayenta da bata cika son yaran nata suna gani ba, musamman Khalid, shisa ma ta daga mishi kai kawai, kayanta ta sake itama, suna hanya tana hamma saboda baccin da ko awa batayi da samun shi ba. Fadan da sukayi da Julde kafin ya fita ya sa taita juyi a gado ranta na mata zafi.

“Bunsuru kika taba kirana Saratu, ko kin manta? Ban canza ba har yanzun, bunsurun ne, ki daina yin kamar baki san abinda zan fita yi ba.”

Duk tashin hankalin da tayi bayan nan ko inda take bai kalla ba, tasani, ta fi kowa sanin me yake fita yi duk daren da zai shirya tsaf ya fice, tana kauda kaine yanda ta saba, tana kuma amaye abinda take ji idan yazo mata wuya. Kamar yanda tayi jiya, sai dai ko yaushe ita ce take faduwa kasa warwas, dan fada da Julde babu riba a cikin shi, ko tace bata samun riba a fada da shi. Sai ya tabbatar ya nuna mata bata da muhimmanci a rayuwar shi, zaman da takeyi da shi zabinta ne, in ta barshi babu abinda zai canza. Hakan yafi mata ciwo fiye da neman matan shi, ba zatayi karya ba, zata so ko kadan ne ta samu wani muhimmanci a rayuwar shi.

Don shi yana da shi a tata rayuwar, akan ce wasu mazan na duba darajar ‘ya’ya, to a idanuwan Julde bata taba cin darajar yaran su ba, zaka rantse da Allah shi yayi dakon cikin su, nakuda da rainon su.

“Saratu”

Julde ya kira cike da kashedi yana kallon Daada da take kwance, da alama bacci takeyi, sanin cewa bai daina halin shi ba shine karshen abinda zai so taji.

“Meye? Baka so ta sani? Baka so taji babu abinda ya canza daga mugun halin ka?”

Runtsa idanuwan shi Julde yayi yana sake bude su akan Daada, ko motsi baiga tayi ba. Likitanta daya gani kafin ya shigo ya fada mishi ciwon zuciyarta ne, amman babu wata matsala in dai ta samu hutu kwana biyu, a kuma tabbatar babu wani abu daya faru da zai daga mata hankali, in dai an kiyaye wannan zata samu sauki. Wannan maganar da Saratu take son ya biye mata suyi na cikin abinda zai daga hankalin Daada. Shisa yaja kujera ya zauna yana yin shiru ya kyale ta. Yana jin yanda take watsa mishi wani irin kallo, kafin ta ja tsaki tana mikewa ta fice daga dakin.

Daman ko bai zo ba, ita gida zata tafi, bata da dalilin zama asibiti, ta dai cewa Madina zata zauna ne dan taje gida ta watsa ruwa ta sake kaya ta kuma dauko musu abinda suke bukata. Salim ne ya tafi ya kaita tunda gari ya waye. Da kanta ta kira Adee ta fada mata, saboda tasan zata kawo abincin kari.

“Saboda Yelwa kawai.”

Ta fadi cikin ranta bayan ta rufo musu kofar. Ko Daada ba darajar Julde take ci ba a wajenta, saboda Yelwa ne, in har mutunci zai shiga tsakanin su bayan tarin kiyayyar da ta nuna mata to saboda Yelwa ne. Julde kuwa numfashi ya sake saukewa yana kallon Daada, wayar shi a kashe take, cikin mota ma yabar ta, sanda ya fito bayan asuba ya zo ya kunna ya ga sakon Khalid, kai tsaye asibitin yayo, sai dai da nisa daga inda yake, tunda yafi zuwa hotels din wajen gari, inda kafin ya hadu da wanda ya sani za’a dauki lokaci, ko gidan gonar da yayi shi don wannan dalilin kawai ba don komai ba.

Kafin yayi wani tunani an turo dakin da sallama.

“Daddy…”

Salim ya fadi cikin gaisuwa, Adee da ta shigo bayan shi da murmushi a fuskarta ta gaishe da shi itama, kallon ta Salim yayi, suna hanyar gidan Daada wayar Salim ta shiga vibrating, dagawa yayi ganin Nawfal ne ya sa shi kai wayar kunnen shi.

“Na kira Hamma Khalid bai daga ba, me ya sami Daada? Yace mun bata da lafiya tana asibiti, me suka ce yana damun ta? Ya jikin ta?”

Yanda yayi duka tambayoyin a numfashi daya yasa Salim fadin.

“Da sauki.”

Cikin taushin murya yana dorawa da,

“Zazzabi ne kawai, da sauki kuma sun riketa ne dan ta huta sosai.”

Duk da baiga Nawfal ba yasan ya ciza gefen leben shi na kasa yanda yakan yi duk idan yana cikin damuwa.

“Dan Allah Hamma ka fadamun gaskiya, ya take? Boye mun ba zaiyi amfani ba, is not like zan iya tahowa yanzun-yanzun, kawai ina bukatar in san halin da take ciki.”

Bai fada mishi dukkan gaskiya ba, amman da sauki, zazzabin ya sauka, da kan shi ya duba kafin su taho, kuma jininta lafiya kalau, bai hau ba.

“Ga Madina…”

Salim ya fadi yana mika mata wayar, saboda baisan me zai fada Nawfal ya yarda da shi ba.

“Madina”

Muryar Nawfal ta daki kunnen ta tana sakata jin wani abu ya tsirga mata.

“Hamma”

Cikin wani irin yanayi Nawfal yace,

“Ya take Madina? Ki fada mun? Ke nasan ba zaki mun karya ba.”

Numfashi ta sauke,

“Da sauki, bata kara yin amai ba, tana ta bacci ne, gani ma Hamma zai kaini gida in watsa ruwa in dauko mana su kafet haka…”

Tana jin ajiyar zuciyar da Nawfal ya sauke yana ma Allah godiya cikin harshen fulatancin.

“Ban san ya zanyi ba in wani abu ya same ta, ban sani ba…na kusa dawowa gabaki daya in shaa Allah, saura yan watanni, ba zan kara nisa ba idan na dawo…”

Madina bata jin ko ya dawo zata daina jin yanda yayi mata nisa.

“Idan ta tashi ki kirani, tana tashi Madina.”

Kai ta jinjina.

“Zan kira ka Hamma…”

Kamar ba zata sake cewa komai ba tace.

“Ka yarda dani, da sauki, da sauki sosai.”

Yanda ta karasa maganar ne ya kasa barin kunnen Salim, kulawar da take cikin muryarta yaji ta sa kirjin shi ya matse, sai kuma yanda ta mika mishi wayar tana fadin

“Hamma ya cika saka damuwa a ran shi.”

Tana saka shi dana sanin bata wayar da yayi, har ya jirata bai daina jin wani zafi-zafi a kirjin shi ba, yanzun ma da yake kallon ta yana jin yanayin na karuwa ne, akan me zata sauke murya da yawa haka, shi bai taba ma jin ta sauke mishi murya cikin kulawa yanda ta sauke ma Nawfal ba, wayar shi da yaji tana zuu cikin aljihun shi ya zaro ya duba.

“Hamma ne?”

Madina ta tambaya, shi dinne, baisan me yasa ya girgiza mata kai yana juyawa ya fice daga dakin kafin ya daga wayar ba.

“Hamma ta tashi?”

Nawfal ya tambaya daga dayan bangaren.

“Yanzun muka dawo Bajjo, bacci takeyi, tana tashi ni da kaina zan kira ka.”

Yana jin Nawfal din ya sauke numfashi cike da damuwa.

“Bacci takeyi, bacci take Bajjo, na taba maka karya?”

Cewar Salim yana jin yanda baya son damuwar Nawfal din da yake karanta ta cikin wayar.

“Zan kara kira.”

Kawai Nawfal yace yana kashe wayar. Dakin Salim ya koma, camera din wayar shi ya shiga yana kashe hasken sannan ya dauki Daada hotuna guda biyu, batare da tunanin komai ba ya bude whatsapp din shi yana tura ma Nawfal.

“Kagani, da sauki, kuma kaci abinci.”

Ya rubuta a kasan hotunan yana sauka daga whatsapp din bayan yaga shigar sakon na shi ya mayar da wayar a aljihu, bashi da matsala da kula da Nawfal, kawai baya son Madina tayi ne, ko kadan baya so, bai taba sanin baya so ba sai yau.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 13Rai Da Kaddara 15 >>

1 thought on “Rai Da Kaddara 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×