Skip to content
Part 1 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Mujahid na kwance kan doguwar kujera a matsakaicin falonsa da ke cikin gidan Baffansa wan mahaifiyarsa, a zahiri kenan amma a badini ya fi son dangantar da ya zaba musu yake kuma fatan ta zama ita ce abin kallo kuma wadda za’a ambata, wato a kira dangantakar da sunan gidan surukansa kuma gidan matarsa wadda yake so, son da bai taba tsammanin an taba yi wa wata mace irinsa ba.

Sai dai inda gizo ke saqar shi ne, shi kadai ya san yana son, filin zuciyarsa da filin mafarkinsa kadai suka bata wannan matsayin, ba su taba juya baya kuma ba su taba cire tsammani ba. Ko bai sami mai fada masa ko ya jinjina masa ba, shi da kansa ya san zuciyarsa jaruma ce wadda ba a saba irinta ba, bata taba karayar jin cewa zata rasa abinda take so ba duk da kuwa abinda take son bai san tana son ba, kuma tana da tabbacin ko ya sani ba zai zama wani abin yabawa ko dada kai da kasa ba.

Binta yar uwarsa yake so, kuma a yau din nan ake kawo kayan lefenta da mijin da ta zaba wa kanta, ta zabawa kanta kawai, shi ne abinda zuciyarsa ta yarda da shi, bai yarda ta zabi abinda take so ba, don yadda zuciyarsa ta haddace Binta da sonta, haka take jin tamkar tana iya jin ko wanne amon zuciyarta a bangaren so da zabi ko wanne iri ne in dai an halicci irinsa a filin duniyar nan.

Shukuranu shi ne saurayin da Binta ta zaba zata aura, daga bangaren asali har bangaren halitta da na abin masarufi shukuranu ba shi da abinda zaa kushe, amma wannan nasarar tasa bai sa ya gamsu sun birge Binta wajen zabo shi ta aura ba, kawai dai ta zabe shi ne, don ba ya cikin irin mutanen da take qi, ko da kuwa ba ya cikin irin mutanen da take so.

Wannan shi ne hangen Mujahid, shi ne kuma abinda zuciyarsa ta yarda ta karba, don ba ta san tarkace abubuwa barkatai wadanda ba zasu sanya ta farin ciki ba ko kuma a cikin kamanceceniyarsu akwai nesanta shi da Binta.

A can cikin gida ana ta shan shagalin karbar dangin ango masu kawo lefe, shi kuwa yana nan qunshe cikin dakinsa son maso wani na gasa masa gujjiya a hannu, ya toshe kunnuwa don ya daina jiyo hayaniyar da zata fayyace masa abinda ake shirin yi na yi masa fashi masoyiya, amma kamar gayya kunnensa bai fasa jiyowar ba, har sai da ya fahimci babu abinda zai yi ya tsira face ya toshe zuciyarsa, to ta ina zata toshu, sannan in ya toshe ta da wacce zai tunana yadda zai qwato wa kansa matar da aka yi masa fashi?

Sai ya ji zuciyarsa na neman kekkecewa, dole ya miqe tsaye don zaton mutuwa a tsaye ya fi kama da jarumta.

Ya dinga safa da marwa a tsakar falon yana canki cankin dafe kirji da kame kai. Cikin wannan halin ya dauki tsawon lokacin da har ya ji gidan yayi dif, sai muryoyi qasa-qasa daga can tsakiyar gidan, alamar an gama kawo lefe dangin Angon fashin zuciya da sauran baqi tuni sun gane makwancinsu, yar hayaniyar da yake jiyowa ta tsirarun mutan gida ce wataqila sun sanya kaya lefe a gaba suna kallo, wasu na yabawa wasu na kushewa, wannan a zaune take.

Ba tare da hayyaci ba ya sami kansa a hanyar cikin gidan kai tsaye. Takunsa na nuna alamun fushi, amma zuciyarsa da niyyarsa ba su rabi ko wanne irin tawaye ba don sun san ba lokacinsa ba ne yanzu, ai ma karfi da zafin rai ba su cika galaba a kwato soyayya ba, yadda soyayya take da laushi haka hanyoyin samunta suke da laushi fiye da auduga, ana sanya musu karfi sai su zama qayoyi don haka kafin aje a tarar da soyayyar ita kanta an rikida ta ta zama qayar.

Bai saka ran zai tarar da Binta cikin masu kallon kaya ba kamar yadda alada ta saba, amarya kan dan yi nesa da kayan har a gama rurumar gani.

To haka ce ta faru, bai tarar da Binta ba, sai tarin kannensu na gidan da na dangi da kuma qawayenta, sai kuma  kanninsa na ciki daya, wato Sani, babu Hajiya mahaifiyar Binta.

Dukkansu hankalinsu yana kan kayan lefen, akwatuna shidda rus! Makare da kayan alfarma, ana zagawa ana gani.

Abinda ya ji a ransa sai da ya rantse cikin ran nasa ya wuce kishi, sai dai wani ciwo mai kama da neman rai, don haka duk yadda ya so ya gayyato siyasar da ya saba gayyata a alamuransa a yau din nan ya gayyato ta ta qi bayar da hadin kai, dole kowa ya ga yayi fuska ya qi duban kayan.

Sai yanzu ka shigo Yaya Mujahid? Tun dazu Anti Binta ke labarin son ganinka

Wata baqa siririyar doguwar budurwa ta tare shi da maganar cikin nuna shaquwa da ladabi.

Ya kawar da kai wanda hakan ya taya shi kawar da wani kason dacin da yake jin ransa na tanadowa.

Me zan mata?

Ya qi bawa neman baasin nasa muhimmanci don ya san ba abin arziqi take nemansa ta yi masa ba, bai wuce gaisuwa, neman alfarma ko wata hirar duniya ba, shi ba abinda yake buqata kenan ba, ita kawai yake buqata a matsayin masoyiya kuma mata, duk wani abu daga gareta in ba wannan ba baya muradinsa.

Ya harari kayan lefen a saye yana son ya juya tare da wayancewa ya ce,

Ina Hajiya?

Ummi qanwarsa da ke gefe ta lura da hararar da yayi wa kayan lefen, sai ta ji gabadaya qumajinta ya bi qasa, bata so abinda ta gani ba ta kuma tabbatar in ba ita ce ta gani ba wani ne ya gani akwai matsala, eh, mana! Yaya za a yi ace mutanen da suka riqe su tamkar su suka haife su ciki ba hatsi ba, amma ace su tasu sabgar ana nuna musu abu mai kama da baqin ciki?

Karima da ta damu da son miqa saqon Binta ta amsa masa,

Hajiya na da baqi a daki, amma Antin Binta ina jin neman da take maka Nabila take so ka mayar gida

Ya ji wani takaici mai zuzuta masa wutar kora ashar ya tunkudo masa, amma ya hana ashar din kutsowa don ya san in ta fito ba zata dira a muhallinta ba, Binta yakamata ya zaga, amma a duniyarsa ta fi qarfin zagi, wadda yake so ya zaga ita ce Nabila, ya haqiqance kuma bata da haqqi, in an zage ta zalinci ne.

Ya rausaya kai yayi gaba yana cewa,

Binta tana ina?

Tana daki

Karima ta amsa da karsashi don tana zumudin ya amsa kiran Binta ko zai samu katarin ganin tarin damuwar da ta gani a idonta dazu dab da zata fara nemansa ya mayar da Nabila gida, tana ma qaddarawa ba mayar da Nabila gida ne kawai mafi aalar neman ba, qila akwai wata a qasa.

Kai tsaye ya tunkari hanyar dakin Binta.

Ummi ta numfasa da kyar a qoqarinta na tabbatar da abinda ta gani, ta ce masa,

Yaya Mujahid ba zaka ga kayan lefen ba

A kanta ya sami gabar fanshe fishinsa, cikin hucin bacin ran da yake ta tarewa ya ce mata,

“Yanzu angon zai turo a mayar masa da abinsa ne da kike ta gaggawar in shiga cikinku yanzu in gani?

Sani qaninsa ne yayi karaf ya karbi zancen cikin son mayar da zancen raha, tsakani da Allah shi kansa bai so yadda Yayansa ke karbar wannan lamari ba, ko ba a kira abinda yayi baqin ciki ba zaa iya kiransa rashin kulawa wanda sam Binta da iyayenta ba su cancance shi ba.

Yana dariya ya ce,

Haba yaushe ango zai turo a mayar masa kaya? Ai kaya sun zo kenan sai dai a hada masa su da amaryarsa a kai masa tare

Mujahid ya so yayi magana, amma yana da yaqinin in dai ya furta ta sai ta batawa kowa rai, don haka ya kora ta da ruwan hakuri ya hadiye, kuma cikin qanqanin lokaci ya bace daga falon yana jiyo abokan wasansa na masa shegantaka da cewa,

Dole fa Mujahid ya shiga damuwa, tare da Anti Binta ake ta yi musu kururuwar sun qi aure har zasu tsofe a haka, abin takaici ta yi auren ta bar shi

Ka ji yan taadda, ba ma zata yi auren ba har sun daura mata auren da shegen bakinsu

Ya fada cikin ransa amma dai bai juyo ya tanka ba.

Kafin ya qarasa dakin yayi kacibis da su ita da Nabila sun fito. Tuni ya shiga taitayinsa, ya tsaya a gabanta tamkar wani wanta mai fada a ji a kanta, a haka ta san shi kuma a haka ta saba da shi, ya sani bata taba cankar ya tanadi halittar sonta cikin zuciyarsa ba.

Murmushin da ta tare shi da shi tun kafin ta dire abinta ya gane na yaqe ne,

Yauwa Yaya Mujahid, gara da ka kawo mana dauki

Abinda ta ce masa kenan.

Yasosa kai da zummar jaddada girma yana cin magani a zahiri, amma azancinsa shi ne ta haka yake hadiye karambanin bayyana so a muhallin da bai dace ba,

Ku na da matsala ko?

Ya tambaya cikin karade dukkansu da ido.

Nabila kyakkyawar budurwa ta fara gaishe shi a nutse, nutsuwarta da iyakacinta ta birge shi a ido a matsayin kanwarsa, ba a matsayinta na budurwa mai kyau kuma mai hankali ba.

Binta ce ta amsa kai tsaye da alamu na kamar ba zabi zata bawa Mujahid ba, umarni zata ba shi,

Abban Nabila ba ya son ta da hawa motar haya, ga direban gidansu ya kai Innoninta sabga, shi ne nake roqon arziqin ka zo ka raka ni mu kai ta gida

Binta ta nemi wata alfarma daga gare shi, abu ne da yake mugun faranta masa rai, amma duk farin cikin da yake samu ba ya hana shi motsa qwanjinsa wanda ya saba boye sonta ga mutan duniya,

Kin manta ba ki biya ni albashina na wannan watan ba, qila sai dai na baki mukullin motar ki kai ta da kanki

Ta tare shi tana dariya,

Dan ma ba baa ce ta kar uwar gizo ba qarar kwana ce, haka kuma zaka zo ka raka ni mu kai ta, mu kadai za mu ina da batun da nake so mu tattauna a hanyar dawowarmu

Ba ta jira cewarsa ba ta yafici Nabila suka yi gaba.

Hakan da ta yi ne kuma ya hana ta ankara da fuskarsa wadda ta kasa hadiye razana ko fargaba batun da take son su tattauna, sai kawai ya bi bayanta tamkar raqumi da akala.

Suka kai Nabila gidansu, suka kamo hanyar dawowa gabansa na cigaba da lugude.

Kasancewar ba shi da wani buri bayan afkuwar duk wata hanya da zata bashi Binta, sai saqe-saqen zucinsa suka dinga zama munana saboda suna nisanta shi da Binta.

Yana shirin ya zunguro ta da zancen don kar zuciyarsa ta fashe da fargaba tun ma kafin ta furta abinda qila shi ne ajalinsa, sai ga shi ita da ta fi shi matsuwa ta gabatar masa. Cikin yanayin jimami ta ce,

Duk ruwan idona, har yau a filin duniyar nan ko a maneji na rasa mijin da zan aura Yaya Mujahid

Wani farin ciki ya kawo masa naushi amma yayi jarumtar coge shi da qoqarin mallakar kai, ya juya ya dube ta fuskarsa babu yabo babu fallasa,

Oh, Shukuranu zaba miki shi aka yi ba zabinki ba ne?

Ta jinjina kai da alamar tarin damuwa,

Ni na zabo shi a sahun maneji, yanzu na fahimci ashe ba a sahun maneji aurensa yake ba, a sahun larura ko ma kai tsaye cutar kai yakamata na sanya shi

Mujahid yayi dif ya bawa farin ciki damar yayi ta dimarsa a qahon zuci, yayi addaua da hasashe duk sun tabbata, sauransa kawai cikar buri.

Yayi fuska ya tsare gida yana tambayarta,

Me ya faru? Ko ma menene ai kin makara

Ta saki baki galala tana kallonsa,

Ko ma menene ka ce Yaya Mujahid?

Eh, haka na ce

Ya amsa mata kai tsaye fuskarsa babu annuri.

Ta kawar da kai tana sakin ajiyar zuciya,

Ba dai ko ma menene ba Yaya Mujahid, ai bai kamata kana raye na auri abinda zai cutar da ni ba

Maganarta na masa zaqi fiye da suga, amma fuskarsa da fatar bakinsa duk sun boye,

Ai ni ba na shiga layin masoya zuciyoyinsu, hauka kenan ki yi ta kawo maza ana sa miki rana kina fasawa ko ki kore su da hali b ki kore su da hujjar da bata isa kallo da ido ba, Qawar zuciyarki ta yi yawa, kin kasa zabawa kanki abokin rayuwa

Ta tare shi cikin rangwada kai yanayinta na nuna abinda zata fada daga zuciyarta kai tsaye zai fito,

Wallahi da gaske nake ka yarda da ni, har yau a filin duniya ban ga irin mijin da nake so ba, ko an halicce shi ne yayi min nisa? Na san dai ko ma meye yana raye, Allah ne kawai bai hada mu ba

Maganarta ta ruda masa kwanya, ya shiga canki-canki qarya da gaskiya a maganarta, wato da gaske take bata ga mijin da take so ba ko kuma shi ta gani amma ta gaza ta furta, tunani fawar zuciyarsa kenan, mai cin alwashin samo masa soyayyarta kullum.

Ya watsar da tunanin don ya ga yana neman haukata shi ya dawo da hankallinsa duniyar gaskiya don yayi maganar gaskiya,

Wanne irin miji kike so?

Ya tambaye ta muryasa a shaqe.

Kai tsaye ta amsa masa a raunane,

Ni ma wallahi ban sani ba, kawai dai ni dai na lura duk mazan da nake gani a duniya har yanzu ban ga irin mijina ba

Wannan kalamin nata ya tsinke masa fata ya kuma qaryata waccan fawar zuciyar tasa mai son faranta masa da kawo masa furanni tunani da alwashi. A sanyaye ya kawar da kai cikin rashin qarfin gwiwa.

Motar ta dauki shiru face motsin numfashin motar da nasu wanda kai tsaye yake bayyana ba daga kafar farin ciki yake fitowa ba.

Can Binta ta dauko wayarta ta budo wani saqon tes ta miqa masa wayar cikin shaqaqqiyar murya tana cewa,

Ka ga saqon da na samu daga Shukuranu dazu, ba jimawa daga fitar danginsa masu kawo lefe

Dama jikin Mujahid a sanyaye yake, gashi kuma ta ambata masa sunan Shukuranu, sai takaicin yayi masa yawa, don haka ya qi miqa hannu ya karbi wayar, ransa a bace ya ce mata,

Ba ki ganin tuqi nake, karanto min kawai na ji.

Ba ta zargi komai dangane da damuwarsa ba kasancewar ta yi masa farin sani a gizago da yawan taqaita dariya, duk cikin yanuwansu ma ita ce take samun arziqin sakewarsa da dariyarsa har su kan taba wasa a tsakaninsu wasu lokutan, zurfin cikinsa ne kuma ya janyo take daukarsa abokin shawara don in an yi shawara da shi ba ya yada sirrin mutum.

Hankalinta kwance ta fara qoqarin karanto masa saqon Angonta nan da sati uku tare da cewa,

Bari na tsallake gaisuwa ka ji muhimmin saqon

A ransa ya ce

Kin kyauta don qila na ji abinda zai hana ni bacci

Ta fara karantowa kamar haka,

An saka ranar aurenmu sati uku, haka ne? na manta wasu sharuda ne wadanda suka kamata na gabatar miki na qashin kaina bayan wadanda suka wajaba a wajen daurin aure.

Na san tuni kin san ni mutum ne me kishi, to ina miki tunin in kin shiga gidana zaki manta da hanyar qofar gida, dama fitar ya mace uku yakamata ta kasance, fitowarta daga cikin mahaifiyarta, fitarta zuwa gidan miji sai kuma fito da ita daga gidan mijin zuwa kabarinta.

Sharadi na gaba shi ne, ban yarda ko wanne dan uwanki namiji ya zo min gida ba, dukkan zumuncinsu zan karba miki, har mahaifinki zan canje ki na dorar da zumuncinki a wajensa.

Na lamunce mata su zo ku ga juna, su ma ba kullum ba, don ni mutum ne mara son fitina da hayaniya

Tuni Mujahid ya sami gefen titi ya tsayar da mota cikin qanqanin lokaci ya hada gumi sharkaf, razanar da yake ji daga tsakiyar hantarsa take tsirowa, cikin numfarfashi da zaro ido ya dakatar da ita,

Dakata Binta, wannan saqon da gaske ne ba sharrinku na mata kike son qulla masa ba?

Binta ta saki wani murmushi da baya bayyana komai sai tsabar takaici,

Me yasa zan masa sharri, in kana tantama bari na kira waya mu bude maganar ka ji da kyau

Bata jira cewarsa ba ta kira wayar Shukuranu, da faraarsa ya zaga yana rangada mata sallama da muryarsa ta Ustazai,

Cikin narke murya tamkar daga ita sai shi ta ce masa,

Masoyina na sami saqonka dazu, sai dai ban fahimce shi sosai ba, shi ne na kira ka don ka qara min bayani

Nan fa Shukuranu ya saki harshe yana zuba da qoqarin fahimtar da ita manufarsa, karshe ya ci bakin batunsa da cewa,

Sau biyu ina neman aure wannan sharadin nawa na rusa shi, ni kuma ban iya qarya don a so ni ba Binta, kodayake na fahimci ma yammatan da na so a baya ba son Allah da Annabi suke min ba, ke kuwa ina da tabbacin ko wuta na nuna miki na ce ki afka ina da tabbacin ba zaki watsa min qasa a ido ba bare wannan karramawar da na yi miki

Haushi da baqin ciki ya hana Mujahid jure wannan rainin wayon na Shukuranu, ya warce wayar a hannun Binta ya kashe ta gabadaya sannan ya cilla ta kujerar baya.

A fusace ya dube ta ya ce,

Wannan gayen dan wacce dariqar ne?

Binta ta dake ta amsa cikin yanayin hadiye baqin ciki,

Ni wallahi ban sani ba

A qufule Mujahid ya tare ta da cewa,

Dan iska ne ma kawai, babu abinda yayi min ciwo a maganganunsa sai maganar wai ba ya son hayaniya, na rantse da Allah da a gabana yake yanzu sai na yafa masa kalar hayaniyar da bai taba tsammanin an halicci irinta cikin ire-iren wadda yake gudu ba/”

Wani guntun nishi kawai Binta ta iya saki, gabadaya qusoshin kanta sun tamke, ba don ma tana samun sassauci da godiyar Allah na bayyanar sharudan Shukuranu a sain da lokaci ba qure ba, sannnan tana samun qwarin gwiwa daga yadda ta ga Mujahid ya karbi alamarin, tana da yaqinin shi zai iya goya mata baya yayi mata jagorar fahimtar da iyayenta dan mafiyan da ta jajibo zata aura.

Mujahid ya tashi motar yana cewa,

Wannan mafarki ne da yakamata kowa ya farka, in an yi auren nan zaa cutu

Binta ta kwanta jikin kujera tana sauke ajiyar zuciya, muryarta cike da jin dadi ta ce,

Na sani kaine gaba wajen share min hawaye, ina roqon Ubangiji yadda ya ba ni gwarzon wa mai share hawaye irinka, Allah ya ba ni mai irin halinka na qoqarin fahimtata da share min kuka

A wannan gabar cikin wasa ya ji kamatar ya jefo fatarsa,

Yayi fuska iyakar fuska ya ce mata,

Ki qara himma, in ma irina gabadaya zaki roqa a miji, to ki roqi Ubangiji ni mana kawai a huta

Ta girgiza kai cikin tsananta dariya,

Fahimtata da share min kuka irin naka fa kawai nake so a kai, in zan yi roqo ni da babban masaki nake, gabadaya nake son a bani abinda nake so ba wai a ba ni wani sashi a hana ni wani ba, in na roqi kai ai na cutar da zabin muhimmiyar zuciyata

Ya ji ciwon maganarta ainun, amma babu yadda ya iya dole ya shanye,

Wanne irin miji kike wa kanki fata?

Kai tsaye ta amsa,

Ni ma ban sani ba, na san in na fara lissafi ba zan iya kammalawa ba, gabadaya ma ni ka san ni da dogon buri.

Murmushi kawai Mujahid yayi ba tare da ya tanka ba, hirar sai ta koma tsakanin shi da zuciyarsa me zuga shi din nan,

Binta rabonsa ce, shiyasa duk saurayin da ta yi sai ta kore shi ko ta qi jininsa da kanta, shi kawai take so, lokacin ta gane hakan ne kawai bai yi ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 17

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Rigar Siliki 2 >>

5 thoughts on “Rigar Siliki 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×