Skip to content
Part 12 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Ta jima tana jiran amsar Nabila kafin ta yafito amsar da qyar.

“Na taho gida ne domin na ba ki sukunin karanta takardar Yaya Mujahid a nutse, kuma in ba na ganin qwayar idonki zan fi iya fadar raayina ko shaawata a kanku kai tsaye, zan kuma fi iya ba ki jawabin kwantar da hankali”

“Ya isa haka.”

Binta ta tare ta, shigen a fusace, sannan ta dora da cewa.

Wacce takardar ce?

A nutse Nabila ta ce.

Ki buda murfin wadrob dinki na jikin bango, akwai wasiqa da wata bouquet mai kyau

Ta tare maganarta da dariya cikin zolaya.

Hargitsawar da kayan cikin Binta ya ke bai hana ta jan wani uban tsakin da Nabila ke qoqarin tare shi da nasiha ba.

Don Allah Anti ki kalli lamarin da idon basira.

Cikin matuqar fushi Binta ta sakar mata tsawa.

To ki adana nasihar taki mana  ki jira na karanta takardar? Ai zan kira ki mu tattauna.

A ladabce Nabila ta ce.

To Anti, in ba ki kira ba ma ni zan kira.

Binta ba ta ko jira su yi sallama ba ta sauke wayar maimakon kuma ta zarce ta dubo wasiqar sai kawai ta kife a gado cikin rasa abin da za ta yi, kuka za ta yi? Ciwo da ta ke ji cikin ranta ya fi qarfin kuka sai dai kashe kai, kuma tana qyashin kashewar ta bar wa maqiyinta duniyar ya ci da tsinke.

Har qarfe goma sha biyu tana juyi a gado cikin tafarfasar zuciya, ta rasa ta inda wannan jidalin ya ganta ya afko mata, sannan ta rasa ta hanyar da za tabi ta kubuta wai duk mazan duniyar nan a rasa wanda zai so ta ido rufe sai Mujahid? Ta gwada ta inda za ta dauki wannan qaddarar ko a suna ne, amma sai ta ji numfashinta na neman daukewa.

Sai da sha biyun ta gota sannan ta haqura cikin rashin hayyaci tana rangaji ta dauko wasiqar hade da fulawar ta dawo baking ado ta zauna ba tare da ta yi wa fulawar cikakken duba ba, ta gutsure mata kai ta yi wurgi da ita sannan ta hau farke wasiqar.

Babu komai a cikinta sai kalmomi uku kacal suna reto a tsakiyar takardar, wato Ina sonki Binta.

Baqin cikinta da takaicinta bai wani sabuntu ba, illa wani irin zazzafan fushi da ya hau kansu ya fara sarrafawa, sai ga ta da waya tana kiran Mujahid.

Duk da ba cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Mujahid ya ke ba, daidai wannan lokacin bacci ya fara tafiya da shi wayar Binta ta farkar da shi.

Yana ganin sunanta ya watsar da magagi da bargo ya tashi cikin zaro ido da kuwwa.

Wuu saqona ya ba da wuta ke nan. Allah tallafe ni.

Cikin dariya ya yi maganarsa, amma da zai amsa kiran sai ya katse dariyar.

Ranki ya dade.

Ya fada cikin ginshirarriyar murya tamkar ba shi ne mabaracin ba, Binta ce.

Ta qara jin wani mugun haushinsa na neman tsaga mata zuciya a zafafe ta ce.

Na ga wata banzar takardarka.

Tana sauke numfashi ya dora muryarsa a sake.

Tare da wata banzar fulawata ko? Ai na fahimci haka.

Ta qara zuwa wuya, don haka duk qoqarinta na ta dan tattala masa girmansa wanda bai kamata cewa yana sonta ya tarwatsa masa ba, ta gaza cikin numfarfashi ta ce.

To ni ba banza ba ce, don haka ba na tare da banzayen abubuwa

Ko sauke numfashi bai barta ta yi ba ya ba ta amsa mai tura haushi.

Sai ki shirya zama banzar tun da banza ya rakito so ya kawo miki ba don ya daina ba.

Ta shaqa iyaqar shaqa amma ta laluba inda za ta fashe ta rasa sai faman jan huci ta ke tana kashe masa kunne, sai can ta sami abin cewa da qyar.

Na gode da dumbin cin fuskar da ka yi min, ka zubar min da girma da mutunci a wajen yarinyar da na turo maka wadda ita ta fi dacewa da kai, kuma ita za ta iya sonka.

Cikin ko-in-kula Mujahid ya ce,

Ayya! Ban san hakan za ta faru ba, amma in kin ba ni dama zan iya kwashe girma da mutuncin da na zubar miki, har ma alakoro zan iya yi miki gyara da shi

Da alama yanzu dole ne ta fashe da kuka ko da ba ta so hakan ba. Ashe Mujahid mugun dan rainin wayo ne? Cikin cusasshiyar muryar da kuka ke wa sallama ta tare shi hade da tsawa.

Malam kar ka ci gaba da raina min hankali ka ji!.

Na ji.

Ya fada da alamun hankalinsa a kwance ya ke ba kamar yadda ta so ta daga masa ba.

Ta yi jiran ya dora ya ce wani abu don ta samu damar sauke masa kwandon rashin kirki da hujja, amma ya ci gaba da yi mata kunnen uwar shegu, sai ita ta kuma tabo shi a tunzure.

Allah ya bi min haqqin wulaqancin da ka yi min.

Nan ma ya sake amsa mata a gajarce.

Amin.

Ta fara shesshekar kuka tana cewa.

Kuma amsa takardarka shi ne ba na sonka ni, kuma ba zan taba sonka ba wallahi sannan fulawarka ka zo toilet ka ga inda na ba da ajiyar banza

Ya tare ta cikin dariyar da ba za ta taba fahimtar ta qarfin hali ba ce.

Daya ke nan daga cikin tabin hankalinki Binta, da ma a takardata kin ga inda na ce ina neman amsa? Ba buqatata ke nan ba, buqatata ita ce ki san ina sonki, ban damu ba don ke ba ki so ni ba, ni dai zan ci gaba da sonki, kuma ina jin qarfin gwiwar zan cika burin son, wato aurenki

Yanzu ta bude kukanta sosai, cikinsa kuma ta amsa masa.

Allah ya isana sona da ka ke, kuma zan ga shegen da zai aura min kai wallahi

Kin ji wani nauin haukan naki.

Abin da ya ce mata ke nan yana dariyar qarfin hali ya kashe kiran.

A can Binta ta dora hannu a ka ta rushe da kuka sosai tana ambaton ta shiga uku, yayin da shi kuma ya fada gado rigingine yana ambaton.

Innalillahi wainna ilaihi rajiun.

Ko da wasa bai ji kalmar ba ta sonsa da ta ambata ba daga zuciyarta maganar ta fito ba, da gaske ne Binta na qinsa, qiyayyar da ba ta rage masa komai a son da ya ke mata ba face qari, wannan ce kuma shi qaddarar da ta afkawa duniyarsa.

Dukkaninsu babu wanda ya yi cikakken baccin dare da ya kai ko rabin daren ba su samu ba suka wayi gari cikin duhun zuciya da laluben ta hanyar da za su sami abin da suke so, Mujahid na son Binta tamkar rai da rayuwa, Binta na qin Mujahid matsayin miji ko masoyi don yaqinin zaa fara auren dole a kanta muddin aka gane Mujahid na sonta, a gefe guda kuma tana son kubuta daga mummunan kallon zargin wasa da hankalin da Nabila za ta yi mata.

Har qarfe goma sha dayan ranar tana labe a dakinta tana jinyar zuciya da idanuwanta da suka kwana kuka ko mahaifinta ba ta sami zuwa gaishe shi ba bare mahaifiyarta.

Sha daya da rabi da kanta Hajiya ta same ta nade a gado.

Ta yunqura ta tashi zaune ta janyo wani qwanqwamemen gilas din gayun da ke ajiye durowar gado ta qwama, shi ma na Nabila ne ta manta shi.

Tana miqar nuna kasala ta amsawa Hajiya.

Na tashi jikina babu dadi Hajiya, Ummi ba ta sanar da ke ba?

Hajiya ta yi fuska ta ce.

Da kin aiko ta da gaske ina da yaqinin ba za ta manta ba za ta sanar da ni.

Sai Binta ta rasa bakin magana illa faman qara gyara rufin bargo kawai da ta ke.

Hajiya ta ci gaba da yi mata kallon kai tsaye, sannan ta kada kai.

Ciwon bai hana ki qwanqwama wannan google din da ko kyau bai miki ba? To wai ciwon me ma ki ke?

Binta ta cije wa qwallar da ke barazanar fado mata qunci, ta shiga gyara google din cikin sarqewar murya tana cewa.

Ai idon nawa ke ciwo Hajiya.

Hajiya ta kawar da kai.

To Allah ya sauwaqe, sai ki tashi ki yi wanka ki je asibiti.

Binta na Allah-Allah Hajiya ta fice daga dakin ta yi saurin amsa mata.

Ai da ma, yanzu zan yi wanka na tafi.

Ta fara qoqarin sauka daga gadon.

Hajiya ta bi ta da kallo kwatsam ta jefo mata batun da ya kusa sanya qirjinta rugujewa.

Ina ta sauraronki in ji yadda ku ka yi da Nabila amma na ji shiru, to yanzu ina son kiranta ne shi ya sa na zo in sanar da ke ko za ki kira ta ki tsara mata abin da za ta ce da ni saboda kar na kira ta ta yi miki kwakyara ko?

Binta ta jima kafin ta dawo kan doka da oda, har ta sami damar bin Hajiya da kallon son fashewa da kuka.

Wai duk me ya cusa wa zuciyarki wannan zargin game da mu Hajiya? Ni ban san me ki ke mana tunani ba

Hajiya ta yi fuska ta amsa mata.

Ni ba zargi na ke ba wallahi, ina da yaqinin akwai abin da ku ke boye min, kuma na fara shinshinawa.

Binta ta bude baki za ta yi magana, Hajiya ta tare ta.

Kar ki ce min komai, ban ce ki tabbatar ba, kuma ba zan yarda da musu ba, in lokaci ya yi zan kama ku hannu da hannu ne.

Ba ta jira cewar Binta ba ta kama hanyar ficewa daga dakin, cikin rakiyar kallon Bintan.

Kafin ta fice ta ce.

Ki dai yi qoqari ki kira Nabila yanzu.

Kawai sai Binta ta rafsa hannu a ka cikin kukan da ya ke neman kashe ta a ciki.

Hajiya na ficewa ta yi tsalle ta murzawa qofar dakinta mukulli, sannan cikin barin jiki ta lalubo wayarta ta hau kiran Nabila ba tare da ta yanke shawarar me za ta ce mata ba.

Hello Antina?

Nabila ta fada cikin faraarta  da ta zame mata sabo musamman a tsakaninta da Antinta.

Cikin qoqarin boye damuwa a murya Binta ta amsa.

Naam qanwata mun tashi lafiya?

Nabila ta yi dariya ta ce.

Lafiya qalau Anti, jiya kuma cikin tsammanin kiranki na yi bacci, ba na son na kira kuma na bata miki rai.

Azancin Binta ya shiga kai komo, a qarshe ta tsaya ga furta.

Ki yi haquri kawai Nabila, abin da zan iya cewa da ke kenan.

Cikin rashin fahimta Nabila ta ce.

Game da me Anti?

Binta ta samu ta goge hawaye sannan ta basar da tambayar Nabilan da cewa.

Hajiya ta kira ki?

Cikin nuna alamun kasa hankali biyu Nabila ta amsa.

Ba ta kira ni ba, wani abu?

Binta ta kada kai, ta ce.

Ah ba komai, kawai dai in ta kira kin kar ki buda qofar da za ta fahinci cewa ba dalilin da ki ka sanar mata jiya ne ya sanya ki tafiya gida ba.

Nabila ta sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, sannan ta nisa da fadin.

Insha Allah kar wannan ya dame  ki Anti.

Binta ma ta sakin tata ajiyar zuciyar.

Yauwa Nabila, haqurin da na ke ba ki duk kan abin da Mujahid ya yi mana ne, kuma wallahi na dau alqawarin sai na rama, ki bar ni da dan iska.

Tamkar Nabila ba ta ji komai ba sai zagin da Anti ta yi wa Mujahid, kuma yanzu ne ta fahinci ramin son da Mujahid ya haqa a zuciyarta ba zai taba rufuwa ba kamar yadda ta zata daga jiya zuwa yau, yanzun nan zagin da Binta ta yi masa ya yi mata dacin da ba ta taba jin irinsa ba, inda za a tara yawan zagin da ta sha a duniya.

Amma dai haka ta hadiye a raunane ta ce.

Me Yaya Mujahid ya yi mana Anti?

Binta ta fara kuka.

Na dauki tsawon lokaci ina yi muku shaawar zama miji da mata, Allah ya sani saboda son da na ke miki shi kuma saboda tsantseninsa da rashin daukar rayuwa da zafi. Na yi iyakar abin da zan iya qoqarina na in hada kanku, Mujahid ya san da haka amma kawai don iskanci da wulaqanci sai ya zo ya ce ni ya ke so? Kuma don tsabar rainin wayo ke zai ba wa takardar ki kawo min? Wannan zunubi ne da ba zan taba yafe masa ba.

Kuka ne a ido da zuciyar Nabila, amma a murya sai ta mayar da shi dariya ta ce.

Ni ban ga wani laifi ba bare a kira shi zunubi Anti, mutum ba ya zaba wa so muhalli, da kansa ya ke zaba, sannan in kin zabar min Yaya Mujahid ne don halayen qwaransa da ki ka yaba, ai daidai ke nan in ke ki ka amfana da su

Binta ta tare ta cikin ci gaba da kukanta.

Wallahi ba na sonsa Nabila, kuma zagewar qarfina zan gwada masa hakan.

Yanzu Nabila ta kasa shanye kukanta yadda ta so,  tabbas in ta bude baki ta yi magana sai an ji shi, don haka ta ci gaba da shiru. Ta fahinci Binta da gaske ta ke tana qin mutumin da ita ba ta ga wanda ya kai shi cancantar a so ba, sam ita ba ta ga ma abin da ya hada layinsa da qiyayya ba.

Can sama ta dinga jiyo Binta na ci gaba da mita cikin kuka.

Ba na sonsa, ban taba mafarkin auren zumunci ba, kuma aqidata ba za ta bar ni auren mutumin da silarsa ba su san darajar mata ba don ina tsoron ya yo gado

Iyakacin abin da Nabila ta iya riqewa ke nan duk da maganganun Binta sun nunka haka yawa, amma a wadannan yan tsirarun ta sami abin cewa, cikin shanye kukanta.

Amma duk da wannan tawayar ta Yaya Mujahid da ki ke lissafawa ni ki ka so min aurensa.

Binta tsakaninta da Allah ta amsa mata.

Kin dace da Mujahid Nabila, kuma kina da kyan da zai sa duk gigin namiji ba zai iya wulaqanta ki ba

Sai dai kar a kuma.

Nabila ta fada cikin ranta don tana ganin babu wulaqancin da ya fice a ce ba a sonka, wulaqancin da Mujahid ma ya yi mata ya dara wannan, haka dai ta daure ta ce wa Binta.

Anti Binta ba ki san so ba kawai, amma so babu ruwansa da kyau ko wani aibu, wanda ka ke so komai kashinsa Sarki ne a wajenka, kuma bakin ranka ka ke son kare martabarsa.

Binta ta yi shiru cikin dogon tunani, amma daga qarshe dai ta ji kamatar dakatar da tona wa Mujahid asiri, ta bige da sauke ajiyar zuciya ta ce.

Ba za ki gane ba Nabila, ni kadai na ga abin da na gani a zuwan da na yi Voto na qarshen nan tare da Mujahid, babansa ina jin Karen gidansa ya fi matansa daraja mu bar maganar kawai.

Nabila ta nemi yawun da za ta juya a harshenta ta sami furuci ta rasa, har Binta ta gama yi mata sallama ta sauke wayar.

Ta bar Nabila cikin tsananin tausayin kansu duka, musamman Mujahid da laifin wani ke shirin yi wa sonsa mahangurba, da kuma ita Binta mai murdadden halin da ba ta sauya fahimta ta dadin rai, amma mai sauqin kan da ta kasa zabar kowa a aminiya sai ita Nabila ma so mai son Bintan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 11Rigar Siliki 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×