Skip to content

Cikin wasu qananan daqiqu Binta da Yaks suka saita kansu daga rikitar da suke ciki, lokacin da suka ji takowar Nabila zuwa falon Bintan da suke zance, suna jiyo darerakunta da mutan gidan, har suka taho tare da Karima.

Duk da Yaks a rikice ya ke bai fasa macewa a shauqin shanya ido ya zura wa qofar falon kallo ba, har su Nabilan suka shigo tana cikin matsananciyar fara’ar da rabonsa da ganinta a  kuncinta tun daga lokacin da ta ke aro gizago ta yafa da zarar ta ganshi.

Abin mamaki yau da fara’arta ta shigo ko don ta san ta gama rura masa zuciya? Ya dai zuba wa sarautar Allah ido lokacin da zuciyar take shirin karbar qaddarar barazanar tarwatsewa.

“Antina!”

Tuni Yaks ya bi jikin kujera ya sheme duniyar da dakin na juyawa da shi, a kan jin son Nabila, narkewa ne kawai ba ya yi. Yana jin wataqila nan gaba zai fara.

Dole Binta ma ta qara rarumo wata siyasar ta shafa wa idonta, bakinta kamar ya yage ta shiga murnar ganin Nabilan.

Suka sha shewa sannan duk suka zazzauna aka gaisa aka fara hira.

Da qyar Yaks ya yi gyaran murya cikin tsananin fargaba ya debo in-ina yana sauke wa Nabila.

“Na…bila… ina… wuni?”

Wani mugun takaici ya tsiri iyakacin zuciyarta kadai ba tare da fuskarta ba, hakan ya sa ta yi namijin qoqarin juyowa ta dube shi tana yaqe da sunan fara’a.

“Lafiya lumi Yaks, ina gajiya?”

Ya yi qoqarin ya amsa sam ya kasa, gabadaya Nabila ta gama gigita shi, ta rikita masa hankali, tamkar ya miqe tsaye ya kwarara ihu ya ke jin kansa.

Har ta dauke kanta bai samu ya amsa ba, sai da Binta ta saci ido ta gasa masa harara, sannan ya sake wata gyaran muryar, jiki na karkarwa ya hau cewa.

“Ba ni tare da wata gajiya ban da ta zuciya, wadda ba ta barina dominki.”

Sai da Nabila ta yaqi fushinta sannan ta iya tanka masa.

“Allah Sarki, to ina maka fatan ya zamo kaffara.”

Da sauri ya amsa, “Amin”

Daga nan bai sake yunqurin yi mata magana kai tsaye ba, illa jefi-jefi ya jefa musu baki a cikin hirarsu, don ya fahimci yana dab da bayar da maza  idan ya ci gaba da nacewar yi mata magana ita kadai kai tsaye, tabbas so yana da kwarjini, kuma wanda ka ke so ba ya sonka ya fi kowanne nau’in so kwarjini.”

Can cikin hira Binta ta tsokano masa wajen da ya ke masa qaiqayi, cikin raha ta ce.

“Kin kusa daukar rai yau Nabila.”

A mamakance ta ce.

“Da na yi me Anti?

Binta ta juyo tana nuna mata Yaks cikin dariya.

“Cikin rashin hayyaci ya shigo gidan nan dazu, wai ya ganki da Yaya Mujahid kuna zaga gari da sassanyar la’asar.”

Nabila ta jima ba ta tanka ba, alfarmar Mujahid za a ci wanda ya ce ta hau roll din wannan wasan da kyau, ba don shi ba yadda zuciyarta ke barazanar tarwatsewa a yanzu da tuni ta nuna rashin kirki.

Ta duqar da kai tsawon lokaci, sannan ta dago da gajeren murmush.

“Ni ban ga wani aibu ba don Yaya ya fita da qanwarsa. Na yi masa rakiya can wajen ne, bayan ya buqaci hakan.”

Binta ta ji wani abu ya soke ta a qirji, musamman daidai gabar da Nabila ta ce, ‘…bayan ya buqaci hakan’. Binta ta sha rantsuwa tsakaninta da zuciyarta cewa, ba kishin Mujahid na son Nabila ta ke ba, amma ta kasa ba wa abin da ta ke ji a qirjinta suna, wanda nan da wani lokaci ta haqiqance idan ta ci gaba da jinsa sai ya haddasa mata hawan jini ko bugun zuciya.

Wannan ne dalilin da tana yaqe ta dubi Yaks ta ce.

“To kai ka ji.”

Yaks ya yi qoqarin ya fadi wani abu mai ma’ana saboda daurewar kai ya kasa, da qyar ya daure ya murmusa da fadin.

“Adadin yadda na ke sonki haka na ke kishinki Nabila.”

A nan ba ta tanka ba, kuma ba ta yi nasarar hadiye gizagonta ba wanda hakan ne ya sanyaya wa Yaks gwiwa ganin tana shirin komawa yanayinta na da.

Da ya ke ko wannensu zuciyarsa da juriya, sai suka bar wannan shafin suka ci gaba da hirarsu sama-sama musamman a kan fim din indiyan da suke kallo lokacin.

Can Yaks ya miqe ya fice, kai tsaye ya wuce zuwa motarsa ya dauko sarqa da dan kunnen gwal din da ya siyo wa Nabila bisa hudubar da Binta ta yi masa.

“Ka dinga yi mata kyauta sosai, ka san ‘yammata da son alheri, kuma ma dai ai Manzon Allah (S.A.W) ya fada cewa, ‘ku yi kyauta za ku so juna.”

Yana komawa falon kai tsaye ya doshi Binta ya ba ta.

“Binta ki ba wa Nabila don Allah, kyauta daga gare ni ta yi min rai ta karba.”

Da tsananin fara’a Binta ta karba, cikin barkwanci ta ce,

“Mene ne a ciki? Me zai hana ma ta karba? Ai shaidan ne ke mayar da alkhairi.”

Ganin Nabila ba ta tanka ba, kuma yanayin fsukarta ba ta sauya ba ya sanya Yaks ajiyar zuciya ya qara kishingida yana cewa.

“Sarqa ce wadda za ta yi wa santalelen dogon wuyanta kyau.”

Da rawar jiki Binta ta hau farke ledar ta zazzago dan akwatin sarqar cikin waro ido bayan da ta ga girman sarqar ta ce.

“Iyeh! Yaks fa babban yaro ne kai, irin wannan gundumemiyar kyautar ka yi wa qanwata?”

Yaks na satar kallon idon Nabila wadda ta yi qasa da kai tana wasa da remote fuskarta ba ta bayyana baqin ciki ko farin ciki, cikin karsashi da murnar cin nasara ya ce.

“Ai qanwarki mai daraja ce, ta cancanci abin da ya fi haka.”

Kamar an jefo Mujahid falon, sai ga shi ya fado da sallama daidai lokacin da Karima ta miqe ta kalli sarqar tana dubawa cikin sowa da taya farin ciki.

Yadda Nabila ta shigo falon da siyasa, haka Mujahid ya shigo duk da babu mai tanka masa fara’arsa, sai Karima wadda ya bige da tambayarta.

“Daga ina aka yi miki kyautar ba-zata ki ke shauqi haka?”

Ba qaramin dadi Binta ta ji wa wannan tambayar tasa ba, karaf kuma ta shiga zancen tana magana cikin yanayi na tura haushi.

“Ba tata ba ce, daga masoyi ne zuwa masoyiyarsa, wato Yaks zuwa Nabila.”

Ta yi  domin ta qunsa wa Mujahid haushi, amma sai ga shi ya fita yanayin dariya da shauqin, kasancewar yana kusa da Yaks a tsaye, kawai sai ya bugi kafadarsa cikin dariya ya ce,

“Ah lallai a gaishe ka jarumin soyayya Yaks, kana da qoqari gaskiya da ka ke yi wa ‘yammata kyauta. Ni ko kobona ba zan iya bai wa budurwa ba, in za ta so ni a haka ta so ni, in ma ta ga ba za ta so ni ba ita ta jiyo, ni dai dole ne in so ta kuma in ta nemi cika ni da rashin kunya ma zan iya daddala mata mari.”

Yaks dai ya zama kamar gunki domin yanayin na Mujahid ya zame masa baqo, ba haka ya zata ba, don haka ya kasa cewa qala.

Binta kuwa  tuni ta hadiya, ta qara cika da tsanar Mujahid don ta haqiqance duk abin da ya fada zai iya, dabi’ar gidansu ce rowa da nuna wa mace fin qarfi, amma dai duk da haka ta kasa cankar wannan salon, ba ta zaci haka daga gare shi ba, furucinsa bai nuna son da ya ke mata ko wanda ya ke wa Nabila ba, shi ya sa zuciyarta ta kasa nutsuwa ta zabi abin nazari.

Nabila ce ma zuciyarta ta ke a nutse, don zuwa yanzu ta fara fahimtar Mujahid ma so ya ke ya zama RIGAR SILIKI kamar yadda ya kira Binta, wato in an sabo shi ta nan sai ya wargaje ta can.

Karima dai da ba ta san dawan garin ba cikin fara’arta ta tsinka masa.

“Haba Yaya Mujahid budurwar? Sai dai idan ba sonta ka ke ba.”

Nan da nan ya amsa mata cikin gadara.

“To wasu ‘yammatan na yanzu ba gara garin kwaki da su ba? Ai alal lararati za a tafi da su, ni wadda igiyar sona ta zargo  ko naira hamsin ka ba ta kana iya sumbatar kuncinta ko fiye da nan. Ke alakoro ma in ta yaba dariyarka sai ta ba ka. To ni babu yadda na iya, ba zan iya fasa sonta ba, kamar yadda ba za ta iya cin moriyar da matan kirki za su ci a matsayinsu na mata a gurina ba.”

Tuni qarfin halin Binta da kuzarinta suka qare, tana rasa tasiri kashi casa’in cikin dari a duk lokacin da Mujahid ya debo cin kashinsa a kan sumbar da ta ba wa Yaks damar yi mata don ta kori sonta daga birnin zuciyarsa. Yanzu haka ji ta ke kamar ta yi girgiza ta zama ba ita ba saboda tsabar takaici da jin nauyi, qila ya fahimci hakan ne ya qara da cusa mata wani haushn inda ya dubi Yaks.

“Idan irin Nabila ce sarqar diamond ma ba sai ka ba ta ba, ga ta kuma kyakkyawa fiye da diamond din”

Binta ta qara mugun muzanta, yayin da Yaks ya qara cika da haushi, ji ya ke kamar ya tashi ya shaqe Mujahid, Nabila kuwa ta yi tsuru-tsuru, abin bai mata dadi ba, ba ta gane maganar sumba ba, amma dai ta san wannan ciye-ciyen fuskar na Mujahid fuskar Binta ya ke yaga yana ci, abin da ba ta so ta laminta ke nan.

Karima kanta ta tsargu,don haka ta tsuke bakinta ta qi tankawa, sai Mujahid din ne ya basar cikn fuskarsa mara yabo da fallasa ya dubi Binta ya ce.

“Au, kin ga ina nema in manta, na zo ne fa in sanar da ke zuwan baqon masoyinki Alhaji Ibrahim, shi ya dinga hada ni da girman Allah akan na shiga duk inda ki ke na zaqulo masa ke.” 

Nan take Binta ta ji ta sami gabar ramawa, cikin hanzari ta miqe tana cewa.

“Alhamdulillah”

Mujahid ya cije lebe don hana dariyar qetarsa bayyana. Yana binta da kallo tana barin jikin shigewa daki, ya ce mata,

“Kin yi katarin samun mijin kirki Binta, don Allah kar ki nuna halin zararki ki watsar da shi, in kin rasa shi da qyar za ki sami irinsa, sannan da alama shi bai iya soyayyar sumba ko shan minti ba”.

Binta ta yi turus ta juyo tana kallon Mujahid tamkar ta dora hannu a ka ta rafshe da kuka, kallon da ta ke masa kai tsaye ya ke bayyana tsabar tsanar da ta ninka masa.

Kawai don rainin hankali sai ya hade hannu alamun ban haquri yana ce mata.

“Mene ne na ga kamar kin fusata? Abin da na ke so ki gane shi ne, shi mutumin kirki ne, ba wai abin fada ba ne.”

Bai saurari cewarta ba ya kada kai ya bar falon yana dariya a ciki.

Kai tsaye ya sami Hajiya a falonta.

“Hajiya Binta tana da baqo.”

Maganar ta bigi Hajiya da kyau, amma sai ta yi saqare tana kallonsa da zargin ko ita ce ba ta ji da kyau ba, ta ce masa.

“Baqo wanne iri?”

Fuskarsa a wartsake ya dan ja fasali sannan ya amsa mata.

“Saurayinta ne, wani mutumin kirki wallahi.”

Sai da Hajiya ta saki rezar da take yanke farce ta fadi qasa, ganin cewa ashe hangenta da fatanta shirme ne? da ma Mujahid da Binta ba son juna suke ba? Ita tuni a kan wannan zato da fatan ta ke, idan akwai abin da tuna shi ke sanya ta farin ciki har ta bangale da dariya ita kadai ba zai wuce ta tuno ‘yarta Binta za ta auri kamili, kuma haziqin yaro Mujahid ba.

To amma ashe duk tatsuniya da mafarkin ido biyu kwanyarta ke shiryawa? Wannan abu ya yi mata dan banzan daci.

Tana dariyar yaqe ta ce.

“Wannan ja’irar yarinyar da janye-janyen tsiya ta ke, ta qi aure kuma ta kasa daina yi wa samari kwatancen gidansu.”

Mujahid ya yi dariya ya ce.

“Sai an ja mata kunne da kyau, wannan mutumin kirki ne, bai kamata ta yi wasa da lamarinsa ba.”

Hajiya ta fara sakin ranta a nutse ta ce.

“Ka sanshi ne?”

Ya kada kai ya ce.

“Eh Hajiya, don Allah ki yi mata magana, in dai tafiyarsu za ta zo daya, to ta daure ta aure shi.”

Shiru Hajiya kawai ta yi, Allah ya sani abin bai yi mata dadi ba, Mujahid ta ke so ya auri ‘yarta ba wani abokinsa ba.

Tana can cikin tunane-tunanenta Mujahid ya yi mata sallama ya silale zuwa dakinsa ya fada gado, sannan ya fara jinyar raunin da ya ke ji cikin ransa. Ga dai masoyiyarsa can ta zama qwallon qafa a hannun masoyanta ita kadai, dan ta’adda Yaks ya buga zai harba wa salihi Ibrahim wanda laifinsa daya da ya so masa Binta, ba don haka ba ko daya salihi irinsa bai cancanta a cuce shi ba, amma dole ne ya cuce shi don ya raba shi da Bintan.

A gare ta Binta ta ci uban kuka a daki kafin ta ba wa kanta haquri ta wanko fuska ta zo tana gyarawa.

Da ta dami kanta da sake tunani sai ta fara jin tamkar ana sake mata zuciya, matsalolinta ta ke so ta magance, Mujahid ne kadai ba ta so a duniya, ke nan daidai ne ta sauya zuciya wadda za ta iya samo mata kowa ta hana ta Mujahid.

Tana sauya zuciyar sai ta fara jin za ta iya zabar Alhaji Ibrahim ta aura ta bar wancan mahaukacin masoyin tun kafin son da ya ke mata ya isa kunnen mahaifanta su qaqaba mata shi dole.

Tun daga nan hawayenta ya dakata kamar an yi masa waigi, zuciyarta kuma wadda ta fara bushewa sai ta ji ta fara tsattsafo da danshi, ita da kanta ta ji tausayin kanta na kama ta.

Duk da ba ta da dabi’ar kwalliya, ta qoqarta ta yi ko domin ta tara wa Mujahid haushi, ya ce ba ya son mace mai yawan kwalliya, lallai ta san dole abin da ta yi yau ya mintsine shi, don kwalliyarta ce za ta fara nuna masa muhimmancin Alhaji Ibrahim a gurinta.

Ta zabi wani kyakkyawan lace dinta crimson kala wanda aka yi wa ado da Indian red  kala hade da ratsin farin qyalli, sai da ta qwalla wa Karima kira ta zo ta daura mata dankwali, ta gyara mata kwalliyar fuskarta  ma, hatta yafen mayafi ita ta yi mata, duk cikin sanyin jiki don maganar gaskiya su ma ba su ji dadin wargajewar soyayyar nan ta Mujahid da Binta ba.

Cikin wannan gayun ta isa wajen Hajiya da tata siyasar ba tare da ta san Mujahid ya riga ta kai abin da ta je kai wa ba.

Duk mamaki ya dabaibaye Hajiya ta shiga kallon Binta tana kwaso inda-inda, qarshe dai ta haqura ta ambata.

“Hajiya, ina da baqo a waje.”

Hajiya ta yi fuska ta kawar da kai.

“Wane ne?”

Binta ta sake kwaso wata in-inar qarshe dai ba ta iya samar da ko wanne furuci ba, ta ja bakinta ta tsuke.

Abinda ya sake ba wa Hajiya haushi ke nan, ta tabbatar wannan din ma qila Binta kore shi za ta yi, don haka ta yi kicin-kicin rai a vlbace ta ce.

“Ya yi miki ne?”

A tsorace Binta ta yi mata duban rashin fahimta.

“Ban gane ba Hajiya.”

Hajiya ta qara daure fuska ta ce.

“Eh, ina nufin kin amince da shi wannan da ya ke sallama da ke? Gaskiya mun gaji da a ce yau ki kawo wannan gobe kuma wani sabo za ki kawo, sai ka ce wata super market, in abin naki ya matsa kawai gara ki haqura ki daina kawo mana kowa Allah basshi gara a ce kina da baqin jini a kan dai a ce kin zama sarkin zarah.”

Saboda takaici da nauyi Binta ba ta ko yi yunqurin ta tanka ba.

Hajiya kuma ta tsattsare ta da ido.

“Ba ki ji abin da na ce ba ke nan?”

Da qyar Binta ta daure a ladabce ta ce.

“Hajiya, a yi min alfarmar ko sati daya ne mu fahimci juna, ni ban san komai game da shi ba, bai kamata kai tsaye na amsa ya yi ko bai yi ba Hajiya.”

A gwasale Hajiya ta ce.

“Yanzu Mujahid ya gama koda shi, ya ce mutumin kirki ne”.

Wani mugun haushi ya sake tokare wa Binta maqogwaro, duk da dai ta shiga rudun manufar Mujahid din na yunqurin a aura mata wani duk da alwashin da ya ke kan ci na qin janye sonta.

In an ture wannan ma, shi ya dinga shiga rayuwarta kenan babu wani abu da za ta mora sai abin da ya zaba mata? Wannan mara amfanin mutumin ya zame mata qarfen qafa.

Da ya ke ba ta da damar wannan qalubaale ga Hajiya, kawai sai ta qara qanqan da kai ta ce.

“Ni dai ina neman wannan alfarmar Hajiya, fahintar Yaya Mujahid daban tawa daban, ai ba shi zai zauna min da mijin ba.”

Har yanzu Hajiya ba ta saki fuskarta ba ta amsa mata.

“Shi ke nan, na ba ki sati daya, amma na rantse miki daga kan wannan mutumin mun gama jiran ki kawo miji, duk wanda idonmu ya fada kansa kawai za mu aura miki.”

Da Binta ta qara duban Hajiya da kyau sai ta fahinci lallai da gaske take, don ta san ta yanayin da ta so nuna kwanjinta na haihuwa da kuma sauran yanayin da ta ke zame mata qawa ko abokiyar shawara.

Jikin Binta a sanyaye ta yi mata godiya ta fice tana tunanin lallai Mujahid ne ya shirya mata wata gadar zaren, amma tsakaninta da iyayenta ba ta taba ganin mafarkin yi mata auren dole ba, duk da tana da yaqinin in sun fahimci Mujahid na sonta za su iya aura mata shi bisa dolen.

A idon Mujahid Binta ta wuce kuma da gayya ta bi hanyar da zai ganta har da tsayawa da dakatawa ta fesa turare.

Kamar yadda ta so ta raunata zuciyarsa qwarai da wannan salon, duk da basirarsa sai da ya fara qila-wa-qalancin ta yi ne da gaske ko kuma ta yi domin ta tura masa haushi.

Haka ya yi kwance warwar a tsakiyar daki, kishi na kawo masa naushin daukar rai ta ko’ina.

Tsawon lokaci ya miqe zaune cikin qwallah, sannan cikin muryar mai rauni ya ambata.

“Allah kana gani, ka jarrabe ni, ina roqon Ka sauqaqa min al’amurana.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Rigar Siliki 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.