Skip to content
Part 23 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Karo na sama da ashirin Alhaji ya shiga falon Hajiya ransa a bace, Hajiyar na tare da Binta ko wannensu fuskarsa babu sukuni.

Alhaji ya tsaya a bakin qofa riqe da labule yana yi wa dukkansu kallon tuhuma.

“Kun ji da kyau kuwa, yau suka ce kuma qarfe goma na safe?”

A ladabce Hajiya ta amsa,

“Na gaji da amsa wannan tambayar Alhaji, in dai ba so ka ke in maka qarya ba”.

Ya juya ga Binta wadda ke ta faman daddana waya hankalinta  ya yi masifar tashi, ba ta san azal din da ke shirin afka mata ba, tun jiya da yamma ta ke kiran wayar Alhaji Ibrahim amma qememe sai dai ta yi ringin dinta ta gama shi ba zai daga ba.

Daga jiya zuwa yau da safe sam ba ta damu ba, amma daga sha biyun rana har zuwa yanzu da ta ke sake kiran Alhaji Ibrahim din yana kife kiran nata hankalinta ba qaramin dugunzuma ya yi ba.

Da a ce babu maganar zuwan dangin Ibrahim a yau, da qyar in abin zai dame ta, amma ga zuwan nasu sannan ga shi duk motsin da za ta yi cikin zargin iyayenta ta ke, kowa sai kwaso buhun sauke mata sababi ya ke, tamkar ita za ta je ta matsa musu su kawo kudin sadakinta.

Lokaci daya Hajiya da Alhaji suka yi magana, Alhaji ya ce.

“Wai shi ki ke sake kira?”.

Hajiya kuma ta ce,

“Kar ki ci gaba da wahalar da mu Binta, in kin yi masa halin naki kin kore shi ne ki sanar da mu gaskiya, mu samu mu sallami wadancan tsofaffin su koma Voto, bai kamata mutum yana da abin yi a muhallinsa ka kawo shi naka ka yi masa jinginar qiru ba.”

Maganar Alhaji Binta ta zabi ta amsa, don ta Hajiya ba qaramin baqanta mata rai ta yi ba, kodayake ya kamata ma ta shanye don tun rana ta ke yarfa mata irinsu.

“Eh sake kiransa na ke Alhaji”.

Ta sauke wayar fuskarta a bace kamar za ta rushe da kuka.

“Wallahi ya qi dagawa”.

Yanayinta ya sanya Alhaji jin wani guntun tausayinta ya kama shi, muryarsa a sarqe ya ce,

“Anya kuwa mutumin nan ba dan yaudara ba ne?”.

Karaf Hajiya ta tare shi.

“Haba Alhaji, sai ka ce ba ka san halin Binta ba? Ai kar ka raba daya biyu ita ta kore shi.”

Hawayen da Binta ta ke ta faman  riqewa ya silmiyo ya fado kuncinta, sai dai ba ta ce komai ba.

Lura da hawayen nata ne ya sanya Alhaji ya qi taya Hajiya mitarta. Ya ciro wayarsa a aljhu yana cewa.

“Ko dai kin yi masa wani laifin ba ki sani ba?”.

Da sauri Binta ta girgiza kai tana kallon mahaifiyarta wadda ta tabe baki ta dauke kai.

“Wallahi iyakar sanina ban yi masa laifin komai ba, ko jiya da safe mun daxlde muna waya.”

“To ba ni lambarsa na gwada a nan”.

Alhaji ya fada a tausashe. Da sauri Binta ta budo ta fara karanto masa.

Ya kwafe sannan ya danna kira yana dan safa da marwa a tsakar dakin.

Sai da ta kusa katsewa sannan Alhaji Ibrahim ya daga cikin sallamar muryarsa babu yabo babu fallasa.

Tun daga nan Alhaji ya sha jinin jikinsa, don ya tabbatar Binta ba zata yi qarya ba, da gaske ne ta kira bai daga ba, kuma yanzu ga shi ya daga baquwar lamba.

Da qyar Alhaji ya yi qarfin halin amsa masa sallamarsa, sannan ya zarce da cewa.

“Hassan ne.”

Yanayin muryar Alhaji Ibrahim da alamun boye damuwa ya ce.

“Hassan wanne? Ban gane ba”.

Kai tsaye Alhaji ya amsa.

“Mahaifin Binta, a nan Fadaman Mada”

Alhaji Ibrahim ya ji wani irin nauyi daa shakka ya ratso masa tun daga kwanya har tafin qafa, bai san Binta za ta iya sanya mahaifinta ya kira shi ba, tun farko ma da ya kashe wayarsa.

Cikin nauyi da in-ina ya sake gaishe shi, yanzu muryarsa na nuna girmamawa.

Alhaji ya amsa da fara’a sannan ya dora.

“Ko Binta ce da kuskure ne, muna nan mun kira iyayenta daga qauye tun safe suna ta faman jiranku shiru?”.

Da Alhaji Ibrahim ya doso in-ina ya ambata kalmomi sun kai dari amma babu cikakkiyar jumla mai ma’ana guda biyu qwaqqwara.

Sai da Alhaji ya ga baragadar ta yi yawa sannan ya tare shi, a tausashe ya ce,

“Kai kuwa ka nutsu ka yi min maganar da za ta gamshe ni mana, ni fa ba tuhumarka na ke da laifin komai ba”.

Da qyar Alhaji Ibrahim ya iya nutsuwar ya yi magana mai ma’ana,

“A yi haquri Alhaji, zan turo ne, a sake ba ni lokaci na yi nazari sosai”.

Ran Alhaji ya yi mugun baci ya kuma gaskata zatonsa na cewa, Alhaji Ibrahm mayaudari ne kawai.

Duk da ransa ya baci bai kasa magana muryarsa tas ba,

“Babu laifi za a qara maka, shekara ya yi maka?”

Alhaji Ibrahim bai iya cewa komai ba, illa.

“A yi haquri Alhaji.”

Don ya san muguwar baqar magana ya yarfa masa, shi ma bai so hakan ba, to amma babu yadda ya iya. Yana son Binta, amma ba zai iya aurenta da waccan dabi’ar tata ba, da ma duk wani so zai bi bayan so domin Allah ne.

Bai ma kula ba sai ya ga tuni ashe Alhaji ya kashe masa waya, kawai sai ya yi zugum cikin zafin qirji rabuwa da macen da bai taba so irin nata ba.

Daga Hajiya har Binta tamkar zuciyarsu ta tsinke saboda fargaba da dokin jin abin da ya wakana, kodayake da ma ita Hajiya a qila-wa-qala ta ke, tana da yaqinin Binta za ta iya korar Alhaji Ibrahim, sannan da ma can ita Alhaji Ibrahim bai kwanta mata ba, Allah ya sani in dai akwai saurayi ba ta son ta auri mai mata.

Binta ce mai damuwar tsakani da Allah, kuma ita ta fara taron Alhaji da maganar bayan ya sauke waya rai a bace.

“Alhaji me ya ce?”

“Me zai ce kuwa?”

Alhaji ya amsa a tunzure.

Daidai lokacin Mujahid ya yi sallama ya shigo, shigowar tasa sam ba ta yi wa Binta dadi ba, kamar ta tashi ta rufe shi da duka ko ta fatattake shi.

Mujahid ya dubi agogo, sannan ya yi fuska ya dubi Alhaji, a ladabce ya ce.

“Anya kuwa Alhaji ba zan wuce ba? Ina da alqawarin ganin wani mutum”.

Bai jira amsar Alhajin ba ya dubi Binta cikin yanayin wasa ya ce mata,

“Masoyinki ya saba mana alqawari.”

Binta ta yi qasa da kai tana tura masa zagi a zuci.

Hajiya za ta yi magana, Alhaji ya riga ta.

“Ayya, ai gara ma ka yi tafiyarka Mujahid, iyayenka ma zuwa zan yi na sallame su na bayar da mota a mayar da su gida”.

Dadi ya kashe Mujahid, amma sai ya dubi Alhaji cikin razananniyar fuska.

“Don me Alhaji? A jira ko shigar dare za su yi baqin, su Kawu ba za su haqura yau daya su kwana ba?”.

A qufule Alhaji ya tare shi da cewa,

“Su kwana su yi me? Sai dai in shekara za su yi, na kira mai son auren Bintan yanzu ya fada min wai a dakata masa zuwa shekara zai sake nazari”.

Binta ta qwalo ido a razane.

Hajiya ta janyo salati mai tsawo.

Mujahid kuma ya rakito fusatar qarfi da yaji, cikin kumfar baki ya ce,

“Ina yi wa mutumin nan kallon dattijo, ashe ban canka daidai ba, ya san kai ne ya fada maka haka?”

Alhaji ya yi gaba yana cewa,

“Babu komai, ai naka ne ke bayar da kai, Allah ba mu rai da lafiya”.

Ya sa kai ya wuce ya bar falon.

Hajiya da ba ta sami damar tankawa ba tun dazu, ta katse sallallaminta ta fara sauke wa Binta mai kokawar goge qwallarta kallon banza.

Binta na jin sukan kallon ta qara neman tsarin hada ido da Hajiya, azal ce dai ta afko mata ba tare da ta zaba ba.

“Ikon Allah, wallahi gabadaya kaina ya kulle”.

In ji Mujahid da ya nuna tsayuwa ta gagare shi ya nemi kujera ya sulale ya zauna.

Hajiya ta sassauta fushinta ta ce masa.

“Kar ka shigar da kanka cikin damuwar da bai kamata ta dame ka ba, wanda ya jawo ruwa ai shi ruwa kan doka, kuma kowa ya yi da kyau, wallahil Azim zai ga da kyau”.

Cikin son fashewa da kuka Binta ta dago ta dubi Hajiya,

“Wallahi Tallahi Hajiya ba ni da hannu a cin amanar da Ibrahim ya yi min, ki fahimce ni, duk wanda zai ji ciwon abin da ya faru wallahi bayana zai bi…”.

Hajiya ta tare ta a fusace.

“Ai babu ma mai biyo bayanki ya ji ciwon, sai dai ki ji abinki ke kadai”.

Za ta sake kwaso kwandon rantsuwa Mujahid ya tare ta a tausashe,

“Kin tabbatar babu abin da kika yi masa?”.

Binta ba ta san lokacin da ta maka masa harara ba, har qoqarin zagba tsaki, amma don idon Hajiya ya sanya ta hadiye shi.

Hajiya za ta yi magana Mujahid ya riga ta.

“Bar batun wasa, wallahi da gaske nake, jiya na yi waya da shi da daddare ya sanar min ya yi miki zuwan bazata gidan nan da yammacin jiya, amma kin yi abin da ya yi mugun bashi mamaki”.

Binta ta ji an sako wasu mayunwatan kuraye daga qirjinta kawai suka hau lashe mata kayan ciki daya bayan daya, tuni idanunta sun yo waje, lokaci daya ta tuno ramin muguntar da ta haqawa Mujahid, ashe ita ta zurma.

Duk da sanyin fanka sai gashi gumi na rufe ta, ta fara fiffita da mayafinta, a hankali kuma ta ambaci,

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”.

Hajiya ta zuba mata ido cikin nazari sosai ta ce

“Yauwa kin tuno abin da kika yi masa ko? Ai ni dama na san ruwa ba ya tsami banza, duk wani ba daidai da za a samu a bangaren neman aurenki, daga bangarenki ya ke fitowa.”

Binta ta rasa bakin magana sai dai kallon wannan ta ke, ta koma ta kalli wancan cike da fargabar kar Mujahid ya fasa mata kwai, don fuskar da ya yi yanzu, ba ta dauke da komai dangane da son da ta san yana yi mata balle ta saka ran rangwame.

Hajiya za ta sake magana Binta ta tare ta cikin son fashewa da kuka .

“Hajiya zuciyata a rikice take, don Allah ki bar ni na tuna wani abu mai amfani, wallahi duk abin da ya faru da ni ba ni na zaba ba, in ni zan zaba ban qi ace na zabi abin da ya fi na kowa kyau ba…”.

Haushi ya sanya Hajiya katse ta,

“Kin manta dai, amma uban wa ya zabo miki shi?”.

Kawai sai Binta ta tashi ta bar falon.

Cikin tabe baki Hajiya  ta bita da kallo, tana dab da ficewa ta ce mata,

“Oho! jibi banza”.

Kawai sai Binta ta qarasa fashewa da kuka.

Mujahid ya fashe da dariya yana duban Hajiya,

“Hajiya kin tunzura ta da yawa”.

Cikin sassauta fuska Hajiya ta ce,

“To me zan mata da ya fice haka? Duk dama da lallashi na yiwa yarinyar nan, duk a banza ta tsaya ruwan ido, da ta tashi zabe kuma sai ta zabo mara kirki”.

Mujahid ya sassauta murya ya fara magana cikin siyasa.

“Ki kwantar da hankalinki Hajiya, lokacinta ne bai yi ba, wata qila kuma ni take jira mu yi aure tare”.

Ya sosa wa Hajiya wajen da yake mata qaiqayi ta ce.

“Kai ma ai ruwan idon ne da kai, ko ka hango wadda ta yi maka?”

Ya karkace kai cikin zaro ido.

“Ni?”

Yana dora hannu a qirji. Dariya kawai Hajiya ta yi, don haka ya dora.

“A wannan marrar zaben mace wuya gare shi, har gara ma a zaba maka, kwanaki na bawa Binta wannan aikin, kawai don na ce mai kama da ita ta tsiri gaba da ni”.

Mamaki ya ishi Hajiya, ashe abin da ya faru a tsakaninsu kenan, da gaske Mujahid ke son Binta ita ba ta sonsa, cewa ta samo masa me kamarta jirwaye ne da kamar wanka ya yi mata.

Cike da jin haushi Hajiya ta yi kwafa ta ce,

“Kyale shashasha mana, ko ita ka ce kana so me za ta daga maka hankali da shi?”

Cikin basarwa Mujahid ya yi fuska ya ce,

“Kamar kina gurin nima abin da na fada mata kenan Hajiya ta nemi sauya min magana.”

Hajiya ta yi kasaqe ta ce.

“Haka ne?”

“Sosai Hajiya”.

Ya sake yin fuska ya amsa.

Hajiya ta kada kai ta ce.

“Bar ni da ja’ira, zan maka maganinta, Binta gata dai kamar mai hankali, amma wata ran sai ka ce mai tabin kwakwalwa”.

Cike da jin dadi Mujahid ya miqe yana cewa.

“Ai ki kyale ta ma kawai Hajiya, tuni ni maganar ta wuce a wajena, bari na je na ji yadda za mu qare da su kawu, Allah yasa dai su yarda su kwana, ya fi tafiyar”.

Hajiya na can duniyar lissafi, sai dab da zai fice ta samu amsawa,

“Bari na zo na taya ku roqonsu, in suruka ta sanya baki ai tana cin alfarmar surukutarta”.

*****

Da dare wajen qarfe goma da rabi Nabila ta kira Mujahid, muryarta akwai alamun gajiya da bacci. Ya tare ta da kulawa.

“Nabila ya ya aka yi, ki daure ki dinga samun lokacin hutu da karatu, na yafe dukkan buqatuna har zuwa ki kammala jarrabawa”.

Yanayinta ta bayyana jin dadin kulawarsa ta amsa masa.

“Kar ka damu, jarrabawa sauranmu guda daya, za mu zana ta jibi, talata kenan”.

Ya yi ajiyar zuciya ya ce.

“To madallah, Allah ya ba da sa’a”.

“Amin.” Ta amsa cikin yanayin qaguwa.

Jin haka yasa ya ce.

“Me ya faru?”

Kai tsaye ta amsa.

“Me ya samu Antina Binta? Yanzu ta kira  ni cikin wani rudadden yanayi, Yaya Mujahid ina fata ba kai ba ne”.

Ya ji ciwon cewa Binta ta rude saboda Alhaji Ibrahim ya fasa aurenta, shi yasa ya yi magana muryarsa a cushe.

“Ni din, ban mata komai ba, me ta ce miki?”

Nabila ta dan sha jinin jikinta, a ladabce ta ce masa.

“Ban fahimci komai a tare da ita ba sai tsananin tashin hankali da damuwa, ta kuma roqi alfarmar gobe in zo tana son ganina…”.

Ya dan kebe baki.

“Eh, kiranki take ki zo ki taya ta jaje, Ibrahim ya fasa aurenta, ko da yake ba fasawa ya yi ba, cewa ya yi ta jira shi nan da shekara”.

Nabila ta jima ba ta ce komai ba, ba ta jin dadin hirar yau da Mujahid saboda yadda yake magana a cunkushe  ba cikin walwala kamar yadda ya saba mata ba. Yanzu tana so ta tambaya da hannunshi a cikin janyewar Ibrahim, amma gaba daya jikinta kyarma yake, ta rasa qarfin gwuiwar hakan.

Da kyar cikin rawar murya ta kwato abin fada ta furta,

“Ko ba na tayar da kai bacci ne? na ji kamar ba ka da walwala”.

Tuna muhimmancin Nabila a rayuwarsa da qudurinsa ya sanya nan da nan ya shiga cikin hankalinsa, ya bayar da ajiyar dukkan damuwa da kishinsa, cikin walwala ya ce mata.

“Kina daga cikin abubuwana muhimmai da na ke watsar da komai dominsu, kar ki zargi komai don Allah”.

“Zai fara”.

Cikin ranta ta aiyana haka, in da Mujahid masoyinta ne wane irin zaqaqan kalamai zai dinga shayar da ita da suka fi wannan? Ta taya Binta jimamin wannan asarar har tana rakito wani tsoho yana daga mata hanci.

Wannan karon taqi yarda ta damu, sai ta sassaitawa zuciyarta  ruwan haquri ta maze ta ce.

“Irin wadannan tausasan kalaman naka Anti Binta take so ta yi asara? Ina mata jaje wallahi”

Tana rufe baki ya ba ta amsa.

“Ai ko kusa ma ba za ta taba samun makamantansu ba”.

Jikin Nabila a sanyaye ta ce.

“Don me?”

Ya sake amsawa da sauri.

“Don ba ta so”.

Cikin rashin fahimta Nabila ta sauke numfashi ta ce.

“Mai son dan tsuntsu shi yake binsa da jifa, kuma kalamai rin wadannan za su taimaka maka wajen shawo kanta”.

Yana dariya ya ce.

“A’a, ni ina da sauqin kai ne a wajen mutum mai kirki wanda ya san darajata da furucina, mutane RIGAR SILIKI irin Binta maganinsu kakkausan hannu wanda da sun sulmiye zai rakito su da qarfi ya mayar muhallinsu”.

A sanyaye Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce.

“Amma kuma rayuwar aure ai ta fahimtar juna da bi sannu-sannu ce”.

Ya sake amsawa yana dariya.

“Ban da tamu, tamu tamkar ta mayaqa ce, ki sanya ido ki gani”.

Nabila ta sake cika da mamaki da kuma guntuwar fargaba, muryarta na rawa ta ce.

“Ai shi kenan, dama zan tambaya ne, akwai sanya hannunka wajen janyewar Alhaji Ibrahim?”

Har zai fada mata gaskiya sai kuma ya tuna ba ko wanne sirri ake danqawa mace ba, rauninta yana janyowa wataran ta fatalar da shi.

Ya yi fuska muryarsa a sake ya ce.

“Babu ruwana yasin”.

Nabila ta fara dariyar rantsuwar da ya yi, cikin dariya da raha ya ce mata.

“To kwarankwatsa dubu kike son na ce?”

Cikin tsananta dariya ta ce.

“Ni ban fada ba.”

Ya sake qara dariyarsa yana jin wani nishadi na shigarsa, Nabila ta kira shi a dame, amma abu qanqani idan ya yi mata sai ya mantar da ita damuwarta, dubi dai yadda take kyalkyala masa dariya, ina ma a Binta ya samu wannan?

Tsawon lokaci yana ta sanya ta nishadi, sannan daga bisani ya gyara murya ya ce.

“Kar ki amsa kiran Binta a gobe, kuma kar ki sanar da ita cewa ba za ki samu zuwa ba.”

A nutse ta ce.

“Wanne shiri kake yi?”.

Shi ma a nutse ya amsa mata.

“Ban gama shiryawar ba tukunna, ina dai hasashen ta in da zan bullo masa, na san Binta na gaggawar kiranki ne saboda ta yiwa shirinta na gaba shigar sauri tun da wannan takun ban sa masa hannu ba ya rushe, ni rigakafi nake son bata, zai toshe duk wani yunqurinta”

Jikin Nabila a matuqar sanyaye ta ce masa.

“To ina maka fatan nasara Yaya Mujahid”.

A hanzarce ya amsa.

“Amin, amma za ki iya zuwa nan da kwana biyu ko uku”

“To Allah ya kai mu.”

Ya sabunta mata godiya sannan suka yi sallama.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 22Rigar Siliki 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×