Skip to content
Part 26 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Kwannansu guda aka sallamo su daga asibiti, Hajiya ta matsa aka bar Nabila a nan ta sake kwana biyu har ta warware, sannan cikin rashin sani ta sanya Mujahid ya mayar da ita gida.

Ummi da Nabila ba su so wannan umarnin ba, amma Mujahid ya so shi, ya dauki  Nabila cikin karsashi suka tafi.

Farkon tafiyar ya fara jan ta da hira kamar da, sannan kamar kanwarsa, ita kuma gabadaya zuciyarta ta toshe, da kyar take qarfin halin amsa masa har suka ci rabin tafiyar.

Da ya fahimci cewa, ba zata rarrasu ta wannan sigar ba sai yayi shiru ya shiga tunanin wata sigar.

Can babu zato babu tsammani ta dago cikin rauni ta ce masa,

“Au Yaya Mujahid na manta ban yi maka Allah sanya alkahiri ba”

Ya juyo ya bita da kallo kawai.

Ta kada kai tana nuna ai babu komai, murmushi ma take.

“Na taya ka murna ka sami abinda kake so, zan je na cigaba da addu’ar Allah ya karkato da hankalin Anti Binta ta san muhimmancinka…”

Ya jima yana kallonta yana murmushi kafin ya tanka bayan ya mayar da idonsa ga Titi,

“Ban zaci zan ji wadannan kalaman na farin ciki da qarfafa gwiwa daga gare ki ba…”

Ta gwaro ido,

“Me ya sa?”.

A tausashe ya ce,

“Kin bi Binta kin suma, don kina taya ta takaicin an aura mata abinda ba ta so”.

Ta dora hannayenta biyu a ka alamar bayyana tashin hankali. Ta dinga girgiza kai tana qarawa, wai meyasa mutane ke qasqantar mata da dalilin suma ne, na’urar likita ba ta gwada qirjinta ta iya gano cewa qirjin nata cike yake da son da kisa ma zai iya yi ba sumarwa ba, sai ta gabatar da dalili mafi rauni, wai wuni ta yi ta kwana ba ta ci abinci ba, to shin shi ma wanda ake so ba zai iya ganin son ba ne da shi kuma zai kwaso wani dan ta’addan dalili mara dadin ji ya jinginawa suman?

Ta dinga dojewa haushi da kukan da suke kawo wa zuciyarta cafka, cikin damuwa da kebe baki ta ce,

“Wallahi Yaya mujahid ba wannan ne dalilin ba, don Allah ka janye zaton da ka yi min , ban cancance shi ba wallahi,”

Nan ma ya dan jima yana kallonta cikin murmushi sannan ya kawar da kai, bai ce komai ba.

Sai jikinta yayi sanyi ganin kamar bai gamsu ba, nan da nan cikin rawar murya ta ci laya,

“Wallahi tallahi Yaya Mujahid ban fi son Anti Binta ta cika burinta fiye da kai ba, na san duk duniya in kai ne na daya akan son ka auri Anti Binta to nice ta biyu akan son hakan ya faru… ka yarda da ni”.

Da sauri ya ce,

“Na yarda, amma me ya kawo kwanyarki ta je hutu daga jin labarin auren?”

Sai ta rasa abinda zata ce masa, ya qaraci jiran amsarta sai kawai ganinsa ta yi yana kada kai yana dariya. Dole ta debo kare kanta a raunane,

“Yaya Mujahid na ga kai likita ya sanarwa dalilin”.

Tana rufe baki ya amsa,

“Ko kuma ni na tsara haka ba”.

Yanzu ma cikin alamun kasa hankali ta ce,

“Me kake nufi?”.

“Ai na yarda da ke, magana ta wuce”.

Ya amsa mata da yanayi na kwantar da hankali.

Tsawon lokaci kowa bakinsa ya je hutu duk da lissafinsu ya wargaje kayan aiki yana ta yi, daga qarshe Nabila ce ta fara samo amsa, ta daga kai cikin rauni da kyakkyawar fuska ta ce,

“Ina neman wata alfarma Yaya Mujahid”.

Ya dan ja fasali kafin ya amsa,

“Ina sauraronki.”

Kai tsaye ta shiga karanto alfarmar,

“Tunda ka sami cikar burinka ka auri Anti Binta, ina roqon ka zaunar da ita ka fada mata shirinka da ke tsakaninka da ni, ka fada mata ba da gaske kake sona ba…”.

Ta yi shiru saboda yadda fuskarsa ta muzanta kuma yana girgiza kai, muryarsa babu alamun wasa ya ce mata,

“Ni duk duniyar nan babu wanda zan iya tara in cewa wai da gangan nake sonki, qarshen rashin karramawar da zan miki kenan, to ma wai waye ya fada miki ba na sonki?”.

Tuni wasu abubuwa masu kaifi suka shiga tsere a kwanyarta, wani suman na kawo mata sura tana dogewa don kar ta suma a wofi mutane su hau yi mata shaci fadi, kallonsa take zuru cikin rashin hayyaci.

Ya kada kafada,

“Kodayake kar na katsi hanzarinki, menene hikimarki na a sanar da Binta?”.

Muryarta na karkarwa ta debo amsa,

“Zai fi maka sauqin ka shawo kanta…”.

Ya tare ta,

“Kar ki damu, in ta fi haka tsinin kai ni na san yadda zan shawo kan abata, sam kar wannan ya dame ki”.

Tana hana kanta shiga wani rudanin ta ce masa,

“Ai ba ka bari na gama fadar hujja ba Yaya Mujahid…”

Ya qara shan kan muryarta,

“Oh! To fadi ina sauraronki”.

Ta dan ja fasali,

“Anti Binta zata nutsu da ni, ta cigaba da riqe ni a matsayin qanwarta, ba wata mai yi mata fashin so ba, in na hada so da ita a ‘yammatanci sam-sam bai kamata na cigaba da hadawa da ita a gidan aurenta ba”.

Wannan karon ya jima bai tanka ba, da alama manhajar lissafin da ya janyo tana da fadi.

Ya juyo ya dan kalleta yana murmushi, sannan ya murza yatsu,

“Na so na fahimce ki, ba laifi kuma kin dan sake ba ni satar amsa, wannan ya sa nake son zama da ke”.

Yayi shiru, ita ma shirun ta yi kawai tana kallonsa don ba ta fahimce shi ba, sannan ta gaji da magana yana canja mata manufa, ita da zai fahimce ta da kyau ya san yadda sonsa ke wasa da numfashinta, da hakan ya zame mata abin barka, ko da zai zamo qarshen numfashinta kenan.

Bai damu da shirunta ba ya cigaba,

“Kina zaton kishi zai sa Binta ta canja miki matsayi, daga qanwa zuwa abinda ba zaki so haka ba?”

Nabila ta girgiza kai da sauri,

“Ina da yaqinin ba zata taba canja min ba har abada…”.

Ya yi saurin tare ta,

“Kar ki wani ci alwashi kan Binta, na fada miki Rigar Siliki ce, in kina jin amincin da ta yi miki ya kai matsayin da ba zata canja miki ba, ni zan iya rantse miki ta ba ni sama da shi kafin na canja mata matsayi ta qwace duk abinda ta ba ni…”

Wani mugun tsoro ya shigi Nabila, abu mafi rashin dadi da zai same ta yanzu shi ne Binta ta tsane ta, don ita marainiya ce ba san komai da kowa ba sai son Mujahid da bai karbe ta ba, babu kuma wanda ya san tana yi, sai ko kakarta da tsirarun dangin babanta da ba sa bi ta kanta kasancewar matar babanta ta hana babanta ya saurare su, sai kuwa gidansu Binta da ya zama gidansu, Binta da danginta suka zama nata dangi, kuma inuwarsu take rabawa ta samo farin ciki a duk lokacin da ta rasa shi.

Da wannan ta sami qarfin halin fuskantar Mujahid,

“In haka ne don Allah kar ka jaza min wannan koma bayan don Allah”.

Ya jima cikin shiru,

“Amma dai kin san cewa, in har Binta zata kyamace ki bisa taraiyata da ke sai idan tana kishina, in kuma zata yi kishina sai idan tana sona, ki sha kuruminki hakan ba zata faru ba, ko jiya ta tabbatar min cewa ba zata taba yarda na zama mijinta ba, ko da kuwa  zata yi tsufa ta mutu da igiyar aurena”.

Nabila ta lushe ido ta bude, amma ba ta ce komai ba. In ta rantse ba zata yi kaffara ba ta san abinda ba zai yiwu ba ne kawai Binta ta fada, a yanzu ne kuma ta fara shakkun in ma ba son Mujahid ne ke dawainiya da Binta ba, qila ma yawa son yayi mata ta haukace.

Mujahid ya dawo da ita daga fagen tunani da cewa,

“Zan yi alfarmar da kika nema amma bisa sharadi biyu, kafinsu kuma akwai togaciya”.

Ta yi saroro tana kallonsa.

Ya dora,

“Togaciyar ita ce, zan canja kalmar da kika ba ni na kai wa Binta, ta cewa wai ba na sonki, ni dai ki bar ni na zabi kalma, ban da wannan”.

Cikin sauri don a wuce wannan maganar ta ce,

“Na bar ka ka zaba, sai ka fada min Sharudan”.

“Na farko, Kar ki sake yarda wani abu ya qara taba zuciyarki ki sake sumewa mutane, don ni ina da dan kaifin hangen, in na sa wa mutum ido har abinda ke zuciyarsa ina iya hangowa. sharadi na biyu shi ne in dai buqatar taimako ta taso min zan sake nemo ki, in kin yarda da wadannan sharudan to ki sa min ranar tarewa da Binta”.

Daga farkon maganarsa har zuwa wajen da ya dasa aya babu wanda bai ruda ta ba, sai dai tana ta qoqarin ta shanye saboda yanzu take dada gane waye wanda zuciyarta ta rakito ta kai wa so, yana kiran Binta Rigar Siliki shi ma a nasa fagen wani rigar Siliki ne na musamman.

Ta girgiza kai a raunane ta ce,

“Me yasa sai ni zan sanya maka ranar tarewa da Anti Binta?”.

Kai tsaye ya amsa,

“Ai saboda muhimmancinki ne ai”.

Ya dan ja fasali,

“Amma kar ki sa min nan kusa, don ina son Binta ta gaji da kukanta yadda ba sai ta je min da shi gida na sha wahalar rarrashi ba”.

Murmushi kawai Nabila ta yi, yanzu ta rasa bakin magana.

Bai damu ba ya sake dorawa,

“Sannan zamu sami isasshen lokacin da zamu shirya a nutse, yaushe zan kawo miki kudi ki shiryo min kayan lefe?”.

Ta fahimci shi babu ma abinda ya dame shi da halin da suke ciki daga ita har Bintan, sabgar gabansa yake kuma duk abinda yake so yake damuwar ganin ya wanzu, babu ruwansa da damuwar wasu ko bin su a sannu ya fahimtar da su su so abinda yake so.

Da wannan take jin in dai bata son zuciyarta ta gaji da riqon so ta fallasa to lallai ya zame mata wajibi ta nesanta kanta mu’amala da shi.

Ta yi fuska ta ce,

“So samu ne ni daga yau ba zamu sake kebewa ba Yaya Mujahid, mun gama wancan kwantaragin, mu koma matsayinmu na da, wato dagawa juna hannu daga nesa mu gaisa, ni na fi sha’awar wannan yanayin…”

Yana da dariya,

“Ashe kina daga cikin masu sanya takobin zalinci su datse zumunci, to ni ban fara zumunci da ke don in daina ba, sannan ba ni da damuwa don mutum  ba ya son zumunci da ni ni in qi shi ba, kamar yadda ba na damuwa in ina sonka kai ba ka sona in fasa son ba, kamar dai yadda mu ke da Binta yanzu, kema haka kuma don ki sani muna tare”

Zata yi magana ya tare ta ta hanyar daga mata hannu sannan ya ce,

“Mu kulle magana haka, ina jiran ki sa min ranar aure bisa wancan sharadin, sai kin sa zan sami Binta da maganar Game din da muka shirya mata”

Bai bata damar magana ba ya miqa hannu ya matsa sauti mai laushi ya fara tashi daga gidan matashin sautin motar.

Har suka kai gidansu babu wanda ya tanka, sai da suka kai qofar shiga cikin gidan ne sannan Nabila ta fahimci zai sha ta basilla sannan ta fadi abinda ke ranta, ta dube shi cikin yanayin zolaya ta ce,

“Yaya Mujahid ka na kiran Anti Binta Rigar Siliki, ka fa fi ta dacewa da sunan”

Ya yi dariya,

“Ba haka ba ne, ku mutanen wannan zamanin sai an zama haka ake samun kanku”.

Ta yi murmushi kawai.

Mujahid ya jima tare da Kakar Nabila suna hira, tsohuwa ce wayayyyiya mai son mutane, musamman masu ganin mutuncin jikarta Nabila.

Ta yi wa Mujahid murnar aure, sannan kuma ba ta munafunce shi ba ta dora da cewa,

“A cikin abokanka ka laluba da kyau ka samo wa Nabila mai kirki irinka don Allah, ta tsaya shirme ta kasa gane manufa ta…”

Jin Inna na shirin kwanto mata damisoshi ya sa ta shiga maganar,

“Wai Inna me ya sa kike ta faman neman kai da ni ne? ni gaskiya ba na son wannan dabi’ar”.

Tana ta faman tura baki ta tashi ta bar wajen tana jiyo Innar tana cewa,

“To ja’ira dama dole sai abinda kike so zan yi?’.

Inna ba ta damu ba ta cigaba da hira da Mujahid tana karanta matsalolin Nabila da dalilin da yasa ta matsu lallai Nabila ta yi aure  yanzu, ta sauke da cewa,

“Rayuwa da mutuwa duka a hannun Allah su ke babu mai lafiya babu mai cuta, amma tanadin duniya da lahira duk ba laifi ba ne.”

Yanzu Mujahid ya fahimce ta sosai, cikin tausayawa ya dinga gyada kai yana cewa,

“Ki na da gasiya fa Inna, ki cigaba da addu’a in sha Allah ke zaki aurar da ita da hannunki kuma ga mutum nagari wanda zai zame mata rumfa har bayan ranta”.

Cike da jin dadi Inna ta ce,

“Allah ya sa.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 7

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 25Rigar Siliki 27 >>

5 thoughts on “Rigar Siliki 26”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×