Skip to content
Part 25 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

LITTAFI NA UKU

An kai Binta da Nabila wani kyakkywan Pribate Hospital da ke kusa da Fadaman madan, babu bata lokaci aka basu daki daya me gadaje biyu, sannan aka koma dakon zuwan likita, wanda suka sami labarin ya fita daga asibitin.

Daukacin mutanen gidan hankalinsu yana tashe, hatta Hajiya wadda farkon faruwar abin ta so nuna babu komai, Binta ta yi sumanta ta gama aure ne an riga an daura, yanzu ta shiga rudu qwarai, don laluben me ya shigo da Nabila gigitar an yi wa Binta auren dole? Sannan in ta dubi Mujahid ma tana jin numfashinta na neman daukewa, don fuskarsa na nuna damuwa ne kawai, amma sam ba ya cikin masu tattalin majinyatan ko yi musu sannu kamar yadda dukkansu suka ke himmar yi musu sannun sai ka ce ita ce zata ba su lafiyar.

Bai sa hannu an shigar da ko waccensu mota ba, haka nan bai shiga motar da aka sa su ba, sai da suka yi gaba sannan ya janyo tasa motar ya biyo su a baya.

Wani abu bayan wannan tunda aka fara danbawar babu wanda ya ji ko da harafi daya ya fito daga harshensa, sai dai yayi ta bin mutane da ido cikin jan ido.

Wadannan abubuwan da Hajiya ta tara suka taru suka ruda mata kai, ta fara zargin anya kuwa ba hasashen wofi ta yi ba shi ma Mujahid ba son auren nan yake ba? Da sauri sai ta kori wannan zargin idan ya zo ranta, musamman in ta ji zuciyarta na neman darewa gida biyu, don ta kwaso rudu ne a lokacin da bakin alqamai ya bushe, an daura auren, in ya zama kure to matakin gyara kuren sai ya tashi hankula ko ma ya wargaza zumunci.

Haka dai suka cigaba da zama wajen Nabila da Binta a dakin da aka kwantar da su, shi Mujahid na can Reception ya zabga tagumi. Zuwa wannan lokacin tuni majinyata sun farfado, Binta sai kuka Nabila kuma sai bin mutane da ido, babu wanda ke iya karanta abinda ke zuciyarta.

Likitan na qarasowa kawai Mujahid ya tashi ya bi shi a baya suka shiga dakin tare, su Ummi suka miqe zasu fita amma Hajiya da Sani suka tsaya.

Likita ya fara yi wa su Hajiya tambayoyi, suna amsawa, inda ya fara da duba Nabila wadda yake ganin kamar ita ta fi jin jiki, domin shi kansa kuka ai samun dama ne.

Su Hajiya suka bi Mujahid da ido lokacin da suka ga ya sha gaban likita, cikin qoqarin daidaita muryarsa wadda damuwa ta shaqe ya ce,

“Doctor duk abinda sakamako ya nuna ni zaka kira ofishinka ka sanar da ni.”

Ya nuna Binta,

“Ka ga wannan matata ce.”

Sannan ya nuna Nabila,

“Wannan kuma qanwata ce.”

Binta ta qara kecewa da kuka saboda tsabar baqin cikin kalmar matarsa da ya ambata mata, abinda ya sa likita sake kallon Hajiya kenan kallo mai nuna son ta gasqata Mujahid ko ta qaryata shi.

Cikin hadiye damuwa Hajiya ta kada kai tana murmushin yaqe,

“Gaskiya ya fada likita.”

Likita ya mayar da hankalinsa ga Nabila yana nuna musu qofa,

“Kar ka damu, amma dai ku ragu ko, kai ko Hajiya sai wani ya zauna”

Ya nuna Mujahid.

Kafin ma ya rufe baki tuni Sani da Mujahid sun kai qofa, saboda haka Hajiya ba don son ranta ba ta tsaya, tana hararar Binta mai cika musu kunne da kuka.

Tsawon minti goma sha biyar likita ya fito sannan ya yafici mujahid suka je ofishinsa.

Sai da duk suka zauna daidai sannan likita ya fuskanci Mujahid,

“Ba fa wani abu ne na damuwa ba, duk sun dawo hayyacinsu, kuma ina zargin irin hakan ba zata sake faruwa ba.”

Mujahid yayi ajiyar zuciya kawai.

Likita ya cigaba da cewa,

“Ina jin kun fada musu wani abu na tashin hankali ne ko? Shi ne ya janyo qwaqwalwarsu zuwa hutun dole.”

Cikin rashin shakku Mujahid ya ce,

“Haka ne, amma ina roqon wata alfarma.”

Likita ya zuba masa ido cikin alamun rashin fahimta,

Mujahid bai yi qasa a gwiwa ba ya gabatar da alfarmar,

“Ita wannan qanwar tawa in ka tashi gabatar da rahoton ciwon nasu, kar ka gabatar da wannan, don Allah ka ce, ta jima rabonta da abincin ne aka sami wannan akasin…”

Cikin mamaki likita ya ce,

“Me yasa ni kuwa zan yi haka, menene hikimar hakan?”.

Mujahid ya kada kai,

“Kar ka zurfafa bincike, amma dai in ka yi zaka ceto mutane da dama daga ciwon damuwa da zai iya kai su ga irin abinda ya samu su wadannan majinyatan, sannan akwai ma wani aure da zaka taimakawa ya sami numfashi mai kyau”.

Likita ya shiga girgiza kai,

“Wannan ba zai yiwu ba, dole ne asibiti ya ajiye haqiqanin record na halin da majinyaci yake ciki, ko don saboda gaba ko kuma yadda wani likitan daban zai zo ya dora…”

Mujahid ya tare shi,

“Haba likita, sai ka ce ba kai ba, in an so taimako ai a na iya file biyu, na gaskiyar da na qarya, in muka gama wannan karon muka bar maka asibitinka kawai sai ka qona na qaryar…”

Ya saki maganar da ya ke ya rarumo takarda a teburin likita,

“Ka ga ni lauya ne na san doka, sannan na san muhimmancin rubutu, mu yi a rubuce zan sa hannu, ko da wata zata taso ka gabatar da shaidarka”.

Bai jira likita ba ya shiga zana yarjejeniyar cikin azama.

Likita tsayawa yayi kawai yana kallonsa, cikin mamakin hayaqin da ke cin kan wannan lauyan.

Bayan Mujahid ya sanya hannu ya tura masa takardar,

“Sa hannu a yi foton takardar a ba ni foton ka riqe Orijinal din.”

Likita ya karbi takardar yana karantawa, sannan ya zaro biro, amma kafin ya sa hannun sai ya dago ya dubi Mujahid,

“Amma dai a matsayinka na Lauya ka san cewa mutum ba ya shiga abinda bai sani ba bare har ya sanya hannu ko…”.

Mujahid na dariyar qarfin hali,

“Iyakar abinda yakamata ka sani kenan, wato kanwata da matata abu daya ya razana su, na ce a boye na daya, faqat! Ko so kake sai na farke maka cikina?”

Likita yayi dariya ya shiga rattaba hannu,

“Shikenan cigaba da dinke cikinka.”

Mujahid yayi dariyar jin dadi, sai lokacin ya fara sauke ajiyar zuciya. Alal aqallah ya dinke barakar da za’a sa wa Nabila ido, sannan an dinke wadda zata ragewa Binta damuwa, don ya san Binta ce kadai ta san cewa Nabila na sonsa, in kuwa ta ga cewa Nabila ta suma akan son nasa, nan ma wani shafi ne mai zaman kansa a zuciyarta da zata yi wa aiki na musamman.

Haka kuwa, da Mujahid ya je musu da labarin sakamakon, yana lura da Hajiya ta sauke wata ajiyar zuciya, Binta ce dai bai ga raguwar komai a fuskarta ba, sai ma wani saban kukan da ta bude, yayin da Nabila ta ja fatun idanuwanta ta rufe zuciyarta na qara duhu, ta ji kuma tana neman tsanar zuciyarta wadda ba ta taya ta damuwa lokacin da ta rasa abin sonta ba, ashe faduwar da ta yi wasa da cikinta da ta yi ne? ba ta zaci haka ba, yanzu duk gobarar da take ji a qahon zuciyarta rashin abinci ne, ba rashin Mujahid  ba ne? sai lokacin ta ji wani zazzafan hawaye me tsada ya bullo mata, ko roqo shi tayi iyakar qiwar da zai mata kenan.

Mujahid ne kadai ya ga hawayen, kuma bai nuna wani aiki ba ya sa kai ya bar dakin. Yana tunanin inda zai je ya boye kansa yayi tunani.

A qofar shigowa dakin ya ci karo da Alhaji ya shigo a gaggauce, suka yi musanyen wasu gajerun kalmomi na maraba da amsa marabar kawai Mujahid ya wuce, Alhaji kuma ya shiga cikin dakin da zaton Mujahid zai biyo bayansa, amma maimakonsa sai Sani da su Ummi ne kawai suka shigo dakin.

*****

Qarfe goma sha daya da rabi Alhaji ya dauki Hajiya zasu tafi gida, bayan qafar masu zuwa dubiya ta dauke, an bar Ummi da Karima su kula da su, don gidansu Nabila ko sanar da su ba a yi ba, saboda dalilin rashin isasshiyar lafiyar kakarta.

Cikin yanayin damuwa Alhaji ya cewa Hajiya,

“Hajiya ba kya ganin akwai matsala kuwa?”

Gabanta na faduwa ta ce,

“Me ka gani Alhaji?”

Cikin karaya ya ce,

“Mujahid ne ya ban tsoro, ban ga alamun son Binta a tare da shi kamar yadda kika labarta min ba”.

Hajiya ta yi dariya gami da ajiyar zuciya,

“Ni ma na zaci haka da farko, amma lokacin da likita ya zo sai ya cire min shakku don ya nuna Binta ya ce matarsa ce, bayan nan ma na qwanqwashi Karima, inda ta tabbatar min a saninta Mujahid tun tuni yana son Binta ita ce dai ta qi bashi hadin kai…”

Alhaji ma yayi ajiyar zuciya,

“To madallah, har hankalina ya dan kwanta, in shi yana qin auren ne za’a fi samun matsala kasancewar shi ne jagora, in kuwa yana sonta ko ba ta sonsa na san zai iya shawo kanta ta so shi nan gaba”.

Hajiya ta bata rai,

“Wannan banzar yarinyar ma ai babu amfani jiran sonta, ta fi so ta yi ta janyo mana magana”.

Alhaji yayi dariya,

“To dai kin matsa an yi mata aure hankalinki ya kwanta ko? Sai ka ce ma a kanki ta ke.”

Ita ma ta yi dariya,

“A idona ta ke kawai, na gaji qannenta su yi ta tasowa a gabanta suna riga ta aure.

  *****

Alhaji da Hajiya na fita daga asibitin Mujahid ya yi wa dakin tsinke tamkar su ne ba ya son gani.

Yana shiga duk mutanen dakin suka doro masa ido, Nabila, Ummi da Karima, in ka dauke Binta da ta ji wani dunqulen abu ya rakito ya fado mata qirji, ta ja wani gundumemen tsaki ta kawar da kai.

Wataqila wannan ne dalilin da yasa ya sha qamshi ya doshi gadon Nabila kai tsaye yana dubanta cikin tsananin kulawa,

“Kanwata sannu da jiki.”

Ummi ta yi saurin miqewa ta ba shi kujera ya zauna.

Nabila ba ta iya tankawa ba, da kyar ma ta janyo qarfin halin da ya taimaka mata kawar da kai daga kallonsa ta shiga kallon wani wajen daban.

In zata yi magana sai an gano ta, sai an ga gazawarta wajen boye son da a yau ta haqiqance ba zai taba boyuwa ba har ta shanye numfashin da aka gwado mata, abinda ya rage mata shi ne ta fara addu’ar Allah ya dau ranta ta huta.

Bai damu da banzar da ta yi masa ba ya cigaba da kula da ita ta hanyar tambayar Ummi,

“Kun ba ta abinci?”

Bakin Ummi na rawa hankalinta na kan Binta da ta juya musu baya da alamun sabon kuka ta sake duk da tana qoqarin boyewa,

Ta amsa masa da cewa,

“Eh ta sha tea, ta kuma dan sha kayan marmari”.

Ya nuna kular abincin da ke ajiye gefe,

“Menene nan a ciki?”

Ummi ta amsa,

“Taliya ce…”

Ya tare ta,

“Yauwa abincin yan gayu irinta, maza zubo mata kadan ta ci a gabana in gani.”

Ummi ta bi wannan umarnin cikin sanyin jiki ba da son ranta ba, don tana ganin zallar rashin mutunci da keta haqqin dan adam a cikin abinda Mujahid yake yanzu, Yaya za’a ce matarka da wata na cikin halin buqatar kulawa lokaci daya, amma ka zo wajen ko sannu matar ba zata sami arziqi ba sai ka tare a gun wata da in an daga dalilin kulawarka za’a rasa? Dole ne Binta ta qara masa farashin qiyayya ko yana so ko ba ya so.

Da kyar aka shawo kan Nabila ta tashi zaune da zummar cin abinci, amma dai shi ma ya gagara, don Mujahid na qara matsowa kusa da ita da zummar taimaka mata, tana hada ido da shi kawai sai kuka ya qwace mata, da gudu ta koma ta kwanta, tana neman hadiye kukan shiyasa take kamar zata shide.

Da sauri Mujahid ya basar, don ya san kukan ne zai iya fallasa halin da take ciki, ya fara cin abincin, dayake yana hannunsa yana cewa,

“To ai shikenan, in kin qara sumewa saboda rashin ba ciki haqqinsa babu wanda kika isa ki dagawa hankali”.

Ya kalli Ummi,

“Ba ni shayi.”

Mintina goma dakin shiru, a hankali Mujahid ke kurbar shayinsa yayin da yake aika qwaqwalwarsa shashe sashe na tunani amma tana dawo masa empty.

Can suka jiyo an nufo dakin a na qwanqwasawa, ba a jira ba kuma aka turo qofa aka shigo, sai ga Yaks ya bayyana.

Mujahid yayi dif! Tamkar ya ga madaukin rai, ko sallamar Yaks ya kasa amsawa bare amsa gaishe gaishen da yake.

Ya zo nan kansu shi da Nabila ya dan tsaya dum, rashin kulawar da ya samu daga Mujahid ya sanya shi kwasar qafa ya doshi gadon Binta.

A nan ne kuma aka ga Kwanjin Mujahid, don ya ajiye kofin shayi ya bi shi a baya, yana zuwa kuma ya janyo kujera ya ajiye masa nesa da Binta, sannan shi kuma ya zauna wajen qafarta yana daure fuska.

A’a! ummi da Karima suka ga wani Game din daban bayan wanda suka gama gani, irin wannan walankeluwar duk kwanyar mutum ba zai iya kintatar abinda ke faruwa ba.

Yaks duk kansa ya daure, jarabar Mujahid kuma ta fara isarsa sai dai ba shi da abin yi.

Ya dinga duba Binta amma ba ta da amsa sai kuka, shi kuma ya dinga ba ta haquri yana fada mata cewa haka Allah ya qaddaro.

Mujahid dai bai tanka ba, har yaks ya gaji da zama yayi musu sallama ya fita bayan ya sake komawa gadon Nabila ita ma ya sake duba ta.

Bayan fitarsa Mujahid yayi fuska ya miqe, da alama wajen zamansa na da zai koma, a nan ne Binta ta gaji da wannan qasqancin, ta fara yunqurin tashi zaune cikin kukanta,

“Wai wa zan wa Allah ya isa ne… an gajarta min rayuwa an dulmiya min ita a ruwan kwatami…’

Mujahid ya daga mata hannu muryarsa tar ya ce mata,

“Ke kika tsaya bata wa kanki lokaci da kuka tun dazu, shin dama kina da aikin neman wanda zaki yi wa Allah ya isa kika tsaya kuka da tsaki?”.

Ta sake kecewa da kuka cikin yanayi na rashin hayyaci,

“Allah ya tsinewa duk wanda ya yarda ni matarsa ce…”.

Yayi dariya ya wuce,

“Ni ban zo magana da ke ba, in na zo magana da ke ba zan baki damar ki fadi abinda kika zaba ba, saboda haka yanzu lokacinki ne, ki yi kuka ko ki yi ashariya duk an baki dama, ni da Nagari da batacce babu wanda ban iya zama da shi ba”

Bai jira cewarta ba ya wuce gaban gadon Nabila ya ce mata,

“Nabila sai da safe, ki yi bacci cikin kwanciyar hankali don Allah, in kuka daga maqwabtanki yayi yawa ki sa hannu ki toshe kunnuwanki.”

Ya juya ga su Ummi,

“Mu kwana lafiya.”

Sannan ya fice cikin nutsuwa.

“Ikon Allah”

Ummi ta fada don ta kasa hadiyewa, Binta kuwa tuni ta yi gum, da alama ita ma tana buqatar sake tunani kafin ta san ta inda wannan dan rainin wayon zai yi dadin aci masa kashi a ka.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 24Rigar Siliki 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×