Skip to content
Part 41 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Mujahid na cikin fushi, amma a hakan ya jin ba zai taba samun kwanciyar hankali ba sai ya san wacece Bintansa kuma da wacce irin qafa ta shiga wancan mafiyayyen asibitin kuma da wanne ta fita?.

Duk da wannan saqar tasa ba ya jin farin ciki sam, fuskarsa daure ya shigo gida ya haye Benensa bayan ya je wajen aikinta aka ce masa tun rana ta tafi.

Bayan sallar isha yana wanka ya dinga jin wayarsa na kadawa, saboda haka yana fitowa ya bi ta kanta, sai ya tarar Nabila ce da kiran, nan da nan ya bi ta, sai ga mummunan labarin cewa ta fitar da Yaks a matsayin wanda zata aura.

In ransa yayi dubu sai da ya baci, sai dai ya kasa cewa komai, to me zai ce? Idan rannan ya nuna wa Nabila yaks tare da mata suna shashanci a titin Allah, ya sanya ta janye aurensa a karo na farko, wannan karon daukarta zai yi ya kai asibitin ya nuna mata yarinyar da ya kawo a zubarwa ciki? Kuma idan yayi hakan wa zai kawo ya aura mata tunda ya hana ta auren Yaks tunda shi ba na kirki ba ne?

Karo na farko da ya ji zazzafar qwalla na bullo masa a cikin lamarin Nabila, haka yayi fuska ya dinga yi wa zabin nata fatan alkahiri har suka yi sallama.

Tana sauke waya ta rafshe da kuka, a yau din nan take fatan mutuwarta akan wannan rayuwar da take shirin tunkara ta auren mutumin da ba ta so da kuma wadda take ciki a halin yanzu, wai ita ke sanar da masoyinta zata auri wani ba shi ba, masoyin da soyayyar da take yi masa tana daga cikin soyayya ta musamman a filin duniya, shi ma kuma cikin rashin sani yake yi mata murna da fatan alkhairi.

Kwanyar Mujahid ta dauki zafi sosai, ya dinga hada lissafin Nabila da Binta yana yi lokaci guda, bai samo komai a Nabila ba face fatar bakinsa da ta maqalewa ambaton,

“Da izinin Allah in dai ina raye ba zaki auri wancan fasiqin ba”

Binta kuma ta yi zaune a zuciyarsa komai nata na zuwa ransa daya bayan daya, daga kan asibiti zuwa gadar zaren da ta shiryawa salihar yarinyar da ko nuna wa da yatsa ba ta cancanta ba.

Ya yardarwa kansa lallai Binta ta fiye son kai, tunda take son rusa rayuwar Nabila bisa ribar da har yanzu bai ga ta inda zata same ta ba, in dai aurensa ne duk qullinta ba saki zai yi ba.

Cikin rashin dadin rai ya shirya tsab yana ta zuba kamshi ya cim mata a falonta.

Tunda qamshin turarensa ya fado hancinta ta ji gabanta ya yanke ya fadi, bare da ya shigo ta gan shi tsab sai ka ce me zuwa wani party na musamman.

Ta kawar da fuska tana satar bin sa da kallo tare da amsa sallamarsa a ciki.

Ya sami kujerar kusa da ita ya zauna, ba tare da dubanta ba ya ce,

“Ki ba ni shayi, in kina da gasasshen nama ki ba ni, in babu ma ki gasa min”.

Ta dinga kallonsa cike da mamaki, maimakon haushi wannan ikon nasa sai ya so bata dariya, amma ta saye fuska ta bige da murmushi, kuma salin alin ta tashi ta fice zuwa Kitchen ta je ta kawo masa shayin, ta janyo teburi gabansa ta jere sannan ta sake ficewa ba tare da dayansu ya tsinkawa dan uwansa ba.

Qamshin da ya fara jiyowa ya sa ya fahimci naman take gasawa, wani murmushi ya subuto masa a kunci duk da bai hana zuciyarsa jin daci ba.

Ba jimawa sosai ta kawo naman ta ajiye ta koma gefe, kamar zai yi mata tayi sai kuma ya share, ya mai da hankali ya dinga cin abinsa hankali kwance duk da cewa fuskarsa babu walwala.

Ta yi zaune kujerar nesa da shi tana ta faman cin magani tana aikin danne-dannen waya.

Ya din ga samun lokaci yana daga kai yana dubanta sannan ya mayar da hankali kan abinda ke gabansa.

Sai da ya gama tsab, ya je ya wanko hannu da baki ya dawo ya zauna sannan ya daga kai ya dube ta sosai.

‘Ki zo ki kwashe kayan nan”

Ba tare da ta dube shi ba ta amsa,

“Ka je kawai abinka, duk lokacin da na tashi zan kwashe”.

“Na je ina?”

Ta daga kai sosai ta dube shi,

“dakinka mana”

Ya dora mata ido har sai da ta ji kaifin shigar kallon ta dago ita ma ta dube shi, bai janye idonsa ba har sai da ta hukuntu ita ta janye nata jiki a salube qirjinta na harbawa, sannan ya nisa ya ce,

“Yau a nan dakin zan kwana tare da ke”’

Yana nuna mata dakin da ta fi kwanciya.

Gabanta ya sake faduwa. Amma ta boye a fuskarta, ta yatsina fuska ta ce,

“Haba sai ka ce a tatsuniya.”

Ya amsa mata,

“Eh dama rayuwarmu ai ta fi kama da tatsuniya, ko hakan aka kira ta daidai ne, ban taba ganin me makahon so irina ba, me son wadda sam ba ta cancanta ba, Wallahi Binta makauniyar zuciyata ke son ki, amma sam ba ki cancanta ba.”

Yanayin muryarsa na nuna lallai da gaske yake maganarsa, wannan ya sanya kwanyarta toshewa ta kasa cankar komai, kallonsa kawai take fuskarta a bace.

Bai jira ta ba ya cigaba da magana,

“Ke kuma me makauniyar qiyayya ko? Babu dalili haka kawai kin dauki karan tsana kin dora min har da bin hanyoyin da zasu kai ki wuta, duk haqqin da kika samu a hanyar qina sai kin ci, ki zalunce ni ki zalunci wancan yarinyar da taba irnta ke jawo wa mutum fushin ubangiji…”

Ta katse shi saboda kishi ya yunquro mata, ta san da Nabila yake, don haka take jin kamar yana kwara mata ruwan zafi,

“Wacce yarinyar?”

Kai tsaye ya amsa,

“Nabila”.

“Me na yi mata?”

Ta tambaya cikin fishi,

“Zaki biya Yaks da aurenta bisa aikin kashe naki auren da kike sanya shi”.

Ta dan yi wura-wura, ita ba manufarta kenan ba, a da ba ta taba mafarkin Nabila ta auri Yaks ba,  hakan ya faru ne bayan babu wani zabin sai shi, in ta bar nabila zata iya nasarar auren Mujahid, ita kuma ko a hira ba ta son hakan ta kasance.

Mujahid ya sake tankawa,

“Ba zan rufe ki ba, qimarki ta qara zubewa a idona, ba na son zalunci, ba na son a zalunci wanda bai cancanta ba, ba na son a cuci mutumin da aka san gatansa ragagge ne, kuma ba na son a cuci mutumin da ya danqa amana”

Ta fara hawaye,

“Duk ni na yi wa Nabila haka?”

Tana rufe baki ya amsa,

“Qwarai da gaske, kin shirya mata gadar zaren da zata auri qatoton fasiqi irin Yaks, ko jiyan nan na gan shi ya kai mace a zubar mata da ciki, wai irin wannan mutumin kika zuga Nabila ta aura, Binta kin ci amana wallahi, da na son inda sonki yake a qirjina da na bi na kwarfe shi don rashin kyan halinki.”

Binta na cikin jin ciwon maganganun Mujahid kamar wasa sai ga Nabila ta kira ta, daga yadda ta daga kai ta dube shi ya san cewa Nabila ce ta kira ta, kawai sai ya taso ya zauna hannun kujerar da take zaune,

Ta yi qoqarin ta tashi amma ya riqe mata hannu dole ta koma ta zauna, ta kuma daga wayar, zazzaqar muryar Nabila me alamun dushewa don kuka ta karade kunnuwansu da cewa,

“Anti na bar agogona a nan?”

Binta ta miqa hannu ta dau agogon a kujerar gefenta ita ma da dusasshiyar tata muryar ta ce,

“Kina maganar yanzu na hange shi kan kujera”

Nabila ta sauke ajiyar zuciya ta ce,

“Alhamdu lillahi”

Binta na qara janye jikinta daga na Mujahid ta ce mata,

“Kai Nabila, wannan agogon da ba wani tsadar kirki gareshi ba kika kasa bacci saboda shi, kin sha mantawa fa da wadanda suka fi shi tsada a gida sai ina binki da su ko in kyautar…”

Nabila ta yi siririyar dariya me shanye ciwon so ta ce,

“Ba agogon ne muhimmi a wajena ba Anti, wadda ta yi min kyautarsa ce muhimmiya.”

Mujahid ya kai hannu ya karbi agogon a hannun Binta, sai ya gane wanda ya taba bata kyauta ne tare da wasu Cosmetics din, nan da nan sai ya ji kansa ya hargitse da kuwwa, hade da tausayi. Yau ba Nabila kadai yake tausayawa ba, har kansa yake tausayawa wanda bai yi sa’ar so ba, kamar yadda Nabila ba ta yi ba, dama Binta ce Nabila, dama it a zuciyarsa ke so, haqiqa da sun zama sahun farko na masu yawan farin ciki a duniya.

A zuci ya dinga kukansa, hawayensa kuma na shawagi a qwallon kansa ya kasa fadowa idonsa da fuskarsa.

Don ya kori damuwarsa sai ya cewa Binta,

‘Nabila ce ko? Allah sarki ba ni na ji da ita.”

Da farko Binta ta so tura masa wayar ya je su qarata, amma sai ta ji wani haushi ya hana ta bashi wayar, tana cigaba da magana da Nabila cikin zumbura baki ta tashi ta doshi daki, shi kuma Mujahid bai yi qasa a gwiwa ba ya bi bayanta, suka yi tsaye cirko-cirko a tsakiyar daki, domin ganin ya biyo ta sai ta kasa zaman da ta yi niyya, nan da nan ta yi sallama da Nabila ta fuskance shi cikin jin haushi,

“Ba ka da lambar Nabilan ne ko kuma ba ka da wayar da zaka kira ta?”

Ya sake yin kasaqe yana kallonta cike da birge shi, kuncinsa da murmushi ya amsa mata,

“Duk ina da su, kawai ba na iya jin Nabila a guri ne ban sa bakina cikin lamarinta ba.”

Da sauri Binta ta dafe qirjinta da ta ji yana barazanar tarwatsewa, da sauri ta ja qafa ta zauna bakin gado tana numfarfashi.

Ya shanye dariya ya bita ya durqushe gabanta ya dafe gwiwoyinta yana qoqarin kai hannunsa inda ta dafe qirji, cikin dakusasshiyar murya ya ce,

“Wai me na fada da ya girgiza ki? Bari na ji”

Da sauri ta doke hannunsa qwalla na sakko wa fuskarta, bata ce komai ba.

Ya sa hannayensa biyu ya riqe nata hannayen, ya shigar da qwayar idonsa cikin nata yana yi mata wasu irin kallo da bata taba ganin irinsa a wajen kowa ba, ta dinga jin barin jiki tamkar ya jona ta a caji, duk wasu qarfin halinta da lagonta ta neme su ta rasa, babu abinda take ji sai tsabar bugun zuciya.

A nan zan dakata, sai mun hadu da safiyar a littafi na qarshe.

Taku Maimuna Beli.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 40Rigar Siliki 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×