Skip to content
Part 39 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Suna tsaye cirko-cirko ko wannensu cikin tashin hankali da takardu a hannu.

Karo na farko da Hajiya ta ji wani tsananin tausayin Binta da jin tsanar Mujahid sun ziyarci zuciyarta, ta yi dakace da danasanin abinda ta yi na yin sanadin da aka aurawa Mujahid din, ashe ita da kanta ta yi mata tayin hanyar mutuwa. Hajiya ta dinga hango fuskokin Mujahid ko wannensu na kirki babu mai nuna cewa mutumin banza ne shi a can waje.

Alhaji ya sauke numfashi ya ce,

“To yanzu menene abin yi?”

Hajiya ta sauke numfashi wanda ya ba ta damar hadiye kaso mai tsoka na jin haushin Mujahid.

“A kira Binta a ji idan suna zuwa shan magani, muna da wani abin yi ne bayan wannan Alhaji?”

“Binta za’a kira ba Mujahid ba?”

Hajiya ta yi saroro tana kallonsa cike da haushi saboda ambatar sunan Mujahid, amma dai ta yi qoqarin fuskarta ta boye takaicinta, kallonsa kawai ta ke.

Ya dan ja fasali sannan ya ce,

“Mujahid din kawai za mu kira ban da Binta”.

Hajiya ta cigaba da kallonsa sarororo, ba ta son yi masa musu.

Shi ya zaci duk rikicewar ce ba wani ta rakici duk laifin ta dorawa ba, don ya san halinta da hangen nesa da kuma yawan adalci, ko daya ba ta nuna bambanci tsakanin danta da wanda ya kawo ya zube mata.

Da qarfin gwiwarsa ya ce mata,

“Ki yi wa Mujahid din waya ki ce ina son ganinsa da dare.”

Qarfin gwiwar da ta gani a fuskarsa ne ya sanya ta karbi umarnin kai tsaye, amma da sai dai shi ya yi masa wayar.

*****

Mujahid bai zaci ko wanne irin abu na rashin dadi ba, bayan sallar magariba ya shiga ya sami Binta wadda ba ta jima da dawowa daga aikinta ba, ya ga kala-kalar damuwa a fuskarta, amma tunda tuni ta mayar da fuskokinta irin haka, sai ya ji babu wani abin damun kai da neman ba’asi ko kuma neman a yaye mata damuwar.

“Zan je gida, in zaki ki zo mu je.”

Tana kallon fuskarsa ta ga ya sake yi mata baqi, babu abinda ta ke gani cikin fuskar tasa sai Nabila, kunnuwanta kuma na hararo mata tattausar muryarsa me magana da Nabila, amsma in ya tashi yi mata magana ita sai ya dinga yi kamar mai cin kashi.

Ta yi iyakar qoqarinta na ta boye quncin da ranta ke ciki wanda ta kasa bawa sunan kishi ta kasa, ba tare da ta zaba ba ta ji kai tsaye ta ce masa,

“Ni ba zarginka zan yi da zaton ka tafi wajen Nabila ba, ba sai ka yi min siyasa ba”

Yayi dum! Saboda kasa cankar takamaimai din inda ta dosa, ba tare da ya canka din ba ya fara tura mata haushi,

‘In zan je wajen Nabila ke wacece da zan boye miki, ko culob zan je ke dai ba wata ba ai ban ga abin yi miki qumbiya-qumbiya ba, me ye naki a ciki?”

Ya tsattsare ta da ido alamun yana jiran ta amsa.

Ta dinga kallonsa cike da wani mugun jin haushi, kamar ta kunduma masa ashar, sai kawai ta rangwada kai ta kawar da fuska muryarta a cunkushe tana cewa,

“Sa qafa ka tafi gidan giya ma ba culob ba, ni ba zan je ba”.

Bai ko bari ta gama direwa ba ya kama hanya ya fice yana cewa,

“Madalla, dama taimakon ki zan yi na dan sama miki faraga na raba ki da wannan quncin, na ga tun safe ke kadai kina cika kina batsewa kamar zaki iya hadiye kanki da kanki.”

Yana fita ta saki kuka, zuciyarta na wani irin suya lokaci na farko kuma da ta fara jin haushin Nabila cikin ranta.

Kamar yadda ya saba ya shiga gidan, amma jikinsa yayi sanyi ganin Hajiya da wata sanyayyiyar fuska da bai taba ganinta da ita ba, sai dai bai kai ga cankar shi ne mai laifin ba, ya fi tsammanin wani abu ne daban ya taba ranta.

Amma da ya ga kamar wani meeting na musamman aka kira shi falon alhaji sai ya fara shan jinin jikinsa.

Ilai kuwa Alhaji ya huro masa wata magana mai hargitsa lissafi,

“Dama roqonka zan yi, ka dubi girman Allah ka san dabarar da zaka yi ka sanar da Binta in har ba ta sani ba din, don ita ma ta dinga zuwa shan magani.”

Razana da tsoro sun bayyana a fuskarsa, don cikin sakannin qalilan ya fahimci inda gizo yayi saqar, wato su Alhaji sun sami zancen tatsuniyar Binta na da qanjamau, qari akan wannan ma shi suke zargin ya sa mata.

Bakinsa na rawa ya ce musu,

‘Maganin me?”

Hajiya ma muryarta na rawa ta ce,

“Don allah ba sai an yi musu ko an ja wata magana ba, ka daure kawai ka yi abinda Alhajin ya ce, mun san komai.”

Mujahid yayi qasa da kai hankali a tashe, ko kadan bai so maganar nan ta zo kunnensu ba ko da kuwa ba laifinsa zasu gani ba laifin Binta zasu gani, yana son Binta matuqar so, ko kadan ba ya qaunar abinda zai bata mata suna. Yana da yaqinin ko ba dade ko ba jima sai wannan cukumurdar ta Binta tare da qiyayyarta ta sha ruwa, kullum fatansa shi ne kafin ta sha ruwan kar ta tafi da mutuncin kowa a cikinsu.

Yayi iyakar kaifafa tunaninsa amma ya rasa me zai cewa surukansa, kare kansa zai yi ya kwarewa masoyiyarsa baya ko kuma masoyiyar tasa zai goyawa baya shi ya bata wa kansa sunan? Rana zafi inuwa quna.

Daga qarshe ya yanke shawarar shi dai da bakinsa ba zai kwarewa masoyiyarsa baya ba, gara dai in sun ji dai gaskiyar maganar a waje yana iya qara musu bayani da kansa, shi ma din dan ya sami kafar wanke Binta ne.

Haka yayi musu zaune tsawon mintuna ashirin da biyar suna ta faman tuhumarsa da yi masa zargin rashin gaskiya amma ya qi tankawa, har sai da suka sallame shi daga qarshe da gargadin lallai ya san yadda zai sanar da Binta da kansa in har bata sani ba, kuma ya dinga kai ta shan magani sannan ya sami bakin magana,

“Ni ba na son na ce komai yanzu, amma dai ina roqon alfarmar sirri, sannan ina roqon kar ku canja min kallo ko ku canja min ruqo, don qila ba ku sani ba ko akwai wata gaskiya bayan wannan, ko kuma akwai wani abin wanda Allah bai sanar da ku ba bayan wannan…”

Alhaji ya dan sha jinin jikinsa, amma Hajiya qara quluwa kawai ta yi, ta ce,

‘To dama ai abin arzaqi ake yadawa ba na tsiya ba, zamu je talla da kai mu burma wa kanmu wuqa ne Mujahid?”

Yanzu ya fara fahimtar Haijya na jin haushi, amma bai nuna fahimtar ba sai ya basar ya ce,

“Yauwa, don Allah ko boto kar a sanar wa, ko da kuwa Goggo ce, kuma don Allah ku qara sa mu a  addu’a.”

Babu wanda ya tanka masa, shi ma bai damu da sai sun tanka din ba ya tashi yayi musu sallama ya wuce gidansa jiki a sanyaye.

Ranar bai ko doshi dakin Binta da zummar kwana ba, Benensa ya haye don yayi tunani a nutse. Gaskiya kansa ya hargitse fiye da ko wanne rudadden lokaci da ya taba samun kansa, ya saqa wannan ya kwance wancan, abubuwa da yawa marasa dadi akan sauran mutane ban da Binta, ya saqa ya kai Yaks da asbitin da Binta ta kwanta qara ya fi a qirga, amma albarkacin Binta yake jin fasawa, kar ya tona mata asiri, kar ta tozarta, kar in an tashi shari’ar a sako da ita, kar hankalinta ya tashi, kar ta kwanta ta kasa bacci, duk bisa irin wadannan dalilan yake barin kowa yana sha duk da shi yana kwana ciki.

Ya gama lalube da qyar ya samo dabara daya wadda yayi wa jiran safiya.

*****

Bayan dawowarsa sallar asuba kai tsaye ya wuce falon Binta yayi kwanciyarsa kan kujera. Tana falon zaune kan sallaya tana azkar, ganinsa ya sanya ta tashi fuu! Ta shige daki don dai ta tuna masa ita fa ta tsane shi.

Ya bi ta da kallo a saye, sai da ta shige daki sannan ya dauke kai cikin ransa yana cewa,

“Wannan yarinyar da kyar in an laluba kanta ba a tarar da shaidanu ba, wannan jin hauka’

Tsawon awa daya da rabi, tunda shida da rabi ta yi ya dinga kasa hankalinsa biyu, yana zuwa qofar dakinta ya kasa kunne ko zai jiyo ta tana wanka, yana komawa idan ya ji shiru har wannan tsawon awa daya da rabin sannan ya jiyo motsin takunta ta nufo qofa. Ya daka tsalle cikin dauke numfashi ya koma kujerarsa ya kwanta.

Ita ma babu abinda ya fito da ita sai ganin yana nan ko baya nan, tana fitowar kuwa suka hada ido, babu mai murmushi a cikinsu, ita tana ta faman fishi, shi kuma yana dubanta da fuska babu yabo babu fallasa. Ta yi iyakar qoqarinta na ta yi masa gaisuwar da babu gara babu dadin da take jifansa da ita wani lokacin ta kasa, sai ta dauke kai ta doshi daya dakin da zummar ta shiga bandakin ciki.

Tana dab da shigewa yayi gyaran murya ya ce,

“Ina kwana? Kar a ce na tsiro da gaba.”

Muryarta a dashe saboda bacin rai ta ce,

“Sha kuruminka, yanzu ban qi a ce mun mutu muna gabar ba, ni bana son jin muryarka.”

Yana dariyar da ke boye bacin ran da ya ji ya amsa mata,

“Ni da nake so mu tashi a aljanna tare ai ba zan so mu mutu cikin fushin ubangiji ba, ko ba kya son muryata zan cigaba da yin ta a muhallan da ya dace, sai na yi miki fatan rashin son jin ya zame miki kaffara”

Haushi ya qara kashe ta, ta yi tsaki a ciki ta wuce.

Sai da ya tabbatar ta shige wankan sannan ya fada dakin da ta kwana a guje ya hau neman wayarta, babu bata lokaci ya samu, cikin zafin nama ya tafi Call recorder ya dinga zabar hirarta da yaks yana turawa wayarsa, kafin ta fito tuni ya ajiye mata wayarta ya samfe benensa.

Yayi kwance kan katifa yana ta sauraron hirarsu daya bayan daya. Da yake ta kasa ya faro sai gashi bai jima ba ya ji hirar makircin jonawa kanta qanjamau da ta yi.

Kalamanta da yawa ba su yi masa dadi ba, don suna jaddada masa qiyayyar da take masa, amma  a wani gefen ya sami sanyin ran yaqinin cewa sharri ne zancen qanjamau kuma yanzu zai iya tunkarar likitan nasu yayi masa barazana yadda zai yi dabarar wanke su wajen Alhaji ba tare da an bata Binta a idonsu ba.

Karo na farko da Binta ta fara jin zata sa wuqar makirci ta raba Nabila da Mujahid, hankalinta ba zai kwanta ba in dai ba ganin Nabila ta yi a dakin aure ba, yadda qin Mujahid ke hura mata wuta a maqoshi haka fargabar kar Mujahid ya auro Nabila ke babbaka mata qirji.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 38Rigar Siliki 40 >>

1 thought on “Rigar Siliki 39”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×