Skip to content
Part 37 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

A wajen Binta wannan ba komai ba ne sai so, wanda take mafarkin kafin ya tabbata to a fara zare ranta.

Tana shiga mota Sani zai mayar da ita gida Mujahid ya same su, cikin nutsuwa ya cewa Sani,

‘Malam gidanta zaka mayar da ita.”

Ta kasa hadiyeawa cikin kuka ta tare shi,

“A mayar da ni gidanka na yi maka gadin gida kai kana nan?”

Yayi fuska ya dube ta ya ce,

“To ke da kike da ciwo in na zo gidan me zan miki?”

Sani bai san dawan garin ba sai ya shiga hirar,

‘Amma dai Yaya Mujahid ai mai ciwo shi ya fi buqatar me dauke masa kewa”

Ya sake yin fuska,

“Ba irin ciwonta ba”

“Ka ga Sani mu je..”

Ta fada cikin alamun zafin rai, shi ma ya bi ta da ko in kula,

“Eh ku je, Sani kai tsaye gidanta zaka kai ta”

Ya juya ya tafi ya basu guri.

Duk suka bishi da ido har suka daina ganinsa, Binta ta kawar da kai ta fara kuka, shi kuma Sani yayi ajiyar zuciya ya tashi motar yana cewa Binta,

“Anti Binta anya kina bayar da kularki akan Yaya Mujahid kuwa? Ya fa canja nesa ba kusa ba, akwai abubuwa da yawa wadanda ba dabi’unsa ba da yake yin su…”.

A tunzure Binta ta goge hawaye tana cewa,

“Sani ni na ce a aura min shi da har za’a aza min kula da shi? In an ga zai canja har canjin ya shafi rayuwarsa kawai a raba mu…”

Sani yayi shiru don yana ganin kamar wannan muhallin maganar ba nasa ba ne, bacin rai ne kawai ya sanya Binta ta sako shi ciki.

Yana jin ta tana ta kukanta, shi kuma dangantakar Mujahid da Nabila na ta zagaya masa a rai, har ya fara cankar ko ita ce matsalar Binta ne? ba tare da ya shirya ba ya ji ya tambaye ta,

“Amma me ke tsakanin Yaya Mujahid da Nabila?”.

mar cikin jin haushi ta ce,

“Ai da ka sani ka tambaye shi.”

Sani ya sake shiru, sai can da ya ga dai shirun ba amfanarsa zai yi ba ya tanka,

“Anti Binta tallafar rayuwa yadda ta samu fa shi ne kwanciyar hankalin ko wacce rai, a zaton kowa da aka ji ku shiru kuna zaune tare an dauka dukkanku kun dauki qaddara, bai kamata bisa dalilin qi ku dinga cutar da rayukanku ba…”

“Qi ba dalili ba ne ko.”

Ta tare shi cikin kukanta, da sauri ya amsa mata,

“Qi dalili ne, amma ai ke naku ba qin ba ne… kowa ya san Yaya Mujahid na son ki, ke ce dai ba a san abinda kike masa ba don ba a yarda qin ba ne…”

“To madalla”

Ta fada cikin alamun jin haushi da sallamawa, sannan ta gyara zama ta ce,

“Shikenan, lokacin da aka zo daki aka tarar da ni na rataye kaina ko kuma aka gan ni mace a gado na sha guba na mutu za’a yarda cewa qin sa nake”.

Dariya kawai Sani yayi wadda ta hadiye jin haushin kausasan maganganun da ake yabawa Yayansa. Ya ce,

‘Ki dai je ki yi nazari da kyau, ko lokaci daya ne ki samu ki kalli Yaya Mujahid a matsayin miji, zaki ji wani farin ciki, kuma zaki ji alfaharin ba dukkan mace ta yi sa’ar da kika yi ba, musamman in kin tsaya kin mori sa’ar ma’ana kin daina qoqarin saba masa ko cinye fuskarsa”.

Turo baki kawai ta yi, alamar ya gina bata shiga ba, ita sai yau ma din nan take jin ta qara bala’in tsanarsa.

Da haka kuma ya bar maganar, shi bai ga abinda Binta ta fi Yayansa ba da zata dinga faman wannan daga hancin ba.

Ya kai ta gidanta ya ajiye sannan yayi wucewarsa.

Har qarfe shadayan dare sannan Mujahid ya dawo gida, tun tana basar da dadewar tasa tana jin babu komai har ta fara jin tana taba mata rai, ba don komai ba sai don ya dade ne don Nabila.

Da qofarta tana rufe ne, amma sai ga ta ta bude qofar lokacin da taji dirin motarsa, duk don dokin ya zo ta tuhume shi son Nabila, da dadewa a sabgoginta.

Aka yi sa’a kuwa ya gwada murza qofar dakin don yana shakkun in bata garqame abarta ba, musamman dayake ya zolaye ta da cewa zai zo ta sa masa ciwonta.

Ya zaqulo ta a can dakin bacci ta qudunduna, ya shiga yaye mata bargo yana mita,

‘Ke wacce irin kasar macace da ba zaki dinga iya jiran miji ya dawo kafin ki kwanta ba? In da kin yi yanga ga miji ai yanzu bai kamata ki cigaba da yin ta ba…”

Ta tashi zaune cikin dacin rai,

“Saboda an halicce ni ne don ka dinga raba dare a waje ni kuma ina jiran dawowarka ko?”

Tana rufe baki ya amsa,

“To meye na zafin? Ni kuma da aka halicce ni don ki zo da mummunan ciwo na cigaba da aurenki fa?”

Ta fara qoqarin hawaye,

‘Au dama don ka riqe ni ka yi ta faman yi min gori ka ce zaka cigaba da aurena a haka?”

Ya amsa,

“Eh, ai kin san ni dai da gori, lokacin da kuka yi ta tsitse-tsotsenku da Yaks ma ai haka na dame ki da gorin, ina da riqe sirri, amma kuma ina da mita kin sani… tashi-tashi, kin sha magani?”

Sai Binta ta ji tana son fashewa da kuka gabadaya, wato shi wannan baudadden mutumin babu abinda ya shafe shi, duk rigimar da mutum zai rakito sai dai ta qare masa shi kadai, shi ba zai shiga ba?

Ta tashi zaune inda ya sa ta gaba suka je falo,

Ya zube a kujera yana cewa,

“Ai ba Matsala in mai qanjamau ta dafa wa mutum shayi ko? Don Allah taimake ni da kofi daya, yau tun safe ba mu gaisa da shi ba, gabadaya ji na nake a birkice…”.

Binta ba ta musa ba, don tana ganin lallai ma tana buqatar ta kebe musamman ta yi kuka ya ishe ta, kai tsaye ta fice ta tafi kicin. Ta jona kettle sannan ta nemi waje musamman ta fara kukanta, sai ga shi ya biyo ta, muryarsa kawai ta ji akanta,

“Ikon Allah, yanzu dan ki tanadi hawayenki ki barbada min a ruwan shayin kika zo kina dafawa kina kuka?”

Ta miqe da sauri tana goge hawayen,

“In kana tsoron mutuwa ba sai ka zo ka dafa abinka ba”.

Nan da nan yayi fuska ya tare ta,

“Wallahi ke zaki dafa, ai guga in bai ci arziqin komai ba yakamata ya ci na igiya, bai kamata ki cigaba da cinye min abinci kina kwanciya kawai ba, tunda kin zo da rudu dole ki dinga ba ni abinci”

Ta ja da baya tana qara bata fuska, ba don ta ji ciwon maganarsa ba sai don qorafin da ke yi mata yawo a maqoshi,

“Ai babu matsala, zan zama kukunka ne a lokacin da kake gidan ko? Lokacin ai kadan ne idan aka kwatantata da cewa dare zaka dinga rabawa kafin ka dawo, Nabila zata iya zama kukun naka a wunin ranar da daren da ka raba.”

Ya kanne dariya yana kawar da kai,

“Eh, ta wawushi kaso mai tsoka ne don ita ba ta tare da tararradi ko wanne iri, ba baqar magana da nuna qiyayya sannan babu fargabar zata tsaga yatsanta ta zuba min jinin a abinci…”

Da sauri ta bar kitchen gabadaya, ta fahimci in dai zata daka ta wannan gayen to lallai a komai sai kwabarta ta yi ruwa, shi ba ya gane komai na kowa sai na kansa, ba ya gane Nabila na sonsa sannan ba ya gane shi ma ya kamu da sonta kamar yadda ma yayi banza da fahimtar ko mace ba ta son mijinta to lallai tana kishinsa.

Dole shi ya kama aikin dafa shayinsa cikin dariya me sauti da gyada kai, daga qarshe ma da ya gaji da jin shauqi a filin zuciya kawai sai ya fito fili ya fada,

“Wannan muguwar rigar Silikin nawa, ta fi kowa qeta, ba ta sona, amma ba ta qaunar ta ga wani ya so ni, ko ya sa ni farin ciki.”

*****

Kwana uku abinda ke faruwa kenan daga gidan rasuwa zuwa gidansu, kai da riqar ta Mujahid a nuna kula da Nabila ta gawurta ma kawai sai yayi fuska ya ce Binta ta zauna tare da Nabila a gidansu tana debe mata kewa har a sadakar bakwai. Dama tana da hutun rashin lafiya a wajen aikinta.

A gaban mutane dangin Nabila da danginta ya fada, shi ne dolen da yayi wa Binta, don babu mai gane cewa don cin fuska Mujahid yayi mata wannan umarnin, tana motsi babu abinda za’a gani sai rashin kirkinta. Dole ta karbi tayin ta yi shirin karbar qaddarar da duk ta shirya afko mata a gadon baya.

A ranar ne kuma hankalin iyayenta ya fara kai wa kanta sosai, bayan sun koma gida da dare cikin juyayi Alhaji ke cewa Hajiya,

“Ba na son na karbi zugar zuciyata, amma na kasa dannewa, abinda nake lura kamar Mujahid bai riqe amanar da muka bashi ba, bai riqe kamar yadda ya ci min alwashi ba…”

Hajiya shanye nata zargin take tana hana kanta kallonsa, cikin sanyin jiki ta ce,

“Na sha zargin haka Alhaji, amma da na tuno halayyar Rigar Silikin Binta sai in ji nan da nan na yi wa zuciyata fada ta kori zargin…”

Ya sake magana cikin sanyin jiki,

“Kin san fa wani lokacin yawanci an fi cutar me yawan bori ko wanda ake zatawa tawaye, ba don ana hukunta su da laifinsu ba sai dan ana hukunta su da zaton su ne masu laifi.”

Hajiya ta ringima kai,

“Haka ne, amma duk da haka ina ji a raina Mujahid ba zai sauya kamar haka ba…”

Alhaji ya tare ta cike da alhini,

“Binta fa ta rame sosai, sannan ko a fuska ana karantar damuwarta, musamman lokacin rasuwar nan, wai me ke tsakanin Mujahid da Nabila ne? na fa kasa gane musu.”

Duk da Hajiya ta ji an tsikaro mata inda yake mata qaiqayi, amma sai ta ji kawai ta binne,

“Babu komai, ka san Nabila da son mutane, Mujahid kuma da kirki, wannan ne dalilin da ake ganin shaquwarsu ta wuce yadda yakamata ta zama.”

Alhaji yayi shiru tsayin wani lokaci, sannan ya nisa,

“Kin fahimci wani abu dangane da kwanciyarta a asibiti?”

Kallonsa kawai Hajiya ta yi, ta kasa magana.

Bai ja da nisa ba ya dora,

“Ina shakkar idan ba a boye mana wani abu dangane da halin da take ciki ba”

A razane Hajiya ta ce,

“Me yasa kake wannan zargin?”

Kai tsaye Alhaji ya amsa,

“Lokacin da likita ya zo sanar da ni abubuwan da suke damunta, ya zare wata takarda da ban yarda da ita ba, sannan kina ganin an jero mana tarin cutuka, amma tsakani da Allah wadanne magunguna kika ga sun ba ta? Sannan yadda Binta ta galabaita, in dai cutukan da suka zano mata a takarda ne ai ina jin da har zuwa yanzu tana kwance a gadon asibiti”

Abinda ya zo ran Hajiya shi ne zargin da Mujahid ke wa Yaks, amma abinda ya zo ran Alhaji kamar yadda ya furta shi ne,

“Akwai abubuwa da yawa da Mujahid ke boye mana, sannan Binta na taya shi”.

Hajiya ta kada kai,

“Ko dai akwai abubuwa da yawa da Binta ke boye mana? Ni na fi zarginta”

Alhaji ya dan ja fasali,

“To ba komai, ko ma meye zan binciko da kaina”

Da sauri Hajiya ta tare shi,

“Asibitin za ka?”

Ya amsa,

“Eh, in ta kama ai har can din za ni”

Sai Haijya ta ji tana goyon bayan qudurin nasa cikin ranta, don daurewa kawai ta ke amma, ramar Binta da alamun rashin kulawar Mujahid gareta ya fara damunta, don haka ta yi murna da jin za’a bincika wani abu dangane da su.

Ranar da aka yi sadakar bakwan Inna tun ma kafin Mujahid ya zo yayi mata izini ta hada kayanta ta koma gidanta, Nabila ma a ranar ta koma ainihin gidan mahaifinta cikin shirin zaman da tun tuni Kakarta ta so guje mata Allah bai yi ba. Dama tun kafin a yi sadakar bakwan matar Baban nata ta fara baza mata hali, duk wadanda suke qaunar Nabila sun hango mata zaman nan sun kuma tausaya mata yadda zata yi shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 36Rigar Siliki 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×