Skip to content
Part 32 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Tuni Binta ta kwashi haushi ta shige cikin gida, tana zuwa ta bude firji ta dauko ruwan sanyi ta fara daddaka. A haka Nabila ta shigo cikin sanyi jiki ta same ta, sai ta yi tsaye rungume da hannu alamar tana shakkun zama.

Binta ta dinga shan ruwan sanyi babu ji babu gani har sai da ta ji ta shanye sama da rabin takaicinta, sannan ta juyo cikin murmushin qarfin hali ta ce,

“A’a Nabila ki zauna mana”.

Hawaye ya zubo wa Nabila, tana rungume da hannu ta ce,

“Da kyar zan zauna Anti, tafiya zan yi”

Cikin sauri Binta ta ajiye kofin ruwa ta zo ta same ta, fuskarta a birkice ta ce,

“Me yasa zaki tafi, ya zuga ki ki tafi ko?”.

Nabila ta so ta rikice da wannan zargin, amma sai ta ga gara kawai ta dinga tafiya kan gaskiyarta ta daina damuwa da ko wanne zargi, tana murmushin qarfin hali ta ce,

‘Shi ba cewa yayi na tafi ba, cewa yayi na jira idan ya dawo ya mayar da ni gida.”

Binta ta saki baki tana bin Nabila da kallo zuciyarta na neman ta qwace mata, ta qalubalanci Nabila ne don ta fada mata abinda zai sanyaya mata rai dangane da abinda ba ta san sunansa ba wanda yake gwaguyar zuciyarta saboda dakatarwar da Mujahid yayi mata, sai ga shi kuma ta sake fada mata abinda ya fi wancan yi mata ciwo. Amma babu yadda ta iya haka ta yaqi fuskarta ta bige da murmushin yaqe ta ce mata,

“To shi ne zaki tafi? Ai karrama ki yayi Nabila, menene na aibu a nan?”.

Nabila ta fara magana rai a bace,

“Ni ba wannan ne dalilin tafiyata ba, kawai dai ba na son zuwa wajen da babu hadin kai ne… ban san haka kuke zaune ba Anti Binta sam ma da ba zan dauko shawarata na ce zan kawo miki ba…”

“To zauna sai mu yi maganar.”

Binta ta daure ta fada cikin tausasawa.

Nabila ta girgiza kai ta qi zama. Yanzu ta fara hawaye,

“Ni ba zan zauna ba.”

Binta tana murmushin yaqe,

“In na ce kin fi son Mujahid a kaina kina musawa, amma ko yadda kika same mu ni a rame shi ya shirya qiba ai yakamata ki zauna ki jajanta min wannan kurkukun da aka wurgo ni”

Nabila ta girgiza kai ta doshi hanyar fita,

‘Tunda haka zaki mayar da maganar bari na tafin kawai”.

Cikin dariya Binta ta sha gabanta ta ja hannunta suka koma suka zauna.

Binta tana ta nuna babu komai ta miqe tana cewa,

“Ki dakata bari na ciyar da mu sai mu zauna mu yi magana, duk tuhumar da kike min ki gabatar da ita zan yi miki bayani iyakar gaskiyata.”

Ba haka Nabila ta so ba, amma ba ta yi musu ba.

Duk wani motsi da Binta ta ke a idon Nabila yake, hawayen zuci kawai ta ke wanda ba kowa take wa ba sai masoyinta da ya fada mummunan hannu, hannun da ba’a san darajarsa ba, hannun da ba zai ba taba sanya shi dariya ba. Ko da wannan takaicin aka bar ta ya ishe ta azabar rayuwa.

Har Kitchen ta bi Binta suna hira suna aikinsu tare, a nan ma ta gane cewa an yi girki, amma babu kwanon Mujahid, nan ma sai da ta sunne kai ta zubar da hawaye.

Binta ta sake wanka ta shirya, amma babu alamun kwalliyar amare hasalima ban da mai da hoda babu abinda ta muttsuka, ta dauko wasu kaya da ko ita Nabila ba zata sanya su a gida a matsayin kwalliya ba, bare kuma a ce kwalliya musamman ta amarya.

Kafin su gama komai an yi la’asar, ga damuwoyi sun gama dabaibaye Nabila, a gajiye ta ce wa Binta,

“Anti mu gama na tafi gida.”

Binta ta dan zuba mata ido,

“Da gaske kin fasa neman shawarar?”

Nabila ta yi fuska,

“Gaskiya na fasa”.

Binta ta qi damuwa,

“Ni na sami wannan koma bayan a wajenki Nabila?”

Nabila ta sake bata rai,

“Wannan ba maganar dangantaka tsakanin mutum da mutum ba ne, magana ce ce ta tsakanin mutum da Ubangiji, ni da na zo neman shawararki da makomata a kan wata bauta wato aure, in ba ki mutunta naki ba ta yaya zan sa rai zaki ba ni damar na mutunta nawa?”

Binta ta dinga gyada kai da alamun shanye kuka,

“Na yarda da ke, amma duk da haka ba zan kasa karambanin ba ki shawara ba, shawarar ita ce kar ki sake ki yi aure huce haushi ko kuma don ki farantawa wani rai, lallai ki yi qoqari ki auri wanda kike so”

Nabila ta ji tamkar Binta ta kirba mata naushi a maqoshi, kodayake Binta ba ta san zuciyarta ba, ba ta san abinda ta ke so ba shiyasa take mata tayin ta aura, cikin rashin hayyaci ta ke bin Binta da kallo amma ta ke yakice zuciyarta take sauraronta, Binta na magana cikin yanayin gaskiya da kuka,

“Babu azabar da ta fi zama da abinda ba ka so, ba na son Mujahid ladan da ake samu a aure yana nema ya tsere min don ba zan iya abinda ake yi a sami ladan ba, ko zuciyata ba irin taki ba ce lallai ina ba ki shawarar kar ki sake ki auri abinda ba kya so, don datsewa kai rayuwa ne… cutar da numfashi ne…”

Ita Binta raunin murya take da hawaye kawai, sai ga Nabila da bare baki ta saki kuka, ta kasa daurewa ta riqe shi, tausayin kanta da Mujahid yana neman ya qarar da numfashinta, ba a son masoyinta, ba za’a iya kyautata masa yayi rayuwar farin ciki ba, sannan gashi ita ma ana yi mata albishir da rayuwar baqin ciki irin wannan idan ta auri wani ba shi ba? Ta dinga kuka har sai da Binta ta fahimci lallai kukan da take ya wuce na jajanta mata halin da ta ke ciki, nata ne na musamman.

Binta ta qarqare da ce mata,

‘Ki je ki yi tunani a kai”

Nabila ta share hawaye tana duban Binta,

“Anti Binta kin san irin son da yaya Mujahid yake miki kuwa? In kin yi asararsa ba zaki taba samun kamarsa ba, masu yin irinsa zasu qirgu a filin duniyar nan …”

Cikin kuka Binta ta ce,

“To ni ba na sonsa Nabila, ba na qaunarsa me yasa ni ba a gasqata abinda nake sai shi, shi yana so ni ina qi, nasa kawai ake kallo ake wa rayuwata hisabi da shi…”.

Nabila ta tare ta cikin dauriya,

‘Don ko yaushe abu mai kyau yana danne mara kyau ne, sannan an riga an baro kari tun ran tubani Anti, yanzu ku ma’aurata ne…”

Ita ma Bintan ta tare ta,

“Duk ku kuka san wadannan darajojin da amfaninsu, ni qiyayyata kawai na sani..”

Nabila ta sake kecewa da kuka. In Binta ta ce tana qin Mujahid zuciyarta neman kekkecewa ta ke, dole ta shirya ta bar gidan.

Tana ta faman hawaye ta janyo jakarta ta je kuma ta zare wayarta daga caji.

Binta ta fahimce ta, don haka ta yi niyyar fito da abinda ke ranta,

“Da Mujahid ya biye ta ni da duk ba mu sami kanmu a wannan halin ba, yanzu ma abu ne mai sauqi ya sallame ni ku auri juna, kin fini sanin darajar so, ke ce zaki alkinta shi, sannan duk da cewa shi ni yake so amma ke yake mutuntawa don yana ganin ke kika cancanci mutuntuwar…”

Nabila ta zaro idanuwa tamkar zasu fado waje cikin dafe qirji.

Binta ta kada kafada alamar ko in kula ta cigaba da magana,

“Mujahid ne ya ba ki labarin irin qaunar da yake min ko? Amma ya fada miki cewa tun da na zo gidan nan ko sannu ba ta taba hada ni da shi ba sai jiyan nan, jiyan ma ni na karya gabar na yi magana da shi? Babu komai tsakanina da shi sai baqar magana daga jiya zuwa yau, ai a gabanki ya ce ba don kin zo ba zan kwana a banki… ciwo yake ji in na ce ba na sonsa, to qarya kuke so na dinga yi masa ina cewa ina sonsa?”.

Yanzu Nabila ta fara murmushin da ba ta san ma ko na meye ba, ta kuma saba jakarta ta doshi qofar falo tana cewa,

“Ki dai fara laluba zuciyarki Anti ki gani kina son nasa ko ba kya sonsa, yanzu ne na fara gane ashe ma ke so ne ya haukata ki… na bar ki lafiya, amma kar ki qara saka ran ganina a gidanki nan kusa”

Binta na kiran Nabila amma ba ta saurare ta ba ta fice, ta biyo bayanta hankali a tashe tana cewa,

‘Motar haya zaki shiga, ba zaki jira ya dawo ya kai ki ba, ba zaki jira direban ba?”

Amma sam Nabila ta qi kula da ita.

*****

Qarfe biyar Mujahid ya shigo gida, tun kafin ya hau sama ya dinga kasa kunne yana so ya jiyo sautin Nabila, amma bai yi katarin ji ba, ya maze ya haye wajensa yayi wanka sannan ya sakko qasa, cikin shirin ko ta kwana ya tsaya qofar  dakin Binta ya hau jero sunan Nabila.

Binta na zaune tana kallo Tb zuciyarta ta dinga tafasa, wasu hawaye masu yaji suka dinga cika mata ido, ta yi ta qoqarin ta share shi ta manta da batunsa ta kasa, sai ga shi ta janyo qaramin mayafi ta yafa ta fito ta same shi tana ta faman huci,

Ya kalle ta fuska sake babu fara’a babu fishi, ita kuma ta gintse murya ta ce,

“Ta tafi”

Da sauri ya juya yana cewa,

“Oh! Yi haquri rashin sani ne”.

Haushi ya qara cika ta, a tunzure ta ce,

“Na bata saqo ta fada maka, amma yanzu na ga yakamata na sanar da kai ma da kaina…”

Ya tare ta cikin basarwa,

“Kar ki damu. Zan yi mata waya yanzu, zata sanar da ni ba sai kin wahalar da kanki ba…”

“Akwai wata wahala dama da zata iya shan gaban wadda na ke ciki yanzu, zama da abinda ba na so, ai duk wahalar da ba wannan ba ‘yar rakiya ce…”

Ya girgije haushi ya ce,

“Gaskiya ne, to bari na tsaya na ji ‘yar rakiya… saqon me kika ba ta?”.

Kai tsaye ta amsa,

“Na ce mata ta taya ni roqonka ne ka sake ni ka aure ta, ita ta san darajar so ta kuma san darajarka, sannan kai da ba ita kake so ba, amma ita kake  iya mutuntawa, gaskiya kun fi dacewa da juna taraiyyarku zata samar da farin ciki”

Mujahid ya juyo ya zuba mata ido, tamkar daga fuskarta yake son hango zuciyarta, da gaske take ko da wasa, kuma menene maqusudi, kishi ko qinsa?

Bacin ran fuskarta ya sa ya kasa fahimtarta, don haka yayi magana a sanyaye,

‘Ke menene abinda nake miki na rashin mutuntuwar? Shin akwai mutumin da na mutunta sama da ke a yanzu, ai qarshen mutuntuwa bata wuce son mutum saboda Allah ba, ba don halinsa ba kuma ba don siffarsa ba, duk karramawar da zan miki bayan wannan zata bi duk da kuwa kin fito kin fada min kin qara cewa ba kya sona…”

Ta fara hawaye,

“Kai da ita ba kwa son jin wannan kalmar, ita ce ba na sonka, ban san me yasa kuke son sai na yi qarya ba… ban san me yasa kuma kuke take gaskiya kuke hukunta ni akan ta ba…”

Mujahid ya runtse ido ya sake budewa, shi kadai ya san ciwon da yake ji in Binta na cewa ba ta sonsa, amma ya san gaskiyar kenan, don haka ya danne da yin maganar da bai san ma ta fito ba,

“Ni da me na hukunta ki? Nabila da me ta hukunta ki?”.

“Ka kawo ni kurkukun gidanka ka ajiye kuma kana gaba da ni…”

Ya tare ta da iyakar tasa gaskiyar,

“Don na san ko me na yi ba birge ki zan yi ba, in zan kwanta ki bi ta kaina ba zaki so ni ba, ba zan sami ko arziqin ‘yan uwantaka ki yi min magana mai dadi ko girmamawa ba, duk da wannan sanin nawa Binta sai na cigaba da bin ki kamar kare ina miki haushi kina kora?”

Cikin hawaye ta ce,

“Shi ne ni ka riqe ni a matsayin karyar kana kullewa a gida kana harara don kana ajiye min abinci?”

Shi ma ya amsa,

“Eh, dan iyakar abinda zan iya samu kenan, ni ko wannan ya ishe ni, ai ba hadama nake a son da nake miki ba, shekarata nawa a cikin gidanku kina gilmawa a idona? Hannunki ban taba riqewa ba kuma ban fasa sonki ba, saboda haka wannan zaman ma kina muhallinki ina nawa kalas!”

Yanzu ta fara yanke qauna, ta fara goge hawayenta tana dubansa,

“Iyakar wannan ne matakinka?”

Ya wurga hannu,

‘Ba ni da zabi, amma duk abinda kika zaba ai gwada tawa sa’ar na ke, ni ba na daga hankali sai na ga wani ya daga”.

“Shikenan, ka ba ni lokaci zan daga nawa hankali, sai ka taya ni ka daga naka.”

“A’a sai dai na taya ki daga naki, amma ni nawa hankalin ba ya tashi a buqatun wasu.”

Kawai sai ta yi qwafa ta juya daki cikin hanzari,

Ya jefe ta da kalmar,

“Kuma muna tare, au ba ki fada min da me Nabila ta ke hukunta ki ba”.

Ta juyo cikin gadara ta ce,

“In na ce ba na sonka sai hankalinta ya tashi, tana baqin cikin in ce ba na son masoyinta, malam ka raba mana hankali da fahimta, ban ga dalilin da a kanka ra’ayina ba zai zama nata ba, sannan ban ga dalilin wasa da hankalin kuna son juna ba zaku aura ba”

Ya ji bari ya tura mata haushi tunda zasu rabu,

“Dalilin shi ne don ba zamu yi abinda ke ce kika zaba ba, idan da rabon mu auri juna zamu aura a lokacin da mu muka so ba ke kika so ba”.

Ai kuwa ta shaqa din, don ta juya harshe ta kasa samo amsar da zata rama da ita.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 31Rigar Siliki 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.