Skip to content
Part 33 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

A daren ya kira Nabila, sai ya ji ta daga wayar tana kuka, karo na farko da ya ji zuciyarsa ta cunkushe tana son dauko sabon tunani akan wannan salihar yarinyar.

Duk da ya san abinda ke akwai amma sai ya binne kamar bai sani ba, cikin kulawa ya ce mata,

“Nabila me ya faru kike kuka?”

Muryarta ta qara rauni,

‘Don Allah Yaya Muajhid ka janye zumuncin da ke tsakanina da kai, ba wai ka datse shi ba, ka rage masa qarfi nake nufi”

Kai tsaye ya ce mata,

“Don dukkanmu Binta muke wa numfashi ko? Sai abinda take so zamu yi, in ba mu yi ba mun saba doka.”

Tana kuka.

“Ba haka ba ne Yaya Mujahid, ni dai ina ganin hakan zai fiye mana alkhairi”

Cikin gwasalewa ya ce,

‘Eh lallai”

Zata yi magana ya tare ta,

“Kin ga saqon da ta baki ta ba ni, duk maganganun da kuka yi ta dunqule min su a ‘yan kalmomi, ta fada min ba kya so ta ce bata sona, shi ne abinda yake sa ki kuka yanzu? Kina nuna damuwa da abinda ya dame ni kamar haka kike maganar na ragewa wa zumuncinmu qarfi? Ni kike so na wulaqantar da hallacinki Allah ya dora Binta a kaina, ko kuma ni kike son kawai ki ga ba na farin ciki babu ke babu Binta?”

Da ta ji shi ma yana neman hada mata wani zafin sai ta ce,

‘Duk mu bar wannan maganar, zan yi aure ne, don Allah ka zaba min cikin mutum biyun nan wa zan aura? Nazir ko Suraj, duk ka san labarinsu a duniyata… Na fasa auren Yaks.”

Nan da nan ya tare ta cikin rashin daukar maganar da Muhimmanci,

“Ni duk cikinsu ban ga mijin aure ba, Nazir dan duniya ne, Suraj kuma kasuwancin da yawon qasashensa ba zai sa ya ba ki kulawar da nake son mijinki ya baki ba, ajiye ki zai yi cikin danginsa cikin babban gidansu ya bar miki uwarsa tana qirga miki nama a tukunya, ba wanda zaki aura.”

Ya qare maganarsa cikin bata murya.

Nan da nan ta ce,

“To ajiye waya sai da safe”.

“Zan ajiye, amma kar ki sake ki yanke wani hukunci ba tare da sanina ba”

****

Binta ta fara aiki, ta fara da salon tashin hankalin da ta so yi wa Mujahid, ranar farkon fitarta ta casa kwalliya kamar mai zuwa gasar sarauniyar kyau, ta cona daurin dankwali qarfe bakwai da rabi na safe ta hau har benen Mujahid ta qwanqwasa masa qofa.

Yana daga bandaki ya jiyo wani hadadden kamshin turarenta da ya sanya shi bugun zuciya, tamkar yadda take bugun qofar dakinsa. Wanka yake amma sai da ya ji gumi na qara masa wani wankan kan wanda yake, kawai sai ya sakarwa kansa shaya tana ta dimarsa har lokacin da ya dena jiyo sautin bugun qofarta amma bai ji saukarta qasa ba.

Bayan ya fito ya dade tsaye a tsakiyar dakinsa yana jinyar zuciyarsa, yana dafe da qirjinsa yayi magana a fili,

“Wannan shashashar yarinyar in ba a yi wasa zata iya kisa.”

Can ya ji motsin jan qafarta a qofar daki tamkar tana tuna masa cewa tana fa tsaye, yayi saurin zira jallabiya yayi fuska ya bude qofar ya leqo, sai ya gan ta tamkar yadda ya zata, ta ci ado ko ranar bikinta albarka, kai ba ma duk amare ba. Ya dinga daurewa yana nuna ba komai, muryarsa cunkushe ya ce mata,

“Qalau?”.

Ita ma ta yi fuska,

“Ai kuwa jiya na tuna maka yau zan fara fita aiki”.

Ya dan kama kai kamar gaske,

‘Ayya sai yanzu na tuna”

Ta bishi da kallo yana qoqarin komawa cikin dakin, ta dan daga murya,

“Zan makara fa.”

Ya amsa ba tare da ya juyo ba,

“Mukulli zan dauko na yi maza na kaiki, ni da ban makara ba har na dawo na shirya”.

Ta kebe baki tana shan bin sa da kallo, don ba haka ta so ba, ta so ta ga ko da motsin jin ciwon fitarta da kwalliyarta a fuskarsa, amma dan tsabar makirci shi ne har da rawar jikin kai ta aiki sannan ya dawo ya kai kansa.

Suka yi tafiyar kurame tamkar wancan lokacin, ya dinga figar motar tamkar mai tashi sama, cikin minti goma ya kai ta ya dire. Sai a lokacin magana ta shiga tsakaninsu, inda ta sunkuya cikin yanga da yamutsa fuska, abin gwanin bayar da dariya ta ce masa,

“Ka ba ni lambarka, in lokacin tashi yayi zan kira ka”.

Yayi fuska ya karanto mata a nutse dan ya nuna mata in dai haushi take so ta bashi fa tana da aiki.

Bai jira wata cewar tata ba cikin hanzari ya janye motarsa.

Sati guda abinda ke faruwa kenan, ta doka sammako ta ci kwalliya ta tafi aiki, ba ta tashi sai bayan magariba, kullum yana kwance a gida zata kira shi ya ya je ya dauko ta, sosai dai ya zama shi ne matar ita ce mijin fiye ma da yadda ya tsani matarsa ta yi aiki ta zama.

Wannan dabi’ar ta fi wahalar da Mujahid sama da komai, ya saqa hanyar da zai kubuta ya fi sau shurin masaqi ya rasa mai bullewa, gashi kuma kullum abun nata qara ta’azzara yake. Don yanzu ma ta daina kiransa ya dauko ta, qiri-qiri sai ta wuce wata unguwar, sai tara na dare ta kira shi ta ce tana can ya je ya dauko ta. Ba ta cika zuwa gidansu ba saboda ta san nan ido a kanta yake, amma musamman gidansu Yaks, a sati ta kan je sau biyu sau uku.

Rannan shi da kansa ya tsaya gaban madubi a Bandakin ofishinsu yake tambayar dodonsa,

“Wai kai Mujahid ne ka zama waina a hannun wacca Rigar Silikin? Ina azancinka ya ke? Lallai in ba ka sa kakkausan hannunka ka yakito ta ba to tana dab da ta zame ta bar ka tsirara.”

A washegarin wannan ranar ma ta ci kwalliyarta ya kai ta Banki ya dire, da gangan ya dinga jan ta da magana tana gasa masa baqar magana har mai aukuwa ta auku, inda babu zato babu tsammani wani gayen dan boko mai tuntu a ka ya zo yana hau daukarta hoto a wayarsa, cikin wata irin kawa ta kamar dama ya san ta,

“Wow! Look at me Baby… yi murmushi… gaskiya yau kin fi kullum haduwa”.

Ta shiga mawuyacin hali na duban mujahid ta dubi yaron, kafin ta tantance komai har ya gama daukarta hoto ya kurda ta tsakanin motocin dake jere, yana fadin,

“Bari na shiga ciki, in kin shigo ina reception”.

Sai ta ji kayan cikinta gabadaya sun hargitsa suna son fitowa ta bakinta, ta dubi Mujahid da yayi saqare cikin tunani da alamar damuwa ya qurawa satiyarin hannunsa ido, bakinta na rawa ta ce,

“Wallahi ban san shi ba, ban ma taba ganinsa ba sai yau”.

Mujahid ya bata fuska tamkar bai taba dariya ba, ya dago ya dube ta ya ce,

“Kin ji na yi qorafi ko na tambaye ki? Ni aurena kawai na yi sha’awar in matsa miki ki yi amma ba bin Allah ba, wannan shi yake shiryar da wanda ya so”.

Bai bata damar ta ce wani abu ba ya figi motarsa.

Ta dora hannu aka amma babu damar ta kurma ihu a zo kallon mahaukaciya, cikin zafin nama ta doshi cikin Bankin domin ta sami wannan gayen ta ji ta inda aka bi aka haihu a ragaya, in bai yi wasa ba sai ta hada shi da ‘yansanda.

Sai dai har ta gama karade bankin ba ta sanya shi a idonta ba, duk wanda ta tambaya kuma zai ce babu wani mai kama da shi da ya shigo.

A ranar ta wuni cikin tsananin tasku, ranar kafin magariba ta hada nata I nata ta doshi gida, ko kiran Mujahid din ba ta yi ba, don ba ta san da fuskar da zata kalle shi ba

Aka shafe sati tana fama da wannan kunyar da tashin hankalin, sai dai ta rage kwalliya, hasalima ko ta yi kwalliyar ta tafi, Mujahid na dire ta yana tafiya zata bata kwalliyar, dama don ta baqanta masa rai take komai.

Ranar juma’a tana isa office aka ba ta sakon enbelop dauke da qunshin katunan saqonnin soyayya. Da aka suffata mata wanda ya kawo katin sai ta ga kammani mai daukarta hoto, nan ma fa ta qara shiga damuwa.

Ranar sha biyu ma a gidanta ta yi mata, ta zauna ta ci kukanta, a fili ta dinga gayawa Allah,

“Allah ka gani, mutumin nan ya zagaye ni ya shiga haqqina, neman rabuwa da shi nake ba neman sabonka ba Allah kar ka hukunta ni da abinda ban ji ba ban gani ba”.

Ranar lahadi bayan ya dawo masallaci sallar asuba ya shiga qwanqwasa mata qofa, ta farko daga baccin da ya fara sure ta gabanta na mummunan faduwa saboda irin haka ba ta taba faruwa da su ba, ta fara qissima abinda ya faru kala-kala, musamman ta bangaren da ya shafi iyayenta. Jiyan nan Hajiya ta fara kawo mata ziyara gidanta, kuma a fakaice ta yi mata wankin babban bargo dandagane da yadda take gudanar da aurenta, qiri-qiri Hajiya ta sanyawa idonta toka ta ce, lallai tana cutar da Mujahid, cikin kuka Binta ta shiga shafa kashin wuya dana hannaye tana cewa,

“Duk yadda na bushe din nan ba ma shi yake cutar da ni ba ni nake cutar da shi Hajiya?”

Hajiya ta ce,

“Dama can a bushenki kike kuma kika zo kika sa cuta a gaba, sannan ga kika jajibowa kanki wani tsinannen aiki da ba ya farantawa kowa naki rai, mijinki ba ya murna ni ba na murna, Alhajin ma da ya ji tausayinki da farko ya amince da aikin, samun labarin cewa sam ba ki da lokacin gidanki da maigidanki ya sanya ya ke kushe abin, ko Mujahid din bai fada miki cewa wancan Satin Alhajin yayi miki zuwan bazata qarfe tara ma dare ya samu sai shi Mujahid kadai a gidan ba ne? wanne banzan aiki ne wannan? Haka ya je gida yana mitar abun”.

Binta dai ta yi tsuru-tsuru tana jin bambamin hajiya, sai ta fara jin to in haka ne ita komai ma bai karbe ta ba, duk abinda ta yi domin quntatawa Mujahid kanta yake dawowa, ta hana kanta hutu tana doka sammako ta fice ba zata sami kanta ba sai dare, kullum ba hutu, ga wani maqiyin Allah can yana son matsawa rayuwarta da qoqarin bata mata suna, nan kuma ashe Iyayenta na can suna shan ciwon abinda ta ke yi alhalin ita Mujahid take son ya ji ciwo shi kuma yana nuna babu komai.

Jiyan dai haka Hajiya ta gama fadace-fadacenta, ta tafi, kafin tafiyarta komai taga Binta ta yi sai ta ce ai bata iya ba, hatta da gyaran falo, wanda dalilinsa ta leqa dakunan bacci, nan ma ta shiga kushewa kan cewa ai ko gyaran gado ba ta iya ba, sannan ta lura wani dakin baccin ma ko rabarsa ba a yi sosai, nan ma ta yi fadan cewa, sabunta wajen kwanciya sabunta farin ciki ne da sanya doki, bai kamata ta nanar da su a waje daya ba.

Duk dai Binta na bin ta da Amin, tana hadiye qwalla, hajiya ba ta san dawan garin ba, ba ta ma san ko qofar dakinta Mujahid bai taba takowa ba bare dakin baccinta, ba ta san Mujahid azzalumi ba ne, shi buqatarsa bata wuce mayar da mace Baiwar baqin ciki ba, ba ta san sai an sabunta zuciya ake iya sabunta dakin kwana ba.

Ta dai lallaba ta ta tafi suka rabu kowa ransa babu dadi, yanzu da ta ji bugun qofa sai ta yi zaton ko ma Hajiyar ta je ta dauko mata Alhaji ne?

Hantar cikinta na faman kadawa tayi saurin dirowa daga gado ta yayimi hijabin sallarta ta saka ta fita,

Angonta ta gani sanye da jallabiya yana riqe da carbi, suka dubi juna sosai, Binta ta kawar da kai tana neman ta dan rikice, daga ita har zuciyarta,

Shi ba tare da ya dauke ido daga kanta ba ya ce,

“An tashi lafiya?”

Ta motsa baki kawai, ta kuma shanye amsawar.

Bai damu ba ya fada mata saqonsa,

“Yau zan je  boto, in zaki je ki shirya mu je”

Ta dan yi dum! Sannan ta juyar da kai ta ce,

“Ba zani ba”.

Ya dan jinkirta kamar zai yi mata dole, sai kuma ya kada kai ya juya ya tafi abinsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 32Rigar Siliki 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.