Skip to content
Part 46 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Ya maze ya tunkari dakin amarya Binta, sai dai bai bar fuskarsa da alamar wasa ko damar karbar raini ba.

Ya sameta kamar da rana tana kance a gado, sabanin dazu yanzu ba kuka take ba, kuma lullube take da bargo, da alamu tana fama da zazzabi.

Yana ganin haka yayi saurin ficewa daga dakin ba tare da ya ce mata komai ba, ya je ya laluba Kitchen babu abinci, ya jona Kettle ya fice ya siyo Kaji ya dawo, lokacin ruwansa ya tafasa ya juye a flask, haka ma naman ya juye a plate ya kwasa duk ya kai dakin da Binta ke kwance har lokacin bata ko motsa ba, sai dai tana hawaye.

Bai tanka mata ba sai da yayi nisa da cin abincinsa sannan yayi magana cikin rarrashi karon farko tun bayan aurensu,

“Don Allah Binta tashi ki wanke baki ki zo mu ci abinci, zo ki taya ni shan shayi ko zai qara zaqi?”   Ta yi qoqarin ta yi masa banza amma wutar da ke huruwa a qirjinta ya sa ta yi saurin rantsewa,

“Kar ka wahalar da kanka da wani maqe murya ko kyau ma bai maka ba, wallahi tallahi ba zan ci ba.”

Ya kada kai,

“Na gamsu, amma dai in na zo da magana zaki saurare ni ko? Wannan damar ta rashin sauraro ita ta kai mu halin da mu ke ciki yanzu, wallahi komai ya faru da ni ko ya faru da ke duk ke kike janyo mana, ba kya ba ni damar na nuna miki soyayyata ba kya ba ni damar in kin yi fushi na rarrashe ki, kin hana ni shiga zuciyarki ko kadan bare na sami damar hangenki lokacin da zaki yi abinda zai janyo mana hukunci ni da ke…”

Ta tare shi cikin kuka,

“Amma dai ka san ba a halicce ni da kunne ko zuciyar da zasu saurare ka ba ko?”

Nan da nan ya amsa mata,

“Na sani, ke ce ba ki san in kin qi saurarona ke ma zaki cutu ba, ke ce ba ki san in baki zaba wa kanki rayuwa ba za’a sami wani daga waje ya zaba miki ba, ke ce ba ki san cewa in an halicce ni da sonki ba lallai ya zamana an halicce ni da liqewa in ta yi miki biyayya ba, ke ce ba ki san cewa zuciya na qara son mai kyautatawa ba, ke ce baki san cewa komai na duniya ana yin sa tsaka-tsaki ba, komai ba ki sani ba Binta yaya kuwa wadanda suka sani ba zasu zaba miki abinda suka sani ba? Komai ba ki sani ba Binta, sai abu daya kika sani shi ne ba’a halicce ki da kunne ko zuciyar da zaki saurare ni ba, in haka ne wanene jahili, ni ko ke?

Ko kadan zuciyarta ba ta samu sarari da maganganunsa ba, sai ma cushewa da take qara yi, kawai a wani qasurgumin dan ta’adda take kallonsa, mara tausayin rai mara tausayin abokin mu’amala, wanda bai san kowa ba sai kansa. Cikin tsananta fushinta ta tare shi da cewa,

“Ni qin zama da kai da nake duk ya fi wadannan abubuwan da ka lissafo nauyi a sikeli, in dai kana tsoron haduwarka da Allah to ka sallame ni ka riqe wadda ke sonka kake son ta, don ni riqe ni zalunci ne…”

Ya fara dariyar yake,

“Ina tsoron haduwa da Allah, amma bisa nasa Umarnin ba bisa naki ba, sannan umarninsa nake bi nake cigaba da riqe ki da haquri da ke bisa adalci da kuma tsammanin rahmarsa wadda zai sakawa maza da matan da suka yi haquri da munanan halayen abokan zamansu.”

Wannan karon ta ji matuqar raunin zuciya, don bayaninsa ya tuna mata in an saka masa bisa nasa aikin kirkin da ya ambata, ita ma za’a saka mata da daidai wanda ta aikata, sai ta kece da kuka cikin tsananin qunan zuciya, qunan da take ji ya fi qiyayyar da ta yi wa Mujahid farkon aura mata shi.

Ya tsaya kawai yana kallonta tana ta faman kukanta, sai ya ji bai ji ciwon da ya ji a zuciyarsa irin kukan Nabila ba, wannan shi ne abinda yake wa Binta gudu, wato ta raunata zuciyarsa me sonta ta saba da damuwarta, yadda har in ta shiga wani hali ba zai damu ba, Manzon Allah (S.A.W) yayi gaskiya, zuciya tana son mai kyautata mata, tana kuma qin mai munana mata. Ba yana nufin sonta yayi rauni a zuciyarsa ba, yana nufin ta kangara shi da kawai ya saba sai dai ya sabe ta da rigima ko baqar magana har kuma in ya gan ta cikin damuwa ba ya jin komai.

Ya jima yana kallonta sannan ya nisa ya ce,

“To yanzu zaki saurari na zo miki da matsayin da kike da shi a zuciyata da kuma wanda shi ne haqiqanina ko kuma kin fi so ki cigaba da ganina a baibai?”

Cikin fusata ta tare shi,

“Ni ko a yaya na same ka duk hagu ne, ba ni da matsala da yadda zaka kasance, matsalata ita ce kasancewa da kai.”

Tana direwa ya miqe yana dariya ya ce mata,

‘Madalla, za mu kasance a haka har lokacin da kika ji buqatar canji, ki sanar da ni”.

Bai sake bi ta kanta ba ya fice abinsa ya kuma haye sama kai tsaye ya shige wanka. 

****

Da safe qarfe tara don kansa ya shirya ya tafi gidansu Binta, don ya san duk inda suke yanzu hankalinsu na kansa, zasu yi ta qaddara masa bijirewa bisa hukuncin da suka yanke qila kuma hankalinsu ya kasa kwanciya, don haka ya hanzarta zuwa ya faranta musu rai da fada musu ya karbi karramawarsu.

Ilai kuwa ya same su hankali a tashe, Alhaji har ya gayyato mahaifin Mujahid din don taya shi rarrashi ko yin dole in ta kama, bai jima da zuwa gidan ba Mujahid ya shiga.

Da fara’arsa kamar yadda ya saba ya dinga gaisawa da Mutane, ya tarar ma ashe babarsa tun jiya ta zo a wajenta ya jima kafin ya je wajensu Alhaji.

Ta dinga shi masa albarka da ta ji qudurinsa har tana qarawa da yi masa alqawarin,

“In ka ji takura na rashin kudaden da zaka yi mata gyaran saman ka zo na sai da gonata ta kan hayi na ba ka kudin.”

Ya ji wani dadi ya rufe shi saboda yadda Iyayensa ke jin dadin biyayyarsa har ma Innarsa duk son kudinta tana jin zata iya sadaukar masa da gona.

Ya gode mata sosai sannan ya ce ba sai ta sayar da gonar ba, ko da rance ne zai iya qarasawa.

Ta ji dadi sosai ta dinga sa masa albarka har ya fice yana jiyo ta.

Yana zuwa wajen Hajiya cikin ajiyar zuciya ta ce,

“Mujahid ka sa mu a fargaba, jiya Babanka bai yi bacci ba, ya damu da ganin ka fitar da shi kunya.”

Ita ma cikin jin dadi ya ce mata,

“Ku gafarce ni Hajiya, na boye kaina ne don na yi jarumtar riqe kaina na yi abinda zaku yi murna ku sa min albarka, in sha Allah ba zan taba zama abinda zaku yi tir ba…”.

Hajiya ta ji tana son hawaye, cikin raunin murya ta ce,

“Abinda Binta ta kasa ganewa kenan, iyayenka ba zasu taba cutar da kai ba, da tana da hankali Nabila ta ishe ta Ishara, ba ta san wa za’a aura mata ba, amma da take kukan hakan damuwarta ita ce, kar a aura mata wanda bai cancanta ba saboda rashin kyan hali.”

Yana murmushin yaqe da tuno yadda ta kulle masa qofa yau har bai ma sami dama yi mata sallama ba ya amsa,

“Tana ganewa mana Hajiya, gashi ta haqura tana zama da ni bisa alfarmarku?”.

Hajiya ta kebe baki ta ce,

“Zaman na je-ka-nayi-ka?”

Ya kada kai yana dariya,

“Ba shi ba ne Hajiya, don Allah ki sa ta zo ki dan rarrashe ta, na ga kamar ta damu…”.

Hajiya ta girgiza kai,

“Ai ka qyaleta kawai, ka bata dan lokaci da kanta zata dawo hanya, kishiya fa ba wasa ba ce…”

Ya shiga dariya,

“Ni ba don horonta na yi aure ba Hajiya, kar ki yi mata baki.”

Sai Hajiya ta yi dariya kawai, cikin ranta tana jin dadi yadda Mujahid yake da son Kyautatawa iyali, tamkar mahaifin Binta ne ya haifo shi, tun daga yanzu alamunsa na nuna zai yi adalci, ko da kalmarsa daya aka yi masa hukunci wadda ta ce,

“Ni ba don horonta na yi aure ba hajiya, kar ki yi mata baki.”

Adalcin wannan maganar tasa babu wanda bata shafa ba tsakanin Nabila da Binta, Nabila aura masa aka yi, amma sai ya ce, na aura, Binta ba ya jin dadinta, amma ya ce ba don ya hore ta ya karbi auren ba.

Irin wannan dabi’ar tasa tuntuni ta sa kowa ya gane shi mutumin kirki ne, kuma wannan ne dalilin da yasa duk suke jin qarfin gwiwar aura masa ‘Ya’ya don sun san zai iya riqewa da adalci.

Da ya shiga wajen iyayensa maza ma wannan albarkar ya sha, har sai da ya ji hawaye na tsiro masa a ido.

Dukkanninsu sun yi masa alqawarin tallafi, sannan daga qarshe Alhaji ya ce,

“Anjima ka je ka yi wa Alhaji Ya’u godiya don Allah, an sallamo Nabila dazu, in da hali ko kadan kar ka bari yarinyar nan ta san dole aka yi maka, don Allah ka riqe ta kamar yadda kake riqe ‘yar uwarka Binta…”

Da alamun yaqini ya ce,

“In sha Allah Alhaji.”

Ya wuni a gidan har azahar cikin nishadi saboda albarkar iyaye, sannan yayi sallama ya koma gidansa yayi wanka, har wannan lokacin Binta na ta faman kumburi da qunci duk da ta rage kuka.

Mujahid ya shirya tsab ya ci manyan fararen kaya sannan ya cimma Binta a daki, cikin walwala ya ce mata,

“Za ni wajen qanwarki Nabila, ki na da saqo?”

Ta yi masa duban sama da qasa, sannan ta shanye ta kawar da kai.

Ya sunkuya ya dauki wayarta ya shiga duba call record, sai ya tarar ko yanzu ba a fi minti biyar ba Nabila ta kira Binta, kuma ba ta daga ba, kafin wannan kiran kuma ta kira ya fi ashirin kuma dukkaninsu ba a amsa kiran ba.

Nan da nan ran  Munjahid ya baci ya dubi Binta a fusace,

“Nabila tana ta kiranki ba ki daga ba, me yasa?”.

Ta fara yamutsa fuska ya san magana zata gasa masa don haka, ya daga hannu cikin daure fuska ya dakatar da ita,

“Nabila matata ce da zaku rayu tare, tana ganin girmanki tana mutunta ki, ba ta hada ki da kowa ba, saboda haka ki yi tunanin sakamakon da zai biyo baya idan kika nuna mata mummunan halin da kike nuna min, abinda zaki fi tunawa shi ne, ita fa ba ni ba ce.”

Bai sake bi ta kanta ba ya cillar mata da wayarta ya fice a fusace, fushin da yake fuskarsa ba ta taba ganin irinsa a fuskarsa ba, don haka ta ji wani tsoro ya shige ta, don alamu ne na cewa Nabila zata zo ta fi ta fawa, tana kuma yawan jin masu kishiya sun a fadar hakan koma baya ne.

Babu shiri ta fara neman canja tunani akan Nabila, wadda in ta shata layi da ita kamar yadda ta shata da Muajahid kwabarta zata iya yin ruwa don ita zata zama Mujiya a cikinsu, kuma dukkansu zasu dinga yi mata kallon mara kyawun hali, don ba zasu iya shiga zuciyarta su gane dalilin da ke sa ta kin jininsu ba.

Mujahid ya rakici abokinsa Jamilu wanda ke ta yi masa shegantaka da cewa,

“Kai ba ka neman mutane sai ka rakito aure, afujajan sai ka ce mu zo mu take maka baya”

Ya san hakan ba daidai ba ne, amma sai yayi dariya ya ce,

“To Jamilu ina ma lokacin ya isa? Ko yaushe mutum ya motsa yana da hidima a gabansa, wasu abubuwan ba sa fado masa rai sai buqatarsu ta taso.”

Jamilu saki kawai yayi don ya san Mujahid dama can ba ya damuwa da hayaniyar abokai.

Suna tafe suna ta hira, Jamilu ya sake rakito wata  tsokanar,

“Lokacin aurenka da Binta, ka yi ta zuzuta mana irin son da kake mata, ina son ya buya har ka sami damar kallon wata ka so?”

Mujahid ya yi qaramin murmushi ya ce,

“Ka gyara tambayar sai in amsa maka ita”.

Jamilu na dariya,

“To kawai gyara min tambayar da kanka yadda zata hau amsarka.”

“Wani zuzutaccen son ka sake karo da shi ne? sai kawai na amsa maka da cewa, ka canka kuwa, ina son Nabila kwatankwancin yadda nake son Binta”.

Kai tsaye Jamilu ya musa da cewa,

“Na fa san ka da siyasa Mujahid, abinda ka fada bai cika faruwa ba…”.

Mujahid ya tare,

“Menene bai cika faruwa din ba?”

“Zafafan so biyu a lokaci daya”.

Jamilu ya amsa,

Mujahid yayi dariya,

“Yadda ka dauki son daban da yadda na dauke shi”.

Jamilu ya tambaya da sauri,

“Kai yaya ka dauke shi.”

Kai tsaye Mujahid ya amsa,

“Babu wani so da ya fice son Allah, don haka a ko wanne karabitin so sai an bi umarnin Allah yake halarta, in ka so abu da zuciyarka kai tsaye akwai haqqin Allah a ciki na bin dokokinsa, idan abu ya shigo rayuwarka ba tare da ka shirya ba, akwai haqqin Allah a ciki na bin dokokinsa, duk daya ne babu komai da babu Allah a ciki, don haka sai ka riqe zuciyarka, ka bi Allah cikin dadin rai shi ne komai ka so domin Allah.”

Cikin zolaya Jamilu ya mayar da fuskarsa kalar tausayi,

“Allah sarki malaman duniyar so.”

Suka yi dariya duka.

Gidan a cike yake don ana gabatar da bikin Sadiya, saboda haka ba su iya shiga kai tsaye ba, dole Mujahid ba don ya so ba ya kira Nabila a waya, ta daga cikin sanyin murya da kasalar rashin abin fada,

“Yaya Mujahid.”

Abinda ta iya cewa kenan, babu kaudin muryar nan tata mai farin ciki da wayarsa, ko daya ma babu shauqin dariya a muryar tata, amma shi ya kasa kunne ya jiyo shauqin sonsa na bugawa a  filin zuciyarsa, saboda haka ya sami qwarin gwiwar yi dariya ya ce,

“Qanwata Nabila”

Sai ta yi gajeriyar dariya kawai.

Ya ce,

“Na zo gida a cike, ina son na ga Alhaji, kuma ina son ganinki zan iya samu kuwa?”

Zuciyarta ta rude da kidan da ba ta san ko na meye ba, jikinta sai bari yake ta amsa masa,

“Bari na yi masa waya, ina jin yana can sashinsa…”

Kafin ta dire ya tare ta,

“Dadi kenan, ke kuma ta ya zan yi na gan ki?”

Ta sake jin kanta na juyawa, tamkar ta yi fuka-fuki tana shawagi a sararin samaniya, ta yi qoqarin ta yi magana amma ta kasa,

Ya sake ce mata,

“Ko yanzu kin min tsada ne?”

Ta sake kunyacewa, bakinta na rawa ta ce,

“Bari dai na yi wa Dadi wayar”

Kafin yayi magana ta kashe kiran.

Ba jimawa sosai Dadi ya turo aka tafi da su.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 45Rigar Siliki 47 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×