Skip to content
Part 58 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Ita ta shiga gida da fargabar ta inda zata fara, ga dai Mujahid din nata da fuskar shanu, ko murmushi babu a fuskarsa bare alamu na zai kawo mata zancen soyayyarsa ta taya shi, kenan dole ita zata fara dauko gangar ta kada, ya Allah ya taya ta da rawa, ya Allah ya bata rai ya kushe ta. Shi kuma ya shiga gida da murnar zai fara sabuwar rayuwa, zazzaqa wadda ba dukkan matashi irinsa yake sa’ar damqar irinta ba, ya sami abinda yake so irin Binta, sannan ya sami mace tagari kyakkyawa irin Nabila wadda sam sonta ma bai kamata a hada shi da komai ba.

Duk wannan dokin ya shanye abinsa yayi fuska, yana zuwa yayi alwala ya fice sallar magariba da isha, daga can kuma bai dawo gidan ba ya wuce dauko matarsa.

Kamar saurayi da ya je zance wajen budurwa, da Nabila ta fito bai tashi motar ba sai da suka share fiye da rabin awa a motarsa suna hira, sannan ya ja suka tafi gida yana mai cike da kewar kar su rabu, musamman da suka zunguro wani batu,

“Ba zan nemi hutu ba sai kin yi wata shidda da haihuwa”.

Ta ce,

“Me yasa?”.

Ya amsa,

“Bebinmu yayi dan qwari, sai ki koma makaranta, zan kular miki da shi sosai tsawon lokacin hutuna, kafin sannan na san ya dada wayo, sai kuma mu bar wa Binta ta karbar mana”.

Nabila ta sha mamaki da murna, har ta ce masa,

“Amma ko Antin Binta ta dade da ce min kana da kishi ba ka son aiki da karatu, me yasa zaka shirya haka?”

Ya daga mata yatsunsa biyu yana dariya,

“Dalilaina biyu ne, shi ne, duk abinda kike so kuma mai amfani ne in dai ina raye sai na samar miki shi, bugu da qari zaki fi jin dadin tarbiyyar ‘ya’yana”.

Ta ji farin ciki na qwallo da ita, muryarta a raunane ta ce,

‘Amma ko Anti Binta ba zata so ba”

Ta zarce da zolayarsa cikin dariya,

“Ka hana ta aiki sannan ka qi yin wani qwaqqwara motsi ta fara haifar nata babyn sai ka ce nawa zata yi reno ni na tafi karatu?”

Ya gwalo ido,

“Au haka ne?”

Ta juya kai, sai yayi magana qasa-qasa yadda ba zata ji ba,

“Yes! Ragwancin Binta ba zai iya ba ta ko dan kiyashi ba, so take ta zama ‘yar rainon”.

“Me ka ce?” ta tambaye shi.

Ya maze ya amsa,

“Kowa ina ba shi abinda yake sha’awa, Binta ba ta da sha’awar karatu ko aiki, dole na taya ta samun abinda take so”

Ta yi shiru ba ta tanka ba.

Ya juyo ya dube ta,

“Kin yi shiru”.

Ta lumshe ido ta bude, murmushi ne sosai a fuskarta,

“Ina tattaro kalmomin godiya ne, duk na rasa kalar da zan tattaro su nuna maka murnata, ni ban san abinda zan baka ba…”

Daidai lokacin ya tsayar da mota qofar gidansu, ya kame kai ya dafe da sitiyari yana nuna alhini,

“Kash! Na so yau wajenki zan kwana don na taya ki farin ciki kawai, ba don kwadayin godiyarki ba.”

Kallo daya ta yi masa ta san da gaske yake, don haka ta ji ita ma kewar ta qaru mata.

Duk suna alhinin rabuwa suka shiga gida lokacin qarfe shadaya saura na dare.

A tsammanin Nabila Binta ta yi bacci, don ta yi ta kira a falonta ta ji shiru, kawai sai ta yi sallama da Mujahid bayan ya bata sumba a kunci ta haye sama cikin gajiya.

Shi kuma ya share ya wuce dakinsa ya shiga wanka cikin tunanuwa barkatai, don dai ba laifi ya karbi saqo Binta, ya ji dakunanta sun cika da qamshin amare irin wanda bai dorar da su ba sai a Nabila, hatta dakin da yake kwana wanda ba ta damu da gyarawa ba yau da ya shiga sai da ya kasa gane shi, saboda gyara da qamshi.

A gaban dresser yana shirin bacci ya tsinci wani katin saqon masoya mai dankaren kyau da qamshi,

Da sauri cikin cikin bugun zuciya ya dauka ya karanta,

You came into my life, and made it wonderful world libe in.

You made me feel so special with all that you do and all that you say…

I love you.

Nan da nan ya fara jin shakkun in abinda yake faruwa gaskiya ne, ya dinga juya katin yana bin dakin da kallo tamkar Bintan na labe na kallonsa, ya tafi cikin sanda yayi tsalle ya dira kan gado, ya kasa rikqe kansa, wai Binta ce take shirin shigowa rayuwarsa da dadin rai? Me zai yi ya bayyana wannan farin cikin?

Yana nan kwance tsakanin qarya da gaskiya na hasashen Binta zata bullo da komawa murnarsa ciki na rashin bullowar tata har ya ji yana shirin yi wa halin da yake ciki kuka.

Sai da ya cire rai sannan ya ji motsin murda kofarta na shigowa dakin. 

Ya runtse idonsa ya sake budewa yana yi wa lamarin zaton mafarki, sai ga Binta ta bayyana sanye cikin pink din kayan bacci ta daura zanin atamfa a kan rigar, kanta da farar hula mai raga.

Yadda qamshin da ta shigo da shi dakin ya halarci hancin Mujahid haka nasa idanuwan suka bi ta da kallon, sai dai ya hana fuskarsa ta bayyana ko wanne irin aiki, Binta ta qayatar da zuciyarsa, kai tsaye ta doshi gonar sonta da ke qirjinsa ta fara noma.

Ta zauna kan sofa tana fuskantarsa yayin da ya kasa dauke ido daga kanta, amma ko kyautar murmushi ya hana kuncinsa yi mata, duk da haka fuskarta akwai qarfin gwiwa, kai tsaye take fuskantarsa,

“Yaya Mujahid ba ka yi bacci ba?”

Ya rarumo qarfin halin da ya ba shi damar kada mata kai, bai ce komai ba amma ya ja jiki ya tashi zaune.

Ta dinga bin dakin da kallo, da alama tanado maganganu take suna kufcewa, da ya ga haka sai ya ga dacewar ya ciba mata,

“Binta akwai damuwa ko?”

Yayi maganr ne da fuskar manyance da ya saba yi mata magana da shi kwanan nan, wannan ne kuma ya ba ta damar yin magana kai tsaye da yanayin yarintar ita qanwa ce kamar yadda yayi mata magana da nasa manyancen,

“Yaya Mujahid ina son canji.”

Ya yunqura ya tashi zaune cikin hadiye juyin farin ciki yana qoqarin saukar da qafafuwansa qasa,

“Binta canjin me?”

Wato yayi kamar bai tuna cewa kullum shi yake gindaya mata sharadin in tana son canji ta yi magana ba.

Ta jima kunya na qwallo da ita kafin ta ce,

‘Wai ba ka ga saqona ba ne?”

Ya dan ja fasali,

“wanne saqon?”

Ta nuna masa dreeser,

“Na bar bayani kan can”

Ya fara murmushi,

“Na gani, amma sai na yi zaton ba Binta ba ce.”

“To Binta ce.”

Tana dariya.

Shi ma ya fara,

“Mafarki nake ko gaske ne?”

Tana ta murmushin da bai taba ganin mai kyau a fuskarta irinsa ba.

“Da me kake son in tabbatar maka ba mafarki ba ne?”

Ya bude hannyensa da sauri,

“Zo gare ni”

Cikin azama da barin jiki ta tashi ta same shi, suka qanqame juna tamkar suna son zama halitta daya, Binta ta fara kuka saboda jin yadda zuciyar Mujahid ke tseren harbawa, tamkar qirjinsa zai rushe, 

Ta dago tana hawaye ta dube shi, sai ta ga shi ma cikin hawayen yake, ita ma da nata bugun zuciyar ta dafa qirjinsa,

“Yaya Mujahid me ke faruwa da kai?”

Ya amsa mata cikin shauqi,

“Sonki ne Binta, zuciyata na murna da samun abinda take so, ba zan iya dakatar da ita nuna farin cikinta ba, ina sonki Binta, na yi murna da kika yarda ki taya ni sonki ya samar min farin ciki, kuma ke ma kika yarda zaki ci albarkacin son…”

Ta sake fadawa qirjinsa cikin kuka,

“Na yi nadama Yaya Mujahid ka gafarta min don Allah… ban san ma sonka ke sa ni hauka ba tun tuni, ban sani ba, ka yarda da ni, ba wai so nake ka huce ba, amma ban taba girmama wani mutum sama da kai ba… hakan ne ya sa ni hasashen matsayin da zan iya ba ka ya fi na miji, ban sani ba sai yanzu, ina qara ba ka haquri don Allah kar ka qwace min son da ka ba ni.”

Ya matsawa kansa dakatar da hankali da kunnuwansa su saurari maganganun Binta, amma tuni yayi nisa da jin jiki a barin jikin da masoyi yake in ya sami masoyiya, sai sunsunarta yake yana numfarfashi tamkar karen da ya bata ya dawo gida ya sami uban glidansa, ya rasa halin da zai kwatwanta yadda yake samun kansa a son Binta, yana kwatantawa da cewa iyakacin aljannar duniyarsa kenan, can cikin rashin hayyacinsa ya gane cewa Binta fa kuka take,sai sannan ya tuna amsa mai kwantar da hankali take jira, ba zata iya fahimtar son da yake mata a shirunsa ba,

“Na jima ina daukar hakan a matsayin qaddara, ban taba gajiya ba kuma ban taba fasa sonki ba, baki san irin son da nake miki ba ne Binta, ba shi da wani mahadi sannan ba ya jiran raddi, duk yadda zaki kasance ba zan fasa son ba kuma kin ga ban yi aikin da so ke sawa ba na yi ne dan tsira da mutunci musamman saboda akwai haqqin wasu a kaina…”

Binta ta datse kukanta don ya ajiye rarrashin haka, yadda ya faro maganar wasu na da haqqi a kansa tana da tabbacin yanzu zai fara yi mata labarin son Nabila, ita kuma ba abinda take son ji kenan ba, nata son ne yayi rauni shi take son yayi ta jaddawa.

Dama ba shi da wasu azanci da yawa, soyayya ce kawai ke qwallo da shi, don haka ya koma bata labarin son nata, shi ne abinda take son ji kuma shi ne abinda yayi musu jagoran farin ciki har suka kusan manta kansu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 57Rigar Siliki 59 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.