Skip to content
Part 55 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Ya sake nisanta tunani a cikin lamarin Binta, yanzu ne kuma ya fara fahimtar lallai da gaske Binta take ba ta sonsa, kuma ba zata taba son nasa ba, don haka ya ji sanyin gwiwar cigaba da duk wani yunquri da zata so shi, ya riqe kansa da damuwarsa a zuci ya bar zolayarta, ya bar yin abu don ya bata haushi, ya shiga tafiyar da ita tamkar qanwarsa ta da can.

a daina biyo Nabila dakinta idan ta shiga ranar girkinta, sannan ya daina ko wacce irin walwala gaban Binta, to da alama wannnan sauyin ne zai sauya masa ita, don ta shiga taitayinta ainun tana jin rayuwar babu dadi sam, yanayin ta fi so a da can, shi ta zaba a tsakaninsu wato zamowarsa wa gareta, har kawo shigowar Nabila ta fi sha’awar wannan matsayin shi take son a sake ta su koma wa, amma yanzu tana jin kamar shi ta fi tsana a duk duniya.

Yau da yamma ya dawo aiki, da qunshin Ice cream dinsa biyu, a dakin Binta ya sami Nabila ya shiga da qasaitarsa kamar yadda ya saba ita kanta Nabila da yake walwalar da ita nata taitayin take shiga idan ya wanzu gaban Binta yana shan qamshi.

Dole Binta ta bi tawagar Nabila wajen yi masa sannu da zuwa duk da kuwa ya dogare a qofa ne ya qi shigowa, hakan ya sanya Nabila  tasowa don su hau sama tunda ta fahimci yanzu haka kammanun ‘yan mazan suke, suna zuwan samansu zai dawo mata masoyinta na asali.

Nabila na qarasawa bakin qofa ya miqa mata kunshin Binta na ice cream yana cewa,

“Miqawa Binta”

Kafin ma ta isa ga Binta tuni ya fice ya hau sama, Nabla ta miqawa Binta wadda fuskarta ke nuna dauriya, amma zuciyarta kuka kawai take rusawa.

Ba ta cikin hayyacinta har Nabila ta yi mata sallama ta wuce sama cikin hanzari, kawai sai ta zauna ta hau kwatancen yadda zasu yi da juna in sun hadu. Ta san Mujahid ko ba da kyau ba, iyakar sanin da ta yi, wanda ya ba ta tabbacin Mujahid ba shi da sauqi wajen yi wa Mace muhalli ko nuna mata so, in ita da take gudunsa tana nuna masa iyakarsa ta sami darajoji na nuna sonsa gareta, to yaya kyakkyawa Nabila kuma wanke hannu ka taba wadda filin zuciyarta babu son kowa sai na Mujahid, yayin da shi kuma babu macen da yake karramawa kuma ya yarda mutuniyar kirki ce sai ita. Dukkaninsu babu ko wacce irin tsatsa ta juna a tare da su.

Kamar Binta ta sani, Nabila da Mujahid hadiye juna ne kawai ba sa yi idan sun hadu, dubin son Mujahid da ke danqare a zuciyar Nabila ya hadu da mai iya masa kuma wanda ya san darajarsa, nutsuwarta ta hadu da adalcinsa, haqurinta ya hadu da dattakonsa, kyakkyawar surarta ta dace da idonsa me qawa wanda bai san yana da ita ba sai bayan ya samu, don a da son Binta ya sa ya zaci ai kawai mace mai kwalliya ba ta birge shi tunda Binta ba ta yi, sai yanzu ya gane cewa ashe son Binta ya dade yana yi masa gizo yana canja masa abubuwansa da ba haka yakamata su kasance ba, sai yanzu da ya samu yake gane dunbin kewar da yayi.

Sun manta da komai sai kansu, har fiye da mintuna ashirin, dama daga hannun Binta ya fado duk sun sha kewar juna na kwana biyu, sai da kyar suka rabu Mujahid ya shiga wanka, ita kuma ta tsaya tana ta qarewa dakin kallo, ta gyara nan, ta sake feshe can da turare har ya fito wanka, ta taya shi ya shirya sannan suka dawo falo suka zauna cin abinci.

Ba ta tare da yunwa, don tare suke cin abincin rana da Binta duk ranar da Bintan ce me Mujahid, don ya kan qi zuwa cin abincin rana, sannan ko ya zo ita dai ba ta ga suna wani cin abinci tare ba, ita kuwa duk ranar girkinta tare suke cin abinci idan ya dawo, in kuma sai yamma dole ne in ya zo ci ta taya shi.

Suna cikin ci ya zolaye ta,

“Kin san me?”

Kallonsa kawai take da idanuwanta masu daukar hankali.

‘Wani lokacin ina kewar samartaka.”

Ta kada kai cikin murmushi,

“Duk auren Qwailaye aka yi min, ina zaune ake daurawa a ce min an min mata, babu wanda ya taba jin ra’ayina ko ina son zuwa in labe a bango in tura a min sallama da budurwa ta zo mu yi hira?”

Nabila na dariya a nutse,

“Gaskiya ina taya ka jimami…”

Ta tare ta shi ma cikin dariya,

“A’a ba wannan nake so ba, taya ni nake so kawai na fanshe, so nake na ji abinda ake ji a zancen qofar gidan.”

Kallonsa kawai Nabila ta ke tana jin wasu sabbabin farin ciki a zuciyarta, gani take duk zamaninta babu matar da ta auri wanda ya dace sama da ita. Kallonsa da tunaninsa duk manyan aljannar duniya ne ne masu sanya ta farin ciki.’

“Ba ki ce komai ba”

Ya ce mata.

Ta girgiza kai da sauri,

“Ai ba sai na ce ba, ko me kake so ni zan maka.”

Ya miqa mata hannu suka tafa, yana cewa.

“Na sani dama, da kina da iko ko damuwar wani ba zaki bari na gani ba bare tawa”.

Nabila ta dai amsa masa ne kawai, amma ba ta fahimci manufarsa ba, har lokacin sallar magariba ta yi bayan yayi alwala ta ga ya bude firji ya dauki ice cream din su da ba su qara tunawa da shi ba ya fice da shi, bayan fitarsa kuma ta ji tashin mota.

Binta na zaune kan sallaya bayan sallar isha ta dinga jin fiton shigowar saqo wayar Nabila da ke zaune kan kujera ta manta da ita.

Rashin nutsuwar zuciya ya sanya ta bi wayar ta dauka ta kuma shiga duba mata saqonni, wanda sunan Mujahid ya mamaye saman yawancin saqonnin da suke wayar.

Gabanta na dakan uku-uku tana jin yakamatar ajiye wayar kar ta karanta ko daya, amma shagalalliyar zuciyarta ta sanya ta bude wanda ya fado yanzu, wanda yake gajere kamar haka,

‘Yammata na qaraso, a halin yanzu ina qofar gida ina jiranki’

Binta ta ji wani irin tashin hankali ya rakito ya fado mata zuciya, ba ta san ma’anar kiran Nabila waje ba, amma ta san ko yaya Ma’anar zata zo kawai tabararsu ce da son nuna wa duniya iyakarta.

Ta kasa sarrafa kanta sai da ta cigaba da karance saqon Mujahid na wayar Nabila, sai ta fahimci ashe kallon ayaba kawai suke mata tana musu kallon birirrika, sharafinsu suke sha ita sun watsa ta kwandon shara, a rana Mujahid ya aiko wa Nabila sakonnin soyayya biyar zuwa goma, tamkar soyayyarta kawai yake bautawa ba shi da wata sabga a gabansa, sai ta ji zuciyarta na neman ta kece, da alama duk waqar sonta da ya sha yi ko kashi daya cikin na Nabila ba ta samu ba.

Kuka ya dinga neman qwace mata lokacin da ta dinga jin sakkowar Nabila daga bene, kamshin turarenta mai sanyin dadi na riga ta qarasowa hancin Binta.

Da sauri ta gyarawa wayar zama ta goge hawayenta ta koma mazauninta ta dau carbi ta hau ja.

Nabila ta shigo da walwalarta tana yafe da mayafi, zuciyarta fal fargabar qaryar da zata yi wa Binta ta fice, ga dai oganta can na ta kwararo mata Hon.

Ta wayance da zaman hira lokacin da ta tarar Binta na sallah, ta dauki wayarta da ta manta tana dubawa, lokacin Mujahid ya gaji da hon da turo saqo ya kira wayar, cikin sanyin jiki ta daga amma ta kasa magana, don dai ta san kwanan zancen, mujahid ya kashe murya ya ce mata,

“Haba My lobe, na yi laifi ne da zaki shanya ni ina jiranki?”

Bakinta na rawa tana dariya,

“Ga ni nan”

Kawai ta tashi ta fice, tana ta sanda ta fice daga gidan kamar yadda Binta ta yi sandar ta leqa ta ta windo har zuwa ficewarta. Sai ta fada kan kujera ta shiga sharar kuka.

Motar Mujahid na kunne, sai sassanyan kidan soyayya da ke tashi a sannu, qofofin motar gaba duk su na bude shi yana zaune a mazaunin direba qafarsa daya na waje yana dan kada ta sannun sannu, yanayin gwanin sha’awa a wajensu duka, ba ga Mujahid da shi ya qirqiro ba, hatta Nabila ta ji wata nutsuwa da farin ciki.

Nabila ta rungume hannu ta jingina da motar tana yi masa maraba kamar gaske, ya fito daga motar yana nuna mata daya qofar,

“To taimaka ki shigo daga ciki mana.”

A yangace ta zagaya suka shiga lokaci guda, Mujahid na jin farin ciki Nabila na jin fiye da hakawa

“To yammata yaya kike?”

“Lafiya kamar kai.”

‘Kamar ni? Amma ko ai ni ba ni da lafiyar”

Ta kishingida sosai ta kwantar da kai jikin kujera tana kallonsa cikin murmushi,

“To meye matsalarka?”

Ya dafa qirji murya a tausashe ya ce,

‘So ne matsalata, in dai rashin bacci cuta ne to gaskiya ni ba ya barina bacci”

Nabila ta yi qaramar dariya,

“Kar ka damu, ai rashin bacci sunnar masoya ce, dole in sun tuna juna su katse ko ma meye don ba wa so haqqinsa na tunani”.

Ya karkato sosai yana qara ba ta muhimmanci,

“Allah? Ke ma kina jin irin abinda nake ji?”.

Ta nuna mamaki,

“To me yasa ni ba zan ji ba?”

Yayi ajiyar zuciya,

“In haka ne ni ba ni da dauriya, fuskokinki sun fi nawa iya boye so”

Ta kada kai, ta so ta yi magana amma sai ta shanye. Tabbas ta iya boye so, amma shi ya fita jarumtar kandamarsa da yawa, yana na Binta da a da take tunanin ya yashe dukkan kason so a qirjinsa, sai gashi yanzu yana tabbatar mata nata son mai nuna kamar nasa muhallin ya fi zurfi, to da wanne abin haqan ta haqa masa nasa muhallin? Sai ta ji tana so ta sani amma ba ta san da fuskar da zata tambaye shi ba.

Ya karkace kai yana binta da kallon cike da shauqi ta cikin dan hasken fitilar da ke hasko masa kyakkywar fuskarta, da ya ga ba ya gamsuwa da kalle ta cikin qaramin hasken da ke ratsowa cikin motar sai kawai ya bude kofar motar haske ya gauraye motar, Mujahid na bambance tsakanin wanda ya fi wani kyau da haske tsakanin fitilar da fuskar matarsa, Nabila ta fi komai kyau a idonsa.

Ya shiga dafa qirjinsa tamkar me yi masa ciwo,

“Ko takurarriya zuciya ce da ni Nabila? Tunda na fara sonki ba na jin ko wanne irin motsi a filin zuciyata sai abinda ya shafe ki, da akwai sunan da ya fi so kwarjini da an taimake ni da shi na jaddada cewa shi nake miki, gaskiya yadda nake jin shawaginki a qirjina Nabila sharafinki ya wuce so”

Nabila ta kasa tanada amsa ko wacce iri ce don so da farin ciki, sai hawaye kawai take jin ya cika mata zuciya da ido.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.2 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 54Rigar Siliki 56 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×