Skip to content
Part 54 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Ta janye hannunsa daga kafadarta tana murmushin yaqe,

“Kar ka damu, ko me zan zama dai ai kai buqatarka Nabila ta yi farin ciki, Alhamdulillahi kuma tana farin cikin.”

Ta nufi daki, shi kuma kawai sai ya bi bayanta.

“Eh to, amma fa ba ta san da wannan sharadin naki ba.”

Ta ji ranta yana dan baci, shiyasa ta jima ba ta tanka ba har ta murza qofar Toilet tana qoqarin shiga tana amsawa,

“To wannan ai ya rage naka, sai ka duba ka gani, idan sanin zai ba ta farin ciki sai a sanar da ita, in kuma ba zata yi farin cikin ba sai mu taru mu yi ta boyewa, mu dai buqatarmu ta yi farin ciki.”

Yayi fuska ya bi bayanta Toilet din,

“Wata mantuwar da na yi, yakamata a tuna yaya makomar naki farin cikin?”

Haushi ya qara kauraye ta, murya cunkushe ta ce,

“In haqawa kaina kabari in shiga mana, ina ruwan wani”.

Ya qi nuna cewa ya gane fushi take, ya matsa gaban zink ya dauki brush din ta ya hau matsa mata man goge baki, don ya san abinda ta shigo yi kenan, yana cewa,

“Haba dai, mu kuma ai babu haka a mafarkinmu, rayuwar ai babu dadi idan babu ke Anti”

Ta hadiye yawun takaici da qyar sannan ta karbi brush din tana nuna masa qofa,

“Ka ga ka je kawai, Allah tashe mu qalau.”

“A ki wanke bakin mu je mana, ai ba ki ba ni amsa ta ba”.

Dole ta kasa magana, ta wanke bakinta yana tsaye yana kalle ta ta madubi, tana son wata hidimar amma dole ta ajiye Brush ta kama hanyar fita, bai yi kasa a gwiwa ba ya bi bayanta.

A dakin bacci tana son sa kaya dole ta zube su bayan ta dauko su da Wardrobe tana sanya musu turare.

Yayi jingine jikin sideboard yana kallonta yanayinta na nuna fushi da rashin hayyaci, duk ya fahimci hakan amma a hakan yake jin yanzu ya fara takura mata,

“Kina neman ki cika turaren nan yadda zai hana mu bacci ko ya sa mu mura fa”.

a dago ta wurga masa wata uwar harara, dama ta gama zuwa wuya, babu abinda ke yawo a ranta face tabarar da ya shafe sati yana sanya Nabila a gaba suna yi mata, kwatakwata ya watsa ta kwandon shara, sai yanzu da ya saba kwana rungume da mace ne zai zo ya yi maneji da ita? Ya ma raina mata wayo.

A fusace ta ce,

“Amma dai ko ciwon zuciya turaren nan zai sanya ni  bai kamata ka sako bakinka ba…”.

Ya fahimce ta don haka ya tare ta da sauri,

Ái ina yi miki maganarmu ne, ni zan iya mura idan turare yayi yawa”

“Kana naka dakin ina nawa?”

Yayi fuska,

“Ai a nan zan kwana.”

Nan da nan ta ci laya,

“Gaskiya ba zai yiwu ba, ni mai yi maka lamuni ce ka je sama ka kwana, na sani dole ne zaka zama cikin kewa, kar a ce na zama mai daukar haqqi”

Ya  lome baki, sannan ya ware da yi mata alamar jinjina,

“Da kyau! Kin fara zama yadda yakamata ki zama, kin fara tunani akan wasu ba kanki kawai ba, tunda kika fara jin lallai zan kasance cikin kewa, na san kin san yaya kewar take shiyasa kike ji min ciwonta”

Ya fara ja da baya yana nufar qofa,

“Zan dan yi jira amma ba mai yawa ba Anti, in kin ji buqatar canji ina qara yi miki tuni, zan zama yadda kika so na zama, saboda haka na ke miki bankwana cikin yi mana jajen kewar da zamu kwana ciki”

Bai tsaya jiran cewarta ba ya fice da baya yana daga mata hannu cikin murmushi.

Ta yi tsaye a wajen saroro hoton murmushisa ya qi acewa daga idonta, sai dai hoton fuskokinsa da Nabila wadda yake wa son da ko quda ba ya son ya taba ta ya qi bace mata daga zuciya, sai ya bar ta da jin neman dora hannu aka ta rusa ihu, sai dai tana tsoron karya sharadin. Ta ja jiki da qyar ta nemi guri bakin gado ta zauna cikin dukan zuciya da fargabar kar ta ji shi yana hawa matakalar bene ya jaza mata tashi babu barin jiki guda.

Amma maimakon haka sai ta jiyo shi ya qure qarar TB a falonta, dole dai sai ya nuna wa Nabila shi fa Binta hoto ce a wajensa, tunda a kwanakinta ko motsin ringing din waya ba a jiyowa a samansu bari na wata TB, sai ka rantse ma babu mutane a gidan, sai idan sun so ci mata fuska ta dawo ta tarar da su a tsakar gida suna wasan guje-guje.

Tana kuka shabe-shabe ta shiga sanya kayan bacci ta haye gado. Ba ta fara jin uqubar ta kira mutuwa ba, wannan tukunna, amma ta fara jin in ma ba ta kira ba to Mujahid ne zai kira mata.

Tana ta zuba idon ta ga abinda zai wakana da safe, zai yi sammako ya fice ne kamar yadda ya saba kafin zuwan Nabila, ko kuma zai dan yi ta idon jinkirtawa don kar ya nuna mata cin fuska a idon Nabila tunda yanzu ta karbi girki?

Ai ina! Tun asuba ya fara nuna mata ba fa kamar yadda take zato ba ne, don bai fita masallaci ba sai da ya sha uban kiran Nabila a waya wai ta tashi ta yi sallah, ba ta daga wayar ba saboda tana silent shi kuma ya haye har saman benen ya shiga kiranta ta tashin. Sai da ya ji muryarta sannan ya fic masallaci, alhalin Binta na uwar daki bai bi ta kanta ba.

Qarfe bakwai ta ji shi a Toilet, shaidar dai zai fice da sammako, sai ta yi bakam tana tattara zuciyarta tana ba ta ruwan haquri, har lokacin da ya cimmata a daki cikin shirin fita, ita kuma ya same ta lamo a kan gado, babu abinda ya fara da shi sai cewa,

“Yauwa kin ajiye aikin ba.”

Kallonsa ta yi ta kawar da kai.

Bai damu ba ya dora,

“Dama na shigo na yi miki tuni, lada ya isa haka, ki dawo gida ki zauna”

Ta yi murmushin yaqe ta kawar da kai.

Ya sake nuna rashin damuwarsa da shirunta, yana duban agogo, sannan ya dago ya dube ta yana shafa ciki,

“Na fa fara manta kalar Yunwa wallahi, ba zan sami komai a dakin nan ba, ko ruwan bunu ai dai yakamata na samu, taimaka ki tafasa min bari na ga lafiyar Nabila na dawo”

Bai saurari cewarta ba ya juya ya fice ya bar ta da juyayi da wasi-wasi, ta yi zaune tana kasa kunnen dawowarsa, yadda a lalace sai da ya shafe sama da minti talatin sannan ya dawo da fuskarsa mai nuna ai babu komai, shi bai yi ko wanne irin laifi ba.

“Ina shayin?”

Yayi fuska ya tambaya.

Kai tsaye ta amsa,

“Ban dafa ba, ai na zaci ka ci a can”

Yana dariya,

“Haba Anti, in na tsaya na ci ai sai ta fara yi miki kallon ba ki iya tattalin miji ba…”.

Ta fara cika da haushi,

“Ya danganta da waye mijin…”

Ya tari numfashita,

“Kuma wacece matar ba”

Ta tabe baki,

“Gaskiya, da ka sani ma kawai ka ci abinka”.

Ya kada kafada yana neman hanyar fita,

“Ai na ci, shiyasa hausawa suka ce gida biyu maganin gobara, na ci amma na yi mata dabara da cewa, girkinta ne ya fiye zaqi.”

Ta so ta tanka amma ta rasa kalmar fada, dole tana kallonsa yana yi mata dan biki ya sa qafa ya bar gida, tana jiyo shi kafin ya fice yana qwalawa Nabila kira yana ce mata ta wuni lafiya.

Kwanaki biyun girkinta haka ta yi su cikin wannan uqubar ta masifar zolayar Mujahid, duk abinda ya san zai motsa mata fushi da kishi sai ya bishi ya yafito, ya san tana gasuwa da wannan matakin nasa, shiyasa yake saka ran babu abinda zai canja masa ita sai hakan, don ya fahimci babu komai yanzu a qwallon kanta sai kishi, sai ya gama shan sharafinsa bai sami mai rarrashinsa ba sannan zata shiga taitayi.

Sai dai ya fahimci hakan ya fara taba Nabila, ta fara nuna rashin jin dadinta da wannan zaman doyar tasu, ko ba ta fito ta furta ba fuskarta na nuna wa musamman a idon Mujahid, sai dai tana ta kawaici tana kawar da kai ba ta son ta yi masa maganar don tare ta gan su, sai dai tana qoqarin kiyaye duk yadda Mujahid zai ci fuskar Binta ta hanyarta. Misali, rannan Binta ce da girki, amma kawai sai ya kwaso musu fita tare, wai ta zo su je gidan wani abokinsa, ba ta fito fili ta musa masa ba, kawai sai ta hau yi masa ciwon qarya, duk da haka sai ta gudu ba ta tsira ba, don kuwa nan ya sami abin rikicewa da rarrashi, tare da neman a je asibiti, yana kirikcen kuma tsakaninsa da Allah, nan ma sai da Nabila ta ji damuwa, don a gabanta ta ga yadda yayi tasa kulawar ga Binta ranar da take ciwon haqori, duk da ciwo ne mai tsanani, iyakarsa yi mata sannu da nuna ta cika wasa da magani, kuma ta je a zare mata haqorin ta huta yar banzar qiwarta ta hana ta.

Kodayake a lokacin ma yana magana ne cikin zaurancen nasa da ya saba magana da Binta cikinsa, yawancin maganarsa da ita zaurance, magana suke da juna yadda babu yadda za’a yi Nabila ta fahimci zantukansu duka sai daidaiku.

Da ta bijirewa fita da shi ranar ma da ciwo, lokacin da ta karbi girki ranar hutu ce, da safe yake ce mata, da yamma yana so su dan zaga gari, ta kasa boye masa damuwarta, inda ta fito fili ta ce masa,

“Yaya Mujahid ka sa Anti ta ajiye aiki ta zauna a gida, me yasa zaka dinga hora ta da kadaici in ka gudarwa kanka shiko ka gudar min?”

Ya nisanta tunani kafin ya amsa mata,

“Nabila wa ke horon horarre? Kar ki dinga manta son da nake wa Binta, duk abinda zan yi ina yi wanda ba zan cutar da ita ba kuma wanda nima ba zan cutu ba, ina yi ne kuma in na san zai faranta mata rai ita ma…”.

Ta saki baki kawai tana kallonsa, sannan a sanyaye ta gyada kai, 

“Yaya Mujahid me zai hana mu fita gabadaya? Ba na son mu dinga barinta da kadaici”.

Ya yi murmushi kawai ba tare da ya tanka mata ba.

Sai da ya bari Binta ta karbi girki sai yayi mata irin wannan tayin, bai sami amsar komai ba sai uwar harara, ta kuma yi tafiyarta ta bashi waje.

Don haka ya canja dabara.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 53Rigar Siliki 55 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×