Skip to content
Part 44 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Tun bayan sallar magariba Mujahid ya ke asibiti wajen Nabila hankali a tashe, ya san akwai sa hannunsa cikin abinda ya sami Nabila, amma ba wannan ne abinda shi yake taba ransa ba, abinda ke taba ran nasa shi ne, gobe ne za’a daura auren aminiyarsa da mutumin da bai cancanta ba, wadda ta sadaukar da nata jin dadin ta taya shi neman abinda yake so har ya samu, amma shi ba ma wai ya taya ta ta sami abinda take so ba, ya ma taya ta kawai ta sami abinda ya cancanta ya gaza.

Yayi kukan zuci yayi na sarari da sunan yana jimamin cutarta, duk sun kasa samar masa mafita.

Bayan sallar isha Alhaji da Hajiya suka zo duba Nabila, suka same shi firgai-firgai wutsiya a zage, kodayake shi ma da ya kalle su hakan ya gansu, musamman Hajiya da har rama ya hangi ta yi, kamar yadda ya ga Bintansa a kwana biyun nan ta rame tamkar mai hadiyar allura, sai dai ita ya mata zaton kawai qin da take masa ne ya motsa, take neman kashe kanta da damuwa.

Yana tare da su har bayan qarfe goma, lokacin Nabila ta dan farfado sai dai ba sosai ba, tana dai gane wadanda suke kanta musamman wanda Zuciyarta ta makance da ganin kowa sai nasa, wato Mujahid.

Ganinsa na qara mata qarfin gwiwar cigaba da rayuwa, tana zargin da yasar da ita yayi qila da tuni ta yi sallama da wannan rayuwar.

Yana ta sauri ya tafi gida, don bai sanar da Binta abinda ya faru ba, ya je zai sanar da ita ma ya gan ta ta buya a bandaki tana kuka, kawai sai ya maze ya fice abinsa, don shi dai ba ya son katsewa mutum hanzarin kuka.

Alhaji ya dube shi ya ce,

“Zaka bi mu gida ina son wata magana mai muhimmanci da kai.”

Wani tashin hankali ya hambari Mujahid, abinda kawai ya zata duk akan maganar Binta ne da cutar qanjamau dinta, ya rasa ta hanyar da zai yi tirjiya ya qi bin su.

Sai can cikin in ina ya ce,

“Binta ba ta san inda na taho ba.”

Alhaji yayi fuska,

“Ka yi mata waya ka sanar da ita.”

Shi ma yayi fuska,

“Babu kudi a wayar.”

Wannan karon Hajiya ce ta amsa,

“Ai ba dadewa zaka yi ba, kar ka damu”

Kawai sai ya saddaqar tunda ya gansu kai a hade ya san akwai shiryayyar da suka shiryo.

Suna motarsu yana take musu baya har suka je.

Kamar yadda suka saba suka titsiye shi a falon hajiya.

Cikin dattako Alhaji ya ce,

“Alhaji Ya’u ya bijire cewa ba zai aurawa Yaks Nabila ba.”

Cike da zumudi da murna Mujahid ya ce,

“Gaskiya yayi daidai, abinda dama yakamata kenan.”

Alhaji ya sami gaba irin wadda yake so,

“Haka ne, amma saboda me ka ce haka?”

Kai tsaye iyakar gaskiyarsa ya amsa,

“Nabila na ba ni tausayi, ta cika sauqin kai, kullum fatana ta sami mutumin kirki ta aura wanda ba zai yi amfani da rashin hayaniyarta yayi ta gasa mata aya a hannu ba…”

Alhaji ya tare,

“In haka ne gaskiya na yi hangen nesa da na goyin bayan mahaifinta, sannan na zabo mata wani mutumin kirkin”

Mujahid ya sake cika da murna, har da sauke ajiyar zuciya ya ce,

‘Gaskiya ka kyauta Alhaji, na yi farin ciki na yi murna wallahi, abinda tun tuni na kasa yi kenan, ni na rasa wa zan ce ya zo ya nemi aurenta, kowa na lissafa sai in ga ba zai biya yadda nake fata ba, na san kai kuwa ba zaka taba yi mata zaben wofi ba”

Cikin dakewa Alhaji ya amsa,

“Eh gaskiya wanda na zabo mata zai iya fiye da abinda kake fata”

‘Alhamdulillah”

Mujahid ya sake fada cike da murna.

“Gobe da shi za’a daura auren, har mun bayar da sadaki sannan mun je mun rarrashi Yaks”

“Alhamdulillah”

Mujahid ya sake fada, murnarsa tana qaruwa, sai yanzu ya ji wani sanyi a ransa, yana da yaqinin Alhaji ba zai zaba mata wanda zata cutu ba.

“Ka san waye?”

Alhaji ya jefo masa tambayar katsahan.

Da kuzarinsa ya girgiza kai,

“Yanzu nake shirin tambayarka Alhaji, ina da tabbacin Nabila zata tashi, in ta ji wani mutumin kirki zata aura ba Yaks ba.”

“Hajiya dai na jin ka kana ci mata fuskar da.”

Alhaji ya fada cikin raha. Duk suka yi dariya, Hajiya ta ce,

“A to! Shi ma dan ne shiyasa ba ya shakkar fadar, don ya san shi ma ba bare ba ne”.

Mujahid dai dariya kawai yake don ya matsu a fadi mijin Nabilan don hankalinsa ya kwanta.

Kamar Alhaji ya san abinda yake rayawa sai gashi ya kantamo masa amsa,

“Gaskiya kai muka zabawa Nabila, ina fatan ba mu yi maka karambani ba”.

Ya ji kansa ya rude da qara, dakin ya shiga zagayawa da shi, ba ya cikin hayyacinsa ya dafe qirji ya ce,

“Ni kuma Alhaji?”

Alhaji ya ce,

“Ba ka ji da kyau ba na maimaita?”

Ya sake rikicewa cikin girgiza kai ya ce,

“Alhaji Nabila fa qanwata ce…”

“Kamar dai Binta”.

Wannan karon Hajiya ta sako baki.

Ya miqe cikin barin jiki,

“Ba ku gane ba ne, ba ni da sha’awar auren mata biyu har abada wallahi, a duba wannan uzurin nawa”

Hajiya ce ta amsa cikin son ta ja hankalinsa,

“Fahimtar haka ne ya sa muka ga gara a raba ka da zaman gwauranci a samo maka mata, Binta ai suna ce.”

Ya amsa kai tsaye tamkar ba su ne surukansa ba,

“Ko Yaya Binta take ita na ke so, ba na son kowa Hajiya don Allah ku bar mu mu rayu mu kadai, wai zancen cutar nan ne ya taba ranku? Na rantse muku daga ni har Binta ba mu da komai…”

Hajiya ta yi shiru cikin tausaya musu su duka, ba shi ba ba Bintan ba ba kuma Nabilan ba, in tace tana maraba da a yi wa Binta kishiya don horo ta yi qarya, kawai dai ita mai sadaukarwa ce ga mijinta, duk abinda ya kawo ba ta tankwabewa ko da kuwa tana hangen zata cutu, in shi yayi farin ciki ya ga biyayyarta ya ishe ta.

Alhaji ne ya amsa masa cikin qwarin gwiwa mai alamar babu gudu babu ja da baya,

‘Sanin hakan ne ya sanya ma muka yanke shawarar ka yi aure Mujahid, mun san komai na dangantakar da ke tsakaninka da Binta tun da ka fara sonta har yanzu da ta zabi ta shiga wuta dan ta rabu da kai, kai kuwa Mujahid menene abin so a irin Binta, to ba a hana ka son ba, amma dole ne ka ajiye iyali nagari a gidanka, nan gaba zaka gode mana, kuma daga sannan ba zaka sake sha’awar yin wani auren ba…”.

Yana nuna Hajiya,

“Ta ishe ka misali, ko mutuwa ta yi zata wawushe damar in ji sassauqa ne in sami kamarta…”

“Don Allah Alhaji a janye min wannan Uqubar… na rantse da Allah ni riqon qanwa nake wa Nabila, ko yaya gidana yake ciki ni haka yake min dadi…”

Alhaji ya tare shi da nuna masa hanyar fita,

“Tashi ka tafi gida ka yi tunani zuwa goben, in kana jin lallai ba zaka iya haquri da karambanin da na yi maka ba to ka zo da wuri ka nuna min iyaka ta, in kuma na ji shiru zan karbar maka aure, Allah basshi idan kana jin qwarin ido kana iya sakinta.”

Da alama Mujahid sam ba ya cikin hayyacinsa, bai tanka wa kowa ba yana ta faman tangadi ya tashi ya tafi.

Alhaji bai ji ko dar ba ya mayar da kallonsa ga Hajiya wadda jikinta yayi sanyi ta yi qasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta, ba ya shakkar in ba mintsinin zuciyarta lamarin ke yi ba, jinjinawa take, wacce macace ta sami Namiji kamar mujahid take watsarwa irin Binta? Ta yi wa kanta.

Ya dawo da hankalinta da yabon da ya saba yi mata wanda yake jin yana qara kashi ashirin na biyayyarta gareshi.

“Yau ma zan gode miki bisa hadin kan da kike ba ni, na san tabbas ba ko wacce maca ce zata goyawa mijinta baya ya rakitowa ‘yarta Kishiya ba, to ni na yi ne don ba ni da haufin yadda kike jin Binta ‘yarki ce, haka kike jin Mujahid da Nabila ‘ya’yanki ne, babu wanda zaki so ya cutu, na gode da samu mace tagari irinki, ina miki fatan Ubangiji yayi miki sakayya da gidan aljanna, sannan ina roqon dukkansu ki sa su a addu’arki.”

Ta yi dabarar goge qwallar da ta taru a idonta tana qara jin wata nutsuwa a ranta, in mijinta ya yarda da ita tana sa ran yardar Allah,

“Insha Allah, Allah ya sa haka ne mafi alkhairi”.

Cike da jin dadi ya amsa,

“Amin” 

*****

Daga lokacin da aka sallace Isha Binta ba ta ga Mujahid ba ta shiga duban hanya da jin shiga ukun ina ya shiga bai dawo ba.

Duk qarar Motar maqota da ta jiyo sai ta sa ran ina ma shi zai shigo, ba don ta damu da ganinsa ba, sai don kawai hankalinta ba ya kwanciya idan yana waje, ba ta son ta bincika don ta san zata iya samun amsar ya je wajen Nabila, a guraren zuwansa nan ta fi tsanar a ce ya je.

Qarfe goma ta ji zuciyarta na neman babbakewa da zargi da kishi, ta kasa shawo kan fushinta da tashin hankalinta sai da ta fara nemansa ta hanyar dabara, wayar Nabila ta kira a zuwan gaisuwa kawai, amma sai ga shi mahaifin Nabila ne ya daga, suka gaisa cikin karramawa, sannan ya ce mata,

“Qanwar taki ce babu lafiya, tun daren jiya aka kwantar da ita a asibiti.”

Ta jinjina cikin jimami da yin jaje, sannan ta yi qorafin rashin sanar da ita da aka yi, sai baban Nabila ya ce,

“Ki yi haquri, ai mun zaci Maigidanki ya fada miki, tunda ya kira wayarta a dazu da la’asar aka sanar da shi, yanzu bai jima ma da barin nan ba.”

Binta na qoqarin boye kuka ta ce,

“Eh, ina wajen aiki na ga Missed call dinsa, babu mamaki abinda zai fada min kenan, Allah ya ba ta lafiya, yanzu dare yayi sai dai gobe zan zo, dama gashi gobe asabar”.

Da haka suka yi sallama ta koma wa taguminta, da jin ciwo kala-kala akan zuwan Mujahid har sama da qarfe goma, da da ne tabbas ta san sai ciwon Nabila ya fi damunta fiye da komai,  amma yau ita ta Mujahid kawai ta ke.

Qarfe sha daya saura ta ji shigowarsa, duk qoqarinta na ta kama kai sai da ta sami kanta da zirga-zirga a falo, so kawai take ta ga ya shigo falon, komai runtsi yau sai ta fada masa ba ta son mannewar da yake wa Nabila.

Amma me? Kamar a guje da yanayin tashin hankali ta ji ya haye benensa, nan fa gabanta ya cigaba da faduwa, tana ta saqe-saqe iri-iri, zai sakko ya shigo, ba zai sakko ba, har aka rufa sha biyu daidai, inda ita kuma ta tabbatar in ta jira gobe, zai yi wahalar ta kai da lafiyar da zata iya bin ba’asi saboda tsabar dukan zuciyar da take ji. Kawai sai ta zura hijabi ta haye benensa.

A bude ta sami qofar dakin, kawai sai ta sa kai, suka yi kacibis yana tsaye cikin yanayin damuwa yana safa da marwa, kallo daya ta yi masa ta tabbatar lallai a cikin matsananciyar damuwa yake, kishi ya soke ta don ta qaddara dalilin rashin lafiyar Nabila yake wa damuwa ko kuma dalilin gobe zata auri wani ba shi ba.

Ba tare da ta shirya ba kawai ta ji ta fara tuhumarsa cikin zafin rai,

“Mujahid ka san kana son Nabila amma tun farko na dinga yaqin hada ku da juna ka dinga tankwabar da tayina?”

Da rashin hayyaci yake kallonta, ko dan kadan kwanyarsa ta kasa karbar tuhumarta ta juya wani tunani akan ta, ya saki baki sosai yana kallonta.

Ta kada kai tana son barkewa da hawaye,

“Kana can wajenta ko? Da ka yarda tun tuni ka aureta qila ita ma da bata janyowa kanta suma a kanka karo na biyu har da zaka je raba dare a wajenta ba”.

Har yanzu ba shi da niyyar tanka  mata, wani mugun haushinta yake ji don ita ta janyo masa ko ma menene, bai taba sha’awar yin mata biyu ba, kuma da akwai sarari na sha’awar ya tabbatar yadda take tsananin sonsa, da tuni da kansa ya zabi auren Nabila, bare wani ya sami damar zabar masa.

To gashi nan taurin kan wannan rigar silikin nasa da dabi’arta na kasa duban abinda zai je ya dawo ta janyo ana neman hargitsa masa zubin labari.

“Kullum kana kira na rigar Siliki kai kuma rigar menene, rigar Satin? Ka na son yarinya ba ka san kana sonta ba? Yakamata ka cece ta tun tuni a matsayinta na wadda ta fada tarkon sonka, amma ba zaka yi jihadin ka aure ta ba? Dole sai ka jawo ni rayuwarka ni da ba na sonka ka cigaba da wahalar da numfashina? In goce yin abinda ya dace shi ne matsayin rigar siliki, kai ka fi cancantar sunan, don babu wata hujja da za a kalla a ce in na aure ka jihadi zan yi, amma in ka auri Nabila shi zaka yi, sannan in ka auri abinda kake so ba ka san kana so ba zama lafiya zaku yi…”

“To ai magana daya kike ta maimaitawa, ki sami wata daban ki fada mana”.

Ya tare ta cikin numfarfashi da alamun gajiyar zuciya da murya…

Bai bata damar ta yi magana ba ya cigaba da magana,

“In abinda kunneki yake muradi shi ne ya ji na wanke kaina da cewa ba na son Nabila, to ina yi masa kaicon har abada ba zai ji ba, wanda na fada ma tun tuni na yi istigfari”.

Ta fara kukan,

“Ai dai ban ce maka abinda nake son ji kenan ba, ni kawai ina qara ba ka labarin cutar da ka yi min ne, kana son ‘yar uwata, ka aure ni?”.

Ya nuna mata qofa,

“To Qurunsqus, in kin gama ba ni labarin sai ki tafi, ina son kadaici.”

Haushin duniyar nan ya cika ta, da kyar ta samo maganar fanshewa,

“In fita in bar ka ka yi kukan zata auri wani ta bar ka gobe dai”.

“Ko kuma ki fita in cigaba da tsallen murnar zan aure ta gobe dai”

Ba ta san lokacin da ta saki tsaki ba, ta juya ta fita tana cewa,

“Nabila ta zama goma ka auro su duka, a kaina zasu zauna? Ni damuwata ita ce zama da kai ba zama da matanka ba.”

“Madalla”

Ya bita da tura haushi, yayin da shi ma haushin yake ta faman cika shi, sakaryar yarinya ana son ta ba ta san ana sonta ba, sai wani ne zata ce yana so bai san yana so ba.

Ya ja dukkan maganganun da ta yi masa ya watsa su cikin wadanda yake nazari.

Ba wai Binta ce kawai ba zai iya fadawa ba ya son Nabila ba, a kunne kowa ma ba zai iya fada ba in dai maganar zata koma kunnen Nabila, dalilin abu biyu, na farko don karamcinta gare shi, na biyu kuma don qila in ta ji ya zama sanadin da zuciyarta zata buga ta rasu ta bar shi da alhakin kashe ta.

Haka ya dinga rayawa, yana tuno hanyoyin da za’a janye masa auren Nabila ba tare da an bayar da labarin shi ya ce ba ya sonta ba.

Har garin Allah ya waye bai tuna komai ba, cikin kwana dayan nan ya fita daga hayyacinsa, tamkar wanda ya rasa iyali duka.

Tun da ya dawo masallaci ya shige dakinsa ya turo qofa har da murza Mukulli, sai ka ce yana hasashen Binta zata sake shigowa ta cika shi da gori da qorafi.

Qarfe tara ya dinga jin wayarsa na ringing yana yi mata banza, don ya qaddara kawai Alhaji ne ke kiransa ya ji ta bakinsa, shi kuma ba shi da abin cewa, amma yana da dabarar babu yadda za’a yi su daura masa aure ba tare da yardarsa ba.

Can dai ya janyo wayar ya duba, abinda ya sanya zuciyarsa bugawa da sauri shi ne, Nabila ce ke kiransa, missed calls Tara.

Ya ji kansa yayi wani nauyi zuciyarsa na neman tsayawa da aiki,

Yana jin qyashin ya kira ta amma zuciyarsa ta damu da son sanin menene Matsalarta? Shi ne mashawarcinta da shi ta saba shawara, sannan ko mai ya taso mata shi take nema, yanzu in ya bar ta yayi adalci?

Yana cikin hada bara da bana sai ga ta ta sake kira, cikin barin jiki ya daga, kukanta ne ya fara dukan kunnesa, sai ya ji zuciyarsa ta karye, sai dai bai tanka mata ba, cikin kuka ta shiga ce masa,

“Dadi ya fasa aura min Yaks Yaya Mujahid, wai wani zai aura min, don Allah ka shiga lamarina ka binciko min waye, kar su je kuma su aura min dan giya”.

Ta sake shaqewa da kuka.

Ya sake shiga damuwa don haka ya kasa rarrashi, kodayake dama bai saba ba, in ma ya saba yanzu Nabilan ba ta cancanci rarrashi ba, to a kan me ma zai rarrashe ta?

“Ayya!”

Ita ce kalmar da ya dage ya fuzgo, ya bata kyautarta.

Da ta cigaba da kuka sai ya ce mata,

‘Kar ki damu, ina nan ina ta yi miki addu’a, har abada ba zaki hadu da abunda ba kya so ba.”

Ta ji wani qarfin gwiwa ya shige ta, nan take ta ja bakinta ta rufe, soyayyarta na da imanin duk Addu’ar da masoyinta yayi mata Insha Allah Ubangiji zai karba, don tana son sa saboda Allah ne, ba bisa wani qyalli ba.

“Na gode yaya Mujahid”

Kalmar da ta dinga maimaita masa kenan, shi kuma ba ya jin komai a zuciyarsa na shauqi ko tausayi, don ma su yi sallama ya ajiye wayar ya ce,

“To Yaya jikinki?”

Ta dan yi nishi,

“Na ji sauqi yaya Mujahid.”

Da sauri ya ce,

“To Allah ya qara lafiya, zan shigo idan na dawo wajen daurin auren.”

Wani kukan ya nemi qwace mata amma ta riqe abinta, don ta san fitowarsa yanzu fallasar abinda ke ranta ne, don dalilinsa shi ne, zata auri wani ba masoyinta ba.

Ya ajiye wayar ko sallama ba su yi ba. Sai Nabila ta ji jikinta yayi mugun sanyi, don ba haka suka saba magana da Mujahid ba. Qwallah ta fara sakko mata daidai da daidai.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 43Rigar Siliki 45 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×