Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Rikon Sakaina by KamalaMinna

Ammi ta faɗi tana kama haɓa, gami da nuna alamun mamaki ta hanya fiddo da idanunta waje sosai, masu kama da ƙwan tsaka. Kafin ta lumshesu a hankali. Zuciyarta taji tana kara tunzura ta, akan ta amince da zancen da Juma ta zo mata dashi wanda ta tabbatar in tayi amfani da shawarar ba ƙaramar biyan buƙata za ta samu ba.

Sai dai kuma in tayi wani tunanin ta taɓa wannan kudirin amma kuma haƙarta ba ta cimma ruwa ba don ta tabbata Maqsood ya ji labarin za ta sake tura Zubaida yawon bara tabbas ba za su kwashe ta dadi dashi ba.

‘Ɗan ki ne fa ke kika haifeshi a cikin ki. Dole ya bi abin da kika ce dashi in har yana neman albarkarki.”

Wani sashi na zuciyarta ya shiga zayyona mata. A hankali ta tura laɓenta na ƙasa cikin baki ta ciza tana mai sake duban Juma wacce tayi ƙasake tana faman gabzar goro bakin nan nata yayi ciɗin-ciɗin da tukar goro laɓɓan sun yi jajir ko yaya ta buɗe bakinta kana hango jajayen haƙoranta da suka fice daga hayyacin su.

“Ba ke za ki wahala ba. Sannan ba jari za ki zuba ba bare ki ce kina tsoron asara. Riba ce kawai ta zallar kuɗi za ta ke kawo miki kina zaune a ɗaki.”

Ɓarin zuciyarta ta sake zayyana mata cike da ƙarfafa mata guiwar ta amince da shawarar Juma da kuma na zuciyarta ta.

Sai dai duk da Maqsood ɗan tane tana jin shakka akansa musamman in akace al’amari ya ta’allaƙa da Zubaida ne rayukar kowa ɓaci yake a gidan. Sai dai kuma a wannan karon ba ta jin akwai wani rai mai motsi da zai hanata cimma burinta game da Zubaida. Dole ta bi umarni da zata ginya mata in har ta buƙatar rayuwa cikin aminci a gidan nan. Ubanta dake iko da ita ya shuri burji. Maqsood shi kuma yana wajan yawon gantalin karatun bokon da ya ƙwallafawa rai wanda bata da tabbacin dawowarsa nan kusa.

“Ammi ki kula da Zubaida. Rauninta yana da yawa don Allah kar ki takura mata akan abin da kika san ba za ta iya shi ba. Na miki alƙawari ko na tafi zan dinga yi miki aike zan kama sana’a acan in na samu faragar karatu. Ban da talla Ammi kar Zubaida tayi talla ki bar ta a iya makaranta kawai. Ko aike in me nisa kar ki tura ta ki samu yaro ko nan maƙota ne ba za su ƙi zuwa ba. Don Allah Ammi ki min wannan alƙawarin.”

Kalamansa ne suka shiga dawo mata a ranar da zai bar ƙauyensu zuwa birni don cigaba da karatunsa na boko. Karatun da tace ita bata ga amfaninsa ba illa ɓata lokaci. Amma ya nuna mata cewa ƙaratu shine ginshiƙin rayuwar duk wani matashi mace ko namiji sannan yana so ya yi karatu ne don tallafar rayuwar Zubaida da lalurarta.

Sai dai a yanzu bata jin wannan alƙawarin na Maqsood zai yi amfani don tuni ta sanya ƙafa ta shure shi gami da murjewa kamar yadda shi ma ya shure alƙawarin zai dinga yo mata aiƙe gashi yanzu kusan watansa biyar kenan da tafiya zuwansa biyu amma me ya haɗa dashi illa dubu uku kacal suma kafin ya tafi dashi aka lashe su a girkin gida.

Don haka ba ta jin zata tsaya jiran tsammanin warabbuka. Bata jin zata tsaya ta shure hanyar samu da ta zo mata a saukaƙe ta ɗauki hanyar da bata da tabbas ina! Hakan ma ba zai yuwu ba.

Gyara zaman ta tayi sosai akan kujera ƴar tsugunno da take kai tana mai duban Juma wacce take ta fama da goro a baƙinta.

“Juma na amince.”

Da sauri Juma ta dubeta bayan ta tofar da tuƙar goron ta washe mata baki gami da tafa hannaye.

“Yanzu naji batu ƴar gari. Amma da kin zauna kina ƙokarin yi wa kan ki sagegeduwa. Ga ki da haja a gida amma kin ƙasa gano yadda za ki yi ki sarrafa ta kawo miki kuɗi.”

“Ya za ayi kenan?”

Ammi ta faɗi tana duban Juma wacce ta tsoma hannu cikin bokitin ƙarfe mai ɗauke da ruwan dauraya na wanke wanke da Ammi take. Ta ɗebo ruwan tana kuskure bakinta dashi ta watsar kafin ta dube ta da yanayi na zaƙwaɗi.

“Ya ya kuwa za ayi?. Ai kawai sanar da ita za ki yi ta shirya wa sabuwar rayuwarta. Ki lallameta ki nuna cewa hanyar samu ce bara ba sisin ka na jari amma zaka samu maɗuɗan kuɗaɗe wanda za ka fita tsara wajan biyan buƙata. Ni na tabbatar miki da cewa in har Zubaida ta amshi wannan tsarin kafin wani lokaci kun fara maido da kumarinku. Sai dai ki ji ana Hajiya Danejo.”

“Da kuɗin barar?”

Ammi ta faɗi cike da mamaki jin abinda Juma tace. Ita kau ganin yadda Ammi ta nuna mamakin ta a fili ya sanya Ata gyara zama sosai.

“Zauna nan ke ce kan ki a duhu. Amma na rantse miki da mijin farkona Salihu. Bara har hajji ta kai masu yinta wasu kau gida ƙerarre suka gina. Wanda ko masu ƙuɗin ƙauyen nan ba su isa su yi irinsa ba.Ke in takaice miki ma ni naga tsohuwa mai bara wacce aka ce motocinta da baburanta da ta saya ta bada haya sun kai arba’in.”

Ammi ji tayi zuciyarta ta buga da hanzari wani shauƙi da hango wata rayuwar dola na haska mata cikin zuciyarta. Tana hango cewa itama gashi ta ƙera gida na fitar hankali sun fita daga ƙauyen nan mai cike da ƙunci da rashin wayewa sun koma birni sun ƙafa rayuwar ƴanci.

Hango kanta take ta zama wata hamshaƙiyar hajiya tana rayuwa mai cike da hutu fatar ta ɗin nan da ta yankwane duk ta murje ta yi haske ta mulka kibarta. Duk a sanadin bara da Zubaida ta hango ta fara yi har ta tara kuɗaɗe na fitar hankali.

“Mota fa kika ce. Motar da aka ce tana kai wa miliyan?”

Harara Juma ta galla mata kafin ta motse baki.

“Zauna nan. Shiyasa rayuwar ƙauye bata yi ba wallahi. Ko ya ya ka shiga birni. Ruwan birni ya wanke ka tuni tunaninka zai sauya wallahi.”

Dafa kafaɗar Ammi tayi ta kureta da idanu kamar mai ƙokarin hango wani muni nata kafin ta nisa.

“Ni na faɗa miki Danejo mota ta sama da miliyan daya akwai ta kuma za ku iya mallakarta. In har kika bi shawarar da na baki. Yanzu dai ina Zubaidar take?”

“Tana makaranta.”

“Dole a datse karatun nan. Karatun nan musamman na boko ba uwar da zai tsinana mata a rayuwa wahalar da kai ne kawai. Ɗiya mace musamman a ƙauye irin wannan ba daraja karatunta ake ba illa in ta girma maƙerin budurci ya fara ƙerata a aurarta da ita. Karatun addinin in ta samu na sallah shikenan can ta ƙarata gidan mijin shikenan rayuwarta.A birni aka san darajar karatun boko ake ɗaukaka shi. Amma ke kan ki kin ga yadda ake wa ƴaƴa mata game da karatun boko a ƙauyen nan. Nayi mamakin yadda kika bar zubaida na karatu.”

Numfashi Ammi ta zuƙa mai cike da damuwa barkatai. Ita kanta ba son karatun bokon nan take ba don bata ga amfaninsa ba amma Maqsood ya ƙwallafa rai akan dole sai tayi shi kullum maganar shi ɗaya ce.

“Karatun nan shine rufin asirinta Ammi. Ba ita kaɗai ba har dake so nake Zubaida tayi ƙaratu har matakin digiri don shi kaɗai ne zai rage mata raɗaɗin raunin da take tattare dashi a rayuwarta. Karatun nan shi zai bata damar taimakon kanta da tsarawa kanta rayuwa mai inganci bata tare da tayi duba da rauni da tawayar da takeda ita ba. Ki bar ta tayi karatun nan Ammi auren da kike magana akai kina kallon dai yadda ake mata kallon nakasasshiya a garin nan. To wa kike zaton zai aureta a hakan?. Tunda sun rigaya sun caffi halittar ta. Ƙarancin imaninsu dana ilimin addininsu ba zai taɓa barin su su fahimci cewa ba ita ta halicci kanta a haka ba. Sannan Ubangijinta ba wai bai sonta bane ya yi ta a haka jarabawar ce ta rayuwarta haka shiyasa naƙe so mu ƙarfafa mata guiwa muyi mata duk waniabu da zai rage mata tunani da damuwar da take shiga game da yadda mutane suke zareta daban. Karatun shine yafi dacewa da ita. Wata rana ba ke ba hatta su mutanan garin sai sun yi alfahari da ita.”

A duk lokacin da ta tuna dogon sharhin nan nasa abubuwa da yawa take ji suna sare mata a zuciya.

“Tunani duk ba naki bane yanzu. Kawai ki datse karatun nan ki rabu da Maqsood shi namiji kome ya yi ado ne sannan ba wanda zai saka shi bare ya hana shi yadda yake da ƙafaffiyar zuciyarnan kamar arnan zamanin annabawa. Alllah in kika biye masa ba za ki taɓuka komai ba sai dai ku kasance a haka iyakar in ya zo ya cika ki da surutun banza irin nasu na ƴan bokoko a wuta.”

Dariya Ammi tayi jin yadda Juma ta faɗin kalmar ‘boko’ ɗin da yadda fuskarta ta nuna kamar taga abin ƙyama.

*****

“Zubaida Ahmadi”

Duk yadda jiƙinta ke rawa da ƙokarin ƙara sauri don isa gida a dalilin nasarar da ta samu na tsallakewa daga aji biyu zuwa aji uku a makarantar su. Sannan ta kasance a sahun farƙo a daliban ajinsu wacce tafi kowa yawan marking. Ji take duniyar gabaɗaya na juya mata da tsananin farinciki da murna tana hango yadda burinta da fatanta za su cika nan gaba kaɗan na zama wata ƙwararriya a harkar zane zane abin da ta fisu kuma take burin zama a rayuwarta.

“Karatun ki shi zai tabbatar miki da burinki. Dagewarki shi zai tabbatar miki da nasararki Zubaida. Ki yi ƙokari sosai ki samu nasara har matakin ƙarshe ni kuma nai miki alkawarin kai ki birni ki ɗaura karatu har ki cimma burinki da fatan ki.”

A duk lokacin da nasara ko ya ya take ta same ta a makaranta ba wanda take tunawa sai ɗan’uwanta rai ɗaya tilo. Wanda duk wani buri nata da son ƙaratu nata shi kaɗai yake goya mata baya tun daga cikin gidansu har kewayan ƙauyen su na karmami. Yaa Maqsood. Shiyasa ko yaushe bata mantawa dashi a duk daƙika na rayuwarta.

ƙwarin guiwa da yake ƙara mata tana jin sa har karkashin zuciyarta yana ƙara tabbatar mata dacewa ita ba musakar da zata kasa cimma burinta bane a rayuwa kamar yadda kowa yake mata kallo. Bata so tasirin maganar mutane game da yadda take jinsa a zuciyarta ya yi tasiri. Shiyasa a kullum take ƙokarin shafe shi sannan ta ɗau ɗammara don shafe musu wannan tunanin nasu nacewa musaƙi bashi da amfanin komai a rayuwarsa illa ya dinga bi gida gida ko bakin hanya yana bara.

Barar da ita kuma a rayuwarta tana sahun farko a shika shikan abin da tayi wa muguwar tsana, tsanar da take jin ta har karkashin zuciyarta a duk lokacin da kalmar bara ta doki kunnuwanta tana jin ɗacinta har saman harshenta shiyasa ko ƙaɗan ta ƙi barin wata ƙofa da zata fito da za a jingita da wannana kalmar. Alkawari tayi wa kanta har abada ba za ta tsinci kanta a wannan yanayin ba.

“Zubaida Ahmadi”

Muryar taji ta sake ratsa kunnuwanta sautin na zarcewa har cikin zuciyarta da wani irin yanayi mai girma da ya sanya gangar jikinta motsawa. Lumshe idanu tayi ƙafin ta kara daidaita tsayuwarta akan ƙafarta ɗaya lafiyayya.

Tunda ya kira sunanta ta tabbatarwa kanta waye don ko a cikin barci taji muryarsa sai ta fahimta balle ido biyu. Numfashi ta shaƙa ta fesar kafun wani murmushi mai nuni da farinciki ya ƙwace mata a ƙyaƙƙyawar fuskarta har dimple ɗinta na lotsawa.

“Uncle…”

Ta shiga ƙokarin faɗi. Amma ganin ya zagayo ya zo gabanta ya harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata mayun idanun nan nasa masu karya mata duk wani ƙwarin jiki dana zuciyarta da take dashi.Hakan ya sanyata yin shiru tana cigaba da murmushin nan dai wanda ya kasance mata na musamman a duk lokacin da abin farinciki ya sameta duk da fuskarta bata rabo da murmushi ba kasafai ake gane fushinta ko damuwarta ba amma dai wannan murmushi kamar yadda Yaa Maqsood ya masa laƙabi da MURMUSHIN ALƘAWARI a duk lokacin da shi kansa ya ganshi a fuskartar yana tabbatarwa akwai abin alheri a tare da ita a wannan lokaci.

“Da wuri haka za ƙi gudu. Duk yau ba mu gaisa ba.”

Ya faɗi yana mai sake ware idanunsa akanta. Shi dai bai san me yasa ba tun ranar da ya fara cin karo da ita a makarantarsu a matsayin ɗan bautar ƙasa (NYSC) sannan Malamin Biology yaji Zubaida ta burge shi sannan lokaci guda ta samu gurbi mai girma cikin zuciyarsa ya ajje ta musamman da ya lura da ƙokarin ta da maida hankali a ƙaratu sannan kuma matashiya mai ƙarancin shekaru mai ɗauke da baiwar zane zane shikenan suka ƙulla ABOTA.

Abotar da yake jin ta ta fita daban a duk wata abota da ake yi tsakanin abokai ko ƙawaye. Abotar da yaji cikin ƙanƙanin lokaci ta riƙiɗe ta koma wani rayayyen abu a cikin zuciyarsa mai kama da so.

Ya yarda yana son Zubaida a lokacin da tunaninsa da mafarkansa suka mamaye da nata a lokacin da idanunsa a buɗe ko cikin barci taswirar Zubaida ta kasance abin ƙawatuwa a cikinsu. Ya tabbatar wa kansa da cewa ya kamu da sonta don duk wasu alamomi na so sun tabbata akansa. Sai dai ya kasa dubanta yace mata yana son nata. Ya rasa ta wacce hanya zai bi don ganin ya sanar da ita. Gani yake kamar ba dacewa a wannan matakin a yanzu. Shekarun ta yake gani sun yi ƙanƙanta zuciyarta bata yi girman da za a dasa mata kalmar so ba. Sannan shi kansa ya san da cutarwa ace ya dube ta ya gurɓata mata rayuwa da soyayya a wannan mataki da ya kamata ace ya bata duk wani hope na ganin ta samu ingantaccen ilimi ta hanyar wankakkiyar zuciyarta mai cike da buri da fatan son ilimin.

Sai dai me ya kasa jure haka yana wahaltuwa yana azabtuwa sosai da soyayyarta. Sai dai kuma wani ɓarin na zuciyarsa yana kashe masa duk wani karkashinsa akan cewa in har ya dube da kalmar so kamar ya ɗauki ƙaifaffen almakashi ya datse mata buri da fata da take dashi akan karatunta.

“Zatona baka zo ba shiyasa.”

“Waya ce miki ban zo ba?”

“Ganin baka shigo ajinmu ba.”

“Me yasa ba ki je Office ɗin mu kin duba ba?”

Da sauri ta ɗago ta dube shi a ɗan razane kafin tayi ƙasa da idanuwanta tun kafin ta rasa ƙarfin guiwarta nayi masa magana. Sai da ta fizgi numfashinta daƙyar kafin ta buɗe baki a hankali.

“Abida Sani ce. Tace min taje wajan Uncle Bashari bata ganka a cikin Office ɗin ba”.

“Shine aka ce miki kuma ban zo ba. Kawai dai ba ki damu dani bane?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Rikon Sakaina 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×