Skip to content
Part 9 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

SADIYA

Sallama na yi gunku mutane ga wani labari

Labarin soyayya ta mai haɗari

Na san in kuka ji shi tabbas za ku yi tausayi

Ƙaddara ce ta sani na faɗa yanayi.

*****

Na faɗa kogin son Sadiya

Ita ce burina kullum a zuciya

Har ma an sa mini suna na Sadiya

Ko ina na bi sai ka ji an ce na Sadiya.

*****

Bari in ɗan baku misalin ta Sadiya

‘Ya ce mai kyau tamkar zinariya

Haske na idanunta kai ka ce zara ce

Murmushinta yakan iya sa ma a haukace.

*****

Kyawawan laɓɓanta ke sani na ɗimauce

In tana dariya sai in ji ni kamar zan zauce

Dogayen yatsunta su ke daɗa ruɗa ni

Kumatunta da laushi babu muni.

*****

Ƙamshi na turaren ta shi ke daɗa tunzura ni

Haske na haƙoranta shi ke faɗa burge ni

Kyakkyawan hancinta dogo mai ɗan tsini

Ke sa in ji kwanyata na hautsini.

*****

Kyawun tafiyarta a kullum ke daɗa ɗasa ni

Sadiya ‘ya ce kuma mai addini

Ta yi riƙo da shi ba wasa ko ƙanƙani

Jama’a na cewa tana da imani.

*****

Sautin muryarta da daɗi kamar na Rani

Ita na zaɓa a cikin damina ko rani

Alaƙar mu ta yi nisa ko ɗaya babu shinge

maƙiyan mu fa sai kallo kuma sannan sai hange.

*****

Shirin auren mu fa kowa shi ya dage

An kammala komai har lefenta babu coge

An ɗaura mana aure kowa na murna

Da ma wannan ranar ita ce burina.

*****

In ga an ɗaura mana aure ne fatana

Bayan an kammala shagali kowa na murna

Ni ko in ganni a ɗakinta shi ne burina

An hau mota da ita da nufin za a kaita gidana.

*****

Motar ta yi hatsari kan titi da rana

Aka kwashe su sai asibiti da rana

Nan take fa ba wasa aka yo kirana

Ko da na ji abin da ya faru da mai sona

*****

Ban san me ya faru ba sai saukar ruwa a jikina

Nan take muka nufi asibitin da abokaina

Mun iske su Abba a gefe ga Ummina

Sun yi jugum fuskar kowa babu murna

Nan take na hau tambayar ina mai sona?

Aka nunan ɗakin na shiga ba na ko kallon gabana

Ko da shiga ta nan take nai wani ƙaraji

Sadiya ce gata a kwance cikin bandeji

*****

Nan take na ji ni juwa nake ji

Na matsa gunta zuciyata na raki

Idanunta suna motsi amma sam ba baki

Na kasa fa cewa komai sai fa rawar baki

*****

Na matsa kusa domin in ji bugun numfashi

Sumba ɗaya tai min tak a goshi

Daga nan komai ya tsaya ba motsi

Sarkin da ya yi ni ya yo Sadiya

*****

Ya karɓe abinsa a yau ba tankiya

Ina miki roƙon rahama da shiga Aljanna

‘Yan uwa wannan shi ne labarina

Ku taya ni du’a’i Allah ya jiƙan mai sona

*****

Domin son ta yana nan a cikin ruhina

Soyayya dai daga yau ku sani na daina

Wataƙila ma har ana bazan ƙara ba

Domin tamkar sadiya ba lallai in samu ba

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 7

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 8Fasaha Haimaniyya 10 >>

2 thoughts on “Fasaha Haimaniyya 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×