Skip to content
Part 12 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Sun isa Ji-kas lafiya, wadda ke karkashin karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa. Maigidan Hajiya, Malam Halilu, shi ne babban limamin garin Ji-kas, saboda haka gidan na Hajiya ba boyayye ba ne. Ga kuma gyaran da Ma’aruf ya yi masa ya zama abin kwatance, in za a yi kwatance za a ce gidan Hajiya Saude farin Gida, kamar ita kada ke da gidan babu kishiya.

Hajiya ba ta kara haihuwa ba tun Ma’aruf, wannan kuma tsarin Allah ne, kuma hakan bai sa Malam Halilu ya taba canza mata fuska ba ko sau daya, don shi yana da ‘ya’yan har takwas duk maza, wadanda ke karatu karkashin kulawar Ma’aruf. Tafiya da Hajiya ke yi ta huta wajen Aisha bai taba damuwa ba. Haka yanzu da ta ke jinyar jikanyarta

Akwai kyakkyawar fahimta tsakaninsu. Kishiyarta Lami ba wai ba ta kishinta ba ne, kawai wutsiyar rakumi ce ta yi nesa da kasa, don gabadayansu har maigidan kamar karkashin inuwar Hajiyar suke, shi ya sa ta shafa wa kanta salama, ta kwantar da kai ta ke cin arziki hankali kwance.

Yaran makota suna ta tsalle suna murna Hajiya ta dawo, don sun san tsarabar chaculet ta zo, suna ta kwaso kayanta suna direwa kofar dakinta. Ta sa mukulli ta bude dakinta, ya yi kura sosai, kwana arba’in da biyu ba kwana biyu ba. Ta rasa me za ta ce musu, tunda yau daga asibiti ta ke ba ta da alawa. Sai ta sa mai aikinta Tambai ta gyara dakin, ita kuma ta salami yaran da kudi ta ce su je su sayi alawar. Ta fada kewaye ta yi wanka, ta yi sallar la’asar da ta riske su a hanya. Ta kwanta tana hutawa, Tambai na ba ta labarin abubuwan da suka faru ba ta nan na suna, biki da mutuwa. Hajiyar ta jajanta, ta ce, in ta huta duk za ta leka, koda yake kwana uku kacal za ta yi, Aminatu na asibiti har yanzu.

Tambai ta gama abinci lafiyayye, ta zubo mata. Lami ta shigo suka gaisa ita ma da nata kabakin abincin. Hajiya ta yi godiya ta zauna tana jajanta jikin Amina, a hakan Malam Halilu ya dawo ya riske su.

“Yau babbar bakuwa gare mu ashe?”

Abin da ya fara fada kenan yana ta fara’a, da gani ya yi murnar ganin matar tasa.

Ta ce, “Ga ni nan dai, duk da ba zama zan yi ba zan koma, har yanzu Mamar Manzo na kan gadon asibiti”

Ya ce, “Assha! Allah sarki uwata, Allah ya kara afuwa. To yaushe za ki koma ke nan?”

Lami da ta ga sun manta ta a wajen sai ta fita ta ba su waje, dan kishi-kishi na cin ranta. Don in ka ga maigidan nasu na wannan fara’ar to tabbata a gaban Hajiya Saude yake.

Bayan sallar isha ya dawo daga masallaci ya ci abincin dare, duk a dakin Hajiyar, ta ke gaya masa abin da ya taso ta rana tsaka, wato nema wa Ma’aruf aure na gaggawa.

Malam Halilu ya gama sauraronta, ya gyada kai.

“Kirawo min shi mu yi magana yanzun nan, akwai kuskure cikin al’amarin nan.”

Hajiya ta dauko wata katuwar (cellular) wadda ake amfani da ita a wancan zamanin, duk da haka sai masu hannu da shuni ke iya rikewa. Ta danna kiran Ma’aruf.

Yana dakin tattaunawa da dukkan ‘yan majalisar Najeriya, ya manta bai kashe tafi-da-gidansa ba, kiran Hajiya ya shigo da sunan da ya yi ‘saving’ dinta ‘MA MERE’ wato

‘uwata’ da harshen faransa. Sai ya fito waje ya amsa saboda dukkan uzurinsa ba ya ignoring kiran Hajiya.

“Karbi, Imam ke son magana da kai.”

Ya karba suka gaisa da Malam.

Malam Liman din ya tambaye shi, “In kana kan uzuri mu bari sai ka koma gida ka samu nutsuwa.”

“Babu komai, mun gama. Yanzu kowa zai tafi”.

Malam Liman ya ce, “Madallah.

Wato na ji kuna son yin wani shirme ne kai da uwarka, aure ba abin wasa ba ne, ba kuma wasan yara ba ne. Umarnin Ubangiji ne, don haka dole a tsarkake niyya wajen yinsa.

Kuna so ku ce don siyasa za ku yi aure, wanda wannan aure ba karbabbe ba ne a wurin Ubangiji. Ka sanya ikhlasi a zuciyarka, cewa za ka yi auren sabida Allah ba don ka ci siyasa ba, sannan ka ga matar sau uku don ka tabbatar da lafiyarta kalau kamar yadda Manzo (S.A.W) ya yi umarni. Ku tattauna, ku aminta da juna, a yi baiko sannan a sanya lokacin aure. Wannan shi ne aure, ba ka ce ta zo ta nema ma aure kai babu ruwanka ba ko ganin matar ba ka yi ba, wannan aure bai yi ba.”

Haka ya yi ta jawo masa nassi na Alqur’ani da hadisi masu nuni da tsarkake zuciya wajen yin aure ba don cimma wata manufa ta duniya ba.

Jikin Ma’aruf ya yi ligib, yana son dattijon ko don farke gaskiyarsa a kan komai, tsakaninsa da Allah ba irin malaman da ke ba da fatawar son rai don a ba su wani abu ba.

Ya ce, “Malam, na yi niyyar aure da zuciya daya, ku zaba min mata kowacce iri ce, zan zo mu ga juna. Amma ni ba zan iya zaba da kaina ba, sai in ta ganin kamar na ci amanar Aisha.”

Maganarsa ta karshe ta bai wa Liman tausayi, shi kansa ya girgiza da gushewar Aisha a doron kasa, ya sha tunanin a ina Ma’aruf zai samo mata kamarta? Sai ya yi saurin kauda tunanin, ya ce,

“Allah zai dubi kyawawan halayensa ya ba shi mace tamkarta, ko fiye da ita.”

“Babu wani cin amana Ma’aruf, Aishar za ta so ka samu nutsuwa a bayan ranta, ba ka yi ta ragaita ba. Yanzu na ji magana, za a bincika, insha Allah Allah zai dubi zuciyarka da halayenka na kyautayi ga kowa, Ya ba ka mata ta gari”

Washegari Hajiya da maigidanta sun gama tunaninsu tsaf! Sun kuma tsaida kan ‘yar maigarin Ji-Kas, wadda ke karatu a jami’ar Jigawa. An sa ranar aurenta har za a yi watannin baya mijin ya ce ya fasa. A ganin Hajiya da Liman, Ma’aruf zai fi dacewa su nema masa ‘yar birni mai ilimin zamani, ba irin yaran kauye ba, zai fi son hakan.

Hajiyar ta shirya da yamma ta tafi gidan Maigari, shi kuma Liman ya tafi wajen mahaifinta.

Kowanne ya fadi abin da ya kawo shi. Amsa iri daya suka samu. Yaransu ‘yammata uku ne, Sadiya, Laila da Asiya. Wadda duk suke so za a ba Ma’aruf ba tare da jan dogon lokaci ba.

Amsa daya su ma suka samu daga Hajiya da Liman, a ba shi wacce ta ke jami’ar, suka ce, Laila kenan. To Allah ya sa a yi a sa’a.

Uwar laila guda ce kawai ba ta rangada ba, ‘yarta aka zabar wa attajiri dan Hajiya Saude farin gida. Nan fa kishi ya tashi, da ma matan uku ne, kuma kowacce na da ‘ya budurwa, wato Asiya da Sadiya, sai dai su bana suka kammala makarantar sakandire. An zabi ta jami’a an bar su. Wannan abu ya yi musu ciwo.

Laila kuwa da ma ba dama ce wajen iya yi da kidifiri. Jin mijin da Allah ya kawo mata rana tsaka bayan Mahadi ya fasa auranta kan tara samari barkatai, ta ce da uwarta, “Ashe gaba ta kai mu?”

Uwar ta ce, “Gobarar titi a Jos!”

Ta ba ta hannu duka kashe tare da rungume juna suna murna, babu godiya ga Allah, kai ka ce wasu kawa da kawa ne ba uwa da ‘ya ba, kai ka ce wata ajiya ce suka yi yanzu suka dauki abarsu. Ita kadai ce mace cikin ‘ya’yanta, don haka ba karamin buri ta ci a kan Laila ba, ga shi tun ba a je ko’ina ba Allah ya fara cika mata.

Kwanan Hajiya uku ta ce Ma’aruf ya baro ayyukansa ya zo su ga juna da matar da suka zabar masa, don a bar sahihiyar magana kafin su bar Ji-kas dukkansu hankalinsu ya koma kan Amina. Sai a lokacin ya gano Hajiya hannun likitoci ta bar Amina, hankalinsa bai tashi da yawa ba, don ya yarda da kokarin Dr. Umar Bolori a kan Amina da kaunar da yake masa.

Motoci uku suka biyo shi a baya zuwa Ji-kas ban da securities dinsa guda biyu da suke tare da shi daga Abuja har Jigawa. Mutane dankam sun yanyame kofar gidan Hajiya, kamar yadda suka saba duk sanda ya zo Ji-kas, to yau ma hakan. Da kyar ya samu ya shige dakin mahaifiyarsa bayan ya sa sakatarensa Idris ya sallame su. Ya yi sallah ya ci abincin da Hajiya ta tanadar masa, sai da duhu ya shigo bayan magriba Liman ya karasa da shi gidan Maigari, lokacin babu idon mutane. Ya sanya ‘dark-shade’ wanda ya boye kwayan idanunsa, yana sanye da shadda (getzner) ruwan siminti da hula zanna kalar shaddar, an yi ma rigar ado da zaren (silver) wanda ya kayatar da shaddar sosai. Da kafafunsu suke tafe suna hira har gida dagaci, wanda ya karbe su hannu bibbiyu, ya shigar da su turakar da yake saukar bakinsa. Ma’aruf ya gaishe su cike da ladabi ya amsa cike da kauna, ya rike hannunsa cikin nashi yana fadin,

“Sai ka yi hakuri da ita fa, duk cikin ‘ya’yana ita ce mai giggiwa.” Abin ya ba wa Liman dariya, ya ya kai da aka zo neman auren ‘yarka ka ke fadar halinta mara kyau? Shi kam maigari iyakar gaskiyarsa ya ke fadi, don kaunar da yake wa Ma’aruf ba tun yau ba bazata bari ya yaudare shi ba.

Engnr. Ma’aruf Ji-kas, yana so ya tambayi Maigari,

“Giggiwa wace iri?”

Amma ba zai iya ba. Ko dago kai ya kasa saboda tsabar girmama manya.

Maigari da Liman suka fita kofar gida, suka dasa hira bayan Maigari ya shiga gida da kansa ya yi kiran Laila.

Laila ta yi dauri ya kai sau goma tana warwarewa, ta sa kaya ya yi sau takwas tana canzawa. Ta fesa turare ya yi kala biyar, amma har yanzu ba ta ji tana kamshi ba. Uwarta na kara zuga ta.

“Ta ina zai ganki ya ce ba ki yi ba? Ai karyarsa ta sha karya.”

A can falon bakin Maigari, Ma’aruf ya fara kosawa. Har ya fara duban agogo. Ba ya son jira a rayuwarsa. Ko wanne minti daya mai amfani ne a wurinsa. Rayuwarshi a kayyade ta ke cikin tsara lokaci, minti goma sha biyar ya tsara zai yi tare da ita, ga shi ta ci minti talatin ba ta ma fito ba.

Ya dan ja tsuka, ya murza zoben tsari na azurfa da ke hannunsa, wanda Baba ya sanya masa da jimawa, don a cewarsa rayuwa irin tashi sai da neman tsarin jiki. Yana son zoben don a kowanne lokaci yana tuna masa da Baban, ya kira shi a waya ya ji lafiyarsa, ko ya zo ya ganshi, ko ya aika a dauko masa shi a duk inda yake (kafin rasuwar Aisha.

Sai lokacin ya ji takun takalmi kas-kas-kas, Laila tsayawa ta yi a soron gidansu hancinta na sirnano mata wani kamshi mai sanyaya zuciya da bata taba jin irinsa a rayuwarta ba. Sai ta ji turarukan da ta gumbudo sun hau mata kai kamar ta juya ta canza kaya. Wata zuciyar ta ce koma canza kaya ki dawo ki tarar ya yi tafiyarsa, duk lokacin da ki ka bata bai ishe ki ba?”

Sai ta fasa komawar, ta yi sallama a dakin tare da daga labule ta shiga.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 11Sanadin Kenan 13 >>

1 thought on “Sanadin Kenan 12”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×