Skip to content
Part 21 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Hajiya ta karba ta mika mata. Ta mika hannu biyu ta amsa, ta koma bakin gadon ta zauna ta fara budewa. Sai da ta karance shi tsaf shi da Hajiya suna magana wadda ta shafe su. Ta zari takarda ta yi rubutu a kai. Daidai sanda ya mike tsaye.

Hajiya ta ce,

“Babu sauran wani abin da ki ke bukata?”

Ta mika wa Hajiya takardar da ta yi rubutu yanzun nan,

“Ga wannan magunguna ne da allurai za a sayo.”

Hajiya ta karba ta ba shi, ya sanya a aljihu.

“Anything more?” Ya sake tambaya, wannan kai tsaye Aminar yake kallo, alamar ita ya jefa wa tambayar.

Ta girgiza kanta a sadde, “Ina da duk kayan aikin da nake bukata. Amma in wani abin ya taso zan sanar da Hajiya…”

Hajiya ta yi saurin katse ta, “Karbi wayarta ka sa mata lambarka. Ki daina maida ni jakadiya a tsakaninku. Ni bakuwa ce, tafiya zan yi da ma don ke na zauna zan yi sati daya, amma ko yanzu ina iya tafiya wallahi ba ni da haufi a kanki Likita Amina.”

Amina ta yi murmushi irin na jin dadin da dan Adam ke samu a zuciyarsa in an yi masa shaida ta gari.

Aka kira shi a waya, ya daga ya wuce yana magana, bai ce komai ba a kan ba ta lambar wayar. Ji ya yi kamar wanda ya kira wayar ya taimake shi. Su duka basu san tanada lambar tasa cikin wayar ta ba.

Da hannayenta biyu ta soma ‘messaging’ jikin Ameena, hankalinta ya tattara sosai a kanta, tana jin Hajiya na mata magana cikin lallashi.

“Ki saki jikinki ki dinga gaya masa komai. Na ga alama kunyarki na da yawa. In aka ce abu lalura, ai ta kori komai. Sannan mutum ne shi mai saukin kai. Idan kin ce ni ce Jakadiyarku idan na tafi ya ya za ku yi?”

Amina ta ce, “Toh”

Haka suka wuni tana ta bai wa Ameena treatment kala-kala. Sai da Hajiya ta matsanta mata sannan ta ci abinci, shi ma kadan don hankalinta na kan Amina. Hirar ma ba sosai suke yi ba, Hajiya tana ta laziminta hankalinta kwance. Ba don ya roke ta da Allah ba a kan ta cika satin yadda suka yi alkawari, da tafiya za ta yi. Haka nan ta samu zuciyar ta da yarda da Amina dari-bisa-dari, kaunarta ta lullube zuciyarta ganin yadda ta ke kula da Ameena bilhakki kamar ita ta haife ta. (Mai Da wawa)!

Da daddare da za su kwanta ba yadda Hajiya ba ta yi da ita ba su kwanta a gadon su uku su sanya  Ameena a tsakiya, Dr. Amina ta ki ta amince. Kan ‘resting chair’ ta jefa filo ta kwanta, sai bacci.

Washegari da safe kamar yadda ya saba in Hajiya na gidansa kafin ya fita office sai ya duba su, ya ga lafiyarsu, ya tambayi Hajiya ko sunada bukatar wani abu, haka in ya dawo kafin ya shiga nasa dakin ko na Laila sai ya ga Hajiya da Amina.

To haka yau ma, da safen ya shigo suka karya kumallo shi da Hajiyarsa, ita tana can gefe tana bai wa Ameena ‘quaker oat’ da ta dama mata. Hajiya tayi-tayi ta zo su ci abincin tare, ta ce ita ba ta jin yunwa.

A ranta ta ce, ‘banda abin Hajiya ina ni ina cin abinci da Ma’arouf Ji-kas? In al’umma ta ji ai sai a sa ni a jarida.’

Suna cin abincin shi da Hajiya jefi-jefi suna hira, ta gama ba ta ‘oat’ din tana ba ta magunguna, ta gama ta yi mata allurai amma ba ta yi kuka ba. Ta fiddo kayan aikinta ta soma yi mata ‘Thermotherapy’. Ta gama ta koma ‘electrotherapy’ abin da bahaushe ke ce ma ‘gashi’, duk yana kallonta yana mamaki, karamar yarinya haka da ba ta fi shekaru ashirin da biyar ba ta samu ilmi mai kyau (at a very young age). In tana aikinta bata tunanin komai, don haka ta manta ma yana dakin, gabadaya hankalinta yana kan Ameena. Don haka ba ta san me suke cewa ba shi da uwarsa.

Kwanansu biyar kenan, jibi Hajiya za ta koma Ji-kas, Amina har ba ta so ta tuna tafiyar dattijuwar nan ma’abociyar ibada, hikima da tawali’u. Ba karamin sabo suka yi cikin ‘yan kwanakin nan ba, kamar uwa da ‘ya, haka suka koma.

Ana i-gobe Hajiya za ta tafi, ya shigo da azahar bayan ya fito daga office.

Hajiya ta dube shi, “Matar gidan ina ta shiga ne? Tun washegarin zuwana ban kara jin duriyarta ba?” Cike da mamakin Laila na yadda ta iya yin tafiya ba tareda ta yiwa Hajiya sallama ba alhalin tana cikin gidan ya jinjina kai. Bai dai ce komai ba ya  ce da Hajiyar,

“Ta je umrah nake jin jibi za ta dawo, sati daya tace zata yi.”

Hajiyar bata dauka da zafi ba tace

“Allah ya kai mu, ni kuma tafiya gobe. Ya ya an gama shirya dakin nasu da kicin din?”

“An gama tuntuni.”

“In ta dawo sai ka yi mata bayanin wace ce Dr. Amina da dalilin zamanta tare da ku. Hakkinta ne ka yi mata wannan bayanin tunda gidanta ne. A kare min mutuncin diya ta a gidan nan, ga ta nan amana na baku kai da matarka, in kuma aka yi miki ba daidai ba Amina ki kira ni, ki gaya min, wayata kullum a bude take.”

Amina ta yi murmushi kawai.

“Tattara kayan mu je na kai ku dakin naku.”

Dakin da aka shirya wa Ameena da ‘patient’ dinta Ameena yana nan a ‘downstairs’ na ginin da Ma’arouf da iyalinsa ke ciki. Wato wata matattakala ce zaka taka guda shidda ka sakko zaka tadda wani katon falon wanda ya kunshi dakunan da aka shiryawa yara, wanda duk ya fisu girma da kayatuwa nan Ma’arouf  ya zabar musu da kicin a cikinsa kamar yadda ta bukata. Hajiya ta yi musu addu’a, a washegari Akilu ya dauke ta suka yi Ji-kas.

Sauki ya nuna sosai a jikin yarinya Ameena Ma’arouf, har wata ‘yar kiba ta yi, kumatun nan ya yi luwai-luwai abin sha’awa, in ta gaji da kwanciya Amina kan sa ta a ‘wheel-chair’ ta dan zazzaga falon da ita. Tana yi mata ‘messaging’ don samar mata ‘pain-relief’ akai-akai, kowanne ‘treatment’ da lokacin da ta ware masa.

Ranar juma’a ya kama za ta tafi gida, a ranar ne Laila ta dawo daga Saudiyya, abin da Ma’arouf bai sani ba shi ne, Dubai ta je ba Saudiyyah ba, ganin likita a duba mata me ya hana ta samun ciki. Sun duba ta, sun ba ta magunguna da za su taimaka mata ta yi ‘conceiving’ sakamakon mahaifarta mai rauni ce. Ta san in ta gaya masa gaskiyar inda za ta je ba zai lamunta ba, shi a kan karan-kansa ba ya fita (abroad) balle iyalinsa, ‘patriotism’ dinsa bai yarda da wannan ba. Sannan abubuwan da ke kansa sun fi karfin ya tsaya yana mata bin diddigi, ta san Saudi-Arabia shi ne waje na karshe da in ta ce za ta je ba zai hana ba. Shi ya sa ta yi masa wannan karyar.

Amina ta shirya tana jiran shi ya zo ya yi mata umarnin tafiya, amma in ta daga ido ta dubi Ameena sai ta ji kamar ta fasa tafiyar saboda tausayin yarinyar da ta ke ji. Sun fara shakuwa sosai, domin zuwa yanzu Ameena Ma’arouf ta dawo hayyacinta, hannunta na dama da kafarta ta dama su ne ba ta iya motsa su, kamar ba a jikinta suke ba. Tana magana jefi-jefi tana kiranta, “Mama.”

Ba ta gaya mata za ta je gida ba, don kada ta damu.

Ta gama yi mata duk abin da za ta yi mata yau. Har karfe sha biyu na rana bai shigo ba kamar yadda ya saba. Ta matsu ta isa ga Goggonta ta ga halin da ta ke ciki. Ga shi ta sa a ranta ita fa ba za ta iya kiran Ma’arouf Ji-kas ba saboda kwarjinin da yake mata. Yana da wata irin haiba da kamala da ba kowa zai iya dosarshi da magana kai tsaye ba. Ta zauna da jakarta a gefe ta yi tagumi tana kallon Ameena da ke bacci bisa lallausan gadonta. Kaunar yarinyar na kara mamaye mata zuciya, jira ta ke ya zo ta ba shi Prescription na magungunan Ameena da yadda za a dinga yi mata ‘messaging’ kafin ta dawo.

Ba shi ya shigo ba sai karfe daya na rana. yana shigowa da sallama hadi da murmushi a fuskarsa ya hada hannayensa biyu, ya ce, “Afuwan, na tsaya wani muhimmin abu ne.”

Kanta a kasa ta ce, “Babu komai”

Wannan karon ma ba ta yarda ya ga fuskarta ba. Ya zauna a kan tebirin gilashi da ke gefe.

“Ya ya ku ka tashi?”

“Alhamdu lillahi.”

Duk sai suka yi shiru. Matukar takura Amina ji ta ke ta takura, kamar ta mike ta ruga a guje ko ta roki kasar ta tsage ta shige. Ba su taba zama su biyu ba sabida koyaushe Hajiyarsa na shiga tsakaninsu ta zama Jakadiya, ga shi yanzu ta tafi ta barta da His Excellency Ma’arouf Habibu Ji-kas. Wani mutum guda daya da ko sunansa ba ta taba kwatanta fada ba ko da a zuciyarta ne, saboda girmansa da kimarsa da ta ke gani fiye da kowa a duniya, in ka dauke iyayenta. Ko sallama ya yi a dakin sai zuciyarta ta girgiza balle su yi magana baki-da-baki.

Ma’arouf ya lura ta takura sosai, saboda rashin Hajiya. Ya mike tsaye, “Babu sakon komai to?”

Ta mika masa ledar maganin da ke hannunta, “Kowanne sau biyu a rana.”

“Ah weekend ina gida, ni zan ci gaba da kula da ita duk abubuwan da ki ke mata na lura na iya, zan gwada ita kokarina, zan rufe kaina a ‘weekend’ ba fita ko’ina daga aikin Amina sai tsare-tsaren abubuwan da zan sa a gaba idan an shiga ranakun sati.”

Amina ta girgiza kai, “What a simple politisian’. Tana so ta ce, ‘Ina matarsa da zai yi wannan aikin?’ Ta ga cewa hakan ba huruminta ba ne, ta ja baki ta yi shiru. Ita tunda ta zo ma ba ta ga matar ba, kodayake ta ji ya ce ya je Saudiyyah. Za ta so ganin wace ce matar Ji-kas? Lallai za ta kasance babbar ‘yar kwalis kamarsa, ma’abocin ado kamar Dawisu.

Ya soma taku zai tadda kofa yana latsa wayar hannunsa.

“Akilu ya zo daukarki, ki same shi a falon farko kafin Ameena ta tashi.”

Ta mike tana tura ‘yar jakar matafiyanta mai tayoyi ita ma ta yi kofar. To bai fice ba ya tsaya a bakin kofar yana waya, sai ta dan dakata daga nesa kadan. Ya rufe wyar ya sanya a aljihu, hannunsa na dama na bisa ‘handle’ din kofar.

“Ranar lahadi karfe nawa zai zo ya dauke ki?”

“Karfe shida”

Ya juyo gaba daya, ya ce, “Bai yi nisa ba Dr. Amina? Na dauka za ki ce goma na safe?”

Amina ta yi murmushi, “Ina kiwo ne, bayan ganin Goggo I want to spend some time with them”

“Kiwon mene ne?”

“Tantabaru”

Ya yi dan murmushi wadda ba kasafai yake yi ba.

“Zan saya wa tawa Ameenar aure biyu ita ma ta kiwa ta, nawa ne kudinsu?”

Amina ta girgiza kai, “Ba na sayarwa ba ne. Amma ita zan ba ta kyauta.”

“Godiya ta ke Dr. Amina, ina son account number.”

“In wata ya kusa cika zan bayar ba yanzu ba…”

Ya tare ta, “Ba albashi zan saka ba, sakon mahaifiyarki ne”

Amina ta girgiza kai, “Zan so kada hakan ya shiga tsakaninmu your Excellency. Ban da albashina babu wani abu makamancin wannan da zai hada mu.”

Ya dan daga kafada, ya tattare gira, “Ki je Akilu na jiranki, yanzu za ki ga ta tashi. Naki asusun ma in kin ga dama kada ki bayar.”

Ya sa kai ya fita. Da alamu bai ji dadin maganganunta ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 20Sanadin Kenan 22 >>

1 thought on “Sanadin Kenan 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×