Skip to content
Part 15 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Dr. Turaki na komawa gida, abinci kawai matarsa Zainab ta bari ya ci, ta kasa bari ya yi wanka kafin ta isar da sakon Ji-kas. Amma ta boye azarbabi da murnarta na ta yi magana da Ji-kas, tauraron taurarin matasa na birnin Bauchin Yakubu.

“Zan kira shi gobe da na shiga office.”

“Haba kai kuwa Baban Aadil, ka kira shi yanzu mana, mu ji mene ne, ka sani ko kujerar Makkah ce?”

Ya tuntsire da dariya.

“Zainab mai idon cin naira. Ki bari Allah ya ba shi kujerar, makkah kin je kin dawo insha Allahu”

Ita dai Zainab ba haka ta so ba, ta so ya kira shi tana zaune ta ji kwaf! Ko samu ne. Tunda mazan mu alamarsu ne boye samu wa matan su.

Kamar yadda ya ce da matarsa washegari yana shiga ofis ya bude tagogi, Ji-kas din ya fara kira.

A lokacin yana bai wa Amina (golden morn), ya dakata ya daga kiran Turakin.

“Sai yanzu ka ga damar kira na? Na san tun jiya an gaya maka sakona. Har yanzu kana nan da shan kamshinka da na sani Usman?”

Dariya ya yi, “Alasabbinani tuba nake”

Shi ma murmushin ya yi. Usman ya san ba ya son a ce masa ‘Alasabbinani’ din nan tuntuni, ba ta kan wannan yake ba yanzu don haka ya zarce da gaya masa makasudin kiran.

“A kan ‘yarka Amina ne. Mun bar gadon asibiti don dukkaninmu ba za mu iya ba, ni da Hajiya ta. Saboda wasu muhimman uzurirrika musamman ni da yanayin rayuwa ta ba na tsuguno ba ne a wuri guda. Don haka ina son hiring professional physiotherapist da za ta ci gaba da baiwa Amina (treatment) a gida, da kula da ita da komai nata bilhaqqi.

Za ta baro asibiti ta zauna da Amina a gida, ta ci gaba da kula da ita tsawon shekara daya mu ga abinda Allah zai yi. Zan ninka mata albashin da ta ke karba a asibiti sau hudu a kowanne wata.

Sai dai Turaki ba kowacce ba, shi ya sa ma na biyo ta kanka, ban bi ta kan likitocin Amina ba, ina son wadda akwai sanayya ta sosai a tsakaninku, ka yarda da ita, ka yarda da amanarta da ikhlasi. Mai tausayi da jin kai. Mata tsoro suke ba ni Turaki, in kana da kudin da za ka ba su babu mai zama da kai tsakani da Allah. Yau na firgita, na tsorata da al’amarin mata yadda ba ka zato Usman. Sun kuma karya min zuciya, sun kara sa ni kewar Aisha. Mata irinta tsiraru ne a cikin al’umma”.

Dr. Turaki ya ja numfashi, zai so ya tambayi abokin nasa abinda ya firgita shi da matan, sai yaga hakan ba huruminsa bane. Babu wadda ta zo masa a rai sai likitar da ya raina da hannunsa, ya kwashe shekaru tare da ita, ya lakanci dukkan halayenta; Dr. Amina Mas’ud Shira.

Dukkan suffofin da Ma’arouf ke so ‘proffessional’ din ta kasance da su Amina ce ta mallake su, a dai likitocin mataccen kashi da ya sani a duniya.

Amma kafin nan, sai ya ce da abokin nasa,

“To me zai hana ka kara aure Ma’arouf? In ta gidan ta na da matsala?”

Cikin girgiza kai kamar Turakin na kallonsa,

“Ka sani ba ni da ra’ayin aure-aure tun ina karami na. Ita wannan din, tunda yanzu na san halinta sai mu gangara a haka, a ba ni gishiri in ba ka manda. In ta yin taka tsan-tsan da ita.

Kamar yadda bana son aure-aure, haka bana son saki, don an yi wa mahaifiya ta ban ji da dadi ba. Na yi ta watangaririya a hannun matar uba, sai dana girma na kwaci ‘yancin kaina. Duk da da babu haihuwa tsakaninmu auren bai jima ba ban sani ba ko gaba Allah zai kawo. Ga tsoron kada in tara su (mata) ya zamo cewa, duk haka suke, in hakan ta faru Turaki ina zan sa raina? In yi ta saki kuma a ce min auri-saki, ko wanda ya kasa rike mace,  yaya za’ayi ya iya rike al’umma? Ka ga gara mu gangara da wannan din tunda yanzu ta bayyana halayenta na fahimceta sosai, ita kuwa har yau ba ta san waye Ma’arouf Habibu Ji-kas ba. Wallahi! ko kwata na ba ta sani ba, suna na kawai take ji, ita kuwa tass! Na santa yanzu.”

Dr. Turaki ya nisa, dama Allah ba ya hada maka komai a rayuwa, idan ya baka wannan sai ya hana maka wancan, shi kuma Engnr. Ji-kas ga ta inda Allah ya jarrabe shi (mata), ban da ita ba shi da sauran matsala a rayuwarsa. Multi-millonnaire ne da ko ya fadi zabensa (wanda da kyar in zai fadin) ba abinda zai girgiza shi. Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta. Duk da ance siyasa bata inda ake tsammanin ta.

“DR. AMINA MAS’UOD SHIRA”. Ya furta masa a hankali da sauti mai dan kauri da ake kira (husky).

Ma’arouf ya amsa, “Wace ce haka?”

“Sunan likitar da ta dace da komai da ka ambata ne Ma’arouf. Daliba ta ce, mu muka koyar dasu, Physiotherapist ce.”

“Ka yarda ta hada duk abubuwan da na lissafa a sama Turaki?”

“Har ma ta zarta. Proffessional ce da ta san kan aikinta. Ta karbi award na Best Physiotherapist of Africa, sannan ‘yar babban gida ce. Ba ina nufin ‘yar masu kudi ba, a’ah, gidan tarbiyya da mutunci. Ina fatan ka gane?”

“Na gane, ka yi mata magana toh, cewa zan dauketa haya na tsawon shekara daya in ba ta da aure. Ta kula min da mai sunanta paralysed diya ta. Zan ninka mata albashinta sau hudu in iyayenta za su amince. Duk ‘weekend’ sai ta tafi gida, ta kwana biyu, ni kuma zan maida ‘weekend’ lokutan zamana da Amina in ci gaba da kula da ita in ba ta nan, ina son mahaifiyata ta huta”.

Dr. Usman wata irin zuciya ta ciyo shi, “Me ye amfanin zama da matarka to idan har ba za ta iya jin kan abin da ka haifa ba, ko da na kwana biyu a sati?”

Ma’arouf ya yi murmushi, zuciyarsa ta hango masa yadda karti biyu suka tube Amina a gaban Laila dake toshe hanci cike da kyankyami, idanunsa suka rine sukayi jajawur.

“Idan har bayanin da na yi maka a sama bai gamsar da kai ba, ban san kuma wane bayani zan yi maka ba. Ban aureta don tazo tayi jinya ba.”

“Kana da sanyi da yawa Ma’arouf (she deserve punishment). Ba kuma na komai ba sai na karin aure.”

“Ba ni da ra’ayi Usman, wannan kadai na neman kashe ni da bakin cikinta ina ga na karo wasu su hadu su taru su haukata ni? Beside, ni fa ba ni da idon kallon mata har in ji sun yi min. Wannan din ma su Hajiya suka kallo min ita, ba su san kara da kiyashi ba ce daukar marar sani. Mu je a haka da Laila Turaki, aurena da ita baida alaqa da diyata.”

Cikin tausayi Dr. Turaki ya ce,

“Ni ka ba ni kwangila in kallo maka. Na rantse ba duka suka taru suka zama daya ba”.

Dariya ya yi kasa-kasa.

“Turaki, ka ki ka gane da gangan, mu bar zancen nan, so boring”.

“Na bari”. In ji Dr. Turaki,

“God bless you”. Inji Ma’arouf .

“Amin”

Duk suka yi shiru.

Zuciyar Turaki na tafarfasa, in shi ne da wannan matar wallahi sakinta zai yi, ko da a ce da gold aka kera ta. ‘Yar guda daya? Marainiya?Mai lalura? Alhalin ubanta ya mallaka miki duk wani jin dadi na duniya? Shi ne alfaharinki, gadararki?

Sai ya tuna kuma fa Ma’arouf dan siyasa ne ba komai zai yi ba ko don ya tsira da mutuncinsa. Ya nisa. Amma ya kasa magana.

Ma’arouf ya katse shirun nasu da cewa, “Yaushe za ka yi magana da likitar?”

“Insha Allahu gobe. Yau tana off kuma sai ta rubuta (leave without pay) in har ta amince. Zan yi kokari a ba ta (leave) din, don ba kowa a ke baiwa ba, kuma yana dan daukar lokaci. Ga shi zabe saura sati biyu, don haka in ta amince cikin sati biyun za mu gama komai. Allah ya ba ka nasara, kuri’unmu na tare da kai Ma’arouf.

Ka dauke ta ka kai ta wurin mahaifiyarka har a gama zabe ya fi sauki, za kuma ka fi samun nutsuwa tunda ka riga ka rabota da asibiti. Da an gama zabe mun ga abin da Allah ya yi sai a dawo da ita. Amina ta zo.

Jikina yana ba ni za ta amince, saboda tana ganin girmana, kuma ba ta yi auren fari ba”

Da wannan suka rufe tattaunawar tasu, Ma’arouf ya yi ta yi masa godiya.

*****

Shi da kansa ya shiga bayan mota tare da Amina, aka sa mata seat belt. Akilu direba da securities dinsa da sauran masu mara masa baya in zai je ko’ina suka dau hanyar Jigawa daga Bauchi. Daga nan suka yanke hanya suka shiga Gwaram suka mika Ji-kas.

Hajiya ta yi mamakin ganinsu. Don ko jiya sun yi waya bai ce da ita za su zo ba. Shi kuma ba ya so ya barta ta kwana cikin (suspense) ne. Ya shigo dauke da Amina a kafadunsa ya kwantar a kan gadon Hajiya. Sannan ya nemi kujera mai taushi cikin kujerun Hajiyar ya zauna.

Ba ta tambaye shi komai ba sai da ta fara cika shi da abinciccika kala-kala a gabansa da ababen sha masu sanyi daga firizarta. Ga shi lokacin zafi ne.

Ya sauko daga kujerar zuwa kilishi Hajiya ta zuba masa ruwa ya wanke hannunsa a silver, Allah ya taimake su sun yi sallolinsu a hanya.

Ta ce, “Me ya faru ne na ganka da Amina?”

Ya yi dan shiru yana tunani, muddin Hajiya ta ji halayen Laila ba za ta dauka ba. Balle abinda ya shafi Amina, bata aje yarinyar nan kusa a zuciyar ta ba, soyayyar da take yiwa mahaifiyarta gabakidaya ta dawo kanta. Karamin hukuncin da za ta yi shi ne, Laila ta koma gidan ubanta, shi ya sa auren gaggawa ba shi da dadi. Shi kuma babu saki sai ladabtarwa a tsarin rayuwarsa.

Tuni ya rufe (account) din da ya bude wa Laila, ya kuma yi alkawarin ba zai sake zuba komai ba, ta nemi guminta daga ’boutique’ din da ya ba ta jari ta bude, kuma ba karamin tashin hankali ta shiga ba da faruwar hakan, don ba wani ciniki mai yawa ta ke yi a ’boutique’ din ba saboda tsadar kayan sai matan manya ke iya saye.

“Na kawo Amina wurinki ne saboda za mu tafi umrah Saudiyyah ni da Laila sai bayan zabe za mu dawo”

Hajiya ta ce, “Masha Allah, to Allah ya ba mu nasara, a je lafiya a dawo lafiya, Allah ya tsare. In ce ko kun taho mata da kayanta da pampers?”

“Eh an taho da su suna mota. Bari na yi wa Akilu magana ya fito da su”.

Mutane dankam sun taru a kofar gidan Hajiya Saude suna jiran fitowarsa. Yau dai duk uzurinsa ya sa a ransa zai saurare su ya yi musu maganin matsalolinsu ya roke su su yi wa Amina addu’a ba a san tsarkin bakin mutum ba.

Falon Baffa Liman na saukar bakinsa aka bude masa. Jama’arsa da securities da sakatare Idris suka shigo, sannan al’ummar Ji-kas suka shiga shigowa daya bayan daya suna fadin matsalolinsu Idris na kirgo abin da ya ce a ba su yana ba su daga brief-case din hannunsa. Yana fadin,

“Ku yi wa yarinya ta Amina addu’a Allah ya sa tana da rabon sake taka kafafunta a doron kasa!”

Ai kuwa Amina ta sha addu’a har ‘ya’yansu kanana sun sa sun yi wa Amina addu’a a makarantun allo.

Daga Ji-kas kai tsaye Abuja suka wuce shi da mukarrabansa, gidansa na Apo ya ma manta da wata Laila.

Bayan ya huta sai ya samu ‘privacy’ ya yi ibada yadda ya kamata, shi kadai a gidansa. Ya roki Allah idan mulkin nan alheri ne a gare shi, Allah ya ba shi nasara, in ba alheri ba ne Allah ya musanya masa da mafificin alherinsa.

Washegari ya wuce Saudiyya umrah.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 14Sanadin Kenan 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×