Skip to content
Part 36 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Duk shawarwarin da suka yi ita da Ilya haka suka aiwatar da su. Goggo ta budi ido ta ganta a wani dankareren gida mai hawa daya  (flat house). Ga dalleliyar mota a rufe cikin tamfol an ce ta kai ta unguwa ce. Duk tarkacenta Amina ta bai wa Inna Zulai ta zuba mata sabo. An karo mata mai aiki sun zama biyu sunanta Rabi, suna ci gaba da yin sana’ar ta Goggo, ita kam nata umarni ne da taimakawa yanzu, ga samari maza uku masu (barrow) da suke aiki tare da Ilya tuntuni sun tsaya madadinsa.

Goggo ba ta da bakin gardama Amina ta gama komai, ta cika burinta na kyautata rayuwar Goggonta a shekarun girmanta kamar yadda ta shanye shekarun kuruciyarta cikin aikin karfi da wahala wajen gina rayuwarta da inganta future dinta.

Hajiya Hawwa tayi kuka sosai don farin cikin haihuwar ‘ya irin Amina, daya tamkar da goma, mace da kamar maza. Ta sanya mata albarka har kamar harshenta zai bushe. Ta ce da Amina,

“Burina daya ne yanzu a rayuwa, Allah ya nuna min mijinki kamin ya dau raina. Saboda kyautayinki ga iyaye Amina, jikina yana ba ni Allah ba zai barki haka ba, zai ba ki miji na gari wanda kowa sai ya daga ido ya kalla, wanda zai rike ki da maraicinki da amana ko bayan raina.”

“Wai Goggo me ya sa ki ke kira ma kanki mutuwa ne? Tsufa ki ka yi? Life began at fourty? Insha Allahu sai kin dauki jikokina ba ma ‘ya’yana kadai ba Goggo. Ki daina cewa bayan ranki, zuciya ta tana girgiza.”

Goggo ta ce, “Na bari Amina, Allah ya ci gaba da raya mu tare, rayuwa mai tsayi da albarka. Ya ji kan mahaifinki, Ya yi masa rahama, Ya ba shi aljannah albarkar faranta min da ki ke yi.”

Amina na dariya ta ce,

“Amin Goggona”

Goggo ta yi dan jim tana tunani, kafin ta tsare Amina da ido.

“Ina ki ke samun wadannan makudan kudi haka? Wannan ya fi karfin albashinki ko ninki goma ne, musamman ginin gidan nan, da motar nan”

A wannan lokacin ne Amina ta yanke shawarar yi wa Goggo gaskiyar bayanin komai, har wayar da suka yi da Dr. Turaki, ta ci gaba da cewa,

“Dr. Turaki ya taba gaya min cewa, da ma ya yi alkawari duk likitan da Ameena ta warke a hannunsa ta sanadinsa, zai ba shi tukwici wanda shi kansa bai sani ba, kuma ya ce a hakan ma ya rage ne kamar yadda shi kwamishina ya ba shi shawara kasancewa ta mace, kuma bukatuna da kudi kadan ne. Na nemi shi Turakin mu raba ya ce wallahi sam, kuma in daina damuwa, a cewarsa a wurin Ji-kas wannan kamar an fidda allura ne daga cikin kogi, sama da haka ma yana bai wa wanda Allah ya ci da shi ko ba su yi masa aikin komai ba”

Goggo ta yi murmushi tana kallon Amina tana mamakin wautarta watarana, kiri-kiri ga alamomi masu yawa da ke nuna Turaki yana sunsunarwa abokinsa takalmi, amma ba ta gane komai ba. Komai ya gaya mata sai ta hau kai ta yarda. Wannan kulawar da yake ba ta, Ubangidansa yake yi wa. Shi din ne dai ba ta da tabbas din hakan daga gare shi tunda ba ta taba ganinsa ba, sai dai ta tsinci abubuwan da ke gasgata mata tunaninta daga kalaman da Amina ke yi a kanshi, kwashe rabin tantabaru a wane dalili?

In tantabaru yake so ya je kasuwa ya saya mana, sai na gado? Jikinta ya ba ta akwai abin da yake son yi wa Amina da tantabarun nan don ta amfana, amma shi me zai yi da su? Ko kuma yana son bullo da alaqa kyakkyawa a tsakaninsu a lokacin shine dalilinsa na cewa lallai ta bashi abinda tafi so a rayuwarta.

Ta nisa a hankali ta dubi Amina,

“Na yarda da ke Amina.”

Amina ta ji dadin furucin Goggo, don ba ta so ta fahimci akwai wani abu binne a zuciyoyinsu ita da Ji-kas din. Tunda ta bangarenta hakan ba zai taba yiwuwa ba duba da hujjojinta masu karfi data fada a baya. Ta nashi bangaren ma watakila ya manta da ita, ya bar maganar, ganin har kwanakinta goma a gida babu wayarsa, text dinsa ko aikensa. Damuwa da tunanin kada hakan ta kasance na kassarata, na sagar mata da gwiwa, taji kamar an bubbuge gabban jikinta da murfin kwano, amma hakan ba ya hana ta jarumtar daukar sanda ta fatattaki damuwar da tunanin daga gabanta, ta cigaba da harkokinta.

Sati biyu kenan da gama aikin Amina a gidan gwamnati, ba Ma’arouf ba wayarsa, babu ko dan aikensa. Ya rage saura sati biyu ta koma bakin aikinta a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa.

Duk da tana fatattakar tunanin da damuwar da rashin jin nasa ya jaza mata, wani lokacin zuciyarta na ingiza ta da ta kira shi a waya ta ji ko lafiya? So ba karya ba ne…… Gashi ya faru da Amina. Kuma ba abu ne da ke wanzuwa a duk sanda mutum ya so ba, a’ah, abu ne dake faruwa a duk sanda ya so akan-kansa, ya gudanar da tunani ya sarrafa gangar jiki… To hakan ce ta faru da Amina da Engnr. Ma’arouf Ji-kas. Juriya da fin karfin zuciya su suka hana Amina kiran Ma’arouf amma ba zuciyarta ba.

Ina Ma’arouf Ji-kas din?

*****

Yana can cikin takunkumin abokinsa, amininsa kuma kwamishinansa consultant Dr. Usman Turaki, wanda ya haramta masa tuntubar Amina ko zuwa inda ta ke ko yi mata aike har tsayin sati biyu.

Ya je masa da bukatarsa ne na ya shige masa gaba su dumfari neman auren dalibarsa. Ya gane cewa shayi ruwa ne, ba zai iya rayuwa cikin sukuni ba tare da ya aure ta ba, Ameena ta dawo hannunta. Hakan ne kadai zai sa ya ji shi cikakkensa (complete) kamar sanda Aisha ke raye, amma yanzun he’s totally incomplete,  shattered!

Turaki ya yi dariya a boye, ya yi farin ciki a fili da boye, amma bai bari ya gane ba.

Ya yarda ‘LOKACI’ ba abinda ba ya canzawa a rayuwar dan adam, kuma babu wani yanayi da yake tabbatacce ga dan adam, in ji Dr. Usman Turaki. Yau ga lokaci ya canza Ma’arouf Ji-kas, wanda shi da ma ya tabbata watarana za a yi haka. Amina ba macen da za a zauna da ita na lokaci kalilan a bari ta wuce har abada ba ce ba tare da an janyo ta ta dawo ba.

Ba don kyawunta kadai ba, sai don dabi’u da halayya, wadanda in ya auna sai ya ga duk irin na Ma’arouf Ji-kas ne, kuma ita kadai ce ta dace da mutum na gari mai kyakkyawar zuciya irin sa. A dai cikin matan da ya sani a fadin duniya. Kasancewarsa likita fitacce, wanda ya yi alaka da mata kala-kala a wajen karatu ne, a wajen koyarwa, a wajen aiki ne, a wajen (counselling) da sauransu.

Ga abin da ya ce da ubangidan nasa, a lokacin da ya zo masa da wannan bukatar tasa na ya shige masa gaba ya auri likita Amina.

Turaki bai yi masa shakiyanci ba, ko tuna masa yadda suka yi a baya, ko don yanzu ubangidansa ne? Oho! Sabanin da kafin ya hau kujerar Gwamna sanda suke abokan makaranta. Ba irin shakiyancin da baya yi masa. Da hannu bibbiyu ya karbi maganar, amma in ya tuna yadda suka yi da Ma’arouf a baya sai dariya ta shaqe shi.

“Zan taimaka, kuma zan shige gaba Yaa Maulaya, to amma sai ka yi min alkawarin ba za ka kara tunkarar Amina ba, ta waya, ta ido da ido ko ta aike sai bayan kwana goma sha hudu.”

Ma’arouf ya zaro ido, “Idan kuma wani ya riga mu fa? Me ye hikima cikin hakan? Kai kamar ba ka tausayi na Turaki? Sati biyu? Yau kwana uku dubi yadda na koma ina ga sati biyu? To amma ban san me ye a zuciyarka ba, me ye hikimarka cikin hakan? Na san dai (your brain is sharp) fiye da ni ko a makaranta.”

“Haka ya kamata ka tambaye ni, ba idan wani ya riga mu ba. Do you think a yanzu Amina za ta iya auren wani ba kai ba?”

Ma’arouf ya dube shi idanu a russune na neman karin bayani. Ya yi murmushi, “Ita ma tana sonka Yaa Maulaya, babban alamun so sune kunya da jin nauyi. Jin nauyinka da Amina ke yi yayi yawa. Za ka iya hada yadda ta ke mu’amala da ni da yadda ta ke yi da kai?

Kwata-kwata daina tunanin wani zai riga mu, sai dai a riga mu a fatar baki, amma ba a riga mu a zuciya ba.

Hikima ta a nan shi ne, a sati biyun nan ta huta, ba daga komawarta gida sai neman aure ba. Sannan a sati biyun nan za ta shiga cikin kewarka da damuwa da rashinka, za ta yi kyakkyawan tunani ba na hanzari ba. Zata tantancewa zuciyarta aya da tsakuwa na cewa son ka take ko ba son ka take ba?

Idan mukayi hakkan (I’m sure) da mun je za ta amshi bukatarmu ba tareda jan rai ba don soyayyar da ke zuciyarta ta yi zafi har ta fara kona ta.

Sai dai ina tabbatar maka ba za ta taba iya fadawa mahaifiyarta ba a dai halinta na kawaici da alkunya da na karanta. Sai dai mu mu sanar da ita. Bayan sati biyun, ka san yadda ku ka hadu sosai ka ji amsarta, ku tattauna, ku aminta da juna daga nan sai mu shiga neman aure da karfin mu.”

Dole kan ba yadda zai yi ya amince da shawarar Turaki, amma fa sati biyun nan ya gansu kamar shekaru goma sha hudu. Dararen cikinsu sun kasance masu tsayi a gareshi. Sai ya kirkirarwa kansa yin tafiye-tafiyen kauyuka duba ‘projects’ har zuwa sati biyu.

Ranar da sati biyun nan ta Ma’arouf ta cika Amina ta shirya za ta tafi Shira gaido Baffanninta, don ta tabbata in ta koma aiki ba za ta samu lokaci ba. Ilya ke janta a karamar motarta data siya (Kia Picanto) kasancewar hannun nata bai gama fadawa ba.

Gida-gida ta bi ta gaishe su, kowa sai murnar zuwan Dr. Amina yake yi don an san ba ta zuwa hannu rabbana. Balle yanzu da labari ya iskesu ta zama attajira ta ginawa Goggonta dallelen gida da mota, ta kaita hajji. Haka kuwa, ba wanda bai samu rabonsa daga Amina ‘yar Mas’udu ba, Baffaninta kuwa jari ta ba su mai tsoka na makudan kudade ta ce, su kara a gona ko su bude tireda. Amina ta sha albarka har ta gode Allah wajen tsaoffinta. Da la’asar suka kamo hanyar dawowa.

Goggo ta jaddada mata lallai ta je gidan Kawu Sule ma, don haka da suka shigo cikin gari ta gaya wa Ilya su je.

Amina dai sai da tambaya suka gane gidan Kawu Sule saboda yadda ya bi ya bushe kyamas ba shuka ko daya, ya ratattake ya lalace ba maigadi ba motocin nan nasa na alfarma. Haka dai suka boye mamakinsu suka shiga.

Ashe cikin gidan har ya fi wajen lalacewa. Kai! Komai na Duniya bashi da tabbas. Atika Babar Hafiz wadda ita ma duk ta canza wahalar rayuwa ya bayyana a jikinta ta yi musu iso dakin Baffan nata Sule. Yana kwance a kan wata tsohuwar kujera.

Ta gaishe shi cikin ladabi ya amsa sai kuma nan da nan ya kama kuka yana rokonta gafara a kan yadda ya yi watsi da rayuwarta. Ya ce, “yanzu alhakin zumunci ya kama ni, dubi yadda karayar arziki ta rufto mini rana daya. Na hada duk abin da na mallaka nasa a wani sari na auno kaya jirgin ruwan da ya dauko su ya nutse.”

Ya ci gaba da sharar hawaye yana rokonta gafara, fadi yake,

“Ban kyauta wa Yaya Masa’udu ba, ba abinda bai yimin ba a rayuwa, ‘yar kwaya daya na kasa rike masa a bayan ransa. Idan na mutu ba ki yafe min ba, ba ni da abin da zan iya yin uzuri da shi ga dan uwana, son zuciya kadai da rudin abin duniya.”

Ta tabbatar masa da cewa, da ma ita da Goggo ba su kullace shi ba.

Ya ci gaba da gaya mata, “Ba don Hafiz ba, da abin da za mu sanya a bakin salatinmu ma babu. Ga shi shi kuma mace ta mallake shi, sai dan abin da ta ga dama ta ke sa wa ya ba mu. Ba kuma ya nan yanzu an canza masa wajen aiki zuwa Adamawa.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 34Sanadin Kenan 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×