Skip to content
Part 34 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Gadan-gadan Ilya ya shiga aiwatar da aikin amanar da Amina ta damka masa. Sai da ya kammala komai, madaidaicin apartment din Goggo mai brown rufi ya kammala, mota kirar (E-Class) ta iso. Matsala daya Ilya ya samu, wato dole Goggo ta je a yi mata fasfot da daukan hoto. Daga baya dabara ta zo masa, ya je ya samu Goggo ya ce ta yi shiri su je wani waje za a yi musu takardar zama ‘yan kasa, kuma dole sai an dauki hoto.

Goggo ba ta yi musu ba ta shirya suka je immigration aka yi mata fasfot ba da saninta ba. Aka dauke ta hoto, ba ta sa wa ranta komai ba, Ilya ya je ya biya kudin kujerar hajjin Goggo, aka yi mata visa da komai aka sanya musu ranar tashi, sannan ne ya zo ya gaya wa Goggo komai ya damka mata fasfot dinta.

Goggo don dadi sai hawaye. Wai ita ce za ta je dakin Allah mai alfarma karkashin inuwar Amina. Lokacin Amina na government house, Goggo ta kira ta a waya.

“Sai kuma na ji wannan abin alheri haka? Aminan Goggo, Allah ya yi miki albarka, Ya ba ki miji na gari wanda zai tallafi maraicinki, ya rike ki da amana da kauna ta gaskiya.”

Dadi ya rufe Amina, cewa ta ke, “Amin-Amin Goggo, Goggo Allah ya bar min ke!!!”

Ranar juma’a su Goggo suka tashi zuwa kasa mai tsarki. Don haka wannan satin Amina ta yi zamanta ba ta zo gida ba, ta ci gaba da kula da Ameena.

Idan Hajiya Hauwa tana dawafi a ka’aba, ba abin da ta ke roko sai miji na gari ga Amina. Idan sujjada ta yi a Maqama Ibrahima, addu’ar da ke kan halshenta kenan. Idan safah da marwah ta ke, roqon Allah ta ke ya fiddo wa Amina miji na gari cikin gaggawa. Yasa jinkirinta ya zame mata alkhairi.  Wannan shi ne kadai sauran burinta a rayuwa, sai neman cikawa da imani.

Goggo na can Makkah, Amina na dakinta na gidan gwamnati tare da patient dinta, wadda ke kwance kan cinyoyinta tana mata messaging a gabobinta. Sai kawai Ameena ta yunkura ta tashi zaune.

Dr. Amina ta ce, “Mene ne Amina?”

“Fitsari zan yi.”

Kafin ta yi wani motsi na taimaka mata don mikewa, Ameenar ta mike da kanta a kan kafafunta (all of a sudden). Ta yi hanyar bayan gida.

Amina Mas’ud Shira, ta rasa abin da za ta fara yi don farin ciki. Sai kawai ta sauko daga gadon ta yi lullubi ta gurfana gaban mahaliccinta ta yi sujjadah.

“Tsarki ya tabbata gare Ka sarkin mulkin da bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba. Ba dabara ta ba ce, ba iyawa ta ba ce, ba gwanintata ba, iko da buwayarKa ne. Wanda in Ya ce, ‘kasance’ sai ya kasance. Tsarki ya tabbata gare Ka zuljalali wal ikrami”. Abinda ta fada cikin sujjadar ta kenan.

Ta dago ta karanta fatiha ta shafa, ta mike ta bi bayan Ameena bayan gida.

Ameena ta yi fitsarinta, ta yi tsarki ta dubi Dr. Amina da ke tsaye bakin kofa, da murmushi ta ce, “Aunty yau na yi tafiya da kaina babu karfe!”.

Da sauri Amina ta share hawayen farin cikin dake kwarara daga idanunta, ta karasa ta rungume ta na mintuna, sannan ta kamo hannunta suka fito. Karo na biyu a tsayin zamanta tare da su, da ta ga ya kamata ta kira Ma’arouf Habibou Ji-kas a waya.

*****

Yana fadar shugaban kasa tare da sauran gwamnonin Najeriya gaba daya na Kudu, yamma, gabas da na Arewa suna tattaunawa ne a kan yadda za a habaka harkar noma a Nigeria da yadda za’a magance haihuwar farashin man fetur.  Kiran Amina ya shigo wayarsa da ke aljihu, wadda ya manta bai kashe ba kafin shiga taron.

“Ameena’s Doc” ke yawo a kan fuskar wayar, in bai manta ba, tsayin watanni goma sha daya da suka yi tare wannan ne karo na biyu kacal da ta taba kiransa a waya. Wani nishadi ya ziyarci zuciyarsa da shi kansa ya ba shi mamaki. Tsam ya mike ya fito daga dakin taron zuwa harabarsa, ya amsa kiran.

“Dr. Ameena, ya aka yi ne?” Ya fada cikin taushin murya, da kokarin boye eager din sa.

Amina bakinta har rawa yake, ga in’ina ta kasa fadin takamaiman dalilin kiranta. Dadi da farin ciki da suna kisa, da yau sun kashe ta.

“Um-um-um Ameena ce……”

“Me ya samu Ameenar?” ya fada cikin jin faduwar gaba.

“In ba’a nesa kake ba, ka zo ka gani da kanka zai fi. Amma fa alkhairi ne, mu wuni lafiya”. Ta kashe wayarta.

Ma’arouf Ji-kas ya dade rike da wayar a hannunsa, ya kasa tantance yanayin da ke cikin sautinta, farin ciki ne ko tashin hankali? Ya ji ‘yar damuwa ta ziyarce shi. A sanyaye ya juya ya koma dakin taron.

Haka aka karasa taron da shi a daddafe ba tare da ya kara fahimtar abin da ake tattaunawa ba.

Bai kwana ba kamar yadda ya tsara, a daren ya nemi jirgi ya taho Bauchi.

Amina da Ameena sun yi wankan barcinsu. Amina ta sanya wa ‘yar tata kayan barci, ita kuma ta nemi doguwar rigar atamfa da kallabinta ta sanya suka bi gado suka kwanta, suka rufa da bargo bayan Amina ta gama ba ta magungunanta. Carbi ne a hannunta tana ja, idonta a lumshe. amma ba ta kai ga yin barcin ba.

Knocking aka yi, ta tashi zaune ta yi lullubi, sannan ta bada izinin shigowa. Ya shigo cikin jamfa da wando na shadda ‘Excelsior’ ruwan makuba, babbar rigar da ya cire rataye a kafadunsa. kansa babu hula kamar koyaushe ya shigo gida cirewa yake yi, ba ya tara suma a kansa sam yanada yawan saisaye. Akwai ‘yar damuwa a kan fuskarsa na rashin sanin me zai tarar duk da tace alkhairi ne, amma ya yi kokari kwarai wajen boye ta. Daga bakin kofar ya tsaya, idonsa ya sauka cikin na Dr. Amina.

“Me ya faru?” Ya tambaya cikin tsaka-tsakin yanayi. Babu fargaba kuma babu farin ciki.

Kawai sai Amina ta dan girgiza Ameena karama. Yarinyar ta bude ido nan da nan, da ma barcin nata ba wani nisa ya yi ba. Ta nuna mata bakin kofa.

“Je ki Daddy ya dawo”

Ta kalli Babanta, sai ta tsallako daga gadon da gudu, ta nufe shi ta rungume.

“Daddy yau ka ga ina takawa da kafata, babu karfe.”

Ma’arouf ya tsaya standstill, ya kasa ko da motsi. Domin bai amince idonsa biyu ba ya fi gasgata mafarki yake yi, ire-iren mafarkansa a dan tsukin, Ameena rungume ta ke da kafafunshi tana ta ba shi labarai. Yawanci dai duk na abubuwan da Auntynta ta yi mata ne, wanda ke sa ta farin ciki, irin su danwake, wainar fulawa, kai ta bakin ruwa a wheel-chair da sauransu.

Lokaci ya ja, in mafarki ne ya kamata zuwa yanzu a ce ya farka, amma shiru! Don haka ya sanya hannuwa a kan ‘yar tasa yana shafawa a hankali. Daga bisani ya rage tsawo ya zama daidai tsawonta ya rungume ta.

Sunkuyar da kai ya yi ba tare da ya saki Ameena ba, sai kuma ga hawaye suna disa a bayan Ameena. Ya zarce da fuskantar alkibla ya yi sujjadah. Ameenah karama da ta ga ya dago daga sujjadar, sai ta kai ‘yan kananan yatsunta tana share masa hawaye, tana tambayarsa.

“Daddy me ye ka ke kuka? Daddy na warke fa.”

Ya tsane hawayensa da hankicinsa ya yi mata murmushi. Ya rike dukkan hannayenta, “kukan farin ciki nake yi Ameena, ko ba ki ga kafafunki sun warke ba? Da taimakon Allah da na Dr. Amina.”

Ameena ta dubi kafafun nata, “Ai kuwa tun dazu na watsar da karafan Daddy, na ce Aunty ta yi maka waya ta gaya maka, ta ce za ka zo, Daddy na warke.”

“Ce ne alhamdulillahi Ameena, mun gode wa Allah, mun gode wa Dr. Amina.”

*****

Kwana uku bayan nan Dr. Amina ta soma hada tarkacenta don barin gidan gwamna Ji-kas, bayan ta kara tabbatarwa a lafiyar Ameena karama babu sauran kalubale.

Sai dai kuma abin da ya ba ta mamaki, duk yadda ta kai ga murnar komawa gaban Goggonta abin da ta fi so a rayuwarta, jikinta a matukar sanyaye yake. Ta fara samun kanta cikin wannan sanyin jikin bayan murnar warkewar Ameena, ga wata irin damuwa da zuciyarta ta shiga in ta tuna lokacin rabuwa ya zo da Ameena da babanta.

Baban Amina kuma? Wata zuciyar ta tambaye ta, tayi wani mugun sabo da shi a tsayin shekara guda ba kadan da suka yi tare, Ma’arouf Ji-kas ya samu wani irin muhalli a zuciyarta da ba za ta iya fasalta shi ba. Ta dade tana nazarin halaye irin nasa masu wuyar samu a wannan zamanin. Ga nagarta, ga tsare mutuncin kai dana duk wanda ke karkashinsa da tsare nasa mutuncin a kan-kansa. Shugaba  ne abin koyi, wanda kowane talaka ya bude baki a jihar Bauchi, alheri yake fadi a kansa. Su da ke cikin gidansa ma sun shaida hakan. Ma’arouf ya tsaya a zuciya da ruhinta da matsayin da ba ta san wane iri ba ne. Tana jin rabuwar nan har cikin bargonta ba zuciyarta kadai ba.

A hankali ta ke ciro kayanta dayya bayan daya daga wardrove tana ninkewa tana jefa wa a ‘trolley’ dinta, Ameena na gefenta tana cin abinci da kanta ta ce,

“Aunty yau ba juma’ah ba ce, ina za ki je? Don Allah ki tafi da ni.”

Amina ta dube ta idonta cike taf da kwallah. Ta kasa ce mata komai, ta dau diyar Gwamna ta kai gidansu a wane dalili? Yaushe ta kai wannan matsayin? Amma ko da zai ba ta da ya yi mata babban adalci. Da duk wannan damuwar kashi hamsin cikin dari ta kama gabanta. Tana tare da jinin Ji-kas, ai kamar Ji-kas ne suka ci gaba da rayuwa tare. Watakila watarana har ta ganshi a dalilin diyarsa.

A’ah! Wai me ke damuna ne ni Amina Mas’ud?” Ta tambayi kanta,

“Ma’arouf Ji-qas!”

Zuciyarta ta bata amsa. Ba tun yau ba sunan nan yake yi mata wani irin nauyi a kwakwalwar ta. Tun sanda ta fara jin sunan, ba ta iya fade a bisa dalilin da bata sani ba amma tafi danganta shi da girmamawa. Amma a yau ta fahimci bayan  girmamawa akwai wani kebantaccen al’amarin da zuciyarta ke lullube dashi, mai girma da tasirin da ya bi ya mamaye zuciyarta, wanda yasa sunan nasa yi mata nauyi a harshe da zuciya da ba za ta iya fassara shi ba. Wasu dumammun hawaye suka ziraro daga idanunta wanda ta tabbatar na kewa da sabo ne. Wanda tasan zasu cigaba da gudana har karshen rayuwarta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 32Sanadin Kenan 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×