Skip to content
Part 29 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

A yau Amina ta sauka a mahaifar mahaifiyarta Hajiya Hauwa, kasar Sierrleone birnin (Magburaka), sai rarraba ido ta ke tana kallon ababen mamaki, wato al’adu da suka sha bamban da wadanda ta saba gani. Tsayin shekarun da Hajiya Hawwa ta yi a Nigeria bai sa ta manta hanyar gidan iyayenta ba.

Hajiya Hauwa ta gode wa Allah da ya sada ta da iyaye da ‘yan uwanta, ana ta murnar zuwansu amma murnar ta fi karkata ga ganin Amina. Ta samu mahaifinta ya rasu, wasu da yawa a bayanshi ma duk sun rasu. Wasu sun hayayyafa, ‘ya’yan sun girma. Haka aka yi ta kai su suna zaga dangi ita da Amina. Mahaifiyarta wadda ta tsufa ainun ta ce da Goggo cikin yarensu,

“Ina fatan kin dawo gida kenan Hauwa’u? Tunda ba aure ki ke da shi ba, ki samu miji a nan ki yi aurenki tunda kin ce kin aurar da Amina, tarewa za ta yi.”

Ai kuwa Amina ta balle musu da kuka da aka fassara mata abinda kakarta tace,

“Na roke ki kada ki kara fadin haka Kaka. Ki yi wa Allah ki bar min Goggona a kusa da ni. Ni kadai ta haifa ba ni da dan uwa ko abokin shawara sai ita. Ba ni da burin da ya wuce duk sanda nake son ganinta in ganta, Kaka don Allah ki yi hakuri ki tausaya min, ke ma ki bi mu, ku ci gaba da zamanku tare.”

Kukan Amina ya yi yawa, sai da Kakarta ta dafa ta tana lallashi.

“Na bar miki uwarki Aminatu, na  amince zan biku mu koma tare in zauna tare da ita nima in ke ganinta duk sanda nake so.”

Duk da hausar tasu ba irin ta Nigeria ba ce, Amina tana ganewa.

Kwanansu uku suka yi sallama da sauran ‘yan uwan Goggo, wadanda duka (far-relation) suke da ita abin nufi, babu na jiki-jiki, duk sun kare. Amina ta saya wa kakarta tikiti suka taho Nigeria.

Kakar Amina sai rarraba ido ta ke tun shigowarsu gida tana mamakin daular da ta ga ‘yarta Hauwa a ciki. Da ta tambaye ta, murmushi ta yi, tace da mahaifiyarta “SANADIN ilmin Amina ne.”

Ranar litinin ita ce ranar da Amina za ta tare a gidan mijinta.

Kamin ranar ta kimtsa komai nata. Har Goggo na yi mata fadan ta ajiye tsofaffin kayan sawarta, Amina ta ce,

“Goggo ki bar min su. A kowanne canjin rayuwa da na samu ina son in ke sanya yadda nake a baya in memory, kada in shagala in manta da yadda na taso.”

Goggo ta tabe baki, “Ai falsafa nan ta ganki ta barki.”

Manyan motoci biyar Akilu ya kawo Shira, aka kwaso gaba daya dangin Amina manya da yara da matan Baffanninta kai har da wadanda ba dangin Iya babu na Baba aka dura su sai gidan Gwamnati.

A cikin gari kuwa dukkan abokan arzikin Goggo, Inna Zulai ita ce kan gaba, su Talatu masu aikin Goggo abu nasu maganin a kwabe su. Makotan Goggo na unguwar da suka baro da na sabuwar unguwa duk haka aka kwashe su Government House.

Sai a wannan lokacin mutane da yawa suka san waye ya auri Dr. Amina. Masu mamaki sun yi, masu gulma sun yi amma masu fatan alkhairi sun fi yawa kasancewar mahaifiyarta mutum ce wadda ta ke zaune lafiya da kowa, kuma ma’abociyar alheri, masoyanta sun rinjayi makiyanta.

Aka bude wa duka ‘yan kawo amaryar guest house aka ce ango ya ce su zauna su huta har tsayin kwana uku. Murna a gurin ‘yan Shira abin sai ya ba ka dariya. Shi kuwa ya sa aka yi ta cika su da liyafa iri-iri, sai da ya kure hadamar kowa, abinci suna gani amma sun kasa ci saboda koshi. Sun manta da Amina wadda aka kai ‘upstairs’ shagalinsu kawai suke yi.

Anty Laila ba ta kasar, ta je umrah, wannan karon da gaske Saudiyyan ta je musamman don ta yi addu’a Allah ya ba ta haihuwa tunda likitoci sun kasa tsinana mata komai a Dubai, sai cin kudinta a banza, ta ga gara ta koma ga Allah don ta ji rade-radin Ma’arouf yana neman aure. Hankalinta in yayi dubunnai to ya tashi, sai dai duk kwakkwafinta an kasa gano mata wa zai aura saboda ba a sa a (media) ba, yau satinta daya a can kuma sati biyu za ta yi.

Hajiyan Ji-kas da jama’arta da suka karbi amarya suna downstairs dakunan da Amina ta zauna, washegari za su koma Ji-kas, Hajiya kuma Lagos za ta, Amina tana kusa da Hajiya lullube cikin laffaya, ta ki yarda ta zauna a dakinta da ke upstairs, self-content ne kamar duka dakunan wanda ke kallon na mai gidan, na Laila kuma yana nesa da nata sai dai duk cikin tafkeken falo daya suke.

Hajiya da ‘yan uwanta da kishiyarta hira suke, har dare ya soma yi. Hajiya ta lura Amina ta fara gyangyadi, ga dare ya yi wajen karfe goma sha daya na dare, ta ce,

“Tashi haka Amina, mu je in raka ki dakinki dare ya yi.”

Amina ta turo baki cikin shagwaba, yadda ta ke yi wa Goggonta don ba ta bambanta Hajiya da Goggo, tana fadin,

“Don Allah Hajiya ki bar ni in kwana cikin mutane. Ni wallahi tsoro nake ji gidan yana da girma sosai, na yi miki alkawarin gobe zan koma.”

Hajiya ta rasa yadda za ta yi da ita don ba ta so ta takura mata ta koma kukan nan da ta yi musu sanda suka banbaro ta daga jikin Goggonta. Kafin ta ba ta amsa ma Amina ta gyara waje a gadon ta yi kwanciyarta, barci ya sure ta.

Sanda angon ya shigo gidan, karfe goma sha biyu na dare ya yi. Wajen Hajiya ya fara dosa da takunsa mara amo, wanda yake yi cikin nutsuwa, ya shiga ne don ya yi mata sai da safe ya wuce wurin amarya.

Duk jama’ar dakin sun yi bacci, wasu a gado wasu a kasa, Hajiya ce kadai ido biyu, makure ta ke a can kusurwar dakin kan sallaya tana lazimi, ba komai Hajiya Saude ke roka ba daga wurin Ubangijinta face nema wa danta Ma’arouf dacewa a cikin wannan auren da zuri’a dayyiba, Allah ya kare mata shi daga duk mai nufinsa da sharri, ya ba shi alherin da ke tare da Amina ya nesanta shi daga rashin alhairanta. Ya sanya ta zamo marufar asirinsa kamar Aisha ya kade dukkanin fitunu daga cikin aurensu.

Jin murdar kofarsa da sallamarsa ya sanya ta yi fatiha ta shafa. Bai shigo ba saboda mutane daga bakin kofar ya tsaya rike da marikin kofar. Hajiya ta amsa sallamarsa fuskarta cike da yalwa. Ya ce,

“Hajiya ba ki kwanta ba?”

“Yanzu dai nake shiri, don gobe sammako za mu yi, zan je ganin Ameena a makaranta (an kai Ameena wata makarantar kwana ta yara ‘yan firamare a Lagos) sannan na wuce Jikas.”

“Ai booking din naki na rana ne Hajiya, ba sai kin yi sammako ba.”

“A’ah, gara dai in yin don ta ji dadi.”

Ya juya zai fita,

“Allah ya ba mu alkhairi Hajiya”

“Amin. Ga Aminar a nan ma bacci ya dauke ta”.

Cak! ya tsaya kamar bai ji daidai ba. Hajiya ta yi murmushi,

“Na yi-na yi ta zauna a dakinta ta ki, abu kuma da gajiya ba ta san sanda bacci ya dauke ta ba.”

Saura kadan ya ce, “Taso ta Hajiya, wannan wane irin abu ne? An taba yin haka amarya a ranar aurenta ta kwana da ‘yan biki? To ni kuma fa? Hajiya kin daina sona da alama!”

Dariya ta kusa kwace wa Hajiya Saude ganin ya kasa tafiya, ya kuma kasa magana. Ta yi niyyar tashinta wata zuciyar ta ce, ‘kyale ta yau daya dai ta huta da gajiyar biki, gobe mu bar muku gidanku ku karata’.

“Ka ce sai da safe kuma ka tsaya, ko in taso ta ne?”

Ya yi gaba yana fadin, “A’ah, Allah ya ba mu alkhairi”.

Hajiya ta ce, “Amin”

Washegari da safe su Hajiya suka yi shiri suka wuce. Bayan ta raka Amina dakinta ta yi mata nasihohi a kan ta zauna lafiya da Laila, ta yi hakuri da ita kamar zamansu na baya. Ta yi musu addu’a suka tafi.

Gida ya saura ‘yan Shira a sassan baki suna ta sha’aninsu. Ba wanda ya damu da ya zo inda amaryar ta ke ban da Ramma matar Baffa Bilya, ita kam ta zo taya Amina hira.

His Excellency bai shigo gidan ba saboda ayyuka masu yawa da suka tsare shi a office. Tunda aka fara hidimar auren bai dauki hutu ba sai yau. Wajejen karfe uku na yamma ya samu ya kira Amina a waya.

“Shirya kayanki da abubuwan amfaninki da za su yi miki kwana bakwai, za mu tafi Abuja.”

Amina ta ajiye wayarta a gefe, wace irin tafiya ce saboda Allah daga kawo ta jiya ko ‘yan biki ba su watse ba? Abin da ta ke fadi a ranta kenan. Hakan kuma bai hana ta bin umarninsa ba, ta samu babbar jaka ta shirya duk abin da ta san za ta bukata. Ya fi karfin ya yi hukunci, ta ce, a’ah! Ya fi karfin komai a gare ta!!

Ya sake kiranta a karo na biyu bayan ta idar da sallar la’asar. A tausashe yake fadin, “Ki fito, direbana yana bakin falon karshe yana jiranki, zai taho da ke filin jirgi. Ba za mu hadu ba sai a jirgi, ina tare da jama’a sosai. Ina rokon kada hakan ya bata ranki, sai kin yi hakuri Dr. Amina, yanayin rayuwar tamu kenan. Are you o.k?”

Ta gyada kai kamar yana ganinta.

“I’m o.k”

Da kanta ta turo jakar tata waje, bayan ta nade jikinta cikin wata lallausar laffaya fara mai ratsin shudi mai hasken sararin samaniya. Ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin kamshi. Kamin ta isa downstairs wani ma’aikacin gidan ya zo don fita da jakarta, direban na jiransu ya karbi jakar ya sanya a bayan motar kirar ‘porsche’ ta shiga suka kama hanya tare da security dinta mace a gidan gaban motar.

A takaice Ma’arouf da Amina ba su hadu ba sai a first class seats na jirgin Azman mai zuwa Abuja daga Bauchi.

Kar ki so ki tona zuciyar kowannensu domin ba za ki iya kididdige adadin farin cikin da ke cikinta ba.

A lokacin da Amina ta zauna a kujerar da ke daf data angon nata. Karo na farko a tarihin rayuwarsu da ya kama hannunta ya rike cikin nasa. Kanta ta sunkuyar, ba ta iya ta dube shi ba amma wata rahma taji ta sauka  a ruhi da zuciyarta, shi din kuwa ajiyar zuciya ya ke saukewa a hankali, cikin ransa yana godiya ga mai tsarkin mulki, wanda ya mallaka masa abin da ya dade yana so da kauna lokaci mai tsawo ba don isarsa ko mulkinsa ba.

Sun sauka a hotel din TRANSCORP HILTON da misalin karfe takwas na daren ranar. Gajiya ba ta bar Amina ta tsinana komai ba. Ta yi alwala ta yi sallar magriba da isha da ta riske su a hanya, a nan kan sallayar barci mai nauyi ya dauke ta.

Ta bude ido ne ta ganta tsakiyar wani ni’imtaccen gado, rufe ruf da lallausar (duvet). Da ta kara bude idon, ta juya sosai, a can gefe bisa wata kujera da dan tebir a gaban kujerar Ma’arouf ne yake cin abinci. Suka kalli juna na ‘yan sakanni, kafin ya ture tebir din kadan ya taso ya tako har inda ta ke ya mika mata hannu. A kunyace ta sunkuyar da kai sannan ta ba shi hannun. Ya mikar da ita tsaye sai inda yake cin abincin. A baki Ma’arouf ke bai wa Amina abinci tun tana jin kunya har ta ware ta ci abincin sosai. Ba ta san ta tara yunwa har haka ba sai da ta ji abincin mai tsananin dadin da ba ta taba cin irinsa ba cikin bakinta. Tare suka dauro alwala suka yi sallar nafila don nema wa aurensu albarka da zuri’a mai albarka.

Abubuwan da suka biyo baya a wannan dare mai dimbin tarihi agaresu zai fi kyau in kira su unexpressable daga ruhi, zuciya da gangar jikin kowannensu. Saboda Biro ya yi kadan ya amayar da su. Amina Mas’ud Shira, ta kira daren farkon ta da ‘night of AMEENAH!’ Wato ita Aminar kadai ta san me ke cikin abinta. Abin sirri ne, sirrin ma ba dan kadan ba.

Gane hakan dana yi ne yasa na soma ja da baya a hankali da birona da tarin ‘full-scaps’ dina har na fice daga TRANSCORP HILTON (murmushi).

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 28Sanadin Kenan 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×