Skip to content
Part 46 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

A daren ranar Laila ba ta runtsa ba sabida cizon sauro, ga Innarta ta hada ta shimfida da kananan yayanta sun jike ta sharkaf da fitsari. Bargon da ta kwanta a kai kuwa jinsa ta ke kamar karzuwa saboda kaushinsa a fatar jikinta.

Wancan zuwan da ta yi da Maarouf ya dage sai ta kwana biyu karbar matar gwamna Inna Saade ta yi mata, gadon audiga ta bar mata ta kwana ita ta kwana a kasa da yake an san bakuntar arziki ta zo. Sai yanzu ta shiga nadamar rashin gyarawa Innarta daki a lokacin da ita ta ke cikin kololuwar daular rayuwa.

Washegari da safe kuwa koko da dumamen tuwo Innar ta dangwara mata a gabanta ko uffan ba ta ce mata ba, cike da haushin ta ki gaya mata abin da ya kawo ta ta barta da kishiyoyi suna yada mata habaici. Shi ma Dagaci bai yi wa kowa zancen Laila ba ya ja bakinsa ya yi shiru, harkokinsa kawai yake yi.

Sai da Laila ta kwana uku a gidansu ganin ba wanda ya zo biko, sannan Maigari ya gaya wa uwarta sakinta aka yi. Hadiyar zuciya ne kawai Inna Saade ba ta yi ba, amma ta fashe da kuka mai karfi wanda ya janyo hankalin abokan zamanta suka zo kofar dakinta suna tambayar ko lafiya?

Ko kula su Inna Saa ba ta yi ba, amma maigidansu ya gaya musu Laila aure ya mutu don shi a wurinsa duk an zama daya. A fili suka jajanta suka wuce dakunansu farin ciki fal zuciyarsu suna labarta wa yayansu har wadanda ke gidan miji sun aika musu.

Yan uwan Laila, Asiya da Sadiya in ban da Allah ya kara ba abin da suke yi, ba za su taba manta wulakancin da ta yi musu da za a yi (swearing  in ceremony) na mijinta ba, suka ce za su zo ta ce ba ta gayyatar gayyar naayya.

Wani cikin gidansu bai taba taka muhallin da ta ke ba, hatta uwar da ta haife ta, to juyayin me za su taya ta don yau ta ga juyin rayuwa? Da ma an ce ka taka duniya a sannu domin ba matabbaciya ba ce.

Kwanan Laila biyar a gidansu ko kofar dakinsu ba ta iya fitowa saboda habaicin su Laminde da dariyar ketar kannenta da yayyenta maza. Kuka ta yi shi har ta gode Allah, nadama kuwa ba irin wadda ba ta yi ba.

Ranar da ta cika kwana bakwai Inna Saade ta soma tila mata wanke-wanke da wankin kayan fitsarin kannenta da girkin gida in ya zagayo kanta, ta ce ba zai yiwu kina kwance a daki ina dafo abinci ina kawo miki alhalin kin fi ni karfi ba.

Ai shi zaman gida cudarni in cude ka ne ba irin gidan miji ba, shi ya sa ki ka ga ko mu da muke kauye lallaba aurenmu muke balle mai auren gwamna ta ce sai abin da ta ke so za ta yi?

Haka Laila ta ci gaba da rayuwa a gidansu cikin wani hali na tagayyara da fita hayyaci. Gaba daya ta zuge ta fita hayyacinta, fatar jikinta ta canza kala hatta gashin kanta ya san uwar dakinsa ta samu gigitaccen sauyin rayuwa na farat daya.

Ba irin kiran da ba ta yi wa Maarouf a waya, ba ya dauka sai ta koma yi masa sako (text) ko karantawa ba ya yi yake gogewa. Ga lokaci na tafiya tsoronta Allah tsoronta lokacin cikar iddarta.

Babban abin da ya kada ta hatta Hajiya Saude ba ta kara waiwayarta ba, kuma tana da labarin ya zo Ji-Kas har sau biyu a bakin kaninta mai bi mata. Haka Laila ta rungumi kaddara ta maida alamarinta ga Allah.

Kullum ta yi sallah sai ta roki Allah ya juyo mata da hankalin Maarouf, in hakan ba za ta yiwu ba tana rokon sa ya fiddo mata wani mijin cikin gaggawa mafi alkhairi a gare ta, ta yi aure ta huta da masifar gidan ubanta.

*****

A wannan satin Ameena karama ta zo hutun (third-term) daga makarantar da Babanta ya kai ta a Lagos. Ta tadda Antinta a upstairs’ tare da Babanta a gida daya kuma daki daya. Ta kuwa hau murna ba yar kadan ba. Kullum tana manne da Antin nata ko tsakiyar iyayen nata biyu tana sakin hira. Farin ciki ya cika ta ta rasa inda za ta sanya kanta don farin ciki.

Amina ta roki Maarouf da ya shirya musu zuwa Ji-Kas ita da Little za su je su yi wa Hajiya kwana uku.

Ya ce, Ni kuma fa? Haka za ku bar ni ni daya kamar maye Amina da Amina?

Kwana uku kamar kiftawar ido ne Your Excellency, na kwana biyu ban ga Hajiya ba, Ameena ma tana ta zancenta. Nayi-nayi ka dawo da Anty Laila ai ka ki saboda irin haka, mai mata daya fa aka ce aminin gwauro ne.

Nan da nan ya yi fuska, Kin jawo wa kanki fasa zuwa Ji-kas din, na kuma gane ba kya kishina ko kadan Amina. Ai sai ki dawo da Lailar tunda igiyar aurenta ai tana hannunki.

Na tuba, na bi Allah na bi ka, ba nufina kenan ba. Kawai na ga ya kamata zuwa yanzu a ce ka huce daga fushin da ka ke yi da ita, amma tunda hakan shi ne decision dinka ba ni da say Baban Ameena.

Da kyar ta shawo kansa ya sauko daga fushin nasa. Wannan ta sha faruwa ba sau daya ba, ba sau biyu ba tun barin Laila gidan da dawowar Amina daga jinya a asibitin da Laila ta yi mata sanadin minor-surgery a cikin kai.

Idan Maarouf ya ce ba ta kishinsa a kan Laila hankalinta yana tashi. Domin da bacin rai yake fada, ko uwar da ta haife shi tunda ya nuna mata ba ya son zancen komen Laila ta daina yi masa sai ita?

A nata bangaren Amina ba rashin kishi ba ne, ba dai ta son zama kwarkwata fidda mai giji, ba ta so a ce a kanta wani ya shiga wani hali ko kankani, zuciyarta mai kyau ce maabociyar imani, idan akwai abin da ta ke kishi a duniya, to Maarouf Ji-Kas ne!Kishi kuwa wanda ko a tarihi babu irinsa. Amma na musulunci.

Ta kudire a zuciyarta ba za ta kyale shi ba, in dai ta samu faraga ta ganinshi cikin nishadi za ta ambato neman alfarmarta na a mayar da Laila ba don halinta ba. Tunda Annabi mai tsira da aminci ya ce, Imanin dayanku ba ya cika har sai ya so wa dan uwansa abin da yake so wa kansa.

Tana so wa kanta Maarouf tana so wa kanta rayuwa da shi. Ta tsaya ma tana cewa tana sonshi bata baki ne, don haka tana kishin abinta. Sai dai ba za ta bari kishin ya dakusar da kaifin imaninta ba.

*****

Sun isa Ji-kas lafiya ana kiraye-kirayen sallar magriba. Hajiya tana alwala sai ji ta yi Little ta dafe ta ta baya. Ta ce, Ho! yar nema, ni kada ki karasa ni.

Little Ameena na dariya ta ce da karfi, Hajiyan Ji-kas!

Ta ce, Ni Saudatu sunana, ubanki ne Ji-Kas!

Amina da kishiyar Hajiyan suka yi dariya, Hajiya da jikanyarta kullum suka hadu sai sun ba da dariya.

Amina ta nemi buta ita ma ta yi alwala suka bi jamin sallar magariba daga masallaci. Hajiya ta rasa ina ta-ka-sa-ka, ina ta-ka-a-je da surukarta, inda duk ta mika hannu kwano ta ke janyowa cike da abincin da makota ke kawo mata da wanda mai aikinta ta dafa mata, fadi ta ke,

Zabi wanda za ki ci Dr. Amina, kin san nan kauye ne ba ma cin cima kala daya. Zabi duk wanda ki ke so.

Amina ta yi murmushi ta zabi burabuskon gero da miyar taushe wanda aka dafa wa Hajiya. Hira suke sosai kamar uwa da yarta yawanci duk a kan abin da ya shafi Maarouf ne da siyasarshi.

Ana haka Amina ta sako zancen Laila, Hajiya ba za ki roki Baban Ameena ya maida Anty Laila ba? Saura kadan fa ta kare iddarta. Bana so su rabu kwata-kwata a dalilina.

Hajiya ta girgiza kai, ko kusa, kada ki kara sanya wa ranki da ke cikin dalilan rabuwarsu. An samu sabanin halayya tsakanin Maarouf da Laila, mun ganganda (rushing) wajen tabbatar da aure a tsakaninsu ba tare da binciken halayya ba, inda za ki san ba ke ce sanadi ba hatta iyayenta da yan uwanta ba sa jin dadinta, sanda tana gidan yaron nan. Sawun barawo naki alamarin ya taka don haka ki daina damun kanki.

Zan tsaya kan ya maida ta din amma ba yanzu ba, sai ta kara tarbiyyantuwa. Don labari yana zuwar min kala-kala tana can nadamar rayuwa ta ishe ta duk surfen gidansu da sanwar gidansu ita ta ke yinta, kin ga ko ai Laila in mai hankali ce dole ta shiga karatun ta-nutsu.

Amina ta langabar da kai, Ni tsorona Hajiya kada iddar ta kare wani ya fito ya aure ta.

Hajiya ta ce, To ba shi kenan ba?Allah ya hada kowa da rabonsa. Ni yanzu na daina gaggawa a kan aure Aminatu.

Dole Amina ta yi shiru don ta fahimci daga Hajiyar har danta sun hau doki guda, ba za ta iya sauko da su ba, sai ranar da Allah ya nufa.

Da za su kwanta ta canza zuwa kayan barci masu kauri ta daura zanin atamfa a kai, ta kakkabe wa Hajiya gado, kayan da ta tara tsibi guda ba ninki bayan ba masu dauda ba ne, ta ninke mata su ta shirya mata a sif, lungu da saqo na dakin Amina ta bi ta kakkale shi tana mamakin wace irin mai aiki ce Tambai da a kicin da dahuwar abinci kawai ta ke aiki?

To daga ita har Hajiyar sun kwana biyu ba za su iya wannan (neatness) din ba. Ta sawa ranta alkawarin zuwa Ji-Kas akai-akai da kula da Hajiya kamar yadda za ta kula da Goggo, ta wanke mata bayi kal sai sheki da tashin kamshi yake kamar ba bayan gida ba.

Ta kuma koya wa Tambai yadda ake wankin bayi na zamani ta gane sosai. Hajiyar sai albarka ta ke sanya mata har suka kwanta barci.

Washegari ita ta yi wa Hajiya girkin rana da na dare. Har zuwa ranar da za su taho ita ke yi wa Hajiya girki da shara da gyaran bangarenta.

Babu abinda Maarouf bai sanya mata ba na saukaka rayuwa, amma ba sa samun kulawa yadda ya kamata sakamakon Tambai din ta kwana biyu, kuma girman kauye ce.

A kwana ukku da Amina ta yi Hajiya Saude gani ta yi sassanta ya dawo sabo kal. Ta yi kewar su ba kadan ba bayan komawarsu Bauchi. Kowa na gidan ya yi kewar Amina don mutum ce mai saukin kai da dadin muamala duk yayan Baba Liman sun saba da ita.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 45Sanadin Kenan 47            >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×