Skip to content
Part 43 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Ta bude ido ne ta ganta tsakiyar wani ni’imtaccen gado, rufe ruf da lallausar (duvet).Da ta kara bude idon, ta juya sosai, a can gefe bisa wata yar kujera da dan tebir a gaban kujerar Ma’arouf ne yake cin abinci. Sanye yake da karamar t/shirt deep-bluesamfurin DKNY da bakin dogon wando samfurin Armani. Sosai yayi mata kyau irin na ranar nan data ganshi cikin kananan kaya, yau fiye da waccan ranar saboda harda hasken amarci tareda shi.Yayi wani fresh dashi (wanke hannu ka taba) inji zuciyar Amina. Suka kalli juna na ‘yan sakanni tana daga kwance cikin duvet din, kafin ya ture tebir din duka ya taso ya tako har inda ta kekwance, tsayawa yayi akanta ya kama kallonta kamar a lokacin ya taba ganinta, gashin kanta da ya sha gyaran Aunty Jalan ya kwanta akan filon ya baje sai sheki yake, da Amina ta kasa jure kallon sai ta lumshe idanunta, siririyar fatar bakinta ta nuna alamar dan murmushi, hakan ne ya baiwa Maarouf damar sunkuyawa ya sumbaci saman idanun nata dake lumshe, ya tafi da gaggawa ya iso kan karan hancinta, kamin yacigaba da mikawa a urunce ya iso tausasan labbanta, anan ya ja birki yayi mata sumba mai tsayi da zurfi. Amina ta tsinci kanta cikin wata duniya da bata taba tsintar kanta a ciki ba.

Shi da kansa ya tuna Amina babu komai a cikin ta, ya dakata, sannan ya mike tsaye, hannun damansa ya mika mata ta kama cikin jin wata irin kunyarshi da bata taba ji a rayuwarta ba.

Tsaye ya mikar da ita ya shiga warware laffayar jikinta, ya saura doguwar rigar robar data bi fatar jikinta ta kwanta kalar (sky-blue). Gigicewa Maarouf yayi, wata irin gigicewa da bai taba yi akan diya mace ba. Yau ne ya ga zahirin Amina diyar Goggo Hawwa, ashe ba karamar ajiya Ubangiji yayi masa ba wadda bai taba tsammani ba?

Tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci wannan sura!. Ya cigaba da kissing dinta ta koina sannan ya rungumeta tsan-tsan a jikinsa kamar mai tsoron kada wani abu yaratsa ta tsakaninsu.

Sun dauki dogon lokaci a haka cikin sauraron bugun zuciyar junansu, kukan da akuyar cikin Amina ta soma yi ne ya ankarar da shi. Gabadaya ya dauketa bai dire ta koina ba sai a tebirin cin abincin.

A baki Maaroufya ke baiwaAmina abincin wanda a rayuwarta bata taba cin mai dadi da dandanonsa ba, tun tana jin kunya tana sunkuyar da kai har ta ware ta ci sosai, sai mamakin Maarouf takeyi soyayyarshi na kara kama zuciyarta, sai da ta tabbatar masa ta koshi sannan ya kyaleta ta shiga wanka, misalin karfe goma na daren ranar mai dumbin tarihi a garesu.

Ince zan tsaya wassafo muku wannan ranar da alamuran da suka wakana cikinta sai biro na yakare, takarduna su cika taf! Ba tare da na gama ba, idan ya kare yaya zanyi in kawo muku karashen labarin? Dr. Amina Mas’ud Shira,ta kira daren farkon ta da night of AMEENAH! Wato ita Aminar kadai ta san me ke cikin abinta. Abin sirri ne, sirrin ma ba dan kadan ba. Sirrin Maarouf da Amina.

Gane hakan dana yi ne yasa na soma ja da baya a hankali da birona da tarinfull-scaps dina har na fice daga TRANSCORP HILTON (murmushi).

*****

Sun mori (honey moon) na tsayin kwana bakwai yadda ya kamata a wannan hotel wanda babu na biyunshi a Nigeria. Sun kara fahimtar juna, so da kaunar junansu ya kara habaka da shaharar da a da, bai yi ba. Sun dinke zukatan junansu cikin na juna sun zama daya. Kowanne ya shiga tababar yadda zai rayu, rayuwa mai inganci ba tare da dan uwansa ba.

A Transcorp suka ajiye tarihin. A can suka baro shi kamar kar su baro, Ma’arouf Ji-kas ya yarda Allah ya sako Amina cikin rayuwarsa SANADIN tashi Ameenar ne don ta gyara ta, ta maye mashi gurbin Aisha, ta wanzar da farin ciki a rayuwarsa wanda ya rasa tun gushewar Aisha. Ta wanke bakin cikin Laila Ji-kas da yake kwana yana tashi da shi. Ta kawo sauyi mai albarka daga rayuwar kadaicin da ya tsinci kansa a ciki tun bayan rashinAisha. Ita din ALHERI ce, kuma AMANA a gare shi (sunan wasu littattafan Takori).

Isowarsu gida ke da wuya tun kafin su isa dakin barcinsu wani mai share-share ya sanar da Ogan nasa, Anty Laila ta dawo.

Fuskarsa ba ta sauya ba, haka komai nasa bai canza ba. Amma Dr. Amina ta ji faduwar gaba matuka. Sai jin tausasan yatsun Ma’arouf ta yi cikin nata, ya rike ta gam ya ja ta sun fara taka matattakalar (upstairs) tare.

*****

Lailah Ji-Kas

Lailah na zaune cikin daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falon, ta dora kafa daya kan daya ta harde, ta ci ado da kayan Larabawa na kece raini har ta gaji. Remote din talabijin ne a hannunta tana sauya tasoshi.

Ta dago kai a yangace kamar yadda yake a al’adarta ta dubi masu shigowa ba tareda ta amsa sallamar da suka yi ba.

Sosai ta saki baki tana kallonsu, Ma’arouf ba zai taba kama macen da ba tashi ba. Wannan na nufin…… wannan na nufin….likitar Ameena wannan ‘yar rainin hankalin ya aura?

An tabbatar mata Ma’arouf ya yi aure tana Saudiyyah, amma ba ta taba kawo Amina ba ce. Ta dauka iyakarta kenan sun rabu tunda Ameena ta warke. To yaushe aka kulla soyayyar wadda har ta kai ga aure tana gidan bata sani ba??? Ta tambayi kanta, bata kuma samu amsa daga kowanne sashe na zuciyarta ba.

Har suka zauna a kujera guda hannunsu na cikin na juna, Amina dai a tsorace ta ke ganin kallon kura ta ga nama da Laila ke mata. ta kawo karfin zuciya ta sanya wa ranta, tana murmushi, ta ce,

“Anty Laila, ina wuni? An dawo lafiya?”

Shiru ta yi mata ba ta amsa ba, har yanzu ba ta dauke ido a kansu ba, irin kallon nan na kun ci AMANATA.

“Wuce dakinki Amina ki huta, zan yi magana da ita.”

Amina ta mike ta nufi dakin nata. Ba ta kai ga isa ba ta ji an shako ta ta baya, an yi mata wani wawan naushi a wuya, an maka mata wani irin abu a tsakar kanta da ya fi kama da kofin gilashi. Fasashshiyar Kwalba! Ta yi gaba luuu! Ta fadi a kofar dakin nata, tana jin sanda Ma’arouf ya yi magana da karfin gaske da iyakacin sautinsa,

“Lailaaa! Kina hauka ne? Kisa? Wallahi in ta mutu a bakin aurenki!”

Ya yi kokarin buga waya don kiran likita, amma ya kasa. Ya kuma kasa isa ga Aminan ya bata wani taimako saboda gigicewa. Hannunsa sai rawa yake yi, haka ilahirin jikinsa, wayar na subucewa yana sake dauko ta. Ita kanta Laila ta dan tsorata da ganin yawan jinin Amina da ke malala a kasa daga tsakiyar kanta, sai mazari ta ke yiamma ta maze, yadda take jin zuciyarta zata iya kashe Aminan kamar yadda ya fada in yaso itama a kasheta.

Ya samu ya lalubo lambar Dr. Isma’el (personal doctor) dinsa,jikinsa na cigaba da mazaridon kuwa Laila ta shammace shi, sanda tayi wuf ta mike bai ankara ba balle isar ta ga Amina kamar walkiya.

“…Ka zo maza-maza har upstairs Isma’el…….”

Babu tambayar ba’asi Dr. Isma’el ya amsa da; “Ga ni nanzuwa ranka ya dade”

Ya isa inda Amina take a kwance a kofar dakinta magashiyyan ya ciccibe ta ya kwantar a doguwar kujerar falon, bai damu da jinin da ya bi ya bata masa jiki ba. Ya soma yi mata firfitababu alamun numfashi a tare da ita. Bai kara bi ta kan Laila ba wadda ke tsaye a kansa tana kuka. Kukan da bai san maanar sa ba.

“Allah ya sa ban yi kisa ba zuciya ce, na shiga uku Ma’arouf ka yafe ni…”

Abinda take fadi kenan cikin rishin kuka.

Ko kallonta bai yi ba, firfita kawai yake wa Amina da gefen babban rigarsa idanunsa sun kada sun yi jazur. Abubuwa da yawa yake kissimawa a ransa da zasu faru da shi  idan ya rasa Amina. A haka likitan ya iske su, bayan Ma’arouf ya ba da umarnin a shigo da shi.

Da kayan aikinsa yake tafe don haka a take ya fara bai wa Amina taimakon gaggawa, har ta farfado. Ya cire kwalbar data nitse cikin kanta yayi dressing din wajen da ke fidda jinin, ya tsayar da gudunsa ya rufe da plasta. Ya dubi Ma’arouf da Laila mai kuka kashirban, Ma’arouf din ya ki ko kallonta hankalinsa da kulawarsa duk suna kan Ismael dake aiki kan Amina wadda ke kwance ido rufe. Nan ya gano bakin zaren, ya dubi Ma’arouf ya ce,

“Garin yaya? Yaya haka your Excellency? Wane ne da wannan danyen aikin? Wannan kan dole sai an je asibiti an yi hotonsa don mai yiwuwa akwai (Internal injury) na kwalbar, da nake addu’ar Allah ya sa bai taba kwakwalwarta ba.”

Laila ta kara gigicewa, daidai da karuwar fushin Ma’arouf a kanta, ya ce da Doctor din,

“Je ka ka zo da (nurses) ku tafi da ita a ba ta duk kulawar da ta dace.”

Cikin dan lokaci Dr. Isma’el ya yi waya asibitin cikin gidan, nurses biyu suka zo suka tafi da Amina. Aka barshi daga shi sai Laila a falon. Ya zauna cikin kujera ya tallabi fuskarsa da hannu bibbiyu cikin damuwa. Laila ta tsugunna a gabansa, ta kama kafafunsa tana kuka.

“Tunda ba ta mutu ba, don Allah kar ka sake ni, wallahi zuciya ce na tuba, zan zauna lafiya da ita insha Allahu.”

Janye kafafunsa yayi, daga rikon da ta yi musu. Bai saki fuskarsa ba har yanzu, haka fushinsa bai sauka ba. Da kyar ya yi mata magana cikin muryar bada umarni,

“Hada kayanki Akilu ya kai ki gida Ji-kas sai na neme ki.”

Laila ta rushe da kuka, “Na roke ka da Allah da manzonSa ka bar ni a dakina, in dai Amina ce na yi maka alkawarin za mu zauna lafiya.”

Zuciyarsa ta so ta fara sanyi, sabida irin kukan da ta ke yi mai nuna nadamarta a fili. Amma ya yi rantsuwa cikin zuciyarsa sai ta je gida ko da bai sake ta ba.

“Hakuri na daya ne Laila, ki je gida sai na neme ki, amma ban sake ki ba, in kuma ki ka kara yi min musuraina zai kara baci, shiga ki tattaro kayanki.”

Ba yadda ta iya, ta juya ta yi dakin nata tana share hawaye. Hankalinta a matukar tashe. Shi kuma ya kira Akilu a waya,

“Zo maza, za ka kai matar gidan nan Ji-kas.”

Ta gabansa Laila ta wuce tanna jan akwatinta, ta yi lullubi da wadataccen mayafi, wanda a da ba ta amfani da irin shi sai raka-ni-gantali. Ta dube shi cikin ido da idanun neman afuwa, ya kauda kai don ba ya son ya ba wa tausayin da ke son rinjayar fushinsa dama ya yi tasiri.

Wannan karon ya yi aniyar daidaita mata sahu in har tana son ci gaba da zama da shi, to dole ta bar duk abin da ba ya so ta kuma zauna lafiya da zabin ransa. Ba ita dake cin alfarmar zabin iyaye ba.

Zaman hakurin da yake yi da ita inda tana da hankali adalci ne ya yi mata. Yaushe ta fara sonshi so na gaskiya da har ta san ta yi kishi a kansa? Kishin ma na jahilai da rashin imani.

Bayan tafiyarta ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai safah da marwah yake yi, yana son jin halin da Amina ke ciki wayar Dr. Isma’el na kashe alamar yana bakin aiki. Shi ba abun ya fita da kansa ya je asibitin ba.

Ya daure ya shiga (master-bedroom) dinsa ya yi wanka da alwala, ya yi sallah nafila ya roki Allah matsalar Amina ta zo da sauki.

Yana kan sallayar bai sauka ba bayan awa daya, sai ga kiran Dr. Isma’el. Da mugun sauri ya amsa wayar.

“Ya ya Isma’eel, is she o.k?”

“Eh, toh, shes conscious now,amma mun samuinternal injury, bayan na wajen, dole zaayi (minor-surgery) akwai bukatar ka sanya hannu, zan kawo maka takardun yanzu kayi signing.

Amma ranka ya dade ya kamata a dinga kula a kuma dinga tsawatarwa iyali idan sun aikata ba daidai ba irin wannan, this issheer rudeness,don dai matsalar ta cikin gida ce, amma da ba za mu barta ta tsaya a haka ba.”

“Kada ka damu Isma’el, it’s o.k, za a kiyaye zaa dau mataki. Yanzu ina Aminan? Ya ya yanayin jikin nata?”

“Alhamdulillahi ta farfado, amma za mu rike ta har muyi aikin ya warke, bari in kawo takardun maza.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 42Sanadin Kenan 44 >>

1 thought on “Sanadin Kenan 43”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×