Skip to content

Sanadin Kenan 4 | Babi Na Uku

Bookmark

No account yet? Register

Har Dr. Ismael ya iso gumi kawai yakeyi a zaune. Bai san yana son Amina har haka ba sai yanzu da take cikin wani hali da yake ji da zai yiwu da ya maido da ciwon jikinsa. Laila zata dandana kudarta yadda gobe ko da kyauta aka ce ta kwatanta rashin hankali irin wannan cikin gidannan bazata soma ba.

Ya yiwa Ismael umarnin shigowa, ya kawo takardun har inda yake cikin girmamawa, ya karba ya rattaba hannu. Mintuna talatin suka dauka suna zare kwalbar data nitse cikin kan Amina amma alhamdulillahi bai tabi kwakwalwar ta ba.

Karfe takwas na dare sukayi waya da Ismael ya tabbatar masa zai iya zuwa ya ganta yanzu. Asibitin nan cikin gidan gwamnati yake don haka akwai tsaro sosai.

Amina na kwance lamoo!A gado, bayanta jingine da filo, ta sha katuwar plasta a ka. Maarouf ya murdo kofar ya shigo, idanunsu suka sarke dana juna, sun dauki lokaci suna kallon juna kafin hawaye ya cicciko idon Ameena. Ya karasa jikin gadon ya kama hannun ta ya ja farar kujera ya zauna a saitin kanta.

Zaiyi magana ta kai tafin hannunta ta rufe masa baki ta san hakuri ne zai bata akan laifin da ba nasa ba.

Don Allah kada ka sake ta na ji sauki wallahi na ji sauki. Kaima ka yi laifi da tuntuni baka fada mata ba, da bazata dauki alamarin da zafi haka ba.

Ido ya zuba mata ya kasa cewa komai, wace irin mutum ce Amina?Wace irin kyakkyawar zuciya gareta? Yake tambayar kansa.

Me kike so yanzu?  Me zaki iya ci? Ya kawar da maganar data yi masa don bashi da amsar da zai bata, babu bayanin da zai yi mata ta fahimci irin zaman auren da yake yi da Laila Jikas wanda babu emotion ko affection a cikin sa da har zaa zauna ana tattauna muhimman alamura da suka shafi rayuwar juna, zaman auren kawai akeyi don ya zama dole.

Amma yau an zo wani limit da yake jin wannan mugun zaman ya kare, babu wanda ya isa ya tankwara zuciyarsa ta sake zama da Laila har ita Aminar kuwa. Bashi da sauran abin nema a wata diya mace, duk abinda ya rasa a Aisha ya sameshi a tareda Amina har ma fiye da ita, ko baayi haka ba ya yanke shawarar kawo karshen zaman nasu don yiwa kansa da ita kanta adalci, yana tsoron kada ya tashi ranar Alqiyama da shanyayyen barin jiki. Zai bi hadisin Manzo  (SAW) wanda yace;

Ku auri abinda yayi muku dadi daga mataye daga dai-dai har hurhudu, idan kunji tsoron bazaku iya adalci ba to ku zauna da daya. (Bukhari).

Ba abinda nake so, Goggo kawai nake so a dauko min don Allah!

Ya dan fiddo ido damuwarsa ta karu kina so a tayar mata da hankali Amina? Ba kankanin abu ke tada hankalin Goggo ba, tanada juriya,idan bata zo ba bazan iya cin komai ba.

Bai yi musu ba wannan karon, ya fiddo waya yana magana da daya daga cikin direbobinsa tunda Akilu ya tafi da  Laila Ji-kas.

Amina na ganin Goggo ta shigo sai kuka, Maarouf yayi kasa da kai ya russuna ya gaida Goggon ya fita, zuciyarsa cike da damuwa, kukan Amina na tada tsigogin jikinsa.Ga nauyin Hajiya Hawwa da yazo ya baibayeshi, ace matarsa ce ta aikata wannan taaddancin yana zaune ma ai sai aga sakacinsa. Ba kuma yadda zaiyi ya hana Amina fadawa Goggonta tunda ta riga tazo.

Cikin nutsuwa Hajiya Hawwa ta zauna a kujerar da Maarouf ya tashi, ko hankalinta ya tashi babu alamun hakan akan kamilalliyar fuskarta. Ta kai hannu ta dafa kafadun Amina don an nade kan da bandeji.

Yi hakuri daina kukan ki gayamin me ya faru daku? Kunyi hatsari ne a hanyar Abujan? Amina ta girgiza kai Goggo ai na gaya miki, Anty Laila ce, kofin gilashi ta kwantsa mini aka. Goggo ta girgiza kai babu mummunan rauni to? Akwai Goggo amma an cire kiyi hakuri, nasan zai dauki mataki Hajiyarsa ma haka, Allah ya kiyaye gaba Allah ya baki lafiya. Tun yaushe rabon ki da abinci? Wallahi Goggo tun a Abuja don a jirgi ma ban ci komai ba. Ni sai da na ganki ma na ji yunwa.

Goggo tayi murmushi bansan yaushe zaki girma ba Amina,  me kikeso ki ci? meat-pie da cakezobo da kunun ayarki murmushi Goggo ta sake yi ta ciro wayarta daga purse din hannunta ta kira Ilya ta gaya masa Amina na asibiti wai zata ci meatpie da cake, zobo da kunun Ayansu, ya jajanta ya kuma tabbatarwa Goggo yanzu zai kawo dama yana cikin gari.

Cikin dan lokaci Ilya ya kawo cikin bokiti, Amina ta shiga ci hannu baka hannu kwarya.

Ya tambayi Goggo abinda ya faru ta sanar dashi. Ilya ya shiga tsokanarta“raguwa kawai, mai tsoron kishiya don me baki bude kwanji kin rama ba? Amina bata kula shi ba, a ranta fadi take baka san Anty Lailah ba, (shes super warrrior) labarinta kake ji ina ni ina gwada yar kashi da ita ta karairayani a banza! Sai da ta koshi ta rufe ragowar tace.

Goggo na ragewa Baban Ameena wannan, nasan shima tunda muka dawo bai ci komai ba, baki ga yadda yake cikin damuwa ba har ya fini damuwa”.Goggo tace to Amina! Ilya ya kama haba yana kallonta bakinsa fal magana amma bai furta ba, sai taji kunya ta rufe fuska tana dariya. Goggo tace ah toh mutum yayi rashin kunyarsa ya nade kayarsa shikadai ba! Ilya yace wallahi kuwa Goggo, oh! Su Ameena dadi miji ta galla masa harara.

A daren Maarouf na shirin kwanciya, hankalinsa ya kwanta ganin Amina ta samu sauki kiran wayarta ya shigo. Ya mika hannu ya dauko wayar daga inda take ajiye gefen gadon sa ya manna a kunnensa ya makale da kafadar sa yana kakkabe shimfidar gadon da dukkan hannayensa biyu zai kwanta.

Yaya akayi my patient? Bakiyi bacci ba har yanzu? Nayi zaton tun dazu kinyi bacci a cinyar goggo kina bukatar hutu. Amina tace ni bana kan cinyarta, gata can ma a gefe sallah take yi. Yaya zan iya runtsawa alhalin nasan baka ci komai ba? murmushi yayi, zuciyarsa na yi masa wani irin dadi  tunda kin samu sauki sai naji na koshi, babu yunwa a tare da ni Amina gashi ni kuma bazan iya bacci ba baka ci komai ba wallahi mai dafa min abincin ya kwanta already, bazan iya kiransa yanzu ba, amma nayi miki alkawarin zan sha tea inada kettle da lipton da Zuma a dakina bana shan sukari. Na rage maka abinda naci, zaka iya cin cimar gidanmu? murmushin sa ya fadada why not? Zobo, Cake, da meat pie din Goggo ko? tayi smiling tareda kara manne wayar a kunnenta ta lumshe idanunta.  Yadda suke maganar goggo dake gefe bisa sallaya bata jin su. A ina ka sani? Wa ya gaya maka? Ya kada kafada kamar tana ganinsa ina ruwanki? Babanki Turaki bai hana ki bin kwakkwafi ba? Ta zarce da murmushin zuwa dariya kamar inyi tsuntsuwa ta sama inzo in ganka.

Maarouf yaji zuciyarsa ta dauke shi ta cilla shi wata hamada mai cike da koramu na madara da Zuma sabida jin dadin kalaman Amina. Sai ji tayi ya kashe wayarsa.

Ta ciro wayar daga kunnenta ta duba sosai, ya kashe. Ta shiga mamakin me yasa ya kashe toh? Ko kalaman data fada ne suka bata masa rai? To amma me tace na bacin rai din? Ta daga ido ta dubi agogon dakin karfe goma sha biyu na dare. Idanunta suka soye ta kasa bacci sai kissime-kissime take yi a ranta na abinda ya sanya rabin ranta kashe mata waya.

Ji tayi ana knocking kofarsu, lokacin goggo tayi sujjadah, ta dauka nurses ne don haka daga kwancen tace Yes!

Ya bayyana a dakin mutum biyu da suka rako shi suka tsaya daga waje, wanda bata taba kawowa ranta gani a lokacin bane, Maarouf Ji-kas ne.

Cikin matsanancin mamaki da alajabi, so, kauna, da bayyanannen farin ciki take kallon sa. Ya daga mata gira ya karaso gaban gadon nata ya mika mata hannu. Gani, bani abincin.

Shudin wandon jeans da farar shirt mai rubutun marks&spencer ne a jikinsa. Sassanyan kamshinturaren (givenchy) ya bakunci hancinta. Rufe ido tayi tana hailala don ta dauka bacci ne ya dauketa take mafarkin sa, saboda yadda zuciyarta ta dokantu da son ganinsa a lokacin. Shine ya bayyana a mafarkin ta. bude idonki, ba mafarki kike ba, nima na kasa baccin. Ya russuna daidai kanta ya fada mata cikin kunnuwanta.

Da sauri Amina ta bude ido tana nuna masa Goggo dake sallah. Yayi dariya ya sumbaci bakinta zuwa wuyan ta sannan ya ja kujerar goggon ya zauna. Amina tayi suman zaune tana kallonsa a marairaice alamar rokon kada ya sake. Yace Ok? To ina kayan dadin da kika cin? Ta mike zaune ta dauko masa bokitin data ci ta rage daga kan locker ta mika masa. Ya karba ya bude ya soma ci.  Ta sauko daga gadon ta isa ga firji ta bude ta dauko sassanyan zobo da kunun Aya wanda baa bude robar su ba da yake Goggo da sababbin robobi takeyi ta kawo masa. Zuwa dawowar ta mazauninta yaci meat pie ya kai hudu. Da kansa ya bude robar kunun ya soma kwankwada, sanyin kunun da gardinsa da ya ratsa shi ba irin na  kowanne ordinary kunun Aya bane, wannan na professional Haj.Hawwa ne.

Daga shi har ita shiru sukayi yana ci yana sha sai da yayi kat! Yayi gyatsa yayi hamdala, da gaske ya azabtu da yunwar ashe. Shi kansa yayi mamakin yadda ya ci snacksdinnan da yawa, kunun Aya roba biyu zobo roba daya.Godiya ga Amina, wadda ta damu da cikin mijinta, wani abu da bai kara samu ba tunda ya rasa Aisha. Ko ya ci ko bai ci ba ba ruwan wani.Daga ido yayi yana kallonta da wata irin siga data sanyata sakin murmushi. Ta russunar da idanun ta.

Amina ta kawar da robobin daidai sanda Goggo ta shafa adduar ta ta juyo don ganin abinda nurse ke yi har yanzu a dakin, sai ta ga angon Amina da Aminarsa, suna hirar da bata san me suke cewa ba. Fuskokinsu dab da na juna, tana kwance a gadon asibiti yana zaune a kujerar mai dubiya. Kallodaya zakayi musu ka fahimci dab suke da su hadiye juna in suna iyawa.

Hajiya Hawwa ta mirgina kai tayi murmushi. Jikin su ne ya basu Goggo ta idar da sallahr ta.  Mai yiwuwa tana kallonsu. Sai tsinkayota sukayi a bakin kofa zata fice. Da sauri Maarouf ya ja baya ya ce Goggo, don Allah kuyi hakuri,ta kirawo ni ne inci abinci. Goggo bata juyo ba tace kuma kuyi hakuri, ai da baka kirawo ni ba ka yi jinyar da kanka Yallabai yayi dariya yace don Allah Goggo ki dawo, wallahi na tafi. Bata tanka shi ba ta fice.Shi da Amina suka sa dariya ya bi bayan Goggo ya rufo mata kofar.

Kwanan Goggo uku a asibitin gidan gwamnati tana jinyar Amina, kaida ne Maarouf ya zo duba jikin nata sau uku a rana, da safe kafin ya shiga ofis, da rana in ya dawo da kuma da daddare kafin ya shiga barci, tun Goggo Hauwa na jin kunyar surukin nata har ta sake dashi, ta lura yanada saukin kai matuka kuma bai aje Amina nan kusa a zuciyarsa ba, don haka bata iya jure ganin su tare yana shigowa zasu gaisa ta nemi wurin fakewa don Maarouf ba ya jin kunyar kama Amina a gabanta da nuna mata kulawa mai nuna soyayyar sa gareta ba kadan bace.

Goggo ta kasance koyaushe cikin godewa Allah akan hakan,  ta kuma amince wani jinkirin alheri ne, inta tuno yadda ta matsawa Amina akan aure ashe kyakkyawan rabon ta na gaba. Goggo kan daga hannu ta godewa Ubangijin ta.

<< Prev | Next >>

How much do you like this post?

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found this post interesting...

Follow us on social media to see more!

nv-author-image

Sumayyah Abdulkadir

Share the story on social media.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.