Skip to content

Sayar da Littafi

Sharudda

Sayar da littafi kammalalle ga Bakandmiya Hikaya yana da sharudda da ka’idoji kamar haka:

 1. Da farko, marubuci ya tabbatar cewa littafin shi ne ya rubuta, ko kuwa shi yake da hakkin mallakar littafin ko ma duka biyu.
 2. Dole littafin ya kasance sabo ne, ba a taba buga shi a wata kafa ba, online ko offline. Idan marubuci na da muhimmin tsohon littafi da ya ke ganin za mu saya, sai ya tuntube mu.
 3. Littafin kada ya gaza a kalla kalmomi dubu hamsin (50,000 words) zuwa sama.
 4. Da zarar an shiga yarjejeniyar, marubuci ba zai iya sayar da littafin ba (kwaya daya ko da yawa), ko sake wallafa shi a wani wuri, har sai bayan shekara guda daga ranar da aka shiga yarjejniyar.
 5. Dole marubuci zai saka (tallata) shafukan littafin guda uku zuwa biyar, gwargwadon yadda zai zama dandano, a shafukansa na sada zumunta da duk wuraren da yake da makaranta inda yake sanya labaransa. Sannan ya saka link din da za’a samu cigaban labarin, wato zuwa Bakandamiya Hikaya.
 6. Bakandamiya na da copyright na juya littafin zuwa audio ko duk nau’in documents, ko ma buga shi a matsayin littafi a koda yaushe. Sannan Bakandamiya na iya dorawa a duk kafafenta na internet ko kuma wurare da take tallata hajojinta don sayarwa. Duk nau’in da aka juya littafin, da sunan marubuci za a buga shi.
 7. Tsarin biyan kudi zai kasance gida uku: karshen watan farko na shiga yarjejeniyar, sannan sai karshen wata na biyu ko na uku, sai kuma karshen wata na uku ko na biyar, gwargwadon yadda littafin ya karbu.
 8. Bakandamiya na iya gyaran fuska ga wadannan ka’idoji a koda yaushe, gwargwadon juyawar zamani.
 9. Karya daya daga cikin wadannan ka’idojin zai iya rushe baki daya yarjejeniyar. Sannan marubuci zai biya kudin da aka biya shi.

Yadda za a turo littafi

Duk marubucin da ke son shiga wannan tsari, to ya aiko mana da wadannan abubuwa a hade cikin document guda.

 • Tsakure (summary) da ba zai wuce kalmomi 1000 ba game da littafin baki dayansa, kuma ya kunshi bayanin babban hadafi da marubuci ke son isarwa a labarin.
 • Akalla babi guda shida daga littafin: babi na 1 da na 2, babi guda 2 daga can tsakiya da kuma babin karshe guda biyu.

A aiko da one document dake kunshe da abubuwan da aka lissafa a sama ta email namu: admin@bakandamiya.com

Sauran ka’idoji

Sauran muhimman ka’idoji da marubuci ya kamata ya kula da su su ne:

 • Jigo da salon labari
 • Ka’idojin rubutu
 • Bangon littafi (a yi designing nashi makamancin wadanda ake da su a Bakandamiya
  Hikaya)

A tuntube mu idan ana bukatar karin bayani.