Zarina
Abdulmalik Muhammad Bn Abdulmalik (Sultan), shi ne Yariman Daulatul Najees, kasancewar shi da ƙanwarsa Nailah ce kaɗai ‘ya’yan Sarki Muhammad Bn Abdulmalik Yusuf, gab ake da naɗa shi sabon sarki sakamakon murabus da mahaifin nasa zai yi. Mahaifiyarsa Sarauniya Basima da Sarauniya Najyla su kaɗai ne matan sarki. Duk inda ake neman namiji mai izza to Yarima ya kai. Ƙaunar Zarina ta mamaye zuciyarsa ta yadda ba ya tunanin zai iya rayuwa ba tare da ita ba. Babban tashin hankalinsa shi ne mahaifin Zarina, bai san yadda za ta ƙarke a tsakaninsu ba. Amma ya shirya tunkarar komai saboda Zarina.
Yasmeenah
Gagarumar matsala ce ta yi wa wasu masoya dirar mikiya a washe-garin ɗaurin aurensu sakamakon canjawar da halittar amaryar ta yi, ta yadda ita kanta ta kasa yarda da cewa ita ce ko ba ita ba ce.
Siddabaru
Ko da yake yasan ba a mutuwa a dawo, bayyanar hotunan gayyatar auren Maryam da ya gani a Facebook tare da cikakken sunanta da ya gani sun ƙara tabbatar wa da Isah cewa lallai akwai wani ɓoyayyen al’amari game da mutuwarta. Ita kuma Jalila ko ya za ta yi da irin halin ko in kula da mijinta ke nuna mata?
Asabe Reza
Hankalin fitacciyar Karuwa Asabe Reza ya tashi sakamakon cin amanar da ƙawarta Fakriyya ta yi mata na aure mata hamshaƙin masoyinta Hamoudi. Wannan ya sa ta sha alwashin tarwatsa musu farincikin da suke fatar samu.
Birnin Sahara
Haidar ya farka daga suman da bai san ya yi ba, yayin da ya tsinci kanshi a wani babban birni da duniya kaf ba ta san da wanzuwarsa ba. Abin ya bashi mamaki ƙwarai da gaske da ya ga tsohuwar budurwar da yake so Nadiya ita ce ke mulkin wannan birnin. Sai dai mamakin shi ya ƙara nunkuwa ne bayan ya fahimci cewa yana da alaƙa ta asali da wannan birni, kuma ya zama wajibi a gare shi ya tsallake wasu matakai domin ya zamo sarkin wannan birni matuƙar yana so ya ceci rayuwar ‘yan uwansa.
Doctor Eysha
Kyakkyawar likita, wadda ake kira da Doctor Eysha ta shiga cikin ruɗani da tausayi mai girma sakamakon wani mummunan haɗari da ya faru wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka masu yawa. Babban abin da ya fi tayar mata da hankali shi ne irin yadda wata yarinya ƙarama ke neman taimako amma mutane sun hana a taimaka mata. Kamar daga sama kuma sai ga Doctor Aryan ya bayyana a wurin, alhalin ta san da cewa an dakatar da shi daga aiki.
Allah Daya Gari Banban
Yayin da matar Abdullahi masunci ta haihu a karo na goma a rayuwarta, sun yi farin ciki sosai. Hakan ne ma ya sa Abdullahi tafiya bakin kogi domin ya yi su ya samo abinda zai ciyar da iyalansa. Amma wani abin mamaki shi ne, sai da ya yi kwanaki arba’in yana zuwa su ba tare da ya kama ko da kwaɗo ba, ga shi yana matuƙar jin kunyar mai gurasa wanda ke binsa bashin da yake ta bashi a kullum ba tare da gajiya ba.
Mafarkin Deluwa
Malam Shitu, Malam Lawal, Malam Tsalha da Malam Zaidu ma’aikatan wata maƙabarta ce da ke ƙauyen Ɗanduƙus. Tsananin firgici ne ya ziyarce su a lokacin da suka ga wata ‘yar wada ta shigo maƙabartar da suke kula da ita tana neman taimakon su binne mata gawar. Saratu, wadda aka fi sani da Deluwa ta yanke shawarar kashe masoyinta Chibunzu, kamar yadda Alhaji Labaran ya umurta domin cika burinta na zuwa Makka.
Sharri Kare Ne
Masu azanci suna yawan ambaton jimlar alhaki kwuikwuyo ne, mai shi yake bi, sai dai a doron kasa akwai wasu nau’in jama’ar da ba su gama amincewa da wannan azancin ba, sun yarda cewa alhari kwuikwuyo ne, amma ba su yarda cewa wata rana ya kan dawowa wanda ya aika shi har ya yi masa mummunar rauni. Fauziya da Aisha suna daya daga cikin irin wadannan nau’in halittun da suka canza ma’anar wancan azancin, wanda shi ya saka suke sheke ayarsu ta hanyar yin gurbataccen rubutu kuma su aita shi wa dimbin al’umma cikin farin ciki da ribar da suke samu, ba tare da tunanin wata rana kaikayi zai koma kan mashekiya ba.
Hawayen Jini
Hamdan da babban amininsa Mahfuz na ta shiri don ganin sun isa wurin taron walimar auren Hamdan ɗin da ake shirin yi a washegarin ranar. Ba zato ba tsammani kawai sai mahaifiyarsa Hajiya Mairo ta ce ba zai auri masoyiyarsa Raslima ba. Ko da Hamdan ya nemi jin dalilin da ya sa ta yanke irin wannan tsattsauran hukunci haka, bai samu komai ba face mari, zagi da hamɓara.
