Skip to content

Sharuddan Views

Sharudda

Sanya labari don samun kudi ta hanyar views, comments da kuma rating yana da sharudda kamar haka:

 1. Na farko, marubuci ya tabbatar cewa shi ne da kansa ya rubuta labarin, kuma yana da hakkin mallakar labarin.
 2. Kowane babi na labarin da za a dora kada ya gaza a kalla kalmomi dubu biyu da dari biyar (2500) zuwa sama.
 3. Marubuci na iya samun kudi N2000 ga kowane babi na labarinsa da ya samu a kalla 500 views, 10 comments (banda replies na marubuci) da kuma 20 ratings (stars). Sai babi a kalla guda biyar (5) sun cika wadannan ka’idoji, sannan marubuci zai rubuto mana ta email namu at: admin@bakandamiya.com yana mai bukatar kudinsa (N10,000). Ya sako links na duk babukan da suka cika ka’idar kuma yake bukatar kudinsu.
 4. Tsarin biyan kudi zai kasance ne a karshen watan da marubuci ya rubuto mana cewa yana bukatar kudinsa.
 5. Da zarar an shiga wannan yarjejeniya, marubuci ba zai iya buga labarin a wata kafa na daban ba, ko wani ya buga a madadinsa, har sai bayan kowane babi ya cika shekara guda da cika ka’idojinsa, ma’ana bayan shekara guda da samun yawan views da comments da kuma ratings da ake bukata. Amma marubuci na iya sharing link don masu karatu su bibiya su karanta.
 6. Bakandamiya na da copyright na sake juya labarin zuwa wasu nau’uka, kamar su audio, video, documents ko kuwa bugawa zuwa littafi da makamantansu. Sannan Bakandamiya na iya dorawa a duk kafafenta na internet ko kuma wurare da take tallata hajojinta don sayarwa. Duk nau’in da aka juya littafin, da sunan marubuci za a buga shi.
 7. Har ila yau, Bakandamiya na iya sanya duk babin da ya rigaya ya cika ka’idoji a cikin tsarinta na subscription.
 8. Dole marubuci zai saka (tallata) shafukan littafin guda uku zuwa biyar, gwargwadon yadda zai zama dandano, a shafukansa na sada zumunta da duk wuraren da yake da makaranta inda yake sanya labaransa. Sannan ya saka link din da za’a samu cigaban labarin, wato zuwa Bakandamiya Hikaya.
 9. Duk karshen shekara, akwai bonus na kudi da shaidar girmamawa (certificate) ga marubuci gwargwadon yawan views, comments, ratings da kuma karbuwa da labarinsa ya samu.
 10. Bakandamiya na iya gyaran fuska ga wadannan ka’idojin a koda yaushe, gwargwadon juyawar zamani. Sai dai duk gyaran da aka samu ba zai shafi yarjejeniyar da ta gabata ba sai dai mai zuwa gaba.
 11. Karya daya daga cikin wadannan ka’idojin zai iya rushe baki daya yarjejeniyar. Sannan marubuci zai biya kudin da aka biya shi.

Yadda za a dora labari

Duk marubucin dake son shiga wannan tsari sai yayi register a Bakandamiya Hikaya, sannan ya je main menu ya latsa My Account – > Dashboard – > Submit Post, sannan ya dora babin farko na labarinsa. Wajen dorawa, akwai zabin tsaruka guda uku, saboda haka, sai marubuci ya zabi duk abin da ya dace da irin tsarin da yake son shiga.

Sauran ka’idoji

Sauran muhimman ka’idoji da marubuci ya kamata ya kula da su su ne:

 • Jigo da salon labari
 • Ka’idojin rubutu
 • Bangon littafi (a yi designing nashi makamancin wadanda ake da su a Bakandamiya Hikaya)

Da zarar editocinmu sun amince da labarin da aka dora, za a buga shi, sannan za a aikowa da marubuci yarjejeniya da zai sa hannu. Bayan ya sa hannu sai ya ci gaba da buga labarinsa.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×